Iran Ta Yi Maraba Da Tsayar Da Wutar Yaki A Tsakanin Indiya Da Pakistan
Published: 11th, May 2025 GMT
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta iran, Dr. Isma’ila Baka’i ya bayyana cewa; Tsagaita wutar yakin da aka yi a tsakanin Indiya da Pakistan abin yin maraba da shi ne, sannan kuma ya kara da cewa; Ya zama wajibi kasashen biyu su yi amfani da wannan dama domin rage tashin hankali a yankin da kuma tabbatar da zaman lafiya.
Baka’i ya yaba da hikimar shugabannin kasashen biyu da su ka dakatar da yaki, yana kuma nuna fatansa na ganin kasashen biyu sun mayar da alakarsu kamar yadda take a baya a cikin gaggawa.
A jiya Asabar ne dai ministocin harkokin wajen kasashen biyu su ka sanar da tsagaita wutar yaki,bayan kwanaki da su ka dauka suna musayar wuta a tsakaninsu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Ce Kafa Hujja Da ‘Yan Tawaye Kan Iran Yankewar Kauna ce Ga Makiyanta
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Amfanin da fira ministan gwamnatin mamaya ya yi da ƙungiyar ta’addanci babbar alama ce ta cikakkiyar yanke ƙauna
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Matakin da fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya dauka na yi amfani da wata karkatacciyar kungiyar ta’addanci ta “MKO” wato kungiyar Munafukai wajen yada labaran karya game da shirin makamashin nukiliyar Iran, don tsoratar da al’ummar duniya kan Iran, wata babbar alama ce ta yanke kauna.
A sakon da ya wallafa shafinsa na X ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa: Yayin da ake ci gaba da zaman tattaunawa ba na kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka, ana ci gaba da fitar da karin “hotunan tauraron dan adam don yada tsoro da fargaba kan Shirin makamashin nukiliyar Iran na zaman lafiya, inda ake murguda gaskiya zuwa karya.
Ministan harkokin wajen na Iran ya kara da cewa: Fira ministan haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu, a matsayinsa na mai neman kawo cikas da zagon kasa, ya yi amfani da dukkan tsoffi da sabbin ma’aikatan da ya dauka a matsayin wani bangare na manufofinsa na “kayyade ayyuka ga Trump.”
Araghchi ya ce: A wannan karon, Netanyahu ya koma yin amfani da bayin Saddam Hussain ‘yan kungiyar ta’addanci ta “MKO” da suka kasance kaskantattu su na shirya masa karairayi kan Shirin nukiliyar Iran, inda dogaro da rahotonnin kungiyar “MKO” babbar alama ce ta yanke ƙauna.