NAJERIYA A YAU: Abin ya sa aka kasa kawo ƙarshen Tamowa a Arewa Maso Gabas
Published: 9th, May 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Hukumomi a jihar Yobe sun ɗora alhakin ƙazancewar matsalar tamowa a kan rikicin Boko Haram da rashin shayar da jarirai nonon uwa yadda ya kamata da kuma gurɓacewar harkar kiwon lafiya, da sauran su.
Bayanin hakan na zuwa ne bayan Babban Jami’i mai Kula da Ayyukan Jinƙai na Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya, Mista Mohamed Malick Fall, ya sanar cewa yara miliyan daya a jihohin Borno da Adamawa da Yobe suna fuskantar barazanar rasa rayukansu sakamakon cutar tamowa a bana.
An kuma ruwaito shi yana cewa wannan adadi ya ruɓanya na yaran da suka fuskanci barzanar a bara.
NAJERIYA A YAU: Ƙalubalen Da Iyaye Ke Fuskanta Wajen Tarbiyyar ’Ya’yansu DAGA LARABA: Ɓoyayyun Dalilan Da ke Sa Faɗuwa Jarabawa A NajeriyaShirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari ne kan hanyoyin da za a bi don magance Tamowa a wasu jihohin Arewa maso Gabas.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Arewa maso Gabas tamowa yara
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Sin Na Matukar Goyon Bayan Tabbatar Da Adalci Ga Falasdinawa Wajen Maido Da Hakkinsu Na Kasa
Dangane da halin da ake ciki game da rikicin Falasdinu da Isra’ila, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana a yau Litinin 22 ga wata cewa, karfin soja ba zai iya samar da zaman lafiya ba, kuma tashin hankali ba zai iya samar da tsaro ba. Kasar Sin tana son yin hadin gwiwa tare da kasashen duniya wajen ci gaba da jajircewa a kan tsagaita bude wuta da kawo karshen yakin da ake yi a zirin Gaza, da kuma matukar nuna goyon baya ga tabbatar da adalci ga al’ummar Falasdinawa wajen maido da hakkinsu na kasa, da kuma kara azamar warware matsalar Falasdinu tun da wuri ta hanyar samar da cikakkiyar mafita, mai adalci da kuma dorewa.
Guo Jiakun ya ce, kawo karshen rikicin cikin hanzari da samar da dawwamammen zaman lafiya, shi ne babban burin al’ummar Falasdinu da Isra’ila da kuma yankin Gabas ta Tsakiya, kuma wannan aiki ne na gaggawa da ke gaban kasashen duniya. Kasar Sin ta yi imanin cewa, a halin da ake ciki yanzu, ya zama tilas a karfafa tsagaita bude wuta a zirin Gaza, tare da daukar matakin gaggawa domin rage radadin bala’in jin kai a yankin.
Ya ci gaba da cewa, ya kamata kasashen da ke da tasiri na musamman a kan Isra’ila su sauke nauyin da ke wuyansu. Dole ne a aiwatar da ka’idar barin “Falasdinawa su mulki Falasdinu” bisa turbar gaskiya, kuma dole ne a kiyaye hakkin kasar Falasdinu kan batutuwan da suka shafi shugabanci bayan yaki da kuma shirye-shiryen sake gina kasar. Kazalika, a cewarsa, dole ne a ci gaba da bibiyar shawarar “kafa kasashe biyu” ba tare da kakkautawa ba, da samar da karin fahimtar juna da cimma matsaya tsakanin kasa da kasa da kuma yin watsi da duk wani mataki na bangare guda da zai iya yin kafar ungulu a kan “kafuwar kasashe biyu”. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp