Jagora: Muhimmin Aikin Makarantar “Hauza” Shi ne Isar Da Sakon Addini
Published: 7th, May 2025 GMT
Ayatullah Sayyid Ali Khamnei wanda ya aike da sako zuwa wurin taron tunawa da cikar shekara 100 daga kafuwar cibiyar koyar da addinin musulunci ta “Hauza” wanda aka yi a yau a birnin Kum, anan Iran, ya bayyana cewa: Aiki mafi muhimmanci na makarantar addini shi ne isar da sakon addinin musulunci domin gina sabon ci gaba na addinin musulunci.
Jagoran juyin musuluncin na Iran ya kuma bayyana cewa da akwai ayyuka masu yawa da suke na cibiyar koyar da addinin musulunci ta Hauza ne da sun kunshi bayar da jawabi akan sabbin batutuwa na zamani da suke bijirowa, ruhin ci gaba, tsarkake zukata, da kuma siffa ta juyin juya hali.”
Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya kuma bayyana cewa daga cikin ayyukan cibiyar ilimin ta Hauza da akwai Shata muhimman layukan da za a gina ci gaban musulunci na zamani akansu, da kuma isar da sakwanninsa a cikin al’umma, kamar kuma yadda aikin Hauzar ne ta yi tarbiyyar mutane su zama masana.
Tun da fari, Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya fara da bijiro da takaitaccen tarihin kafuwar cibiyar koyar da addinin musulunci ta Hauza a Kum, da rawar da Ayatullah Haj Sheikh Abdulkarim Ha’iri ya yi, har zuwa lokacin da ta rika bunkasa da ci gaba.
Jagoran juyin musuluncin na Iran ya bayyana Imam Khumaini ( q.s) a matsayin daya daga cikin malaman da Hauza ta haskaka da su, wanda ya yi nasarar kawo karshen tsarin sarauta na maha’inta.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Batun Ceto Wanda Ake Zargi Da Kwaya: Kwamishinan Kano Ya Yi Murabus
Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano, Alhaji Ibrahim Ali Namadi, ya ajiye aikinsa bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karɓi rahoton kwamitin bincike da ke duba rawar da ya taka a batun ceto wani da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi, Sulaiman Aminu Danwawu.
Wannan matakin na murabus ana kallonsa a matsayin wani muhimmin cigaba da ke nuna jajircewar gwamnatin jihar wajen kare gaskiya, bayyana ta da kuma ɗaukar nauyin ayyukanta a bainar jama’a.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, Kwamishinan ya bayyana cewa ya yanke shawarar murabus ne duba da muhimmancin al’amuran da suka shafi jama’a da kuma halin da ake ciki.
Ya ce: “A matsayina na ɗaya daga cikin masu fada-a-ji a wannan gwamnati da ke yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi, ya dace na ɗauki wannan mataki, koda kuwa zai sosa zukata.
“Ko da yake ina ci gaba da musanta hannuna a lamarin, ba zan iya watsi da irin yadda jama’a ke kallon batun ba, da kuma bukatar kare ƙimar gwamnati da muka ginata tare.” In ji shi.
Alhaji Namadi ya nuna godiya ta musamman ga Gwamna Abba Kabir Yusuf saboda ba shi damar yi wa jiharsa hidima, tare da jaddada aniyarsa ta ci gaba da bin manufofin gwamnatin.
Ya ƙara da cewa: “A matsayina na ɗan ƙasa nagari, dole ne in ci gaba da kare amana da hangen nesan da muka haɗa kai wajen shimfiɗawa a jiharmu. Zan ci gaba da kasancewa mai biyayya ga akidun da suka kawo wannan gwamnati kan mulki.”
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karɓi murabus ɗin cikin farin ciki, tare da yi masa fatan alheri a duk wani yunƙurinsa na gaba.
Gwamnan ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa wajen tabbatar da adalci, ladabi, da kuma yaki da miyagun dabi’u da laifukan da suka shafi kwayoyi da sauran matsalolin da ke shafan matasa da al’umma baki ɗaya.
Ya kuma ja hankalin duk masu rike da mukaman siyasa da su kasance masu hikima da taka-tsantsan wajen hulɗa da al’amuran jama’a, tare da neman izini daga hukumomi mafi girma kafin su shiga cikin wani lamari da ke da tasiri a bainar jama’a.
Abdullahi Jalaluddeen