Aminiya:
2025-05-07@21:48:47 GMT

Dalilin faɗuwar ɗalibai a jarabawar JAMB bana — Ministan Ilimi

Published: 7th, May 2025 GMT

Ministan Ilimi a Nijeriya, Tunji Alausa ya ce hana satar amsa ne ya janyo faɗuwar ɗalibai a jarawabar shiga manyan makarantu da JAMB ke shiryawa a kowace shekara.

Tunji ya bayyana haka ne yayin tattaunawa da gidan talabijin na Channels a ranar Talata.

‘Raini ne ya sa ake ƙalubalantar yunƙurin kafa ƙungiyar Hausawa zalla’ Majalisar Dattawa ta kafa kwamitin lura da gwamnan riƙo na Jihar Ribas

Ya ce sakamakon bana da aka samu, ya nuna irin yadda aka ƙara inganta yanayin rubuta jarabawar yadda ya kamata.

Ya bayyana cewa hakan kuma ya nuna yadda tsarin rubuta jarabawar ya daƙile satar amsa da ɗalibai ke yi.

Alausa ya ƙara da cewa kada a ɗauki sakamakon na JAMB a matsayin koma-baya, maimakon haka a kalle shi a matsayin yadda ɗaliban da suka ci suka nuna hazaƙa lokacin rubuta jarabawar.

“JAMB na gudanar da jarabawarta ta hanyar amfani da tsarin kwamfuta wato CBT.

“Sun ɗauki ƙwararan matakai da ya janyo aka samu raguwar satar amsa matuƙa,” in ji shi.

“Saboda haka daga shekara mai zuwa muna so duk wata jarrabawar ɗalibai masu kammala sakandire ta koma tsarin amfani da komfuta.”

A ranar Litinin ne JAMB ta fitar da sanawar fitar da sakamakon bana tana mai cewa yawancin ɗaliban da suka zauna jarabawar sun gaza samun maki 200 daga cikin maki 400.

JAMB ta ce ɗalibai miliyan 1.95 ne suka rubuta jarabawar, amma cikin wannan adadi, miliyan 1,534,654 ne wanda ya kai kaso 78 cikin 100 suka samu maki ƙasa da 200.

Alƙaluman sakamakon ya nuna cewa kashi 0.63 ne na ɗalibai ƙalilan da suka samu makin da ya haura 300, wanda a jimlace suka kai ɗalibai 12,414.

A matakin maki tsakanin 250 zuwa 299 kuma, an samu ɗalibai 73,441 yayin da ɗalibai 334,560 suka samu maki tsakanin 200 zuwa 249.

Rukunin da ya fi yawan ɗalibai shi ne na maki 160 zuwa 199, inda aka samu ɗalibai dubu 983,187 wato kashi sama da 50 cikin 100 ke nan.

Haka kuma, ɗalibai dubu 488,197 suka samu maki tsakanin 140 zuwa 159, sannan dubu 57,419 suka samu tsakanin 120 zuwa 139.

Ɗalibai 3,820 kuma sun samu maki tsakanin 100 zuwa 119, sannan ɗalibai dubu 2,031 sun gaza samun ko da maki 100.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Ɗalibai Satar Amsa rubuta jarabawar

এছাড়াও পড়ুন:

Kungiyar Ansarullahi Ta Yemen Ta Sanar Da Cewa Ayyukan Yemen Na Tallafawa Gaza Ba Zai Tsayawa Ba

Shugaban tawagar kasar Yemen, Mohammed Abdul Salam, ya sanar da cewa ayyukan Yemen na tallafawa Gaza ba zai tsayawa ba

Shugaban tawagar shiga Tsakani na kasar Yemen Abdul Salam ya bayyana cewa: Yemen ta samu sakon bukatu daga Amurka ta hanyar masarautar Oman, kuma wanda ya sauya matsayinsa Amurka ce, ba Yemen ba.

Ya kara da cewa ikirari da Amurka ta yi na mika wuya, yana nuni ne ga gazawa, saboda Amurka ba zata iya kare jiragen ruwan haramtaciyar kasar Isra’ila daga hare-haren Yemen ba.

Abdul-Salam ya kara da cewa: Fahimtar farko da aka samu tsakanin Amurka da Yemen ba ta da wata alaka da matsayar Yemen kan goyon bayan Gaza, yana mai nuni da cewa za a samu ci gaba ta hanyar da ta dace, tare da jaddada cewa Yemen zata mayar da martani ga duk wani ta’addanci daga ko wane bangare.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Jakadan Sin A Najeriya Ya Gana Da Ministan Harkokin Wajen Najeriya
  • Ministan Ilimi Ya Ce Hana Satar Amsa Ne Ya Sa Ɗalibai Suka Faɗi JAMB A Bana
  • Kungiyar Ansarullahi Ta Yemen Ta Sanar Da Cewa Ayyukan Yemen Na Tallafawa Gaza Ba Zai Tsayawa Ba
  • Alƙaluman sakamakon jarabawar bana — JAMB
  • Jigawa Ta Kaddamar Da Kwamitin Likitocin Da Su Duba Lafiyar Mahajjatan Bana A Saudiyya
  • Dalilin Da Ya Sa Ɗan Sanda Ya Gyara Wa Ganduje Igiyar Takalmi – Hadimi
  • Artabu Tsakanin ‘Yan Bindiga Da ‘Yan Banga Ya Ci Rayuka Da Dama A Bauchi
  • Umaru ’Yar’adua da shugabannin Najeriya da suka rasu a kan mulki
  • Kasar Iran Zata Mayar Da Martani Mai Tsanani Kan Duk Wani Hari Da Zata Fuskanta Daga Makiya