2025-05-09@21:58:44 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3604

«aka yi watsi da ita»:

    Bugu da kari, Sanarwar ta ce Sin da Rasha na goyon bayan kasancewar MDD jigo na shugabancin batutuwan da suka shafi kirkirarriyar basira ko AI, da jaddada muhimmancin martaba ikon mulkin kai na kasashe daban daban, da nacewa bin dokokin kasashe mabanbanta, da martaba ka’idojin MDD yayin gudanar da hakan. (Saminu Alhassan) Daga kanmu,...
    An ƙaddamar da tashin sahun farko na maniyyatan Nijeriya zuwa ƙasar Saudiyya domin gudanar da Aikin Hajjin 2025. Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ne ya ƙaddamar da tashin maniyattan a filin jirgin Sam Mbakwe da ke birnin Owerri na Jihar Imo. ’Yan kungiyar asiri sun kashe masu shirin tafiya NYSC a Bayelsa JAMB ta saki...
    A wani lokaci a gobe Asabar ne ake sa ran ministan harkokin wajen Iran zai fara wata ziyara a kasashen Saudiyya da kuma Qatar. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa, ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi zai ziyarci Saudiyya da Qatar a, bayan rahotannin da ke cewa akwai yiwuwar yin wata sabuwar tattaunawa...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce za a gudanar da zagaye na hudu na tattaunawa tsakanin Iran da Amurka ranar Lahadi. Araghchi ya bayyana a yau Juma’a cewa Oman ce, zata kasance mai shiga tsakani, kuma ita ce ke tantance lokaci da wurin da za a yi tattaunawar. Ya kara da cewa bisa...
    Wannan mataki ya haifar da gagarumar muhawara a duniya. Yayin da manufar ke da nufin farfado da Hollywood da karfafa shirya fina-finai na cikin gida. Amma mu tambayi kanmu, shin da gaske wannan ita ce hakikanin manufar? Amma bari mu yi la’akari da wannan hasashen mu gani, ko shi ne ya fusata Amurka ta maka...
    Hukumar JAMB mai shirya jarrabawar neman shiga makarantun gaba da sakandire a Nijeriya, ta sanar da sakin sakamakon jarrabawar da ɗalibai suka zana a bana. Wata sanarwa da shugaban hukumar, Farfesa Ishaq Oloyede ya fitar ranar Juma’a, ta ce an riƙe sakamakon ɗalibai 39,834 wanda a cikin wannan adadi tana bincike kan sakamakon ɗalibai 1,426....
    An kama mutane 78 tare da kwace tulin miyagun kwayoyi da makamai da kayan sata a wani samame da ’yan sanda suka kai kwanan nan domin ayyukan laifi a Jihar Kano. A yayin samamen, an kama gawurtaccen dillalin miyagun kwayoyi, Sulaiman Danwawu, da wasu haramtattun kwayoyi bayan an taba kama shi a shekarar 2022. Daga...
    Gwamnatin Nijeriya ta sanar da dakatar da tsarin bai wa ɗalibai tallafi domin samun damar zuwa ƙetare ƙarin ilimi. Ministan Ilimi, Tunji Alausa, shi ne ya sanar da wannan mataki, da ke nufin cewa za a kawo ƙarshen wannan tsari da aka share tsawon shekaru ana aiwatarwa. Yadda yara 5 suka mutu a cikin motar...
    Wasu kananan yara biyar sun mutu a cikin wata mota da aka yi watsi da ita a harabar wani gida a yankin Agyaragu da ke Karamar Hukumar Obi da ke Jihar Nasarawa. Yaran sun rasu ne a sakamakon daukewar nunfashinsu a cikin motar, lamarin da ya jefa mazauna yakin yankin, wadanda yawancinsu manoman ne, daga...
    Kotun tarayya da ke Abuja ta ɗage ƙarar tuhumar tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello kan zargin badaƙalar kuɗi da hukumar EFCC ta gabatar zuwa ranakun 26, 27 ga Yuni da 4, 5 ga Yuli don yanke hukunci kan buƙatar masu gabatar da ƙara ta “yi wa shaidar tambayoyi” da kuma ci gaba da shari’ar....
    Farfesa Bamaiyi ya bayyana ainihin aikin IAR a matsayin habaka nau’ikan dimbin amfanin gona da kuma jure fari wadanda suka dace da bukatun noma a Nijeriya. Ya bayyana masarar TELA a matsayin wata sabon salo da kirkira ta zamani a kimiyyance domin magance matsalolin da ake ci gaba da addabar amfanin gona, kamar kwari da...
    Alkaluman hukumar kwastam ta kasar Sin sun nuna cewa a watan Afirilun bana, hada-hadar cinikayyar shige da ficen hajoji ta amfani da kudin kasar yuan ta karu da kaso 5.6 bisa dari. Alkaluman da hukumar ta fitar a Juma’ar nan sun nuna cewa, adadin hajojin da kasar Sin ta fitar ya karu da kaso 9.3...
    Ƙungiyar Allied Group of Nasarawa Professionals (AGNP), wadda ta ƙunshi ’yan kasuwa da masu sana’o’in hannu, ta goyi bayan tsohon Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Mohammed Adamu, wanda ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Gwamnan Jihar Nasarawa a 2027. A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a ofishinta da ke Keffi, AGNP ta ce matakin...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Masana harkokin masana tsaro sun nuna rashin amincewarsu da iƙirarin sojojin Najeriya cewa baƙi daga ƙasashen waje ne ke kai yawancin hare-haren da ake kaiwa al’ummomin ƙasar, musamman a jihohin Filato da Benue. Wannan ƙalubalen ya fito ne bayan wata sanarwa da Hedikwatar Tsaro ta yi a ranar Alhamis, cewa yawancin hare-haren da ake kai...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Yau Juma’a, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci bukukuwan cika shekaru 80 da cimma nasara a yakin kishin kasa na tsohuwar Tarayyar Soviet. An gudanar da faretin soja na ranar samun nasara, wanda ke ayyana cika shekaru 80 da samun nasara a yakin kishin kasa na Tarayyar Soviet ne a birnin Moscow. Shugabanni daga...
    A wani bangare na manufofinsu na kara yawan masu kada kuri’a, Alhaji Gamawa ya bayyana cewa, kungiyar mai zaman kanta za ta taimaka wa ‘yan kasa wajen karbar katin zabe, “Lokacin da INEC ta bude dandalin rajistar katin zabe, za mu taimaka musu wajen karbar katin zabe domin su bada gudunmawa a zabe da kuma...
    Masana harkokin masana tsaro sun nuna rashin amincewarsu da iƙirarin sojojin Najeriya cewa baƙi daga ƙasashen waje ne ke kai yawancin hare-haren da ake kaiwa al’ummomin ƙasar, musamman a jihohin Filato da Benue. Wannan ƙalubalen ya fito ne bayan wata sanarwa da Hedikwatar Tsaro ta yi a ranar Alhamis, cewa yawancin hare-haren da ake kai...
    Amma an fi so a yi da Rakumi ga wanda yake da iko. A Aikin Hajji, an fi son yawan nama sabanin Layya da aka fi son nama mai dadi da kitse. Shari’a ta yarda mutum bakwai su hada kudi su sayi Rakumin hadaya guda daya. Idan Alhajin da hadaya ta hau kansa bai samu...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Hukumomi a jihar Yobe sun ɗora alhakin ƙazancewar matsalar tamowa a kan rikicin Boko Haram da rashin shayar da jarirai nonon uwa yadda ya kamata da kuma gurɓacewar harkar kiwon lafiya, da sauran su. Bayanin hakan na zuwa ne bayan Babban Jami’i mai Kula da Ayyukan Jinƙai na...
    Minista Tuggar ya bayyana cewa, kasar Cuba ta taka mihimmiyar rawa wajen samar da ‘yancin kai ga wasu kasashen Afrika a lokacin da ake gwagwarmaryar kwato ‘yanci daga ‘yan mulkin mallaka a shekkarun 60s, 70s, 80s da 90s. “Cuba da Nijeriya sun yi aiki tare wajen yaki da ‘yan mulkin mallaka a kasashen Angola, Namibia,...
    Kwamandan dakarun kare juyin musulunci na Iran Janar Husaini Salami ya bayyana cewa; Dangane da Shirin Nukiliyar Iran, muna bai wa diplomasiyya fifiko, amma kuma a lokaci daya muna cikin Shirin fuskantar kowane irin yaki duk yadda ya zo. Janar Salami wanda ya gabatar da jawabi a wurin karrama shahidan yi wa kasa hidima, a...
    Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyid Abdulmalik al-husy ya bayyana cewa kisan kiyashin  da HKI take yi wa Falasdinawa a tsawon  watanni 19 a jere, shi ne laifi mani muni  akan bil’adama da ya faru a cikin karni daya. Sayyid Abdulmalik al-Husi ya kuma ce, abinda ya kara munin wannan laifin shi ne yadda...
