Aminiya:
2025-05-12@15:32:44 GMT

’Yan ta’adda sun ƙwace makaman sojoji na tiriliyoyin naira —Majalisa

Published: 12th, May 2025 GMT

Ɗan Majalisar Wakilai, Honorabul Yusuf Gadgi, ya yi iƙirarin cewa mayaƙan Boko Haram sun ƙwace makaman sojoji da kuɗaɗensu ya kai tiriliyoyin naira a hare-haren da kungiyar ta kai kan sansanonin soji a yankin Arewa maso Gabas.

Gadgi ya bayyana haka ne a yayin da yake tsokaci kan ƙudirin da Honorabul Ahmed Satomi daga Jihar Borno ya gabatar a zauren Majalisar, kan gobarar da ta tashi a ma’ajiyar makamai ta rundunar soji da ke Barikin Sojoji na Giwa da ke Maiduguri da kuma ƙaruwar hare-haren Boko Haram a jihohin Borno da Yobe a baya-bayan nan.

Ɗan malisar ya ce yawan yadda ’yan ta’adda ke lalata kayan yaƙin sojoji a yanzu, ba a taɓa ganin irinsa ba a baya. Ya ƙara da cewa rashin ɗaukar mataki cikin gaggawa zai haifar da mummunan sakamako musamman ga zaɓaɓɓun shugabanni.

Ya ce, “Na firgita da abin da Boko Haram ta yi a Barikin Giwa da sauran cibiyoyin sojoji. Akwai abin damuwa game da tsaro da amincin ’yan Najeriya da ma ita kanta ƙasar.”

Yusuf Gadgi ya ce Majalisa ta ware wa sojoji kuɗaɗe a cikin kasafi domin sayen motocin yaƙi sama da 40 da sauran kayan yaƙi, da kuɗinsu ya kai tiriliyoyin naira, domin tsaron ’yan Najeriya.

Ya ce. “To yaya za mu samu tabbacin tsaron al’umma a irin wannan yanayi, idan ’yan ta’dda sun kwace waɗannan kayan yaƙi?”

Ya ci gaba da cewa “Majalisa tana yin iya bakin ƙoƙarinta wajen yin magana da kan sha’anin tsaro, amma wajibi ne hukumomin gwamnati su ɗauki mataka. Ya zama tilas shugaban ƙasa ya binciki shuagabannin sojoji da sauran hukumomin tsaro game da wannan sakacin, sannan ya ɗauki mataki a kansu.

“Sannan ya zama dole mu gayyaci hukumomin gwamnati domin su rika bayani a game da gazawarsu wajen gudanar da ayyukansu,” in Honorabul Yusuf Gadgi.

Ya bayyana cewa yawan halin ko-in-kula daga gwamnati da hukumomin tsaro zai haifar da rashin yardar al’umma da su, wanda hakan babbar barazana ce ga shugabannin siyasa.

Ya ce ya zama wajibi a ɗauki mataki, idan ba haka ba, “’yan Najeriya za su ɗauki matakan kare kansu da kansu, kuma za su yake mu kamar yadda za su yakar Boko Haram.”

 

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: yan ta adda Boko Haram kayan yaƙi Tsaro

এছাড়াও পড়ুন:

Yaran Bello Turji sun tayar da ƙauyuka 4 a Sakkwato

’Yan bindiga da ake zargin yaran fitaccen jagoran ’yan bindiga Bello Turji ne, sun ƙwace yankin Bafarawa, garin su tsohon gwamna Attahiru Dalhatu Bafarawa.

’Yan bindigar sun kai harin tare da ƙwace wasu ƙauyuka huɗu ne a ranar Asabar a Ƙaramar Hukumar Isa ta Jihar Sakkwato.

Harin, wanda ake zargin wani kwamandan Turji mai suna Danbakolo ne ya jagoranta, ya kuma shafi ƙauyukan Gebe, Kamarawa, Garin Fadama da Haruwai.

Ana zargin harin da aka kai da kusan ƙarfe 11 na safe ran Asabar, martani ne ga ayyukan sojoji na baya-bayan nan da suka yi niyyar fatattakar ’yan bindiga a yankin.

NAJERIYA A YAU: Gaskiyar Tasirin Amfani Da Irin Noma Na GMO NDLEA ta kama matar da ta ɓoye hodar iblis a al’aurarta

Majiyoyi a yankin sun ce an kashe mutane uku—ciki har da wata mata da ɗanta—a lokacin harin, wanda wasu mazauna ke zargin na hannun Turji ne ya jagoranta.

Maharan sun yi wa Bafarawa ƙofar rago, inda suka zargi mazauna da bai wa sojoji bayanan sirri.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa wakilinmu cewa maharan, “Sun tafi kai tsaye fadar Sarkin Gabas na Bafarawa, Alhaji Muhammad Dalhatu, wanda shi ne babban ɗan uwan tsohon gwamnan.

“Sun yi ta neman sa, sun tafi da kuɗinsa da wayoyinsa, kuma sun yi wa al’umma gargadi game da haɗa kai da jami’an tsaro.”

Mazauna ƙauyukan da abin ya shafa sun gudu zuwa garin Shinkafi da ke kusa domin tsira.

Sai dai rahotanni sun ce sojoji sun ƙarfafa musu gwiwa da su koma gida a ranar Lahadi, tare da ba su tabbacin ingantaccen tsaro.

Lokacin da aka tuntube shi domin jin ta bakinsa, kakakin ’yan sanda na Jihar Sakkwato, DSP Ahmad Rufa’i, ya musanta faruwar lamarin.

Ya ce, “Ba na tunanin akwai wani abu kamar haka saboda akwai jami’an tsaro da yawa a waɗannan yankunan.”

Duk da musantawar, majiyoyi da yawa sun tabbatar da cewa hare-haren sun faru kuma sun bar mazauna cikin tsoro.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sojoji Sun Kashe ‘Yan Boko Haram 5, Sun Kwato Makamai A Borno
  • Yaran Bello Turji sun ƙwace garin su tsohon Gwamnan Sakkwato, Bafarawa
  • Yaran Bello Turji sun tayar da ƙauyuka 4 a Sakkwato
  • Sojoji Sun Cafke Dillalan Sayar Da Bindigu A Filato
  • Ɗan Majalisa Ya Tallafawa Mata 400 A Sakkwato
  • Muhawarar da ta ɓarke kan saya wa Sarkin Kano motocin naira miliyan 670
  • Iran Ta Bayyana Damuwarsa Da Makaman Nukliyar HKI A Sanda Ake Takura Mata
  • Matsalar Tsaro: Zulum ya haramta sayar da man fetur a Bama
  • Rikicin Filato Ya Sa Makiyaya Yin Asarar Naira Miliyan 300 Cikin Wata 2