Kwanaki 40: Iyalan Maharban Da Aka Kashe A Edo Na Neman A Biya Su Diyya
Published: 7th, May 2025 GMT
Malam Bala Dutse, wanda ɗansa Amadu yana cikin waɗanda aka kashe, ya bayyana cewa gwamnati na ƙoƙarin mantawa da al’amarin.
“An ce an kama wasu, amma har yau ba mu ji komai ba. Na rasa ɗana, kuma rayuwata ta shiga taka mai wuya. Mafi ƙaranci, gwamnati ta fito ta faɗa mana abin da ke faruwa,” in ji shi cikin hawaye.
Hauwa’u Isa, matar ɗaya daga cikin waɗanda aka kashe, ta ce tana wahala da ’ya’yanta uku.
“Sun ce za su taimaka mana da adalci, amma har yau babu wani taimako. Ba zan daina fatan samun adalci ba, amma har yaushe za mu jira?” in ji ta.
Idan ba a manta ba gwamnonin Kano da Edo, Abba Kabir Yusuf da Monday Okpebholo, sun ziyarci iyalan maharban a baya, inda suka yi alƙawarin za a yi adalci da kuma ba su tallafi.
Gwamna Abba ya kafa kwamitin bincike ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Gwamna Aminu Abdulsalam Gwarzo.
Sai dai bayan kwanaki 40, iyalan na ci gaba da kukan cewa babu wani ci gaba da aka samu.
Mataimakin Shugaban Ƙaramar Hukumar Kibiya, Nasiru Adam Abdulaziz, ya ce ya fahimci halin da ake ciki, amma ya roƙi su da su yi haƙuri.
Ya tabbatar da cewa an kama wasu kuma an kai su Abuja, amma ya nemi a yi shari’a a bainar jama’a domin tabbatar da adalci.
Wannan kisa ya nuna irin matsalar rikice-rikicen ƙabilanci da ake fama da ita a Nijeriya.
Da dama na ganin cewa gwamnati na yin alƙawuran da ba ta cikawa, lamarin da ke hana mutane yarda maganganunta.
Yayin da aka yi addu’ar 40 ta mamatan, iyalansu sun ce ba za su daina nema wa ’yan’uwansu adalci ba.
“Za mu ci gaba da magana har sai an yi mana adalci,” in ji Malam Bala Dutse.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Diyya Iyalai Maharba
এছাড়াও পড়ুন:
An rantsar da shugaban Kamaru Paul Biya karo na 8
An rantsar da Paul Biya a matsayin shugaban ƙasar Kamaru karo na takwas mai shekaru 93 a majalisar dokokin ƙasar da ke Yaoundé.
Paul Biya ya shafe shekaru 43 yana mulkin ƙasar, kuma yanzu zai fara wani wa’adi na tsawon shekara bakwai nan gaba.
Ƙungiyyar Ƙwallon yashi ta Kada BSC ta fatattaki Kebbi BSC Kwalara ta kashe mutum 10 a Ƙaramar Hukumar AdamawaBiya wanda shine shugaban ƙasa mafi tsufa a duniya, ya sami kashi 54 na ƙuri’un zaɓe, yayin da abokin takararsa, Issa Tchiroma Bakary ya samu kashi 35%, a cewar sakamakon zaɓen hukumar ƙasa.
Tchiroma Bakary dai ya yi iƙirarin cin nasara a zaɓen da aka yi yana kuma zargin cewa an yi maguɗin zabe, wanda hukumomi suka musanta.