HOTUNA: An ƙaddamar da tashin sahun farko na maniyyatan Nijeriya zuwa Saudiyya
Published: 9th, May 2025 GMT
An ƙaddamar da tashin sahun farko na maniyyatan Nijeriya zuwa ƙasar Saudiyya domin gudanar da Aikin Hajjin 2025.
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ne ya ƙaddamar da tashin maniyattan a filin jirgin Sam Mbakwe da ke birnin Owerri na Jihar Imo.
’Yan kungiyar asiri sun kashe masu shirin tafiya NYSC a Bayelsa JAMB ta saki sakamakon jarrabawar 2025Sahun farko na maniyyata 315 waɗanda suka kama hanyar ƙasa mai tsarki sun fito ne daga jihohin Imo da Abia da Bayelsa inda jirgin Air Peace ne ya kwashe su.
Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma da Shugaban Hukumar Alhazan Nijeriya, Farfesa Abdullahi Usman da Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’adu Abubakar III da sauran manyan jami’an gwamnatin Nijeriya ne suka tarbi Kashim Shettima domin ƙaddamar da tashin maniyyatan.
Aƙalla mutum 43,000 ne waɗanda suka yi rajistar gudanar da aikin hajji daga jihohi 36 da birnin tarayyar ƙasar za su tafi ƙasa mai tsarki domin sauke farali.
Hukumar alhazan ta ce jirgin Air Peace zai kwashi maniyyata 5,128 daga Jihohin Abia da Akwa Ibom da Anambra da Bayelsa da Benue da Cross River da Delta da Ebonyi da Edo da Ondo da Ribas da Taraba.
Sai kuma jirgin FlyNas zai ɗauki maniyyata 12,506 daga Abuja babban birnin Nijeriya da Kebbi da Legas da Ogun da Osun da Sokoto da Zamfara.
Sannan kuma jirgin Max Air zai ɗauki fasinjoji 15,2043 daga Jihohin Gombe da Jigawa da Kano da Katsina da Kwara da Oyo da Filato.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Imo maniyyata Sarkin Musulmi ƙaddamar da tashin
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan sanda sun ƙaddamar da ƙwararrun Jami’an tsaro saboda makarantu a Bauchi
Babban Sufeto Janar na ’yan sandan Najeriya, IGP Kayode Egbetokun ya ƙaddamar da Ƙwararrun Jami’an tsaro da za su kare makarantu a Bauchi, Egbetokun ya ƙaddamar da tawagar ne a ranar Alhamis a Bauchi.
A wajen ƙaddamar da taron masu ruwa da tsaki na ‘Saɓe Schools’ a ɗakin taro na otal ɗin Hazibal. Ya ce, ta hanyar haɗa kai da masu ruwa da tsaki ne jami’an tsaro za su iya kaiwa ga samar da ingantaccen tsaro a makarantu ga yaran Najeriya.
An gurfanar da mutum 10 kan yi wa nakasasshiya fyaɗe a Kaduna An zaɓi Robert Prevost sabon fafaromaEgbetokun wanda ya samu wakilcin AIG Abubakar Sadiƙ Aliyu, ya shawarci Kwamishinan ’yan sandan jihar da ya yi amfani da ƙwarewarsa da gogewarsa da tunaninsa wajen samar da sabbin dabaru da tsare-tsare masu inganci waɗanda za su inganta tsaro da ƙarƙo a makarantun jihar.
Ya ce, rundunar na daga cikin tsare-tsaren kare lafiya a makarantu da Sufeto Janar na ’yan sanda, Kayode Egbetokun ya ɓullo da shi kuma ya umurci Kwamishinonin ’yan sanda na jihohi 36 da kuma babban birnin tarayya Abuja da su haɗa hannu da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da tsaron makarantu daidai da tsarin da aka yi a ƙasa baki ɗaya.
Egbetokun ya bayyana shirin a matsayin wani gagarumin ci gaba ga tsarin da ya haɗa da kare makarantu cikin aminci da sauran muhallin koyo.
Ya ce, ya zama wajibi hukumomin ilimi na Najeriya da shugabannin al’umma su haɗa kai da jami’an tsaro wajen ƙarfafawa da kuma kare makarantun daga duk wata barazana.
Ya kuma ba da tabbacin cewa, ’yan sanda a shirye suke a kodayaushe don ci gaba da kare rayuka da dukiyoyi da kuma tabbatar da yanayin koyo mai kyau da aminci ga ɗalibai.
Gwamna Bala Mohammed ya ce, ya kamata hukumomin tsaro daban-daban su faɗakar da wasu shugabannin ɗalibai da ƙungiyoyinsu dabarun gano duk wata barazana da sanar da hukumomin tsaro cikin lokaci.
Gwamna Bala wanda ya samu wakilcin mai ba shi shawara na musamman kan harkokin tsaro, AIG Ahmed Abdulrahman ya shawarci shugabannin ɗaliban da su yi amfani da hanyar da ta dace wajen sanar da Jami’an tsaro a duk lokacin da suka ga wani mutum ko wani lamari da ya taso.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Sani-Omoloro Aliyu ya yi ƙarin haske kan yadda ake samun ƙaruwar satar mutane, hare-hare da tashe-tashen hankula da ake kai wa makarantu, ɗalibai da ma’aikatu.
“Wadannan munanan al’amura ba wai kawai sun kawo cikas ga harkar ilimi ba, har ma sun sanya tsoro da fargaba a tsakanin iyaye, ɗalibai da kuma al’ummar ƙasa baki ɗaya, wanda ’yan sanda tare da haɗin gwiwar gwamnatin tarayya da masu ruwa da tsaki daban-daban suka mayar da martani tare da samar da shirin kare makarantunmu cikin aminci.