Bukhaiti: HKI Ta Ketari Jan Layimmu, Ta Jira Maida Martanimmu
Published: 6th, May 2025 GMT
Mamba a majalisar gudanarwa ta kungiyar Ansarulla ta kasar yemen Muhammad Bukhaiti ya bayyana cewa hare-haren da HKI da Amurka suka kai fararen hula a kasar yemen wuce jan layi, ko ketare haddi ne na kungiyar don haka su jira maida martani mai tsanani.
Kamfanin dillancin labaran Iran ya nakalti yana fadawa tsahar talabijin ta Al-mayadeen ta kasar Lenamon a yau Talata.
Albukhaiti ya kara da cewa sadaukarwa da mutanen kasar Yemen suke yi saboda Gaza, ba zai tsaya ba, sannan muna son fadawa kasashen Amurka da ingila da kuma HKI kan cewa su ji maida martanimmu. Ya kuma kara da cewa, hare-haren da suka kaiwa ma’aikatu da kuma wuraren fararen hula a kasar Yemen ba zai yi wani tasiri a cikin goyon bayan da muke yiwa mutanen Gaza ba. Yace kasar Yemen a shirya take ta fuskance dukkan bangarorin guda 3.
A safiyar yau Talata ce jiragen yakin HKI suka kai hare-hare kan tashar jiragen sama na Sa’a inda suka kai mata hare-hare har guda 15. Sammam labarin ya kara da cewa jiragen yakin HKI kimani 30 suka yi wammam aikin.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: a kasar Yemen kara da cewa
এছাড়াও পড়ুন:
Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar
Ofishin kula da zirga-zirgar kumbuna masu dauke da mutane na kasar Sin ya ce, an harba kumbon Shenzhou-21 mai dauke da ‘yan sama jannatin kasar Sin 3 cikin nasara, a daren jiya Juma’a, agogon Beijing.
Daga baya kumbon ya sarrafa kansa wajen hade jikinsa da na tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin, ta yadda ‘yan saman jannatin suka shiga tashar, inda tsoffin ‘yan saman jannati 3 da suka dade a cikin tashar, suka yi musu maraba. Hakan ya shaida haduwar sabbi da tsoffin ‘yan sama jannatin kasar Sin karo na 7 a tashar binciken sararin samaniya ta kasar.
Bisa shirin da aka yi, wadannan ‘yan sama jannati 6 za su kwashe kimanin kwanaki 5 suna aiki tare a cikin tashar, kafin tsoffin ‘yan saman jannatin 3 su kama hanyar dawowa gida.
Zuwa yanzu, kasar Sin ta riga ta tura ‘yan sama jannati 44 zuwa sararin samaniya. (Bello Wang)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA