Aminiya:
2025-05-12@17:06:24 GMT

Tankar mai ta sake fashewa a Neja

Published: 28th, January 2025 GMT

Wata tankar man fetur ta sake fashewa a garin Kusogbogi da ke Ƙaramar Hukumar Agaie ta Jihar Neja.

Majiyoyi sun shaida wa wakilinmu cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 6:00 na yammacin ranar Litinin, amma babu rai ko ɗaya da ya salwanta.

Aminiya ta ruwaito cewa, tankar wadda ke maƙare da lita dubu 60 ta man fetur ta faɗi ne sannan ta yi bindiga a tsakanin ƙananan hukumomin Agaie da Lapai.

Wani mazaunin Lapai, Mallam Mahmud Abubakar, ya ce lamarin ya faru ne a sakamakon tsala gudu da direban tankar ke yi, lamarin da ya kai ga dungurar wata babbar motar dakon kaya da ke tsaye a gefen hanya kuma nan take duk suka kama da wuta.

Wannan dai na zuwa ne ƙasa da mako guda da aukuwar gobarar wata tankar mai wadda ta haddasa asarar rayuka aƙalla 100 a jihar ta Neja.

Lamarin kamar yadda rahotanni suka tabbatar ya faru ne a kusa da Dikko Junction da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna a Ƙaramar Hukumar Gurara ta Jihar Neja.

A cewar Kwamandan Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC) shiyyar Neja, Kumar Tsukwam, akasarin waɗanda abin ya rutsa da su talakawa ne mazauna yankin da suka yi gaggawar ɗiban man da ya zube bayan motar ta kife.

 

 

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Jihar Neja Tankar tankar mai

এছাড়াও পড়ুন:

Shugaba Tinubu Ya Rantsar Da Sabbin Kwamishinonin Hukumar INEC

Shugaba Bola Tinubu ya rantsar da sabbin Kwamishinonin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) kafin fara taron Majalisar Zartaswa ta Tarayya a fadar gwamnati da ke Abuja.

 

Sabbin Kwamishinonin INEC din da aka rantsar su ne Mallam Tukur Yusuf, mai wakiltar yankin Arewa maso Yamma, da Farfesa Sunday Aja, mai wakiltar Jihar Ebonyi.

 

Haka kuma, an rantsar da mambobi biyu na Hukumar Da’a ta Kasa (CCB).

 

Mambobin su ne Ikpeme Ndem, daga Jihar Cross River, da Mai Shari’a Buba Nyaure mai ritaya, daga Jihar Taraba.

 

Daga Bello Wakili.

 

 

 

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shugaba Tinubu Ya Rantsar Da Sabbin Kwamishinonin Hukumar INEC
  • Yanzu-yanzu: Matatar Man Dangote Ta Sake Karya Farashin Man Fetur
  • Kantoma Na Ƙaramar Hukumar Shira Ya Rasu Kwanaki Kafin Zaɓen Cike Gurbi
  • 2027: PDP Ta Mutu, APC Na Shirin Sake Yin Nasara – Martanin Ganduje Ga Lamido 
  • Rikicin Filato Ya Sa Makiyaya Yin Asarar Naira Miliyan 300 Cikin Wata 2
  • Noman 2025: Dole Ne Manoma Su Kiyaye Hasashen Hukumar NiMet
  • Mambobin APC Sun Buƙaci EFCC Ta Sake Buɗe Binciken Matawalle
  • Hukumar Fina-Finai Ta Kasar Sin Ta Kulla Takardar Hada Hannu Da Hukumar Al’adu Ta Kasar Rasha
  • Yemen ta sake kai hari kan filin jirgin saman Isra’ila da makami mai linzami
  • Hamas ta yi tir da Isra’ila kan rufe makarantun MDD