Kungiyar Hamas Ta Amince Ta Saki Fursinan Yaki Wanda Yake Da Jinsiyar Amurka Da HKI
Published: 12th, May 2025 GMT
Kungiyar Hamas wacce take iko da yankin Gaza, ta bada sanarwan cewa a shirye take ta saki fursina mai suna Edan Alexander wanda yake da jinsiyar Amurka da HKI don bude kofa ga tattaunawar tsagaaita wuta a gaza da kuma bude kofar rafa don samar da kayakin abicni a gaza.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Jami’an kungiyar tana fadar haka a jiya Lahadi.
Khalil Al-Hayya shugaban kungiyar ya bayyana cewa Hamas ta amince da hakan ne bayan wata tattaunawa da Amurka kan batun. Ya kuma kara da cewa kungiyar tana son a fara tattaunawa da gaske tsakaninta da HKI ta hanyar masu shiga tsakani, don kawo karshen yakin da kuma ficewar sojojin yahudawa gaba daya daga Gaza. Da kuma bude kofar Rafa don shigowar kayakin agaji da abinci cikin yankin.
Khalil Al-Hayya ya kara da cewa hamas ta yadda a hada wata tawaga wacce zata gudanar da harkokin shugabanci a yankin.
A wani labarin kuma an tabbatar da cewa Falasdinawa kimani 109,000 ne suka yi shahada a zirin Gaza, tun ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023.
Binciken da aka guddanar ya nuna cewa sojojin yahudawna sun kashe falasdinawa akalla tsaknain 77,00-109.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Yi Maraba Da Tsayar Da Wutar Yaki A Tsakanin Indiya Da Pakistan
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta iran, Dr. Isma’ila Baka’i ya bayyana cewa; Tsagaita wutar yakin da aka yi a tsakanin Indiya da Pakistan abin yin maraba da shi ne, sannan kuma ya kara da cewa; Ya zama wajibi kasashen biyu su yi amfani da wannan dama domin rage tashin hankali a yankin da kuma tabbatar da zaman lafiya.
Baka’i ya yaba da hikimar shugabannin kasashen biyu da su ka dakatar da yaki, yana kuma nuna fatansa na ganin kasashen biyu sun mayar da alakarsu kamar yadda take a baya a cikin gaggawa.
A jiya Asabar ne dai ministocin harkokin wajen kasashen biyu su ka sanar da tsagaita wutar yaki,bayan kwanaki da su ka dauka suna musayar wuta a tsakaninsu.