Aminiya:
2025-06-15@01:54:06 GMT

Shin sojoji sun kama Bello Turji ba?

Published: 28th, January 2025 GMT

Hedikwatar Tsaro ta Nijeriya ta yi tsokaci a karon farko kan  labarin da ke yawo cewa sojojinta sun kama ƙasurgumin ɗan ta’adda, Bello Turji.

Rundunar tsaron ta sanar da gaskiyar lamarin ne bayan raɗe-raɗin kama Bello Turji ya karaɗe kafofin sada zumunta.

Daraktan Yaɗa Labarai na Hedikwatar Tsaro, Manjo-Janar Edward Buba, ya sanar cewa babu ƙamshin gaskiya a labarin kama Turji, amma suna neman shi ruwa a jallo.

A jawabinsa ga ’yan jarida, Edward Buba ya shawarci ’yan Najeriya su yi watsi da labarin ƙaryan, da cewa, “duk labarin da ake bazawa game da kama Bello Turji ƙanzon kurege ne.”

Tun bayan da sojoji suka tsananta ragargazar sansanonin ’yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas, musamman Jihar Zamfara inda ya fi yin ɓarna, aka daina jin ɗuriyarsa.

A makon jiya sojoji suka kashe ɗan Bello Turji, da manyan yaran ɗan ta’addan, ciki har da babban mataimakinsa da manyan kwamadoninsa bakwai.

Bello Turji na daga cikin manyan ’yan ta’addan da a tsawon shekaru suka addabi jihohin Zamfara da Katsina da Sakkwato da Kaduna da Kebbi da hare-hare inda suke yi wa jama’a kisan gilla tare da garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa da sace dabbobi da ƙona dukiyoyi.

A yayin da jami’an tsaro ke faɗi-tashin murƙushe su, lamarin ya sake ɗaukar sabon salo bayan ɓullar wata sabuwar ƙungiyar ’yan ta’addan ƙasashen waje, wadda aka fi sani da Lakurawa, musamman a jihohin Sakkwato da Kebbi.

Aƙalla shekara goma ke nan da ’yan bindiga suka addabi yankin Arewa maso Yamma, inda suka rabba dubban ɗaruruwan mutane da garuruwansu, suka hana harkokin noma da kasuwanci, baya ga karɓar daruruwan miliyoyi a matsayin kuɗin fansa ko haraji da suka ƙaƙaba ba al’umma.

Ko a kwanakin baya, wasu labarai sun yi yawo a kafofin sada zumunta cewa dakarun sojin ƙasar Jamhuriyar Nijar sun kama Bello Turji bayan da sojojin Najeriya suka fatattaki shi. Amma daga baya ta bayyana cewa labarin shaci-faɗi ne.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Edward Buba Sakkwato Tsaro Turai Zamfara

এছাড়াও পড়ুন:

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Aike Da Sako Ga Al’ummar Iran Bayan Harin Da Iran Ta Fuskanta

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya aike da sako ga al’ummar Iran bayan harin da yahudawan sahayoniyya suka kai kan kasar

A yammacin jiya ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gabatar da sakon ta gidan talabijin ga al’ummar Iran bayan harin ta’addanci na baya-bayan nan da yahudawan sahayoniyya suka kaddamar kan kasar Iran.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana a cikin wani sakon da ya aike ta gidan talabijin ga al’ummar Iran cewa: Sojojin Iran za su yi aiki da dukkanin karfinsu, kuma za su mayar da martani kan wannan mugunyar aniya ta ‘yan sahayoniyya kaskantattu marasa tunani da basira.

Jagoran ya jaddada cewa: Yahudawan sahayoniyya ba za su fita cikin wannan aika-aika ba, kuma wajibi ne al’ummar Iran su tabbatar da cewa ba za a yi sassauci ko sakaci kan hakan ba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sojoji Sun kama ɗan China da wasu 4 kan zargin safarar makamai a Borno da Yobe
  • Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Aike Da Sako Ga Al’ummar Iran Bayan Harin Da Iran Ta Fuskanta
  • An kama ’yar Najeriya da laifin safarar ɗalibai 15 a Australia
  • Ƴansanda Sun Kama Shahararren Ɗan Damfarar Yanar Gizo A Bauchi
  • Harin Isra’ila a kan Iran ya jefa yankin Gabas ta Tsakiya cikin zama dar-dar
  • Nijeriya Ce Ta 3 A Manyan Kasashe Masu Karfin Masana’antu 10 Na Afirka
  • Sojoji sun kashe kasurguman ’yan bindiga 3 a Zamfara
  • Sojoji Sun Kashe Auta, Ƙasurgumin Ɗan Ta’adda Da Wasu 13 a Jihar Zamfara
  • EFCC Ta Kama Mutane 11 Kan Zargi Aikata Damfara A Intanet A Kaduna
  • Ministan Tsaro Na Kasar Iran ya bada Labarin Gwajin Wani Sabom Makami Mai Limzami Mai Daukar abubuwan Fashewa Har Ton Biyu