An Yi Aka Yi Bikin Haihuwar Tauraro Na 8 Daga Taurari 12 Wasiyyan Manzon Allah (s)
Published: 11th, May 2025 GMT
Miliyoyin mutane, mafi yawansu mabiya mazhabar iyalan gidan manzon All..(s) sun taru a hubbaren limami na 8 daga limamai masu tsarki wasiyan manzon All..(s)..12.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, miliyoyin mutanen kasar Iran da kuma wasu bakin da suka zo daga kasashen waje sun yi cincirindo a hubbaren Imam Aliyu dan Musa Al-rida(a) limamai na 8 daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon Alll.
An kawata hubbaren na sa da fulawowi wasu na lantarki sannan malamai suna bayyana matsayinsa a wajen raya addinin kakakinsa manzon All..(s), musamman a lokacinda sarki Mamun daga cikin sarakunan Abbasiyawa ya tilasta masa kaura daga madina zuwa Maru cibiyar mulkinsa. Da kuma yadda ya bayyana dimbin ilmin da All..ya basu sannan ya bayyana addinin musulunci na gaskiya wanda manzon All..(s) ya zo da shi.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
A Koyi Darasi Daga Tarihi
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp