2025-09-18@02:05:51 GMT
إجمالي نتائج البحث: 161

«a Gwamnatin Tarayya»:

      Wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Folasade Boriowo, ya fitar, ta ce a karon farko cikin shekaru da dama, daliban Nijeriya za su ci gaba da karatun tarihin Nijeriya tun daga Firamare 1 zuwa karamar Sakandare 3 yayin da daliban SSS 1 – 3 za su koyi sabon darasin da aka samar na ‘Civic and Heritage Studies’, wanda ya hada tarihin Nijeriya da Ilimin zamantakewar Jama’a. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin Tarayya ta ce Najeriya na rasa sama da Dala Biliyan 10 duk shekara sakamakon asarar amfanin gona bayan girbi. Ministan Noma  Sanata Abubakar Kyari ne ya bayyana haka a wajen kaddamar da shirin Hanyar Inganta Noma da Kayayyakin Mire Rayuwa a Yankunan Karkara G.R.A.I.N a ƙaramar hukumar Birnin Kudu ta  Jihar Jigawa.   Ya ce asarar na faruwa ne saboda rashin ingantattun wuraren ajiya, karancin ababen more rayuwa, sauyin yanayi da kuma ambaliya. Kyari ya bayyana cewa noma na bada gudunmawar kashi 24 bisa 100 na Jimillar Darajar Kayayyaki da Ayyuka da Kasa ta Samar a Cikin Shekara GDP, inda ƙananan manoma ke samar da sama da kashi 70 bisa 100 na abincin da ake ci a ƙasa....
    Hukumar Tsaron Farin Kaya a Nijeriya DSS, ta gurfanar da fitaccen ɗan gwagwarmayar nan, Omoyele Sowore a kotu. A ƙunshin ƙarar da DSS ta gabatar a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta haɗa da shafukan sada zumunta na X da kuma Facebook, inda take zarginsu da ba da ƙofar aibata Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Bida Poly ta sa sojoji kula da jarrabawar ɗalibai Kukan al’umma kan lalacewar hanyar Dukku Darekan shigar da ƙara na Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya, M.B Abubakar da wasu lauyoyi huɗu —M.E. Ernest da U.B. Bulla da C.S. Eze da kuma E.G. Orubor, ne suka shigar da ƙarar a madadin Gwamnatin Tarayya da kuma hukumar ta DSS. DSS wadda ta kafa hujja da sashe na...
    Mataimakinsa kan harkokin majalisa Honarabul Attahiru Danmadi ne ya wakilci dan majalisar ya kuma tabbatarwa wadanda lamarin ya shafa kokarinsa kan daukar matakan da suka kamata domin tabbatar da tsaron rayukan su da dawowa da zaman lafiya a yankunan.   Garuruwan da ‘yan bindigar suka tarwatsa a gundumar Kuchi sun hada da Fakku, sha’alwashi, tulluwa da Rafin- gora a inda mutane bakwai suka rasa rai. A gundumar Jabo kuwa kauyukan da lamarin ya shafa su ne; Gesolodi, Hilya, Guraye, Guma, Chakai, Modo, Badariya, Tafki, Balera, Gudumawa da Rafin shinka.   “Mun girgiza kwarai da wannan halin da kuke ciki. A matsayina na wakilin ku, zan ci-gaba da kokarin da ya kamata a majalisa domin ganin jami’an tsaro sun kawo karshen...
    Dokar ta ba da damar dakatarwa na ɗan lokaci ko kuma cire rajistar Tax ID gaba ɗaya idan mai riƙe da shi ya daina gudanar da kasuwanci. A gefe guda, Dokar Kafa Hukumar Haraji ta Nijeriya, 2025, ta ba Shugaban Zartarwa na Hukumar babban ikon, wanda zai kasance shugaban Kwamitin Gudanarwa na hukumar. Kwamitin zai haɗa da wakilai daga Ma’aikatan Kuɗi, Tsare-Tsaren Ƙasa, Shari’a, Man Fetur, Babban Bankin Nijeriya, Haraji da Kwastam, Hukumar Kula da Harkokin Kamfanoni, da sauran muhimman hukumomi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga...
    Tabbatar da dakatar da amfani da HCFC-141b a tsarin sandwich panel, spray, da block a ayyukan cikin gida na Vitapur. Daraktan Zartarwa na Vitapurs Ltd, Mista Taiwo Adeniyi, a jawabin maraba da ya yi, ya bayyana cewa cibiyar za ta ƙara ƙwarewa wajen gwaje-gwaje, bincike, da horo tare da amfani da sinadarai masu ƙarancin GWP, ƙara ƙarfin haɗa kayan ODS-free don samfuran rigid PU, da faɗaɗa ayyukan ɗakin gwaje-gwaje wajen nazarin kayan aiki da samfuran ƙarshe, da kuma tasirin tattalin arziki da muhalli. Ya ƙara da cewa Optimized System House zai inganta samar da ayyukan yi da canja fasaha, rage buƙatar kuɗaɗen waje ta hanyar rage dogaro da shigo da kaya, tallafa wa tafiyar masana’antu ta Nijeriya ta hanyar rassan...
    Ministan Ilimi, Dr. Maruf Tunji Alausa, tare da Karamar Ministar Ilimi, Farfesa Suwaiba Sa’id Ahmad, ne suka sanar da sabon tsarin a ranar Laraba, inda suka bayyana shi a matsayin wani ƙwaƙƙwaran mataki na “rage yawan masu neman aiki a ma’aikatun gwamnati da na masu zaman kansu, ta hanyar koyar da dabarun kasuwanci, daidai da ka’idojin duniya, da kuma shirya matasan Nijeriya don samun ayyukan yi a nan gaba. Kwasakwasan da aka ɓullo da su Kwasakwasai na koyar da dabarun Kasuwanci 26 da gwamnatin ta bullo da su, sun hada da Brick Laying, Block Laying and Concreting, Painting Decoration and Finishes (Interior Design), Woodwork, Carpentry and Joinery, Welding & Fabrication, Plumbing and Pipe Fitting, Computer Hardware & GSM Repair and...
    Gwamnatin Tarayya za ta gurfanar da manyan shugabannin ƙungiyar ’yan ta’adda ta Ansaru a kotu a yau Alhamis. Za a gurfanar da su ne a Babban Kotun Tarayya da ke Abuja. Tinubu ya bayar da umarnin a sake karya farashin kayan abinci EFCC ta tsare Mele Kyari kan binciken matatun mai Mutanen da za a gurfanar su ne Mahmud Muhammad Usman, wanda aka fi sani da Abu Bara’a, da mataimakinsa Abubakar Abba, wanda aka fi sani da Mahmud Al-Nigeri ko Mallam Mamuda. Za su fuskanci tuhume-tuhume 32 da suka shafi ta’addanci. Tuhuma ta farko ta ce, mutanen sun taimaka wajen tsara da jagorantar ƙungiyar ta’addanci ta Ansaru tsakanin 2013 zuwa 2015. An haramta ayyukan Ansaru a Najeriya kuma tana da...
    Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da jami’an Hukumar Kula da Man Fetur ta Nijeriya (NMDPRA), wakilan kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC, shuwagabannin kamfanin ‘MRS Holdings Limited’ da kuma kungiyar ‘yan kasuwa ta kasa (TUC).   Da yake bayyana bude taron, Minista Dingyadi ya jaddada aniyar gwamnati na sulhu a tsakanin kungiyar da masu gudanar da masana’antu. Ya bayyana bangaren mai da iskar gas a matsayin jigon tattalin arzikin Nijeriya, yana mai gargadin cewa tsawaita yajin aikin zai haifar da mummunan sakamako ga kasar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya...
    “Muna miƙa ta’aziyyar mu ta musamman ga iyalan waɗanda abin ya shafa, gwamnatin jihar da kuma al’ummar Neja. Jimamin mu da addu’o’in mu suna tare da duk wanda wannan ibtila’i ya shafa.”   Ministan ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta umurci Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) da ta samar da dukkan tallafi da ake buƙata ga iyalan waɗanda suka mutu da waɗanda suka tsira, tare da yin aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnatin Jihar Neja domin tabbatar da gaggawar tallafi da taimako.   Haka kuma, gwamnatin ta umurci Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Ƙasa (NOA) da ta gudanar da babban kamfen na wayar da kai a faɗin ƙasar nan domin ƙara faɗakar da jama’a kan matakan tsaro...
    Da yake ganawa da ‘yan jarida a ranar Litinin, tsohon shugaban kungiyar masu tsara gidaje a Nijeriya, Aliyu Wammako, ya ce, rashin biyan ‘yan kwangila kudadensu na shafan tattalin arziki sosai. Ya bukaci gwamnatin tarayya da ka da ta tsaya bata wani lokaci ta kama biyan ‘yan kwangila kudadensu da hakan zGwamnatin tarayyar Nijeriya ta kaddamar da wani kwamiti da zai tattauna batun basussukan da suka dabaibaye harkokin jakadancin Nijeriya a kasashen ketare. Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin kasashen waje, Kimiebi I. Ebienfa, shi ne ya shaida hakan ya cikin sanarwar da ya fitar a ranar Litinin a Abuja. Ebienfa ya ce an dauki matakin ne domin tabbatar da cewa an yi amfani da kudaden da aka tura domin...
    Ya ƙara kira ga ‘yan Nijeriya da su kasance masu bin doka da kula da tsaro tare da goyon bayan manufofin gwamnati da nufin ƙarfafa haɗin kan ƙasa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Juma’a, biyar ga watan Satumban 2025 a matsayin ranar hutu albarkacin ranar haihuwar Annabi Muhammad (S.A.W). Ana dai yin bikin ranar ce dai da ake kira ta Mauludi a duk ranar 12 ga watan Rabi’ul Auwal, wat ana uku a shekarar Musulunci. DAGA LARABA: Yadda Mata Dake Auren Gwaji Suke Yamutsa Hazo ’Yan bindiga sun sace basarake a Kogi Ministan Cikin Gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa, ranar Laraba a madadin gwamnatin, kamar yadda Babbar Sakatariyar ma’aikatar, Dr Magdalene Ajani ta sanar. Ministan ya kuma taya ’yan Najeriya murna, inda ya bukace su da su yi koyi da kyawawan halayen Annabin na zaman lafiya, kaunar jama’a, hakuri, tawali’u...
    Gwamnatin Tarayya ta ɓullo da sabon manhajin karatu na makarantun firamare zuwa sakandire wanda zai fara aiki a sabon zangon karatu na bana da za a soma a watan Satumbar nan. Wannan na zuwa ne bayan kammala nazari mai zurfi kan manhajoji karatu a fannin ilimi a matakin farko da na manyan makarantun sakandire da kuma fannin fasaha. Manchester City ta ɗauki golan PSG, Gianluigi Donnarumma Ndume ya koka kan sabbin hare-haren Boko Haram a Borno Gwamnatin ta ce ta ɗauki wannan matakin ne da nufin rage nauyin karatu kan ɗaliban da kuma inganta tsarin koyarwa a faɗin ƙasar. Ƙaramar Ministar Ilimi, Farfesa Suwaiba Sa’id Ahmad, ce ta bayyana hakan a madadin Ministan Ilimi, Dakta Maruf Tunji Alausa a ƙarshen...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Nafisa wacce ta wakilci Nijeriya a karkashin Kwalejin Tulip International ta Nijeriya, ta buge abokan karawarta fiye da 20,000 daga kasashe 69, ciki har da kasashen Turanci.   Gasar ‘TeenEagle’ babbar gasa ce ta duniya wacce ke bibiyar ƙwarewar ɗalibai cikin harshen Turanci, kaifin basira, da ƙwarewa a salon magana. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    “Mun yi tattaunawar gaskiya, amma gwamnati tana yi mana wasa,” in ji shi. Ya ce an yi watsi da rahotanni masu muhimmanci, an kafa manufofin da ke cutar da ilimi, sannan an jefa malaman da suka yi ritaya mummunan hali. “Wannan gwamnati ta raina ilimi da malamai. Mun gaji,” in ji shi. Shugaban ASUU ya yi gargaɗin cewa idan gwamnati ta ƙi ɗaukar mataki, za ta ɗauki alhakin duk wata matsala da za ta biyo baya. Ya kuma kira mambobin ASUU da su fito ƙwansu da kwarkwata wajen tarukan da za a gudanar a manyan jami’o’i a ranar Talata, 26 ga Agusta, 2025, yana mai cewa wannan shi ne mataki na farko da ƙungiyar za ta ɗauka don nuna rashin...
    Hukumar Hisbah ta kama mutane 62 kan zargin aikata haɗala a Cibiyar Fasahar Sufuri ta Kasa (NITT) da ke Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu a Jihar Kano. Mataimakin Kwamandan Hukumar, Mujahid Aminudeen, ya ce mutane — maza 27 da mata 35, “A ranar Lahadi, jami’anmu tare da haɗin gwiwar NDLEA suka su su 62 a cibiyar horarwa ta NITT da ke Dawakin Kudu, bayan samun bayanan sirri daga wasu masu kishin ƙasa.” Ya ce mutanen sun yi amfani da saukar ruwan sama da ake samu lokaci-lokaci a yankin don aikata  baɗala. “Muna amfani da wannan dama don gargaɗi ga matasa masu aikata abubuwan batsa da su daina, ko su fuskanci hukuncin doka. Hisbah ba za ta zauna ba tare da daukar...
    Gwamnatin Tarayya ta rage farashin jinyar ciwon ƙoda daga kimanin N50,000 zuwa N12,000 a Asibitocin Tarayya — ragin da ya kai kashi 76 cikin 100. Wannan saukin farashi ya samu ne bayan amincewar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, kamar yadda mai ba shi shawara kan harkokin sadarwa da manufofi, Daniel Bwala, ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin. Bwala ya ce hakan zai kawo saukin rayuwa ga dubban ’yan Najeriya da ke fama da cutar, wadda ke bukatar yin jinya sau da dama a kowane mako. “Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da tallafin tarihi domin rage farashin jinyar ciwon koda ga ’yan Najeriya. An rage farashin kowace wankin ƙoda daga N50,000 zuwa N12,000 kacal,...
    Ministan Ma’aikatar Kula da Kiwon Dabbobi, Alhaji Idi Mukhtar Maiha, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta amince da gina sabon asibitin dabbobi, da cibiyar ajiye dabbobi, tare da samar da allurar rigakafi a Jihar Kwara. Ministan ya bayyana hakan ne yayin gabatar da sakamakon nazarin taswirar fadin jihar(Geospatial Mapping) da aka gudanar  a Ilori babban birnin Jihar Kwara. Da yake wakiltar Ministan, Richard Mbaram ya bayyana wannan shiri a matsayin babbar nasara a tarihi wajen samo mafita ta dindindin ga rikicin manoma da makiyaya a ƙasar nan. Ya ce aikin na daga cikin tsare-tsaren Shirin Sauya Hanyar Kiwo na Kasa (National Livestock Transformation Plan) na tsawon shekaru goma (2019-2028) wanda ya mayar da hankali kan gyara harkar kiwo a Najeriya....
    A cikin jahohin da aka lissafa, Kebbi ce ta fi kowacce yawan garuruwa a jerin sunayen, inda take da garuruwa kusan 10 da suka hada da Kamba, Kangiwa, Kalgo, Ribah, Sakaba, Saminaka, Gwandu, Jega, da Birnin Kebbi. Gwamnatin tarayya ta fitar da sanarwar gargadin samun ambaliyar ruwa ga jihohi 15 daga cikin 19 na Arewa. Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya, wacce ta yi wannan gargadin a madadin gwamnatin tarayya, ta bayyana cewa dole ne a dauki matakan da suka dace a cikin al’ummomin da abin ya shafa. Sanarwar da Ma’aikatar Muhalli ta fitar ta ce, biyo bayan hasashen da ta yi na samun ruwan sama mai karfi a jihohin, za a iya samun ambaliyar ruwa tsakanin 10 ga Agusta zuwa 14...
    Gwamnatin Tarayya ta yanke shawarar dakatar da ƙirƙirar sabbin manyan makarantu har na tsawon shekaru bakwai masu zuwa a duk faɗin Nijeriya. Dakatarwar ta shafi ƙirƙirar sabbin jami’o’i, kwalejojin ilimi da kuma kwalejojin kimiyya da fasaha na tarayya kamar yadda Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta tabbatar. Tinubu zai tafi ziyarar ƙasashe 3 An naɗa sabon Sarkin Alkaleri a Bauchi Wannan mataki, a cewar Ministan Ilimi Dakta Olatunji Alausa, an ɗauke shi ne domin rage yawan makarantun da ba a amfani da su yadda ya kamata, lamarin da zai ba da damar mayar da hankali wajen gyara da inganta waɗanda ake da su yanzu. Da yake zantawa da manema labarai bayan taron na FEC a fadar shugaban ƙasa ranar Laraba,...
    Alausa ya ce dakatarwar, wacce ta shafi dukkan nau’o’in manyan makarantun gwamnatin tarayya an yi hakan ne da nufin dakatar da maimaici da barnatar da dukiyar gwamnati, inda za a yi amfani da kudin domin inganta makarantun da ake da su. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Majalisar Dokokin Jihar Zamfara karkashin jagorancin Bashar Aliyu Gummi, ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta hada kai da ayyukan tsaro a Jihar domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma, kamar yadda babi na biyu na kundin tsarin mulki ya tanada.   A zaman taron na ranar Talata, mambobin sun yi zargin cewa, ‘yan bindiga sun mamaye al’ummomi da dama a fadin jihar Zamfara, kuma sun zargi Gwamnan da mayar da hankali kan burin siyasa da kuma zargin abokan hamayya.   Sun kuma yi zargin cewa, Gwamnan bai kai ziyara ko aika tallafi ga al’ummomin da hare-hare ya shafa ba, inda suka ce ziyarar da ya shirya kai wa al’ummar Banga da ke karamar hukumar Kaura Namoda ta kasance da...
    Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bai wa Gwamnatin Tarayya ranakun 24, 25 da 26 ga watan Satumba domin ta kammala shari’ar da ta shafe shekaru goma tana yi wa tsohon mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Kanal Sambo Dasuki mai ritaya, kan zargin mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba da kuma halasta kuɗin haram. Mai shari’a Peter Lifu ya bayar da wannan umarnin a ranar Talata, bayan amincewa da buƙatar gwamnati ta ɗage zaman domin kawo ƙarin shaidu da kuma ba wa Dasuki damar fara kare kansa. Nijeriya ta sake ƙulla alaƙar tsaro da Isra’ila Tinubu na amfani da EFCC ya muzguna wa ’yan adawa — Atiku Ya kuma umurci gwamnati ta kira sauran shaidunta domin...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin Tarayya ta yi hasashen ruwan sama mai karfi da zai iya haifar da ambaliya a jihohi 15 na Arewacin Najeriya da wasu wurare 68, a cikin kwanaki biyar masu zuwa. Wannan gargadi ya fito ne daga Cibiyar Lura da Gargadin Ambaliya ta Kasa, karkashin Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya, inda aka bukaci hukumomi da al’umma su dauki matakan gaggawa don kare rayuka da dukiyoyi. Cibiyar ta bayyana jerin jihohi da wuraren da ambaliyar za ta iya shafa sun hada da: Adamawa: Jimeta, Mubi, Mayo-Belwa, Wuro-Bokki, Yola, Farkumo Bauchi: Jama’a Nasarawa: Keffi Kaduna: Jaji, Kafanchan, Zaria, Birnin-Gwari Katsina: Katsina, Bindawa, Kaita Kebbi: Kamba, Kangiwa, Kalgo, Ribah, Sakaba, Saminaka, Gwandu, Jega, Bunza, Birnin Kebbi, Bagudo, Argungu Kano: Bebeji, Gwarzo, Karaye, Sumaila, Tundun-wada...
    Sanarwar ta zayyana wasu fitattun garuruwa da al’ummomin da ka iya fuskantar mummunar ambaliyar ruwa da suka hada da Jimeta, Mubi, Keffi, Kafanchan, Birnin Kebbi, Minna, Gusau da Sakkwato.   A cikin jihohin da aka lissafa, Kebbi ce ta fi kowacce yawan garuruwa da aka fi tsammanin ambaliyar za ta yi kamari, ga su guda 10 kamar yadda ta bayyana: Kamba, Kangiwa, Kalgo, Ribah, Sakaba, Saminaka, Gwandu, Jega, da Birnin Kebbi.   Bokani ya bukaci mazauna yankin da hukumomin jihar da su dauki matakan kare rayuka da dukiyoyi cikin gaggawa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin...
    Kyari ya ce, a yanzu ana noma Waken Soya da ya kai kimanin tan miliyan 1.35, wanda kuma buƙatar da ake da shi a ƙasar ya wuce tan miliyan 2.7. Ya sanar da cewa, wanan tsari zai kuma amfani tattalin arziƙin ƙasar da ƙara samar da ayyuakn yi da kuma ƙara haɓaka samar da wadataccen abinci a ƙasar. Shi kuwa a nasa jawabin a wajen ƙaddamarwar, Gwamnan Jihar Biniwai, Hyacinth Iormem Alia, ya jaddada muhimmancin da za a amfana da shi a tsarin. “Dabarun faɗaɗa noman Waken Soya na ƙasa, mataki ne da ya dace wajen yin haɗaka, domin samar da kuɗaɗen shiga ga ƙasar a duk shekara da suka kai kimanin Naira tiriliyan 3.9 da ƙara ƙirƙiro da ayyukan...
    Idris ya ce a tsawon shekaru ‘yan Nijeriya suna tafiya Amurka saboda dalilai daban-daban, ciki har da yawon buɗe ido, kasuwanci, karatu, da kuma neman magani.   Ya ce: “An san Nijeriya a duniya a matsayin ƙasar da ‘yan ƙasar ta suke yawan yin tafiya zuwa ƙasashe daban-daban, suna hulɗa da ƙasashen duniya ta fuskar harkar kasuwanci, ilimi, yawon buɗe ido, da sauran muhimman fannoni. Amurka na ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin wuraren da ‘yan Nijeriya suka fi ziyarta, abin da ke nuna zurfin dangantaka mai tsawo tsakanin ƙasashen biyu.   “Yawancin ‘yan Nijeriya suna zuwa Amurka ne domin karatu, aiki, neman magani, ziyartar ‘yan’uwa, yawon buɗe ido, da damar zuba jari.   “Wannan mu’amala mai ƙarfi tana...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin tarayya ta ce tace a shirin ta sauya wuraren dake bushe a sassan arewacin Nijeriyaza a raba naira miliyan  miliyan 3.4 kuma akasarin wadanda zasu amfana da wannan za su kasance mata ta hanyar Shirin ACReSAL.   Da yake jawabi a wajen bude taron kwanaki 10 na masu ruwa da tsaki kan tsarin kula da tsare-tsare (SCMP) na sabbin magudanan ruwa guda 11 a fadin Jihohi bakwai na tarayya a Ilorin, kodinetan ayyukan ACRESAL na kasa, Mista Abdulhamid Umar, ya ce za a gudanar da aikin ne ta hanyar shirin kawo sauyi na dogon lokaci.   Jami’in kula da ayyukan na kasa na ACRESAL Adamu Shettima wanda ya samu wakilcin kwararre a bangaren kula da ayyukan ruwa na gwamnatin...
    Gwamnatin Tarayya ta gabatar da karramawar kasa da kuma tukuicin kudade ga kungiyar kwallon Kwando ta mata ta Najeriya, D’Tigress, bayan nasarar da suka samu a gasar cin kofin kwallon kwando na mata ta FIBA karo na biyar a jere.   A wata liyafar karrama su da aka yi a fadar shugaban kasa, mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, mai wakiltar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa kowane dan wasa zai karbi dala 100,000, yayin da koci da kungiyar kwararru za su samu dala 50,000 kowanne, tare da karramawar kasa ga daukacin kungiyar. Ya kuma yi alkawarin karin tukuicin da zai zo.   Shettima ya ce ba wai don murnar nasarar da kungiyar ta samu a cikin shekaru 78-64...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    “daidaita farashin ya kasance hanya daya tilo da za a iya amfani da ita wajen tafiyar da harkokin kasuwa da kuma tabbatar da gaskiya,” in ji shi. Edun ya nuna ƙalubale a tsarin biyan ciniki a Nijeriya, tare da lura da cewa har yanzu ana samun yawan hada-hadar kasuwanci ta hanyoyin da ba kamata ba. Ya bayyana cewa gwamnati na binciken gyare-gyare da nufin ƙara bayyana gaskiya, ciki har da yiwuwar gudanar da cinikin danyen mai daga ƙasashen waje da na naira. “Yawancin mu’amalar kasuwancinmu ana gudanar da su ne a waje da tashoshi na yau da kullun. Muna aiki kan gyare-gyaren da za su inganta tsarin,” in ji shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni...
    A cewar NANNM, sun dakatar da yajin aikin ne domin ci gaba da tattaunawa bisa alƙawarin da gwamnati ta ɗauka na aiwatar da buƙatun cikin ƙanƙanin lokaci. Takardar ta ce, “Kwamitin zartarwa na ƙasa ya yaba da matakan da gwamnatin tarayya ta fara ɗauka, musamman yadda ta bayyana lokacin da za ta aiwatar da buƙatunmu guda tara da muka gabatar.” Takardar da shugaban ƙungiyar NANNM, Kwamared Haruna Mamman, da sakataren janar, Dr. A. Shettima suka sanya wa hannu, ta umarci mambobinsu da su koma bakin aiki nan take. Haka kuma shugabannin na ƙasa za su ci gaba da lura da yadda gwamnati za ta cika alƙawuran da ta ɗauka. Ƙungiyar ta kuma gargaɗi duk wata cibiyar lafiya ko hukuma da...
    Jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara, ta bayyana matukar damuwarta kan yadda matsalar tsaro ke kara ta’azzara a jihar, inda ta bayyana hakan a matsayin abin ban tsoro da rashin fahimta.   A wata sanarwa dauke da sa hannun sakataren yada labarai na jam’iyyar, Yusuf Idris Gusau, jam’iyyar APC ta ce yawaitar ‘yan fashi da makami, garkuwa da mutane da kashe-kashe a Zamfara ya kai matakin da ba a taba ganin irinsa ba, yayin da ta zargi gwamnatin jihar a karkashin Gwamna Dauda Lawal da nuna halin ko in kula.   A cewar sanarwar, jam’iyyar ta damu matuka da wani faifan bidiyo na baya-bayan nan inda aka ga sama da mutane 200 mazauna Kaura Namoda suna rokon a taimaka musu biyo...
    Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karɓi baƙuncin ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Kiru da Bebeji na Jihar Kano, Abdulmumin Jibrin Kofa. Aminiya ta ruwaito cewa Kofa, wanda makusanci ne ga jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, kuma ɗaya daga cikin jiga-jigai a jam’iyyar NNPP, ya ziyarci shugaban ƙasar ne a yau Laraba. Za a kammala shimfiɗa layin dogo daga Kaduna zuwa Kano a 2026 — Gwamnatin Tarayya Tattalin arzikin Nijeriya zai ci gaba da bunƙasa har zuwa baɗi — IMF Har yanzu dai babu wasu bayanai dangane da abin da suka tattauna, amma ziyarar wadda hadimai daga ɓangarorin biyu suka riƙa yaɗawa na ci gaba da ɗaukar hankalin jama’a.
    Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa za ta kammala aikin shimfiɗa layin dogo wanda ya taso daga Kaduna zuwa Kano a cikin shekarar 2026 mai zuwa. Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris ne ya bayyana hakan cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a yau Laraba. Kazalika, takwaransa na sufuri, Sa’idu Ahmed Alkali ya jaddada hakan ne a yayin jawabinsa a wajen wani taron tuntuɓa tsakanin ’yan ƙasa da gwamnati da ke gudana a Jihar Kaduna. Tattalin arzikin Nijeriya zai ci gaba da bunƙasa har zuwa baɗi — IMF Tinubu ya naɗa sabon shugaban hukumar kashe gobara ta ƙasa A cewar ministan, lokacin da Shugaba Bola Tinubu ya hau mulki kashi 15 cikin 10 na aikin kawai aka...
    An shawarci gwamnatocin jihohin Sakkwato, Kebbi da Zamfara da su kirkiro hanyoyi na wayar da kan al’umma dangane da shirye-shiryen tallafi da ayyukan ci gaba da gwamnatin tarayya ke aiwatarwa domin bunkasa tattalin arziki da tabbatar da tsaro a yankunansu. Shugaban sashen kimiyyar zamantakewa na Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato, Farfesa Chika Umar Aliyu, ne ya bayar da wannan shawara yayin gabatar da takarda a wajen taron shekara-shekara na kungiyar Nigerian Institute of Management reshen jihar Sokoto na shekarar 2025, wanda aka hada da gabatar da lambar yabo ga wadanda suka cancanta.   Farfesa Chika ya bayyana cewa, gwamnati tarayya na da shirye-shiryen tallafi da dama da suka hada da na noma, kasuwanci da kuma koyar da sana’o’in hannu...
    Don haka nema tayi kira da jama’a kada suyi amfani da shi labarin daya zaman a kanzon kurege da ake ta yadawa,idan wani bayani suke bukata su tuntubi kafa da suka san ba zata yi zuki ta malle ba,ko kuma jami’an ma’aikatar ilimi ta kafar sadarwarsu ko kuma na, WAEC, da NECO. “An ja hankalin ma’aikatar ilimi ta tarayya akan wani labara ko rahoton da ya karade kafafen sadarwa na zamani,inda aka yi maganar cewar ban soke jarabawar WAEC ta shekarar 2025 da aka yi saboda an samu laifin aikata magudi lokacin da ake yin ta. “Ma’aikatar tace don haka tana sanar da jama’a cewa ta yi nesa da kanta,dangane da ita sanarwar ko labarin saboda kuwa ai na kanzon...
    “Dole ne kasar nan ta samar da wata sabuwar hanya, domin samar da Kifin da zai wadace ta, wanda hakan zai kuma taimaka matuka wajen rage dogaro da shigo da Kifin daga kasashen waje da kuma kara habaka fannin” in ji Ministan. Oyetola ya kara da cewa, gwamnatin tarayya ta himmatu kwarai da gaske wajen bai wa fannin goyon bayan da ya dace, musamman ta hanyar yin amfani da tsarin kimiyyar fasahar zamani da kuma zuba makudan kudade a fannin. Kazalika, ya jaddada cewa; gwamnatin tarayya za ta kara kaimi wajen ganin ana samar da wadataccen Kifi a kasar, musamman domin rage dogaro a kan wadanda ake shigowa da su daga kasashen ketare, duba da cewa; fannin na bayar da...
    Kwamitin ya nemi a mayar da sama da Naira miliyan 124, kusan dala 795,000 zuwa asusun gwamnatin tarayya, an kuma bayar da karin wasu kudade da suka hada da Naira miliyan 31.7 da dala 155,923.00, a matsayin wadanda aka kashe ba bisa ka’ida ba. An umarci ma’aikatar da ta kwato Naira miliyan 49.4 da aka biya, domin yin gyaran ba tare da bin ka’idojin sayen kayayyakin ba. Kazalika, an raba Naira miliyan 9.2 ga jami’an ofishin jakadancin, ba tare da cikakkiyar shaida ba. Haka nan kuma, an binciki bankin noma; kan basussuka kimanin Naira biliyan 75.6. Kwamitin ya umarci hukumar da ta buga jerin sunayen wadanda ake bi bashi a akalla a jaridu guda uku na wannan kasa tare da...
    A cewar ministan, shi da sauran abokan aikin sa, Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Ali Pate, da Ministan Kuɗi, Mista Wale Edun, sun halarci bikin ƙaddamar da ɗaya daga cikin manyan ayyukan, wanda ya gudana a Jihar Katsina.   Cibiyoyin da aka ƙaddamar na cikin zagaye na farko na shirin gina sababbin cibiyoyin maganin ciwon daji guda shida a manyan Asibitocin Koyarwa na Tarayya a ƙasar nan.   Wannan cigaba wani muhimmin mataki ne wajen rage wahalar da marasa lafiya ke fuskanta wajen samun ingantacciyar kulawa, da kuma hana fita ƙasashen waje don neman magani.   Gwamnatin ta tabbatar da cewa sauran cibiyoyin da suka rage za su kammala nan ba da jimawa ba domin cika alƙawarin samar da ingantaccen tsarin...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran Dr. Isma’ila Baka’i ya ce; Amincewa da aikata zalunci, ya yi daidai da hada baki da mai aikata shi.” Kamfanin dillancin labarun “Mehr” ya nakalto Dr. Baka’i wanda ya wallafa sako a shafinsa na X cewa; Shugaban gwamnatin kasar Jamus yana ci gaba da nuna goyon baya ga munanan ayyukan da HKI take aikatawa wanda yake cin karo da yarjeniyoyin MDD da kuma dokokin kasa da kasa.” Haka nan kuma Dr. Baka’i ya ce; Abinda Jamus din ta aikata zai mayar da ita wacce za ta amsa tambayoyi a matsayin wacce take yin zuga a aikata laifi. A lokacin da HKI ta fara kawo wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran hare-hare dai shugaban...
    Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Gashuwa (FUGA) a jihar Yobe za ta gwangwaje Uwargidan Shugaban Sasa, Sanata Remi Tinubu, da gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, da wasu fitattun ’yan Najeriya shida da digirin girmamawa. A cewar jami’ar, za a ba su shaidar ce saboda gudunmawar da suka bayar a bangarori da daman a ci gaban kasa. Mataimakiyar Shugabar Jami’ar, Farfesa Maimuna Waziri ce ta bayyana hakan a lokacin da take ganawa da manema labarai a jami’ar. Isra’ila ta kashe Falasdinawa 24 a Zirin Gaza Ba Tinubu kaɗai ne ya sa Buhari ya ci zaɓe a 2015 ba – Boss Mustapha Ta ce za a karrama su ne a yayin bikin yaye dalibai karo na farko na jami’ar da zai gudana...
      Tsohon ɗan takarar gwamna ƙarƙashin jam’iyyar CPC ta shuɗe a Jihar Kaduna, Alhaji Haruna Sa’eid Kajuru, ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta gudanar da cikakken bincike kan kisan da aka yi wa wasu mazauna Zariya da suka je dauren aure a Jihar Filato kwanan nan.   Alhaji Kajuru ya yi wannan kira ne a lokacin da ya kai ziyara ta jaje ga iyalan waɗanda suka rasa ‘yan uwansu a Zaria, inda ya nuna alhini da ta’aziyya ga dangin waɗanda wannan al’amari ya shafa.   Tsohon Akanta Janar na Jihar Kaduna, Alhaji Haruna Kajuru, ya yi Allah-wadai da kisan, yana mai jaddada cewa babu wani mutum ko ƙungiya da ke da ikon da kundin tsarin mulki ya ba shi na kashe...
    Wannan matakin ya biyo bayan shawarar Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) na ASUU wanda ya amince da tsarin “Ba Albashi, Ba Aiki” saboda yawan jinkirin biyan albashi da suke fuskanta. ASUU ta ɗora laifin hakan kan Ofishin Akanta-Janar na Tarayya. Shugaban ASUU na ƙasa, Farfesa Chris Piwuna, ya bayyana a ranar Litinin cewa gwamnatin na nuna halin ko-in-kula kan batun. Ya ce duk da yawan ganawa da jami’an gwamnati, malamai na fuskantar jinkirin albashi ba tare da wani dalili ba. “Muna so mu yi aiki, amma ba za mu iya ba saboda ba su ba mu damar yin haka ba. Wannan aiki ne da aka yi da gangan. Matsalar ba daga wajen tsarin biyan albashi ba ne, matsalar tana wajen...
    Shugaban kasa Bola Tinubu ya ce gwamnatin tarayya za ta gudanar da aikin samar da wutar lantarki ga jami’ar tarayya ta Kashere da ke jihar Gombe domin tabbatar da samar da isasshen wutar lantarki domin inganta harkokin ilimi.   Shugaban ya bayyana hakan ne a wajen taron hadaka karo na uku na jami’ar tarayya ta Kashere da ke karamar hukumar Akko a jihar Gombe.   Shugaba Bola Tinubu ya kuma bayyana cewa ma’aikatar albarkatun ruwa ta tarayya za ta fara aikin gina madatsar ruwa a kogin Kashere domin tallafa wa shirin koyar da aikin gona na jami’ar da inganta samar da ruwa ga al’ummomin da ke kewaye.   Ya jaddada kudirin gwamnatinsa na inganta samar da ingantaccen ilimi ta hanyar...
    Cikin tawagar akwai Ministan Shari’a kuma Antoni Janar na Ƙasa, Yarima Lateef Fagbemi, SAN; a Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris; da Ƙaramin Ministan Harkokin Gidaje da Cigaban Birane, Hon. Yusuf Abdullahi Ata; da kuma Hassan Abdullahi, Daraktan Tsaro na Cikin Gida a ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro (NSA), wanda ya wakilci NSA. Wasu fitattun malamai na addinin Musulunci da suka kasance cikin tawagar sun haɗa da Dakta Bashir Aliyu Umar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, da Limamin Masallacin Ɗantata da ke Abuja, Khalifa Abdullahi Muhammad. Jami’an Ofishin Jakadancin Nijeriya da ke Jiddah sun haɗu da tawagar, ƙarƙashin jagorancin Ambasada Ibrahim Modibbo, tare da Ambasada Mu’azzam Ibrahim Nayaya, da Manjo Janar Adamu Hassan,...
    Babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta sanya ranar 22 ga watan Yulin wannan shekara domin sauraron bukatar ba da belin da Tukur Mamu, da ake zargi da daukar nauyin ta’addanci Mai shari’a Mohammed Umar ya tsayar da ranar ne biyo bayan dage shari’ar da lauyan Manu, Johnson Usman, SAN, ya nema, domin ba shi damar yin nazari tare da ba da amsa da ya dace kan karar da lauyan gwamnatin tarayya, David Kaswe ya shigar a kansa. A cikin bukatar da Mamu ya gabatar a jiya Litinin 30 ga watan Mayu, ya nemi a bayar da belinsa dsaboda yanayin rashin lafiyarsa. Gwamnan Bauchi zai ƙirƙiro sabbin masarautu NAJERIYA A YAU: Halin da al’ummar Mokwa ke ciki wata guda bayan...
    A bisa jagorancin Alhaji Mustapha Junaid, iyalan mamacin, da suka haɗa da matan sa da ‘ya’ya da jikokin sa, sun tarbi tawagar, kuma sun yi masu godiya. Minista Badaru ya miƙa saƙon ta’aziyya daga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana cewa, “Rasuwar Baba Aminu ta taɓa Shugaba Tinubu matuƙa. Yana addu’ar Allah ya yi masa sakayya da gidan Aljannar Firdausi, kuma yana ba dukkan iyalan sa haƙurin su yi jimirin jure wannan babban rashi.” Jakaden Nijeriya a Saudi Arebiya, Ambasada Ibrahim Modibbo, da Babban Jagoran Aikin Jakadanci, Ambasada Mu’azam Ibrahim Nayaya, da Jami’in Kula da Tsaro a Ofishin Jakadanci, Manjo Janar Adamu Hassan, duk suna cikin tawagar. Malaman da aka je da su kuma duk sun yi addu’o’i ga marigayi...
    Ya ce a tare da shi a cikin tawagar, akwai Ministan shari’a, Antoni-janar na tarayya, Yarima Lateef Fagbemi, SAN; Ministan yaɗa labarai, Alhaji Mohammed Idris, da ƙaramin Minista a ma’aikatar gidaje, Hon. Yusuf Abdullahi Ata. Tawagar ta kuma haɗa da wasu manyan Malamai, waɗanda suka ƙunshi, Dr Bashir Aliyu Umar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa da Limamin masallacin Ɗantata da ke Abuja, Khalifa Abdullahi Muhammad.   Daga nan ma’aikatan ofishin Jakadancin Nijeriya da ke Jidda, ƙarƙashin Jakada Mu’azzim Ibrahim Nayaya, wanda da ma shi ke kai-kawo wajen shirya yadda jana’iazar za ta gudana, duk sun haɗu da tawagar don gudanar da ita a yau Litini.   Alhaji Ɗantata dai ya rasu ne a Abu Dhabi ta Haɗaɗɗiyar Ɗaular Larabawa...
    Ya nemi ‘yan jarida da su riƙa amfani da kafafen su wajen haska labarai da ke nuna sauye-sauyen da aka samu a hukumomi, yadda jama’a ke shiga cikin harkokin gwamnati, cigaban ababen more rayuwa da bunƙasar tattalin arziki, a matsayin wani ɓangare na rawar da kafafen ke takawa wajen ƙarfafa dimokiraɗiyya. “Yayin da muke bikin shekaru 26 na ci gaba da mulkin dimokiraɗiyya a Nijeriya, dole ne kafafen yaɗa labarai su riƙa yaɗa labaran da ke bayyana nasarorin da dimokiraɗiyyar ƙasar nan ta samu, irin su gyaran hukumomi, gina ababen more rayuwa, shiga jama’a cikin harkokin gwamnati, da kuma cigaban tattalin arziki,” inji shi. Idris ya ƙara da cewa yayin da kafafen yaɗa labarai suke haska waɗannan nasarori ta hanya...
    “Za a sauƙaƙe hakan ne ta hanyar Bankin Raya kasa na KfW da Asusun Kalubalan Kasuwancin Afirka.”   An gudanar da bikin sanya hannun ne a ofishin ministan kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arziki, Abubakar Bagudu, wanda ya wakilci Nijeriya.   Sakatare na farko kuma shugaban hadin gwiwar raya kasa a ofishin jakadancin Jamus a Nijeriya, Dr Karin Jansen, da wakilin bankin raya kasa na KfW, Gerald Keuhnemund, duk sun halarci rattaba hannun. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    An samu rahoton cewa guguwar ruwan sama ta yi ɓarna a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya (Federal Polytechnic), Idah a Jihar Kogi, inda ta ɓarnata  kadarori da gine-gine da dama. Rahoton na cewa, wata mummunar guguwar ruwan sama da ta biyo bayan ruwan sama da aka kwashe tsawon sa’o’i ana yi a ranar Laraba ce ta haddasa barnar, inda ta lalata rufin gine-gine da tagar gine-gine da dama a makarantar. Tinubu na ƙaddamar da wasu ayyuka a Jihar Kaduna Za a dawo da dukkan Alhazai gida ranar 28 ga Yuni – NAHCON Ana cikin haka, an ba da rahoton cewa ɗakunan karatu da ɗakunan gwaje-gwaje da ɗakunan kwanan ɗalibai da ke cikin harabar kwalejin  guguwar ruwan saman ta haddasa...
    Haka kuma, an ce ta ƙara da cewa: “Mu tambayi Shugaban Majalisar Dattawa, me ya sa ya janye jami’an tsarona tun farko, idan ba don ya sa a kai min hari ba? Ya ce a kashe ni, amma a kashe ni a Kogi.” Gwamnati ta bayyana cewa waɗannan kalaman suna da nufin ɓata suna, kuma hakan ya saɓa da Sashe na 391 na Dokar Laifuka 89, Dokokin Tarayya na shekarar 1990. Hukuncin laifin yana ƙarƙashin Sashe na 392 na wannan doka. A wani tuhumar daban, an zargi Sanata Natasha da yin irin waɗannan kalaman game da Akpabio a cikin wata tattaunawa ta waya da wata Sandra C. Duru a Abuja, a ranar 27 ga watan Maris, 2025. An ƙara tsaurara...
    Ya ce duk da cewa akwai damuwa kan yadda za a aiwatar da hakan, Gwamnatin Tarayya na da damar tsara ƙa’idoji da dokoki na musamman ga kowace jiha don hana amfani da ‘yansandan wajen cin zarafi. A halin yanzu, gwamnonin jihohi daga faɗin Nijeriya na gudanar da wani taron gaggawa a Babban Birnin Tarayya, wanda ke gudana a sakatariyar Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF). Taron ya samu halartar gwamnonin jihohi da mataimakansu daga dukkanin jihohi 36 na ƙasar. Koda yake ba a bayyana cikakken ajandar taron ba, kasancewar mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, da Ministan Tsaro, Mohammed Badaru, na cikin mahalarta taron, ya nuna cewa batutuwan tsaro ne ke kan gaba a tattaunawar. Taron na...
    Sanarwar ta ƙara da cewa ana aiki tare da hukumomin cikin gida da na ƙasa da ƙasa domin ganin an gudanar da aikin kwasar cikin tsaro. Sanarwar ta ce: “Ma’aikatar Harkokin Waje na sanar da jama’a cewa, sakamakon rikicin da ke ƙara ƙamari tsakanin Isra’ila da Iran, Gwamnatin Tarayya tana shirin ƙarshe na kwaso ‘yan Nijeriya da suka maƙale a waɗannan ƙasashe. “Saboda haka, ana shawartar dukkanin ‘yan Nijeriya da abin ya shafa da su kiyaye matakan tsaro da kuma tuntuɓar ofishin jakadanci mafi kusa domin yin rijista da samun ƙarin umarni.” Baya ga haka, Gwamnatin Tarayya ta sake kira da a dakatar da faɗa tsakanin Isra’ila da Iran, tare da buƙatar ɓangarorin su rungumi tattaunawa, su mutunta dokokin kare...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin Tarayya ta roƙi ƙasashen Isra’ila da Iran da su daina rikici, su zauna lafiya su sasanta tsakaninsu.  A wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Waje ta fitar, ta bayyana damuwa kan yadda rikicin ke ƙara ta’azzara, inda ta nemi ɓangarorin biyu da su kai zuciya nesa don samar da zaman lafiya a duniya baki ɗaya. Mahara sun kashe mutum 26 a sabon hari a Binuwai Mulkin Tinubu ya fi kowane muni tun bayan dawowar mulkin farar hula — Dalung Sanarwar ta ce faɗa da ramuwar gayya na jefa rayukan fararen hula cikin hatsari, kuma yana iya haddasa rikici mai muni a yankin Gabas ta Tsakiya, wanda hakan zai iya barazana ga tsaron duniya da kuma ci gaban tattalin arziƙi dunuya....
    Gwamnatin Tarayya ta roƙi ƙasashen Isra’ila da Iran da su daina rikici, su zauna lafiya su sasanta tsakaninsu.  A wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Waje ta fitar, ta bayyana damuwa kan yadda rikicin ke ƙara ta’azzara, inda ta nemi ɓangarorin biyu da su kai zuciya nesa don samar da zaman lafiya a duniya baki ɗaya. Mahara sun kashe mutum 26 a sabon hari a Binuwai Mulkin Tinubu ya fi kowane muni tun bayan dawowar mulkin farar hula — Dalung Sanarwar ta ce faɗa da ramuwar gayya na jefa rayukan fararen hula cikin hatsari, kuma yana iya haddasa rikici mai muni a yankin Gabas ta Tsakiya, wanda hakan zai iya barazana ga tsaron duniya da kuma ci gaban tattalin arziƙi dunuya....
    Ma’aikatar Gona da tsaron abinci ta tarayya ta sanar da gudanar da addu’a da azumi na kwanaki uku domin neman taimakon Allah wajen kare ƙasar nan da kuma tabbatar da wadatar abinci. Wannan na ƙunshe ne a wata takarda da aka fitar a ranar 11 ga Yuni, 2025, wadda Daraktar Gudanarwa, Mrs. Adedayo Modupe O., ta sanya wa hannu. A cewar sanarwar, dukkanin daraktoci, da mataimakan daraktoci, da shugabannin sassan sarrafa kayayyakin amfanin gona da sauran ma’aikatan ma’aikatar za su halarta. An sanya wa wannan shiri suna “Neman Taimakon Ubangiji Don Kariya da Cigaban Kasa.” Kudaden Da Ake Karba A Kogin Hadejia Jama’are Daga Hannun Manoma, Ba Haraji Ba Ne – HJRBDA Gwamnatin Gombe Ta Yi Albishir Ɗin Gina Babban...
    Biyo bayan sauya sheka da aka yi kwanan nan, a zauren majalisar dattawa, APC na da kujeru 68; PDP na da 30; LP na da 5; SDP na da 2; NNPP na da 1; APGA na da 1 da kuma kujeru guda biyu da babu kowa, guda daya daga Jihar Edo da daya daga Jihar Anambra. Masana harkokin siyasa na ganin cewa bisa yadda lamura suke a halin yanzu, adadin na iya haurawa lokacin da majalisar tarayya ta dawo daga hutu, bayan sauya shekar Gwamna Umo Eno na Jihar Akwa Ibom daga PDP zuwa APC. Ana sa ran wasu daga cikin ‘yan majalisar tarayya na jihar za su iya bin sahunsa. A halin yanzu, Jihar Akwa Ibom tana da sanatan...
    Ya yabawa hukumar bisa yadda ta aiwatar da dokar da ta ba da damar, ‘Dokar Ci Gaban Man Fetur da Gas ta Nijeriya (NOGICD) ta 2010. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Da yake maida martani, Mokwa ya ce gwamanti ta fara biyan bashin tallafin rage radadin ga ma’aikata. Ya ce za a ci gaba da biyan kudin ne kashi-kashi har zuwa nan da watanni hudu masu zuwa. “Mun fara biyan bashin nira 35,000 ga ma’aikata. Illar kawai wasu ma’aikatu da suka kasance masu cin kashin kansu da suke biyan tallafin kai tsaye, misali, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa. “Amincewa da tallafin naira 35,000 ga ma’aikata shi ne mafita ta wucin gadi da gwamnatin tarayya ta yi kafin amincewa da mafi karancin albashi na naira 70,000. “Wannan ya faru a cikin watanni biyar, amma kungiyar kwadago ta ce ba a fara biya a kan lokaci ba, yanzu kenan akwai bashin...
    Ya ce Jihar Kurus Ribas ita ce ta farko a yankin kudu da ta shiga a dama da ita a harkar noman alkama, lamarin da ke nuni da gayar nasara wajen samar da abinci a kowani sassa na kasar nan. Kyari ya kara da cewa shirin rabar da takin zamani ya taimaka wajen bunkasa samar da shinkafa zuwa tan 58,000, lamarin da ya bai wa gwamnatin tarayya sanya tallafi a bangaren rabar da shinkafa ga jihohin da ambaliyar ruwa ta shafa. Ministan ya ce akwai bukatar kare masu amfani da kuma kayan da ake nomawa, “kaso 80 cikin 100 na abincinmu manoman cikin gida ne suka samar da su.” A daidai gabar da ake hasashen adadin ‘yan Nijeriya zai kai...
    Tinubu ya bayyana cewa, aikin titin, wanda aka yi watsi da shi tuni duk da muhimmancin titin a cikin taswirar Abuja, amma yanzu ya kammalu a karkashin jagorancin Ministan babban birnin tarayya.   Shugaba Tinubu ya yi addu’ar Allah ya bai wa babban birnin tarayya zaman lafiya, da ci gaban Nijeriya, da kuma bai wa sojojin Nijeriya aminci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Jimillar fursunoni: 80,879 Adadin cibiyoyin gyaran hali: 256 Kashi na rijista da aka kammala: 74% Umar ya jaddada cewa sauran fursunonin da ba a yi wa rijistar ba za a cigaba da yi musu, kuma an kafa duk wasu hanyoyi da za su tabbatar da nasarar kammala aikin cikin sauki. Hukumar ta bayyana wannan aikin a matsayin wani muhimmin mataki na inganta tsarin dijital, da sake gyaran rayuwa, da shigar da fursunoni cikin tsarin ƙasa. Ya kuma buƙaci kafafen yaɗa labarai da su tabbatar da sahihancin bayanansu daga hukumomin da suka dace kafin wallafawa domin kaucewa yaɗa bayanan da za su iya dagula fahimtar jama’a ko rage ƙwarin gwuiwar al’umma. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan Bunƙasa Harkokin Ƙarafa, Shuaibu Abubakar Audu, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya na samun ci gaba wajen farfaɗo da tsohon kamfanin ƙarafa na Ajaokuta da ke Jihar Kogi. Ya bayyana hakan ne a wani taro da ya gudanar da manyan jiga-jigan jam’iyyar APC na Jihar Kogi a garinsu Ogbonicha da ke Ƙaramar Hukumar Ofu. Mutum 9 sun rasu a hatsarin mota a Jigawa Magidanci ya shiga hannu kan kashe matarsa mai juna biyu da duka Ministan, ya ce Gwamnatin Tarayya ta riga ta rattaba hannu kan yarjejeniya da kamfanonin da za su samar da kayan aikinkamfanin. Ya ƙara da cewa gwamnati na ƙara neman masu saka hannun jari daga ƙasar China domin su zuba jari a kamfanin. “Muna yin aiki...
    A jawabinsa a wajen taron kaddamar da tsarin tattaunawa kan shirin yin amfani da fashar zamani na samar da yin rjitsar ta manoman kasar (NDFR), wadda aka gudanar a babban birnin tarayyar Abuja, Babban Sakatare a Ma’aikatar Aikin Noma da Samar da Wadataccen Abinci, Dakta Marcus Ogunbiyi, ya bayyana cewa; sabon tsarin zai taimaka matuka, wajen rage duk wani matsayi da manoman kasar suke ciki, musamman manoman da ba su mallaki wata gona ba. “Za mu tabbatar mun yi rijistar sunayen manoman kasar da kuma gonakinsu, sannan kuma ba wai kawai yin rijistar ba, har da irin nau’in amfanin da suke nomawa da kuma nau’in irin kasar da ke gonakin nasu,” in ji Marcus. Dakta Marcus ya kara da cewa,...
    Domin shawo kan wannan matsalar, ministan ya zayyana kokarin da ake yi a karkashin dabarun bunkasa kiwon dabbobi na kasa, wanda ya mayar da hankali kan ginshikai guda 10 da suka hada da bunkasa kimar dabbobi, inganta kiwo, kiwon lafiyar dabbobi, samar da kudi, sauya salon kiwo da karfafawa matasa da mata gwiwa kan dogaro da kai. Maiha ya yi tunin cewa zuwa yanzu ma’aikatar ta samu cimma wasu nasarori da suka hada da yin rajistar nau’in kiwo guda takwas, “na farko a cikin shekaru 48” da kuma samar da wani shiri na kasa kan albarkatun halittun dabbobi tare da hadin gwiwar FAO. “Dabbobinmu na cikin gida suna samar da lita 1-2 na madara a kullun, idan aka kwatanta da...
    Ya ce an samu yawan mace-macen ne saboda rashin bin umarnin gargadin ambaliyar ruwa daga mutane a jihar. Ya bukaci jihohi su dauki matakai don hana mummunar ambaliyar ruwa da ka iya lalata rayuka da kadarori, ministan ya ce, “Ma’aikatar Tarayya ta Albarkatun Ruwa da Tsabtace Muhalli tana mika ta’aziyya ga gwamnatin da al’ummar Jihar Neja, musamman ga al’ummomin da lamarin ya shafa a Mokwa, wadanda suka fuskanci asara, mutuwa da canjin wuri sakamakon wannan bala’i na ambaliyar ruwa. “Ina jaddada cewa ambaliyan da aka samu ba ta kasance saboda sakin ruwa daga dam din Kainji ko Jebba ba ne, domin duka dam din suna cikin tsaro. “Mun yaba da kokarin gaggawa na gwamnatin Jihar Neja da hukumomin yankin, da...
    Ministan ya bayyana gabatarwar da C-WINS ta yi a matsayin mai motsa zuciya kuma mai cike da ƙarin haske. Ya ce: “A yau na koyi abubuwa da dama. Yawancin ’yan Nijeriya, kamar ni kai na, sun san cutar masassarar cizon sauro amma ba su san da ƙyandar jamus da mummunan tasirin ta ba. “Gaskiya batun cewa za a iya haihuwar yara makafi, kurame ko kuma masu nakasar zuciya sakamakon kamuwa da ƙyanda daga uwa a lokacin ɗaukar ciki babbar masifa ce da ya kamata mu haɗa kai mu daƙile ta.” Ya ƙara da cewa ma’aikatar za ta haɗa hannu da sauran hukumomin da suka dace wajen tsara saƙonnin faɗakarwa da shirye-shiryen ilimantar da al’umma. Ya kuma shawarci tawagar da su...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumomi na roƙon mazauna yankunan da ambaliya ta shafa da su bi umarnin kwashe jama’a daga yankunan da ke cikin haɗari tare da haɗa kai da jami’an agaji don tabbatar da tsaron lafiyar kowa da kowa. A cikin sanarwar, Gwamnatin Tarayya ta miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasu, tare da jaddada cewa al’ummar ƙasar nan suna tare da su a wannan lokaci na jimami, kuma ba za a yi ƙasa a gwiwa wajen tallafa masu ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Jami’ar Jos ce ta zama gwarzon gasar wasannin ma’aikatan jami’o’in Nijeriya karo na 14 (NUSSA), wadda Jami’ar Bayero da ke Kano ta karɓi bakuncinta. Jami’ar ta Jos ta lashe lambobin yabo guda 13, ciki har da Zinare 7, Azurfa 3 da Tagulla 3, wanda ya ba ta damar darewa saman teburin nasarori. A matsayi na biyu kuma, Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria, ta samu nasarar lashe lambobin yabo 12 – zinare 6, azurfa 3 da tagulla 3. Jami’ar Tarayya ta Dutsinma ta zo ta uku da zinare 4, azurfa 4 da tagulla 5. Gasar Wasanni Ta Kasa Wata Hanya Ce Ta Hada Kan Matasan Nijeriya– Obasanjo Kyawawan Halayen Annabawa Da Ke Nuni Da Cikarsu (AS) Babban abin da ya dauki hankali...
    Ya ce a nemi bayani daga wurare daban-daban kamar Kungiyar Ma’aikatan Kananan Hukumomin Nijeriya (NULGE) da Ma’aikatar Kudi, ya kara da cewa sakataren gwamnatin tarayya shi ne shugaban kwamitin aiwatar da hukuncin. Abubuwan da mutane yawa suke gnin ya janyo jinkirta aiwatar da hukuncin shi ne, shigar da sabon sharadi daga Babban Bankin Nijeriya (CBN), wanda ke bukatar dukkanin hukumomin gwamnati 774 su bayar da akalla shekaru biyu na rahotannin kudinsu kafin su iya karbar kasafin kudadensu kai tsaye daga asusun gwamnatin tarayya. Babban bankin ya bayyana cewa dole ne gwamnatocin kananan hukumomi su cika bukatun kafin su bude asusu don kura musu kudadensu kai tsaye. Ka’idojin da aka gindaya wa kananan hukumomin ya kara janyo tsaiko wajen jinkirta aiwatar...
    “Ina isar da wannan sakon ba wai a matsayina na tsohon shugaban kasa ba, har ma a matsayina na dan jihar Ogun cike da alfahari, na kasance tare da ku a lokacin bikin bude gasar, na kalli wasannin a cikin dakina, kuma hakika wasannin sun nuna cewa ba wai kawai wasanni ba ne, alama ce ta hadin kai, baje kolin hazaka, da kuma kishin kasa.   “Daga karshe Obasanjo ya jinjinawa jihohi 36 na tarayya da babban birnin tarayya, da kuma kananan kungiyoyin da aka gayyata bisa jajircewarsu, inda ya kara da cewa, kwamitocin da suka shirya gasar, abokan hadin gwiwa, da masu aikin sa kai na hukumar wasanni ta kasa sun cancanci a yaba musu saboda mayar da wannan...
    A wani babban ci gaba na kawo sauyi a tsarin kiwon lafiyar Najeriya, gwamnatin tarayya ta yi  ta kaddamar da ayyuka 16 a asibitin masu tabin hankali na gwamnatin tarayya dake Kware a jihar Sokoto.   Da yake jawabi a wajen bikin kaddamarwar, Ministan Kasa a ma’aikatar Lafiya da walwalar jama’a, Dokta Iziak Salako, ya jaddada cewa ayyukan na daga cikin ajandar sabuwar fata ta gwamnati shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na karfafa cibiyoyin kiwon lafiya na kasa.   Ya ce FG ta himmatu wajen samar wa asibitoci kayayyakin more rayuwa, kayan aiki da kudade, da tallafi don inganta ayyukan hidima a fadin kasar.   Dakta Salako ya ci gaba da bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta samar da muhimman ayyuka...
    Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da ɗaga darajar Kwalejin Kimiyya da Kere-kere ta Tarayya da ke Kabo a jihar Kano, zuwa Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Tarayya, Kabo. Wannan cibiyar ilimi, wacce aka kafa a shekarar 2022, yanzu ta zama jami’a ta uku ta gwamnatin tarayya a jihar, bayan Jami’ar Bayero Kano da kuma Jami’ar Ilimi ta Tarayya da aka assasa a  kwanan nan, wacce aka sanya wa sunan marigayi Yusuf Maitama Sule. Matashi ya shiga hannun ’yan sanda kan kisan matar aure a Kano Tinubu zai ciyo bashin Naira tiriliyan 39 daga kasashen waje Kano na kuma da jami’o’o’i biyu mallakin gwamnatin jiha. Wannan ci gaban ya zo ne a daidai lokacin da ake fama da damuwa...
    “Fanin na kuma taimaka wa wajen samar da ayyukan yi da samar da abinci mai gina jikin Dan’adam da kuma bunkasa hada-hadar kasuwanci, musamman duba da wayar da kai da ake yi na samar da abinci mai gina jiki,“ in ji shi. Shi ma, a nasa jawabin a wajen taron, Daraktan Cibiyar Bunkasa Samar da Takin Zamni ta Kasa da Kasa (IFDC) da ke kasar nan, Dakta Yusuf Dramani ya bayyana cewa; cibiyar na aiki kafada da kafada da Hukumar NIRSAL, musamman don cike gibin da ake da shi a kasar, wajen samar da rancen kudaden noma ga manoman kasar. “Duk da cewa, fannin aikin noma na kasar nan, na bayar da gagarumar gudunmawa wajen kara bunkasa fannin tattalin arzikin...
    Ministan ya kuma zayyano jerin shirye-shiryen da gwamnatin tarayya ta kirkiro da nufin zaburar da matasa rungumar kiwon dabbobi, musamman don samun riba ciki har da sama musu hektar noma 51,000, a karkashin hadaka da shirin fitar da kaya na ‘Gulf’ na jihohi da kuma shirye-shiryen farfado da guraren kiwon dabbobi 417 a daukacin fadin kasar nan. “Muna da abubuwan da za mu yi amfani da su a kasar nan, domin yakar yunwa a fadin kasar baki-daya,” in ji Ministan. “Akalla a kasar nan, muna da Shanu kimanin miliyan sha biyar da Tumakai miliyan 60 da Kaji da miliyan 600 da Akuyoyi da miliyan 1.4 da Rakuma miliyan 700,000 tare kuma da kasar noma, amma sai dai har yanzu, kasar...
    Daga Bello Wakili Dukkan ‘yan majalisun tarayya daga Jihar Katsina sun bayyana goyon bayansu ga Gwamna Umar Dikko Radda domin ya sake tsayawa takara a wa’adin mulki na biyu karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben shekarar 2027 mai zuwa. An bayyana wannan matsaya ne a lokacin wani taron hadin gwiwa da ‘yan majalisar suka gudanar, inda Honourable Sada Soli, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Jibia da Kaita, ya yi magana a madadin takwarorinsa. Ya bayyana cewa wannan shawara ta samo asali ne daga nazarin hadin gwiwa da suka yi kan nasarorin da gwamnan ya samu da kuma goyon bayan da al’ummar jihar suka nuna daga kowane bangare. ‘Yan majalisar sun yaba da irin salon shugabanci na Gwamna...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
      Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bayyana muhimman nasarori da ta cimma a fannin noma da tabbacin isasshen abinci, karkashin shirin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Renewed Hope. Rahoton rabin wa’adi na aiki daga watan Mayu 2023 zuwa Afrilu 2025, wanda Ofishin Mai Baiwa Shugaban Kasa Shawara kan Tsare-Tsare da Hadin Gwiwa ya fitar, ya bayyana ayyukan da Ma’aikatar Noma da Tsaron Abinci ta gudanar domin cika alkawurran yakin neman zaben shugaban kasa. Daya daga cikin manyan nasarorin da aka samu a rahoton shi ne sabunta da inganta dakunan ajiya na abinci na kasa, wanda ya taimaka wajen rage karancin abinci da daidaita farashi a kasuwanni. Ma’aikatar ta kuma kaddamar da ayyukan gina hanyoyin ban ruwa da tafkunan ruwa domin kara...
    Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta kaddamar da Kamfanin Bayar da Lamuni a Najeriya (CREDICORP), wani muhimmin shiri a karkashin tsarin sabunta fata na Shugaba Bola Ahmed Tinubu, da nufin rage radadin talauci da bunkasar tattalin arziki ta hanyar fadada hanyoyin samun lamuni.   Da yake jawabi a wani gangamin wayar da kan al’adu a Kano, Shugaban Kamfanin na CREDICORP, Uzoma Nwagba, ya jaddada bukatar sauya ra’ayi game da lamuni, inda ya bukaci ‘yan Najeriya da su dauke shi a matsayin wani makami na bunkasa maimakon akasin haka.   “CREDICORP, wacce aka kafa a karkashin tsarin sabunta fata na Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wata cibiya ce ta kasa da ke aiki don tabbatar da dimokaradiyya ta hanyar samun lamuni ga duk ‘yan...
    Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta sayar da gidaje 753 da aka ƙwato daga tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele. Wannan sanarwar ta fito ne daga Ministan Gidaje, Ahmed Dangiwa, a ranar Talata yayin da yake karɓar takardun mallakar gidajen daga hannun Hukumar EFCC. Mun dakatar da sanya tallan magungunan gargajiya a fina-finai – Abba ’Yan sanda sun cafke ’yan fashi 6, sun ƙwato motocin sata 4 a Kano Gidajen suna cikin Babban Birnin Tarayya, Abuja. Ministan, ya gode wa EFCC saboda yadda ta ke aiki tuƙuru wajen yaƙar cin hanci da rashawa. A cewar sanarwar da kakakin ma’aikatar, Salisu Haiba, ya fitar, an tabbatar cewa waɗannan kadarori na daga cikin dukiyoyin da aka ƙwato daga hannun...
    Gwamnatin tarayya ta jaddada kudirinta na horar da matasa sana’o’i daban-daban a fadin kasar nan.   Sakataren Ma’aikatar Agaji da Rage Talauci, Dokta Yakubu Adam Kofar Mata, ya bayyana haka, a lokacin da ya kai ziyarar wayar da kan mahalarta shirin “Skill to Wealth” na shiyyar Arewa maso Yamma, wanda aka gudanar a Kano.     Dokta Kofar Mata ya jaddada cewa, makasudin bayar da horon shi ne don cika sabbin alkawurran da gwamnati mai ci ta dauka na karfafa matasa.     Shirin bayar da horon na da nufin wadata matasa sana’o’in da za su iya dogaro da kansu da kuma bayar da gudunmawa wajen ci gaban tattalin arzikin kasar.     Ko’odinetan shirin na Jiha Dokta Mahdi Isa...
    Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya roƙi Gwamnatin Tarayya da ta ɗauki matakan da suka dace domin ganin cewa garin Marte bai koma hannun ’yan Boko Haram ba. Zulum, ya kai ziyara garin Marte domin duba halin da ake ciki da kuma yadda za a tabbatar da zaman lafiya. Mawaƙan APC sun zargi gwamnatin Jigawa da yin watsi da su Yadda Boko Haram ta kashe manoma 90 a Borno cikin wata 5 Kafin zuwansa, ’yan ta’adda sun sake karɓe iko da Marte bayan harin da suka kai a ranar Juma’a, inda mutane da dama suka tsere zuwa garin Dikwa. Gwamnan, ya ce mutane kimanin 20,000 ne suka tsere daga Marte, wanda hakan ka iya kawo matsala musamman ga matasa...
    “Amma sai ku ga cewa daya bayan daya, mun magance yawancin wadannan matsalolin. Har yanzu akwai sauran aiki a gabanmu, amma muna kan samun nasarori.” Da yake jawabi a wajen taron, wakilin AON, Obiora Okonkwo ya yi maraba da wannan sabon ci gaban, inda ya bayyana cewa zai inganta ayyukansu. A cewarsa, “Abin da muke gani a nan a yau wani babban ci gaba ne daga jerin abubuwa da dama.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A cewarsa, ba ga wannan akwai shirin kawo sauyi kan manyan kalubale da suka hada da lalata na’urorin wutar lantarki, gudanarwa, matsalolin yankuna da suke janyo cikas ga gudanar da ayyuka. Ya umarci hukumar kula da wutar lantarki a Nijeriya (NERC) da ta tabbatar kamfanonin rabar da wutar lantarki sun bayar da hadin kan da ake bukata domin samun nasarar gudanar da aikin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Idris ya jaddada cewa Gwamnatin Tinubu tana da ƙudirin kare ’yancin faɗin albarkacin baki da ’yancin kafafen yaɗa labarai, waɗanda ya ce su ne ginshiƙan dimokiraɗiyya a ƙasar nan.   Ya ce: “Na bayyana ra’ayi na ga Jakaden, kuma na kuma jaddada ƙudirin gwamnati na ci gaba da kare ’yancin faɗin albarkacin baki da kuma rashin takura wa ‘yan jarida wajen gudanar da aikin su. Za mu ci gaba da kare wannan.   “Muna ganin aikin jarida da kafafen yaɗa labarai wani muhimmin ɓangare ne na dimokiraɗiyya.   “Babu wata dimokiraɗiyya da za ta yi nasara ba tare da kafafen yaɗa labarai ba.”   Sai dai kuma ministan ya buƙaci ‘yan jarida da su riƙa amfani da ‘yancin da suka...
    Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) reshen jihar Jigawa ta naɗa Kwamared Sani Muhammad Gumel da Kwamared Usman Mohammed Usman a matsayin mambobin majalisar kungiyar na musamman (Ex-Officio). Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakatariyar ta kungiyar, Kwamared Aisha Abba Ahmed, ta sanya wa hannu kuma ta rabawa manema labarai a Dutse. Ta bayyana cewa, an yi waɗannan naɗe-naɗen ne a matsayin girmamawa da yabo ga jajircewarsu, ƙwarewa, da kuma gudummawar da suke bayarwa wajen haɓaka aikin jarida a Jihar Jigawa da ma ƙasa baki ɗaya. Aisha Abba Ahmed ta ƙara da cewa, duka waɗannan mutane biyu sun dade suna nuna ƙwazo da biyayya ga manufofi da burin ƙungiyar. Ta ce, ana sa ran waɗannan mambobin na...
    Sanarwar mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar ta ARD-FCTA, Dokta George Ebong, da babban sakataren kungiyar, Dr. Agbor Affiong, sun yi Allah wadai da matakin da gwamnati ta dauka na cire ma’aikatan da abin ya shafa daga cikin tsarin albashi ba tare da sanarwa ko tuntuba ba, inda kungiyar ta ya bayyana matakin a matsayin “rashin gaskiya da adalci”.   A cewar kungiyar, ma’aikatan da aka kora da suka hada da likitoci, ma’aikatan jinya, masu kula da bangaren magunguna, da masana kimiyyar dakin gwaje-gwaje, an yi kuskure ne aka bayyana su a matsayin ma’aikatan bogi ko kuma wadanda basu zuwa aiki, duk kuwa da gudummawar da suke bayarwa wajen gudanar da ayyukan asibiti. Daga kanmu, magana ta ƙare....
    Mambobin Jam’iyyar PDP shida a Majlisar Wakilai daga Jihar Delta sun sauya sheka zuwa Jam’iyya APC. Kazalika wasu biyu daga Jihar Enugu sun sauya sheka daga Jam’iyyar adawa ta LP zuwa PDP. Shugaban Majalisar Wakiliai, Abbas Tajuddeen, ne ya sanar da hakan bayan dawowar majalisar daga hutu a ranar Talata. Shugaban Majalisar ya bayyana cewa ’yan majalisar sun yanke shawarar sauya sheka ne sakamakon rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam’iyyun nasu a matakin jiha da kuma kasa. Wadanda sauka sauya sheka zuwa APC su ne: Victor Nwokolo,  Julius Pondi, Thomas Ereyitomi, Nicholas Mutu, Okodiko Jonathan, da kuma Nnamdi Ezechi. Wadanda suka bar LP zuwa PPD su ne Mark Obetta da kuma Dennis Nnamdi. Idan ba ma manta ba a kwanakin baya...
    Saleh ya ce, kaddamar da injin kyankyasar, musamman saboda jajircewar ma’aikatan sashen kan wannan aiki, tuni Jami’ar ta fara ganin sakamako mai kyau.   Ya kara da cewa, samar da wannan inji, ya kara nuna irin mayar da hankali da Jami’ar ta yi, wajen habaka fannin aikin noma ta hanyar amfani da kimiyyar zamani da kuma samar wa daliban fannin kimiyyar Jami’ar kayan aikin zamani da za su rika gudanar da ilimin yin gwaje-gwaje da kuma bayar da gudunmawa wajen kara samar da wadataccen abinci a kasar.   Kazalika, wannan nasara ta kuma nuna a zahiri irin kyakkyawan shugabancin Shugabar Jami’ar, Farfesa Maimuna Waziri, duba da irin kokarinta na dora Jami’ar a kan turba mai dorewa, musamman a bangaren samar...