Al-Husy: Yakin Gaza Shi Ne Kisan Kiyashi Mafi Muni A Cikin Karni Daya
Published: 9th, May 2025 GMT
Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyid Abdulmalik al-husy ya bayyana cewa kisan kiyashin da HKI take yi wa Falasdinawa a tsawon watanni 19 a jere, shi ne laifi mani muni akan bil’adama da ya faru a cikin karni daya.
Sayyid Abdulmalik al-Husi ya kuma ce, abinda ya kara munin wannan laifin shi ne yadda yake faruwa a tsakiyar duniyar musulunci,kuma dukkanin duniya tana Kallon abinda yake faruwa.
Shugaban kungiyar ta “Ansarullah” ya kuma yi gargadin cewa da akwai sakamakon da zai biyo bayan wadannan manyan laifuka,yana mai kara da cewa. Alummar musulmi, a sahun gaba larabawa suna da alhakin abinda yake faruwa.
Haka nan kuma ya jaddada cewa babu wani dalili da zai sa a yi watsi da jihadi saboda Allah da kuma kalubalantar azzalumai, sannan ya kara da cewa, yin watsi da wannan farilla mai tsarki, zai iya jefa al’umma cikin fushin Allah madaukakin sarki, da hakan yake tattare da mummunan sakamako a duniya da lahira.
Sayyid Abdulmalik ya kuma bayyana cewa; Ci gaba da kau da kai da al’umma take yi akan abinda yake faruwa a Gaza, bai dauke mata nauyin da ya rataya a wuyanta ba,yana mai kara da cewa; Sakamakon da za a fuskanta daga Allah yana karuwa gwargwadon yadda ake samun koma-baya wajen yin abinda ya kamata akan al’ummar Falasdinu.
Akan tsayin dakar al’ummar Falasdinu kuwa, shugaban kungiyar ta “Ansarullah” ya jaddada cewa, ‘yan gwgawarmaya suna da dukkanin abinda suke bukatuwa da shi domin ci gaba da fuskantar ‘yan sahayoniya. Ya kuwa jinjinawa gwagwarmayar da kuma al’ummar Falasdinu baki daya.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: yake faruwa
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban IWGA: Birnin Chengdu Zai Karbi Bakuncin Gasar Wasanni Mafi Kyau A Tarihi
Yayin da ya rage kwanaki biyu a yi bikin bude gasar wasanni ta duniya karo na 12, shugaban kungiyar shirya wasanni ta duniya (IWGA) Jose Perurena Lopez, ya bayyana shirye shiryen da aka yi a Chengdu a matsayin wadanda suka zarci tunani, yana cewa abu ne da zai kafa tahiri.
Perurena ya shaidawa kamfanin dilancin labarai na Xinhua a yau Talata cewa, cikin shekaru biyu da suka gabata, yana da burika sosai kan gasar, amma yana ganin abun da aka shirya ya zarce tunaninsa.
Ya ce suna da tabbacin birnin Chengdu zai gudanar da gasar wasanni mafi kyau a tarihi saboda ingancin wuraren wasa da na masu aikin sa kai da ma na kwamitin shirya gasar, na nuna matukar kwarewa. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp