HausaTv:
2025-05-12@15:43:58 GMT

Falasdinawa 1500 Ne Su Ka Zama Makafi Sanadiyyar Yaki

Published: 12th, May 2025 GMT

Shugaban Asibitin ido dake Gaza, Dr. Abdussalam Sabah, ya sanar da cewa, adadin Falasdinawan da su ka rasa ganinsu sanadiyyar yaki sun kai 1500.

Dr. Abdussalam ya kuma yi gargadin cewa da akwai wasu Falasdinawa da sun kai 4000 da suke fuskantar barazanar rasa idanunsu saboda rashin kayan aiki a asibiti da kuma magani.

Likitan na asibitin idanun Gaza, ya kara da cewa; Rashin kayan aiki a asibitin domin yin tiyatar ido, yana yin barazanar tsayuwar aikin asibitin baki daya.

Dr. Abdussalam ya kara da cewa; A halin yanzu almakashi 3 kadai ake da shi a asibitin, irin wanda ake amfani da shi domin yin tiyatar ido.

Da dama daga cikin masu lalurar idanun sun same ta ne sanadiyyar fashewar abubuwa masu karfi na hare-haren HKI dake da bukayuwa da kayan aiki na musamman.

Haka nan kuma ya ce, matukar kungiyoyin kasa da kasa ba su tsoma baki ba, to nan gaba kadan Asibitin zai sanar da durkushewarsa.

A wani labarin mai alaka da wannan, ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza ta sanar da cewa, da akwai karancin magunguna a yankin,kuma wadanda ma su ka saura suna ci gaba da yin kasa sosai.

Har ila yau ta ce, da akwai nau’oin da sun kai kaso 65% na magunguna da babu ko da kwaya daya da ya saura. Haka nan muhimman magununan da ake da bukatuwa da su a cikin yankin sun kare kakaf da kaso43%.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Hajjin 2025: Rukunin Farko Na Alhazan Jihar Kwara Ya Tashi Zuwa Kasa Mai Tsarki

Rukunin farko na maniyyata dari biyar da sittin (560) daga jihar Kwara tare da jami’an hukumar aikin hajji ta kasa NAHCON su biyu, sun tashi daga Filin Jirgin Sama na na Babatunde Idiagbon da ke Ilori zuwa Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin shekarar 2025.

Yayin da yake jawabi ga maniyyatan kafin tafiyarsu, Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya bukace su da su kasance masu kamun kai da kuma wakiltar jihar da kasa Najeriya.

Gwamna AbdulRazaq, wanda mai ba shi shawara ta musamman, Alhaji Saadu Salaudeen, ya wakilta, ya yi kira ga dukkan maniyyata 2,174 daga jihar da su yi addu’a domin zaman lafiya da hadin kai a jihar da kuma kasa baki daya.

Gwamnan ya kuma gargadi maniyyatan da su nisanci duk wani hali da zai iya bata suna ko kimar jihar da kasar nan, tare da jaddada bukatar zaman lafiya da fahimta a tsakanin maniyyatan.

A jawabansu, Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kwara, Farfesa Mashood Mahmood Jimba, da Amirul-Hajj na bana, Olupo na Ajase-Ipo, Oba Ismail Yahaya Alebiosu, sun shawarci maniyyatan da su kasance masu hali na gari a tsawon lokacin aikin hajji.

Shi ma a jawabinsa, Shugaban Hukumar Jin Dadin Maniyyatan Musulmi ta Jihar Kwara, Alhaji Abdulkadir Abdulsalam, ya bayyana cewa za a yi sahu 4 wajen jigilar jimillar maniyyata dubu biyu da dari daya da saba’in da hudu (2,174) a matsayin wani bangare na shirye-shiryen aikin hajjin bana.

Maniyyatan sun tashi ne a jirgin Max Airline da karfe goma sha biyu da minti arba’in (12:40) na rana, zuwa kasa mai tsarki.

 

Ali Muhammad Rabi’u 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Hajjin 2025: Rukunin Farko Na Alhazan Jihar Kwara Ya Tashi Zuwa Kasa Mai Tsarki
  • Kungiyar Kurdawan Turkiya Za Ta Ajiye Makamanta Na Yaki
  • Mahara sanye da kayan ’yan sanda sun kashe malami sun sace mata 3 a makaranta a Zamfara
  • Kungiyar Hamas Ta Amince Ta Saki Fursinan Yaki Wanda Yake Da Jinsiyar Amurka Da HKI
  • Pakisatan Ta Kore Cewa Ta Keta Yarjejeniyar Tsagaita Wutar Yaki
  •   Iran Ta Yi Maraba Da Tsayar Da Wutar Yaki A Tsakanin Indiya Da Pakistan
  • Tarihin Sarkin Katsina Muhammadu Dikko (5)
  • Gaza:Falasdinawa 7 Sun Yi Shahada Da Safiyar Yau Asabar
  • IRGC Ya Kaddamar Da Sabon Sansanin Jiragen Yaki Na Karkashiun Kasa