    Shugabannin kasashen Rasha da China Sun yi alkawalin fuskantar siyasar Amurka akansu,a yayin wani taro da su ka yi a birnin Moscow a daidai lokacin bikin tunawa da zagayowar cikar shekaru 80 da samun galaba akan ‘yan Nazi na kasar Jamus. Shugaba Vladmir Putin na Rasha da takwaransa na China Xi Jing Ping sun yi...
    Hukumar kare hakokin masu sayayya ta ta kasa tare da haka da Hukumar Kare Data ta kasa NDPC ne, suka gudanar da binciken na watanni 38.   A cikin binciken na su, sun bayyana yadda ake take saba ka’ida tare da take dokar kasa da kuma take hakkin ‘yan Adama na kasa da kasa.  ...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana a yau Alhamis cewa, a yayin da ake fuskantar sauye-sauyen da ba a taba ganin irinsu ba a duniya, kasashen Sin da Rasha sun ci gaba da zurfafa amincewa da juna ta fuskar siyasa, da hadin kai bisa manyan tsare-tsare, da kiyaye daidaito da hadin gwiwa a harkokin...
    Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni a ranar Alhamis ya ziyarci sojojin Hedikwatar Task Force Brigade ta 27 Buni Gari, domin jajantawa waɗanda aka kashe kan harin da ’yan tada ƙayar baya suka kai.  A cikin jawabinsa Gwamna Buni ya bayyana cewa, abin takaici ne ga sake ɓarkewar tashe-tashen hankula da kuma hare-haren da ake...
    A yau Alhamis ne shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Rasha Vladimir Putin suka rattaba hannu kan wata sanarwa ta hadin gwiwa game da kara zurfafa hadin gwiwar abokantaka bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni tsakanin Sin da Rasha a sabon zamani. (Mai fassara: Mohammed Yahaya) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna...
    Babban Sufeto Janar na ’yan sandan Najeriya, IGP Kayode Egbetokun ya ƙaddamar da Ƙwararrun Jami’an tsaro da za su kare makarantu a Bauchi, Egbetokun ya ƙaddamar da tawagar ne a ranar Alhamis a Bauchi. A wajen ƙaddamar da taron masu ruwa da tsaki na ‘Saɓe Schools’ a ɗakin taro na otal ɗin Hazibal.  Ya ce,...
    Wata kotun majistare da ke titin Ibrahim Taiwo a Kaduna ta gurfanar da wasu mutane 10 da suka haɗa da kaka, bisa laifin yi wa wata yarinya ’yar shekara 16 fyaɗe a ƙauyen Likoro da ke ƙaramar hukumar Kudan ta jihar. An ruwaito cewa wanda ake zargi mutum na 11 na hannu a lokacin da...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa akwai bukatar kasashen Indiya da Pakisatan su daure su daina musayar wuta a tsakaninsu saboda tabbatar da zaman lafiya a yankin Asiya. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a safiyar yau Alhamis bayan isarsa birnin News Delhi. A...
    Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Kasim, ya bayyana cewa mutanen kasar Lebanon zasu ci gaba da gwagwarmaya da HKI wacce ta ke mamaye da wasu kasashen larabawan yankin har zuwa nasara. Tashar talabijibn ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Sheik Kasim yana fadar haka a wani jawabin da ya gabatar ta...
    Wasu yan jaridu masu bincike a kasar Amurka sun gano sunan sojan HKI wanda ya bindige yar rahoton tashar Aljazeera ta kasar Qatar a shekara ta 2022 a lokacinda take Shirin bada rahoton hare-harenn da sojojin yahudawan suke kaiwa kan wata unguwa ta Falasdinawa a birnin Jenin na yankin yamma da Kogin Jordan. Tashar talabijin...
    Tsohon ministan kudin kasar Amurka John Connally ya ce, dala kudi ne na Amurka, amma matsala ce ga sauran kasashen duniya. Yanzu haka tsarin kudin na haifar da karin radadi ga kasashe daban daban, sakamakon matakan kasar Amurka na kashin kai, lamarin da ya sanya dimbin kasashe neman kauracewa tsarin dalar Amurka. Misali, a rubu’in...
    A yau ne aka bude kasuwar baje koli na kayakin da suka shafi man fetur da gasa wadanda aka kera a JMI karo na 29  a yau a nan birnin Tehran. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa kasuwar zata ci ne daga yau 8-11 ga wannan watan na mayu da muke...
    Fadar Vatican ta sanar da Robert Prevost a matsayin sabon fafaroma, wanda zai maye gurbin Fafaroma Francis. Sabon fafaroman wanda shi ne na farko daga ƙasar Amurka kuma wanda zai jagoranci cocin na Katolika na duniya. Ficewar ’Yan Majalisa 3 a PDP: Raɗɗa ya halarci zauren Majalisar Wakilai An kama mutum 6 da ake zargi...
    Yau Alhamis, kakakin ofishin jakadancin Sin dake Amurka ya amsa tambayoyi game da taron koli na tattaunawa kan batun ciniki da tattalin arziki tsakanin Sin da Amurka.   A cewar kakakin, bangaren Amurka ta aikewa kasar Sin sakwanni da dama ta hanyoyi daban-daban don bayyana fatanta na tattaunawa da Sin kan batun harajin kwastam da...
    Eze na cikin jerin da rundunar tsaro ke nema ruwa a jallo saboda hannu da yake da shi wajen kai hare-hare da garkuwa da mutane a yankin Kudu maso Gabas. Manjo Janar Kangye, ya ƙara da cewa, a watan Afrilu, sojojin sun ceto mutane 173 da aka yi garkuwa da su, sannan sama da ‘yan...
    Da safiyar Alhamis ɗin nan ne Gwamnan Jihar Katsina Dikko Umar Raɗɗa ya halarci zauren Majalissar Wakillai ta ƙasa domin sheda ficewar Ƴan Majalissa uku na Jihar Katsina daga Jam’iyyar PDP zuwa Jam’iyyar APC Ƴan majalissar sun haɗa da Ɗan majalisa mai wakiltar (Mashi/Dutse) Hon. Salisu Yusuf Majigiri, da na (Bakori/Ɗanja) Hon. Abdullahi Balarabe Dabai,...
    Hukumar jindadin Alhazai ta jihar jigawa ta gudanar da taro da shugabanin shiyya shiyya da kuma jami’an alhazai na kananan Hukumomi Jihar 27 a shelkwatar hukumar dake Dutse gabannin fara jigailar maniyatan aikin hajjin bana. A lokacin da yake jawabi, Darakta Janar na Hukumar Alhaji Ahmed Umar labbo ya ce taron yana da muhimmanci kasancewar...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Akwa Ibom ta ce, ta kama wasu mutum shida da ake zargi da yin garkuwa da wasu mutane a jihar kwanan nan. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan, DSP Timfon John ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya sanarwa manema labarai a ranar Alhamis a garin Uyo,...
    Tawagar jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal ta haɗa da sakataren gwamnatin jihar, da masu ba da shawara na musamman guda biyu, da babban sakataren ZITDA, tare da Siobhan Wilson, shugaban Oracle na Ingila da kuma babban mataimakin shugaban EMEA.   Sanarwar ta ƙara da cewa: “Gwamnatin jihar Zamfara ta rattaba hannu kan wata...
    Dakarun Birget na 6 na Sojin Najeriya da ke Jalingo Jihar Taraba sun cafke wasu mutane huɗu da ake zargin cewa ’yan ta’adda ne. Kama waɗanda ake zargin ya biyo bayan wani samame da sojojin  suka gudanar a ranar 7 ga Mayu, 2025 a Ƙaramar Hukumar Arɗo-Kola da ke jihar. Kakakin Rundunar, Kyaftin Oni Olubodunde,...
    Amurka ta matsa wa gwamnatocin wasu ƙasashe da Shugaba Donald Trump ya ƙaƙaba musu haraji su  amince da kamfanin intanet na Starlink mallakin Elon Musk a ƙasashensu. Elon Musk shi ne mai kuɗin duniya kuma babban makusanci ne ga Shugaba Donald Trump. Jaridar Washington Post ce ta ruwaito hakan a ranar Laraba, tana mai ambaton...
    Shugaban kasar Sin, Xi Jinping ya aike da wasikar taya murna ga taron musayar al’adu da cudanyar al’umma da aka shirya domin murnar cika shekaru 80 da samun nasarar yakin turjiya da jama’ar kasar Sin suka yi a kan zaluncin Japan da kuma kazamin yakin ceton kasa na tsohuwar tarayyar Soviet. A cikin sakon nasa,...
    ’Yan sanda sun gano harsasai guda 500 a wata maɓoyar masu aikata laifuka da ke kusa da hanyar Bauchi a Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato. Kwamishinan ’yan sandan jihar, Emmanuel Adesina, ya ce an gano harsasan ne ta hanyar rahotannin sirri, inda ya bayyana hakan a matsayin babbar nasara a yaƙi da...
    An kwantar da wasu matan aure kishiyoyin juna a asibiti bayan da suka sha maganin kara sha’awa domin burge mijinsu bayan ya auro mata ta uku. Kishiyoyin biyu da ke yankin Dakwa a Abuja sun sha maganin gargajiyan, wanda aka fi sani da kayan mata ne, kwana uku bayan amaryar da mijinsu ya auro ta...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp