Waji Jirgin Amurka Samfurin F-18 Na 3 Ya Fadi A Tekun “Red-Sea”
Published: 7th, May 2025 GMT
Rundunar sojan Ruwan Amurka ta sanar da cewa; Jirgin sama samfurin F-18 wanda kudinsa ya kai dalar Amurka miliyan 67 ya fadi akan jirgin dakon jiragen ruwa na ” USS Harry Truman” a tekun “Red Sea”.
Jaridar ” Washington Post” ta buga labarin dake cewa; Jirgin ta fado ne a lokacin da yake kokarin sauka akan doron jirgin ruwan dakon jiragen saman na ” USS Harry Trauman”.
Sanarwar ta kuma kara da cewa; Matuka jirgin sun fice daga cikinsa ta hanar lema, kuma an tserato da su daga cikin ruwa ta hanyar jirgi mai saukar angulu. Matukan, kamar yadda sanarwar ta sojojin na Amurka, sun ji rauni.
Wani jami’in soja wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya fada wata kafar watsa labaru cewa; Yawan faduwar da jiragen yakin samfurin F-18 suke yi, ya ja hankalin manyan kwamandojin sojan Amurka.”
A ranar 28 ga watan Afrilu ma dai rundunar sojan ruwan Amurkan ta sanar da faduwar jirigin yakin samfurin F-18 a lokacin da yake sauka.
Bugu da kari a cikin watan Disamba na shekarar da ta wuce, wani jirgin saman ya fado ya ci karo da jirgin dakon jiragen yakin kamar yadda rundunar sojan ruwan Amurkan ta sanar.
Wasu masu bin diddigin abinda yake faruwa a yankin suna danganta fadowar jiragen saman na Amurka da hare-haren kungiyar Ansarullah ta Yemen.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kakakin Gwamnatin Iran Ta Yi Suka Kan Masu Son Canja Sunan Tekun Fasha Saboda Jahilcin Tarihin Iran
Kakakin gwamnatin kasar Iran ta bayyana cewa: Duk wanda ya canza sunan Tekun Fasha, tabbas ya jahilci tarihin dubban shekaru na Iran
Mai magana da yawun gwamnatin Iran Fatimah Mohajerani ta yi tsokaci kan rahotannin da suke cewa: Shugaban Amurka Donald Trump na yunkurin sauya sunan yankin tekun Fasha. Ta jaddada cewa “wadanda ke neman canza sunan Tekun Fasha ba su fahimci tarihin dubban shekaru na Iran ba.”
Malama Mohajerani ta rubuta a dandalin na X cewa: Tekun Fasha bai takaita da kasancewa sunan yanki kadai ba, a’a ya zama wani muhimmin bangare na tarihin al’ummar Iran.
Ta kara da cewa: “Wadanda ke neman canza sunan ‘Tekun Fasha’ ba su fahimci tarihin Iran na dubban shekaru ba. Wannan yunkuri na nuna rashin sanin gaskiya da tarihi kafin ya zama batun neman tunzura Iran.”