Aminiya:
2025-09-24@11:21:12 GMT

Gidauniya ta yi wa masu cutar gwaiwa dubu 12 tiyata kyauta a Katsina

Published: 10th, May 2025 GMT

Gidauniyar attajirin ɗan kasuwar nan na Jihar Katsina, Alhaji Dahiru Mangal, ta yi wa masu fama da cutar gwaiwa da taruwar ruwa a wasu sassan jiki fiye da 12,300 tiyata kyauta.

Da yake yi wa wakilin bayani, Malam Husaaini Kabir, mamba a kwamitin amintattu na gidauniyar ne ya tabbatar da hakan a Katsina, a lokacin ƙaddamar da aikin kashi na biyu.

Za a faɗaɗa Gasar Kofin Duniya ta Mata zuwa ƙasashe 48 — FIFA Sauya sheƙa bayan cin moriyar jam’iyya butulci ne — Kwankwaso

Kabir ya bayyana cewa gidauniyar tana gudanar da aikin tiyatar da bayar da magani kyauta a duk bayan watanni uku tun lokacin da aka kafa ta a shekarar 2013.

Ya ƙara da cewa, “majinyata masu rauni tsakanin 500 zuwa 600 ne ke cin gajiyar aikin tiyatar gwaiwar da na rage ruwan kyauta a jihar.

“Wannan shiri ba wai yana taimaka wa mutanen garin Katsina ne kawai ba, yana kuma tallafa wa mazauna ƙauyukan jihar da kuma yankunan da ke makwabtaka da su.

“Manufarmu ita ce rage nauyin biyan kuɗin kiwon lafiya ga mutane masu ƙaramin ƙarfi waɗanda ke gwagwarmaya don biyan buƙatun yau da kullun,” in ji shi.

Kabir ya buƙaci sauran ƙungiyoyi da masu hannu da shuni da su tallafawa irin wannan shiri, musamman don taimaka wa ƙoƙarin gwamnati a fannin kiwon lafiya.

Ya jaddada mahimmancin aikin tare don tunkarar ƙalubalen kiwon lafiya a cikin al’ummomin da ba a yi musu hidima ba.

Wasu da suka ci gajiyar shirin sun yaba da shirin tare da ƙarfafa gwiwar gwamnati, ƙungiyoyi masu zaman kansu, da masu hannu da shuni da su yi koyi da hakan.

Sun bayyana cewa sun jure yanayin da suke ciki na tsawon shekaru amma ba za su iya yin tiyatar ba saboda matsalar tattalin arziki.

Aminiya ta ruwaito cewa gidauniyar ta kuma bayar da maganin ido da tiyata kyauta ga marasa lafiyar idon a jihar.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Gidauniyar Mangal Gwaiwa Jihar Katsina Tiyata

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnan Gombe ya bai wa maharba kyautar motoci da babura don bunƙasa tsaro

Gwamnan Jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya bai wa ƙungiyar maharba ta ƙasa (PROHAN) reshen Gombe, kyautar motoci Hilux guda biyu da kuma babura guda biyar domin taimaka musu wajen yaƙi da ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane.

An miƙa wa shugaban ƙungiyar, Rabiu Baushe (Baushen Gombe) kyautar, wanda yana cikin shirin gwamnatin na ƙara bunƙasa tsaro da bayar da kyautar kayan aiki don kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

’Yan sanda sun kama mutane 5 kan zargin satar abincin yara a Borno Birtaniya za ta amince da ƙasar Falasɗinu

Gwamna Inuwa ya ce: “Tsaro shi ne ginshiƙin ci gaban al’umma. Ba za mu samu ci gaba, ba tare da zaman lafiya ba.

“Gwamnatina za ta ci gaba da tallafa wa jami’an tsaro da ƙungiyoyin sa-kai domin kawo ƙarshen barazanar ta’addanci.”

A nasa jawabin, Rabiu Baushe, ya gode wa gwamnan bisa wannan tallafi, inda ya bayyana cewa motocin da baburan za su ƙara musu ƙarfi wajen yin sintiri da shawo kan hare-hare a yankunan karkara.

Ya kuma yi alƙawarin cewa ƙungiyar PROHAN za ta ci gaba da haɗa kai da jami’an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya a dukkanin sassan Jihar Gombe.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gavi Zai Yi Jinyar Watanni 5 Bayan Yi Masa Tiyata
  • Gwamnatin Kano Ta Tabbatar Da Ɓullar Cutar Mpox A Jihar
  • Gwamnatin Kano Ta Tabbatar Ɓullar Cutar Mpox A Jihar
  • Taron Canada: Haɗin Gwiwa Afirka Ke Buƙata Ba Agaji Ba – Gwamnan Zamfara 
  • Hisbah ta kama masu safarar mata zuwa Saudiyya a Kano
  • An rufe sansanin NYSC da kasuwanni saboda rashin tsaro a Kwara
  • Gwamna Kefas Ya Bamu Damar Ƙwatar Mulkin Taraba A 2027 – APC
  • Karin ƙananan hukumomi 2 sun yi sulhu da ’yan bindiga a Katsina
  • Mata 400 sun amfana da kayan haihuwa a Gombe
  • Gwamnan Gombe ya bai wa maharba kyautar motoci da babura don bunƙasa tsaro