NNPP Ta Yi Asarar Ɗan Majalisa A Kano, Ya Koma APC
Published: 12th, May 2025 GMT
Ɗan majalisar jihar Kano mai wakiltar mazabar Sumaila, Hon. Zubairu Hamza Masu, ya bar jam’iyyar NNPP ya koma APC.
A cikin wasiƙar murabus da ya aika wa shugaban majalisar, Hon. Ismail Falgore, Masu ya bayyana cewa rikice-rikice da shari’o’in cikin NNPP a matsayin dalilin ficewarsa.
Tsohon Dan Takarar Gwamna A NNPP A Jihar Ondo Ya Yi Murabus Daga Jam’iyyar 2027: PDP Ta Mutu, APC Na Shirin Sake Yin Nasara – Martanin Ganduje Ga LamidoShugaban majalisar ya karanta wasiƙar a zaman majalisa na ranar Litinin, inda ya bayyana cewa Masu ya fice daga NNPP tun daga ranar 12 ga Mayu, 2025, kuma ya samu amincewa ga shugabannin APC a dukkan matakan da suka dace su karɓe shi.
Ɗan majalisar ya kuma bayyana cewa wasu mutane daban-daban a matakin jiha da na ƙasa suna da’awar shugabancin NNPP, ciki har da Dr. Suleiman Hashim Dungurawa da Sanata Mas’ud El-Jibrin Doguwa a matakin jiha, yayin da Dr. Ahmed Ajuji da Dr. Agbo Major ke da’awar shugabancinta na ƙasa, tare da shari’o’in kotu da ke dagula jam’iyyar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Inganta Harkokin Gwamnati: Oyebanji Ya Sauke Kwamishinoni 19
Gwamna Oyebanji ya godewa ‘yan majalisar zartarwar jihar da abin ya shafa tare da yi musu fatan samun nasara a ayyukansu na gaba.
Sai dai, umarnin bai shafi babban Lauyan jihar da kwamishinan shari’a ba.
Har ila yau, daga cikin wadanda sallamar ba ta shafa ba, akwai Kwamishinonin Lafiya da Ayyukan Jama’a, Noma da Tattalin Abinci da Ayyuka.
Bugu da kari, kwamishinan ciniki, saka hannun jari, masana’antu da kungiyoyin hadin gwiwa; Mai ba da shawara na musamman kan Ilimin masu bukata ta Musamman; da mai ba da shawara na musamman kan tsare-tsaren kasa, duk suna nan kan mukamansu.
Haka kuma, duk Daraktocin da ke cikin majalisar zartarwa ta Jihar, za su ci gaba da rike mukamansu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp