Hadar Cinikayyar Waje Ta Kasar Sin Ta Karu Da Kaso 5.6 Bisa Dari A Watan Afirilu
Published: 9th, May 2025 GMT
Alkaluman hukumar kwastam ta kasar Sin sun nuna cewa a watan Afirilun bana, hada-hadar cinikayyar shige da ficen hajoji ta amfani da kudin kasar yuan ta karu da kaso 5.6 bisa dari.
Alkaluman da hukumar ta fitar a Juma’ar nan sun nuna cewa, adadin hajojin da kasar Sin ta fitar ya karu da kaso 9.3 bisa dari a shekara zuwa yuan tiriliyan 2.
Cikin watanni 4 na farkon shekarar bana, jimillar hajojin da Sin ta shigo da su, da wadanda ta fitar ketare a hada-hadar kudin kasar yuan sun karu da kaso 2.4 bisa dari zuwa yuan tiriliyan 14.14.
Tsakanin wannan wa’adi, Sin ta fitar da hajojin da suka karu da kaso 7.5 bisa dari, wato na kimanin yuan tiriliyan 8.39, yayin da adadin hajojin da ta fitar suka ragu da kaso 4.2 bisa dari zuwa yuan tiriliyan 5.75. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: yuan tiriliyan karu da kaso
এছাড়াও পড়ুন:
Xi Ya Yi Kiran Zurfafa Gyare-gyare Da Bude Kofa A Yayin Rangadin Aiki A Guangdong
Xi ya jaddada cewa, domin lardin Guangdong ya samar da sabbin damammaki da cimma sabbin nasarori, ya zama dole a ci gaba da himma wajen aiwatar da manufar yin gyare-gyare da bude kofa, da aiki da ruhin yankunan tattalin arziki na musamman, da kuma karfafa samun ci gaba mai inganci ta hanyar zurfafa gyare-gyare da bude kofa.
Ya yi kira da a yi kokarin zurfafa hadin gwiwa tsakanin Guangdong, Hong Kong da Macao, da kuma tallafa wa inganta hadewar Hong Kong da Macao da kuma hidimta wa ci gaban kasar baki daya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA