Rasha Da China Sun Sha Alwashin Fuskantar Amurka
Published: 9th, May 2025 GMT
Shugabannin kasashen Rasha da China Sun yi alkawalin fuskantar siyasar Amurka akansu,a yayin wani taro da su ka yi a birnin Moscow a daidai lokacin bikin tunawa da zagayowar cikar shekaru 80 da samun galaba akan ‘yan Nazi na kasar Jamus.
Shugaba Vladmir Putin na Rasha da takwaransa na China Xi Jing Ping sun yi tattaunawa ta fiye da sa’oi 3, sun rattaba hannu akan yarjeniyoyi a tsakaninsu da su ka kunshi kara yawan hannunu jarin da su ka zuba a cikin kasashen junansu, haka nan kuma yin aiki a tsakaninsu domin tabbatar da zaman lafiya a duniya sannan kuma da zurfafa girman alaka a tsakaninsu.
Bayanin bayan taron kasashen biyu ya kunshi nuna damuwa akan yadda Amurka take kara ayyukanta na soja da kuma kera makaman kare dangi, tare da jaddada aniyarsu ta kalubalantar siyasar Amurkan akan kasashen nasu.
Haka nan kuma Putin da Xi sun bayyana kin amincewarsu da Shirin da shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da shi wanda ya shafi mayar da sararin samaniya filin yaki.
Haka nan kuma sun yi ishara da kokarin Amurka da kawayenta na tayar da rikici a Asiya da yankin tekun “Pacific”, sun kuma bayyana cewa da akwai yiyuwar barkewar yakin Nukiliya a duniya saboda yadda alaka a tsakanin kasashen da su ka mallakin wadannan makaman ta tabarbare.
A kan yakin kasar Ukiraniya kuwa, kasashen biyu sun jaddada goyon bayansu ga dukkanin kokarin da ake yi da zai taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya.
A karshe kasashen biyu sun ce, karfafa alakarsu da suke yi baya da nufin fada da wata kasa a duniya.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Janar Salami: Muna Cikin Shirin fuskantar Yaki A Duk Yadda Ya Zo
Kwamandan dakarun kare juyin musulunci na Iran Janar Husaini Salami ya bayyana cewa; Dangane da Shirin Nukiliyar Iran, muna bai wa diplomasiyya fifiko, amma kuma a lokaci daya muna cikin Shirin fuskantar kowane irin yaki duk yadda ya zo.
Janar Salami wanda ya gabatar da jawabi a wurin karrama shahidan yi wa kasa hidima, a hubbaren Imam Ridha ( a.s) ya kuma kara da cewa; Ya kamata Amurkawa su kwana da sanin cewa, idan su ka yi mana barazana, to a shirye muke domin fuskantar kowane irin yaki, a duk yadda ya zo.
Kwamandan dakarun kare juyin juya halin musuluncin na Iran ya kuma zargi Amrukawa da cewa su, ba masu cika alkawali ba ne, saboda yadda su ka yi wa Iran barazana da kuma kakaba mata sabbin takunkumai.
Janar Salami ya kuma ce; Jamhuriyar musulunci ba ta da azamar kera makamin Nukiliya bisa zabinta, ta kuma cire shi daga cikin akidarta ta tsaro.
Kwamandan dakarun kare juyin musuluncin na Iran ya kuma ce; Muna gargadin abokan gaba akan cewa idan har su ka tafka wani kuskure, to za a bude musu kofofin jahannama.
Janar Salami ya yi ishara da hare-haren “Wa’adussadiq 1, da na 2 da Iran ta kai wa HKI,sannan ya kara da cewa: Idan har ba za ku iya jurewa makami mai linzami guda daya daga Ansarullah jarumai daga Yemen ba, to yaya za ku yi da daruruwa da kuma dubban makamai masu linzami da za a harbo muku ?
Kwamandan na dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran ya yi jawabi akan cikar shekara da rasuwar shugaban kasa Ayatullah Ra’isi yana mai cewa; Ya kasance mutum wanda ya tattara soffofi na kamala, don haka ya cancanci yin shahada domin ita ce ta dace da shi.
Haka nan kuma ya yi jinjina ga shahidai irin su Kassim Sulaimani, Isma’ila Haniyyah, Yahya Sinwar, Sayyid Hassan Nasrallah, Safiyuddin, Zahidi, Musawi, ali-Hashim da kuma Rahmati.