Yanzu-yanzu: Matatar Man Dangote Ta Sake Karya Farashin Man Fetur
Published: 12th, May 2025 GMT
Wannan rangwamen farashin duk da cewa ba a hukumance yake ba, amma ya bai wa kwastomomin Dangote damar siyar da mai akan farashi mai rahusa a tsakanin Naira 830 zuwa N835 kan kowacce lita.
Wannan nasarar ta zo ne makonni kadan bayan da matatar ta yi ragin farashi sau biyu a jere a cikin mako guda a cikin watan Afrilu, inda ta rage farashin man ta daga N880 zuwa N835 kan kowace lita.
Ana kyautata zaton cewa, ragin na da nasaba da sabunta tsarin sayen danyen mai da takardar Naira, biyo bayan dakatarwar da aka yi na wucin gadi.
Kokarin samun wata sanarwa a hukumance daga Kakakin Rukunin Dangote, Anthony Chiejina, kan batun rangwamen ya ci tura har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Kefas Ya Bayyana Alhininsa Bisa Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi
Daga Sani Sulaiman
Gwamnan Jihar Taraba, Dr. Agbu Kefas, ya yi jimami kan rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wanda ya rasu a ranar Alhamis 27 ga watan Nuwamban 2025, yana da shekaru 102.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai bai wa gwamnan shawara na musamman kan Yada Labarai da Hulda da Jama’a, Mista Emmanuel Bello, ya sanyawa hannu.
Gwamnan ya ce rasuwar wannan babban malami babban rashi ne ga kasa, yana mai nuna cewa a wannan lokaci ne ake matuƙar bukatar irin gudummawar da yake bayarwa, duba da kalubalen da kasar ke fusfuskanta.
Ya kara da cewa marigayi Sheikh ya koyar da ilimi da zai ci gaba da jagorantar kasa kan batun zaman lafiya tsakanin addinai.
Haka kuma, Dr. Kefas ya yabawa halayen Sheikh Bauchi, wanda ya bayyana shi a matsayin mutum mai tawali’u, jin kai, da haƙuri.
Saboda haka, Gwamna Agbu Kefas ya yi kira ga jama’a da su yi koyi da jagorancin wannan fitaccen malami.
Ya ce al’ummar kasa za su ci gaba da bin tsarin ladabi da tarbiyyar da marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya koyar.
A wani bangaren, Dr. Kefas ya ja hankalin ‘yan Najeriya da su ci gaba da kasancewa cikin zaman lafiya da juna ba tare da la’akari da addininsu ba.
Ya jaddada muhimmancin jurewa da girmama ra’ayin juna maimakon nacewa a kan namu ra’ayin, tare da tabbatar da aniyarsa ta ci gaba da hidima ga dukkan ‘yan Jihar Taraba bisa adalci ba tare da la’akari da addini ko kabilarsu ba.