Pakisatan Ta Kore Cewa Ta Keta Yarjejeniyar Tsagaita Wutar Yaki
Published: 11th, May 2025 GMT
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Pakistan ta jadada cewa ko kadan sojojin kasar ba su keta tsagaita wutar yaki da Indiya ba.
A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen ta Pakistan ta fitar ta ce; kasar tana ci gaba da aiki da tsagaita wutar yaki wacce aka sanar da ita, kuma sojojin kasar sun kai zuciya nesa, duk da cewa Indiya ce ta keta wutar yakin.
Saanrwar da Pakistan ta biyo bayan zargin da Indiya ta yi wa kasar ne cewa tana keta yarjejeniyar wutar yaki bayan an cimma yarjejeniya a kan hakan.
Jami’i a ma’aikatar harkokin wajen Indiya Bigram Maisari ne ya bayyana hakan a wani taron manema labaru da ya gabatar a yau, sannan ya kara da cea; Muna yin kira ga kasar Pakistan da ta dauki matakan da su ka dace domin kawo karshen keta wutar yakin da take yi.
Shi kuwa Fira ministan yankin Jammo da Kashmir Umar Abdullah cewa ya yi an ji kararrakin fashewar abubuwa masu karfi a garin Sirinigar, da shi ne babbar birnin Kashmir dake karkashin Indiya.
Wasu shaidun ganin ido sun kuma bayyana cewa, an ga jirage marasa matuki suna zarya a sararin samaniyar yankin.
Tun da fari, Fira ministan Pakistan Shahbaz Sharif ya bayyana cewa; Kasarsa ta yi nasara akan makiya, yana mai jinjinawa sojojin kasar da su ka mayar da martani akan wuce gona da irin Indiya da karfi, kuma cikin kwarewa”
Shahbaz ya kuma ce; Indiya ta shelanta yaki akanmu ba tare da wani dalili ba, yana siffata abinda Indiya din ta yi da cewa; Abin kunya ne.”
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Da Take Kula Da Nukiliyar Pakistan Za Su Yi Taron Gaggawa
Fira ministan kasar Pakistan Shahbaz Sharif ya kira yi Majalisar kasa wacce take kula da makaman Nukiliyar kasar da su yi taro.
Wannan matakin da ake yi wa Kallon mai hatsari yana faruwa ne a daidai lokacin da kasar ta Pakistan take yaki da Indiya.
Ita dai Majalisar kasar Pakistan dake kula da makaman Nukiliya da kuma manufofin kasa na koli, ta kunshi manyan kwamandojin soja, da fararen hula, aikinta kuma shi ne kula da manyan batutuwa da su ka shafi kasa daga ciki har da siyasar makaman Nukiliya da kuma makamai masu linzami.An kafa wannan majalisar ne dai a 2000.
Tashar talabijin din “Sama News” ta bayar da labarin dake cewa; Mahalarta taron za su yi bitar halin da ake ciki ne na yaki, da kuma tattaunawa matakan da za a dauka a fagen diplomasiyya da kuma hanyoyin tsaro da kare kai.
Ita dai kasar Indiya tana cewa ba za ta taba zama wacce za ta fara amfani da makamin Nukiliya ba, don haka ba za ta zama ta farko da za ta kai wa Pakistan hari ba. Ita kuwa Pakistan ta gina akidarta ta tsaro ne akan cewa za ta iya fara amfani da makamin Nukiliya da Zarar ta faminci cewa wanzuwar kasar tana fuskantar rushewa.
Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana aiki tukuru domin ganin ta shiga Tsakani da kawo karshen rikicin dake tsakanin kasashen biyu da suke makwabtanta.