2025-05-04@16:48:02 GMT
إجمالي نتائج البحث: 838
«da Falasdinawa»:
113-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyarmu a yau, shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata wadanda suka shafi siyasa tattalin arziki zamantake tsaro da sauransu inda muke masu karin bayani sannan daga karshe mu ji ra’ayin masana dangane da su. Da fatan masu sauraro zasu kasasnce tare da mu. ///…Madallah, masu sauraro shirimmu na yau zai yi magana dangane da cewa {gwagwarmayar kwace kasar Falasdinu zai fara da tube Mahmood Abbas daga shugabancin kungiyar Kwatar yencin Palasdinawa PLO}. Shugaba Mahmood Abbas, shugaban gwamnatin jeka na yi ka na Palasdinawa ya dade yana hana ruwa guda a gwagwarmayan da Falasdinawa Musamman a Gaza suke yi...
Mahajjata hudu – daya daga Maroko sauran kuma daga Sifaniya – sun isa kasar Saudiyya a kan dawakai a wannan makon da ya fice don gudanar da aikin Hajjin 2025, wanda hakan ke tunatar da al’ummar Musulumi tsarin zuwa aikin hajji a shekaru da dama da suka gabata. Mahajjatan sun isa zuwa kasar Saudiyya ne ta kan iyakar Al Hadithah da ke Al Qurayyat, inda jami’an gwamnati suka tarbe su tare da duba lafiyarsu, da kuma basu abubuwan sha don jinjin irin tafiyar da suka yi ta tsawon makonni. Ya Kamata Mata ‘Yan Fim Su Rike Mutuncin Kansu – Aisha Tafida Gombe Nijeriya Ta Yi Asarar Naira Biliyan 118 Sakamakon Barnatar Da Iskar Gas A Watanni 2 Hotunan yadda suka...
Shugaban karamar hukumar Babura ta jihar Jigawa, Malam Hamisu Muhammad Garu, ya kaddamar da shirin karfafa aikin gona da nufin sanya matasa aikin noman shinkafa a wani bangare na kokarin inganta ayyukan yi da samar da abinci a yankin. Da yake jawabi yayin bikin kaddamar da aikin aka gudanar a garin Babura, shugaban ya bayyana cewa, Gwamna Malam Umar Namadi ne ya bullo da shirin a matsayin wani muhimmin mataki na samar da guraben ayyukan yi ga matasa, da habaka tattalin arzikin kananan hukumomi, da karfafa samar da abinci a fadin jihar. A cewarsa, gwamnatin jihar ta samar da muhimman kayayyakin amfanin gona da suka hada da takin zamani, magungunan kashe kwari, irin shinkafa mai yawan gaske, da...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya yaba da sadaukarwar da ‘yan jarida suka bayar da suke ba da labaran irin wahalhalun da Falasdinawa ke ciki A wani sako da ya wallafa a shafinsa na twitter na ranar ‘yancin ‘yan jarida ta duniya, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana jin dadinsa ga irin sadaukarwar da ‘yan jarida suka yi, wadanda suka rubuta irin wahalhalun da al’ummar Falastinu suke yi da kuma laifukan da yahudawan sahayoniyya suka yi a tsawon shekaru biyu da suka yi a zirin Gaza. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ya rubuta a shafin sada zumunta na “X” a jiya Asabar cewa: Ranar ‘yancin ‘yan jarida ta duniya ta tuna da jarumtakar ‘yan...
Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta tabbatar da cewa: Adadin wadanda suka yi shahada sakamakon ayyukan ta’addancin ‘yan sahayoniyya ya karu zuwa 52,495 Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta sanar a jiya Asabar 3 ga watan Mayu, shekara ta 2025 cewa: Falasdinawa 77 ne da suka yi shahada da suka hada da gawarwakin mutane 7 da aka gano, da kuma wasu mutane 275 da suka jikkata an kai asibitoci a zirin Gaza cikin sa’o’i 24 da suka gabata. Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu a cikin rahotonta na kididdiga ta yau da kullum kan adadin shahidai da jikkata sakamakon hare-haren da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke kai wa a Zirin Gaza: Har yanzu akwai adadin wadanda abin ya rutsa da su a karkashin baraguzan...
Ana gwabza kazamin fada a Sudan, inda dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces suka kashe fararen hula kusan 300 A tsakiyar bala’in Sudan, ana ci gaba da gwabza kazamin fada tsakanin sojojin Sudan da dakarun kai daukin gaggawa, a daidai lokacin da ake fama da munanan ayyukan jin kai da ke ba da mummunan hoto kan makomar kasar. A yammacin jihar Kordofan, sojojin kasar Sudan sun sanar da janyewa daga birnin Nahud, bayan kazamin fada da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces, wadanda suka sanar da kwace iko da birnin da kuma hedikwatar Brigade ta sha takwas, baya ga birnin Al-Khawi. Yayin da ake ci gaba da gwabza fada, gwamnatin Sudan ta zargi dakarun kai daukin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar jin daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce ta miƙawa Hukumar Alhazai ta Ƙasa NAHCON kuɗi sama da Naira biliyan 6 a matsayin kuɗin jigilar maniyyatan jihar na 2025 na zuwa Saudiyya. Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Darakta Janar na Hukumar Alhaji Ahmed Labbo a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Dutse, ya ce hukumar ta raba tare da sayar da kason kujerun aikin Hajji sama da 1,000 na jihar ga ƙananan hukumomi 27 ga mahajjata. Sojoji sun kama jami’an tsaro da ke haɗa baki da ’yan ta’adda ISWAP sun kai wa sojoji hari a Yobe Umar Labbo ya bayyana cewa, hukumar ta kammala shirye-shiryenta da suka haɗa da biza ga maniyyatan jihar, inda a yanzu...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Isma’ila Baka’i ya bayyana cewa; Manufar HKI akan Syria a fili take ba a boye ba.” Baka’i ya ci gaba da cewa; Manufar HKI ita ce rusa duk wani karfi da Syria take da shi na yaki, da kuma lalata tattalin arzikinta, domin share fagen shimfida iko a kasar da kuma a cikin wannan yankin. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya kuma ci gaba da cewa; matsayin jamhuriyar musulunci ta Iran akan kasar Syria, a fili yake wanda shi ne kare hadin kan wannan kasa da hana ta tarwatsewa da kare daukakarta a matsayinta na kasa mai ‘yanci da kuma al’umma mai tsawo tarihi na ci gaba,sannan kuma mai tasiri a cikin...
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce duk wani ci gaba da za’a samu a tattaunawa da Amurka ya dogara ne da muhimmancin da Washington ta ba tattaunawar. A wata tattaunawa ta wayar tarho da Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, Araghchi ya ce barazana da kuma takunkumin da Amurka ke kakaba wa Iran, ya kara haifar da shakku game da aniyar Washington na neman hanyar diflomasiyya. “Don ci gaba a kan wannan tafarki dole ne dayan bangaren ya nuna kyakkyawar niyya cewa da gaske ya ke,” in ji shi, kafin ya ce: “Iran, a matsayinta na mamba a yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT), dole ne ta ci moriyar makamashin nukiliya don dalilai na zaman lafiya.” Ministan...
A yayin da jam’iyyun hamayya ke ci gaba da shirye-shirye tunkarar babban zaɓen shekara ta 2027, a bayabayan nan an ga yadda suke haɗuwa da juna, inda tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya tabbatar wa duniya cewa, suna tattaunawa domin ganin sun yi haɗakar da za ta kayar da Jam’iyyar APC mai mulki a zaɓen mai zuwa. Ko da yake yaƙi ɗan zamba ne, abi da har yanzu bai fito fili ba zuwa yanzu shi ne dabarar da ’yan adawar ke son yin amfani da ita wajen tunkarar APC a 2027, ganin yadda Jam’iyyar ke ta ƙara karɓar masu sauya sheƙa daga wasu jam’iyyu. Guguwar APC ta girgiza ’yan adawa Wasu na ganin sauyin sheƙar na iya kawo babban...

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Tattauna Da Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Kan Zaman Tattaunawan Amurka Da Iran
Ministan harkokin wajen Iran ya sanar da babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ci gaba da ake samu a shawarwari makamashin nukiliyar Iran tsakanin Amurka da Iran amma ana buƙatar gaskiya da hangen nesa daga ɗayan ɓangaren A yammacin jiya Juma’a ne ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Araqchi ya tattauna ta wayar tarho da Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres, inda suka yi musayar ra’ayi da musayar mahanga da kuma tattaunawa kan ci gaban yankin da kuma kasa da kasa. Araqchi ya kuma yi wa Guterres bayani kan sabbin abubuwan da ke faruwa a shawarwarin da ba na kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka, da kuma shirye-shiryen da masarautar Oman ta yi na tsara zagaye na...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya soki mummunar rawar da Faransa ke takawa Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya soki kasar Faransa saboda abin da ya bayyana a matsayin gurgunta rawar da take takawa a kokarin diflomasiyya kan matsayin Shirin makamashin nukiliyar Iran na zaman lafiya. A wani rubutu da ya yi a dandalin X, kakakin ya yi tsokaci kan zargin na Faransa, yana mai cewa: Ikirarin da ministan harkokin wajen Faransa ya yi na cewa Iran na daf da kera makamin nukiliya, da’awa ce ta karya kuma marar tushe. Ya kara da cewa: Wadannan kalamai na karya, tare da barazanar sake kakabawa Iran takunkumi, suna kara karfafa ra’ayin cewa matsayar Faransa na rikidewa zuwa wani matsayi na...

Falasdinawa 40 Ne suka Yi Shahada A Zirin Gaza Sakamakon Ta’addancin Sojojin Mamayar Isra’ila A Jiya Juma’a
Falasdinawa 40 ne suka yi shahada a hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan Zirin Gaza tun daga wayewar garin jiya Juma’a Rahotonni sun bayyana cewa: A yammacin jiya Juma’a, Falasdinawa fararen hula 8 ne suka yi shahada yayin da wasu kuma suka jikkata sakamakon wani hare-haren da jiragen saman sojin mamayar Isra’ila suka kai kan wani gida a sansanin Jabaliya da al-Balad da ke arewacin zirin Gaza. Haka zalika hare-haren sun yi sanadiyyar shahadar Falasdinawa 6 sannan wasu 8 suka jikkata a wani harin da jiragen saman yakin mamayar Isra’ila suka kai kan taron fararen hula da ke kusa da mahadar Abd al-Aal da ke kan titin al-Jala’a da ke arewacin birnin Gaza. A cewar majiyoyin cikin gida,...
Babban darektan hukumar kula da tattara bayanai da yada su ta bangaren teku ta kasar Sin, Shi Suixiang, ya bayyana cewa, manufofin tallafi da aka bullo da su a matakai na tsakiya da na kananan hukumomi sun karfafa ci gaban yawon shakatawar. Ya kara da cewa, gwamnatin tsakiya ta inganta fadada hanyoyin jiragen ruwa da kayayyakin yawon shakatawa yayin da kuma ake kara daidaita tsarin rajistar jiragen ruwa da kuma shigar da su cikin hada-hada. Wasu manazarta dai sun bayyana cewa, a sa’ilin da lokacin goshin damina ke gabatowa, ana sa ran yawon shakatawa na bakin teku da tsibirai a yankin kudu maso gabashin kasar Sin ya bunkasa, tare da kara samun balaguro ta ruwa da nufin cin...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa gwamnatin JMI ba zata amince da tattaunawa tare da kara tsuge takunkuman tattalin arziki na koli da aka dorawa kasar ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a yau Jumma’a ya kuma kara da cewa yin haka sabawa dokokin kasa da kasa ne. Har\ila yau take hakkin mutanen kasar Iran ne da kuma shigar da shakku a cikin tattaunawar da Amurka take yi da kasar. Kafin haka dai gwamnatin kasar Amurka ta bada sanarwan kakabawa mutanen da kamfanoni 7 wadanda suke mu’amala da kasar Iran a kasashen UAE da Turkiya saboda sayan danyen man kasar Iran da kuma sinadaran manfetur na kasar. Har’ila...
Limamin da ya jagoranci sallar Jumma’a a nan Tehran Hujjatul Islam kazim Sadiki ya bayyana cewa kasar tana da kwararru wadanda suke da kwarewa a sanin fasahar nukliya da kuma hanyoyin dublomasiyya a tattaunawar da Iran take da Amurka dangane da shirin Nukliyar kasar. Tashar talabijin ta Al-alam a nan Tehran ta nakalto limamin yana fadar haka a khudubobinsa na sallar Jumm’a. Ya kuma kara da cewa, lalle tawagar kasar Iran a tattaunawar suna ci gaba da tattaunawa, sannan suna matukar iyawarsu don kare hakkin Iran na mallakar Fasahar Nukliya wacce take da matukar muhimmanci. Hujjatul Islam Sadiki ya kara da cewa tawagar Iran a wannan tattaunawar, suna amfani da tajruban da suke da shi a tattaunawar baya, sannan sauran...
Gwamnatin HKI ta kai farmaki kan tawaga masu rajin kare hakkin bil’adama dauke da kayakin agaji a cikin jirgin ruwa dauke da kayakin agaji zuwa zirin Gaza wacce ta hana shigar abinci cikinsa kimani watanni biyu da suka gabata. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto majiyar gwamnatin tsibirin Malta na cewa HKI ta kai hari kan jirgin agajin ne tare da amfani da jirgin yaki wanda ake sarrafashi daga Nesa, a ruwayen kasa da kasa. Labarin ya kara da cewa jirgin agajin ya tashi daga tsibirin Malta da nufin isa Gaza, saboda isar da kayakin agajin da suke dauke da su zuwa Gaza, wacce aka killace. Yahudawan saun kai hari da misalign karfe 12.23 a lokacin Malta...
“Siyasar da na sani ba ita ce abin da ke faruwa a yau ba. Siyasar da na sani ita ce gwagwarmayar muradun jama’a don tabbatar da cewa suna da kyakkyawar rayuwa a duk fannoni kamar ilimi, ruwa, kiwon lafiya, da sauransu. “Na kasance a siyasa tsawon shekaru 48 da suka gabata,” in ji shi. Ya bayyana yanayin siyasa a matsayin wanda ke cike da rudani da son kai, yana mai jaddada cewa ‘yan siyasa da talakawa sun rikice. “Saboda wannan, akwai rudani ga masu nema da kuma wadanda ake nema. Masu neman suna makancewa, ba su da imani ko tausayi. Manufarsu kawai ita ce tabbatar da matsayi a gare su. A halin yanzu, talakawa sun tsunduma ciki yunwa, talauci, da...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Amurka ta kawo ƙarshen cire haraji kan wasu kayayyaki da ba ma su tsada ba da ake shiga da su ƙasar daga China. A baya Amurkawa na iya sayan kayayyakin China da ba su haura dala 800 ba, idan za su yi oda ta intanet ba tare da wani haraji ba, amma yanzu za su biya kashi 120. Ana sa ran harajin zai fara aiki nan take, kuma wasu Amurkawa masu sayayya za su ji a jikinsu. Hakazalika su ma yawancin kamfanonin China da ke samar da kayan da shigar da su can.
Kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC reshen jihar Kano ta yabawa gwamnatin jihar Kano kan kudirin ta na daidaita bashin da ake bin ‘yan fansho da ya haura naira biliyan 16. Da yake jawabi yayin bikin ranar ma’aikata da aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha da ke kofar Mata a Kano, shugaban kungiyar kwadago ta NLC, Kwamared Kabiru Inuwa, ya bukaci ma’aikatan Nijeriya da su jajirce wajen tabbatar da adalci da walwala. Kwamared Inuwa ya bayyana cewa duk da nasarorin da gwamnatin ta samu wajen horas da ma’aikata, har yanzu akwai bukatar karin ma’aikata masu tallafawa a ma’aikatun gwamnati da na kananan hukumomi. Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jaddada kudirin gwamnatin sa...
Gwamnatin jihar Kebbi, ta baiwa ma’aikatan jihar tabbacin ci gaba da jajircewa wajen kyautata jin dadin su da kuma kare hakkokinsu. Gwamna Nasir Idris wanda ya ba da wannan tabbacin a lokacin da yake jawabi ga ma’aikata domin bikin ranar watan Mayu a Birnin Kebbi, ya jaddada cewa ma’aikata aminai ne masu kima wajen ci gaban jihar Kebbi, kuma su kasance masu ruwa da tsaki da ba za a yi watsi da su ba. Gwamna Idris, wanda ya bayyana bikin ranar Mayu a matsayin wani muhimmin lokaci, ya yabawa ma’aikatan bisa jajircewarsu da irin gagarumar gudunmawar da suke bayarwa wajen ci gaban jihar. “Kwazonku da jajircewarku sune kashin bayan tattalin arzikinmu. Ina yaba muku kan kokarinku na...
Gwamna Umar Namadi ya bi sahun kungiyoyin kwadago domin tunawa da irin gudunmawar da ma’aikata ke bayarwa wajen ci gaban jihar Jigawa. Da yake gabatar da jawabinsa, Gwamna Namadi ya yaba da jajircewar ma’aikatan Jigawa, inda ya bayyana ma’aikata a matsayin masu kawo ci gaba. Ya bayyana cewa, ma’aikata a dukkan bangarori suna aiki da gaske a matsayin injin da ke ba da kuzarin motsa al’umma zuwa ga ci gaba. Ya kuma kara jaddada kudirin gwamnatinsa na samar da walwalar ma’aikata, inda ya bayar da misali da nasarorin da aka samu da suka hada da aiwatar da mafi karancin albashi na Naira 70,000, gina gidaje masu saukin kudi ga ma’aikatan gwamnati, da kuma shigar da sama da...
Al’ummar Arewa mazauna yankin Obalande da ke Jihar Legas sun yunƙura domin tunkarar matsalolin da ke ci musu tuwo a ƙwarya, musamman yadda suka ce ’yan ƙasa ke musu cin kashi. Sun ce sun gaji da irin tsangwama da ƙasƙanci da ’yan ƙasa a yankin ke nuna wa ’yan Arewa, musamman Hausawa mazauna. Sun bayar da misali bisa yadda samarin Yarabawa daga wasu unguwanni suka mayar da unguwar tasu filin ƙwallon ƙafa, inda suke tilasta musu rufe rumfunansu na kasuwa, har sai an gama buga ƙwalon kafin su ci gaba da sana’arsu. A kan haka ne suka yi wani zama da Shugaban Karamar Hukumar Ikoyi Obalande (LCDA) Fu’ad Lawal Atanda da shugabannin siyasa ’yan Arewa a jihar, da nufin cire...

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ya Ce Kasar Oman Ce Ta Bukaci Dage Zaman Tattaunawan Iran Da Amurka
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: An dage zaman tattaunawan Iran da Amurka ne bisa shawarar kasar Oman Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi nuni da cewa: Ministan harkokin wajen kasar Oman ne ya sanar da sauyin lokacin zaman tattaunawan ba na kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka, yana mai bayanin cewa, dage shawarwarin ya zo ne bisa shawarar ministan harkokin wajen kasar, kuma za a sanar da wata sabuwar rana daga baya. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya sanar da manema labarai cewa: An canja ranar da za a gudanar da zaman shawarwarin ba na kai tsaye ba na gaba tsakanin Iran da Amurka, wanda aka shirya gudanarwa a...
Ministan Tsaron kasar Iran ya bayyana cewa: Gwamnatin yahudawan sahayoniyya ta zama babbar alamar ta’addanci a duniya Ministan tsaron kasar Iran Birgediya Janar Aziz Nasirzadeh, yayin da yake yin Allah wadai da kisan gillar da yahudawan sahayoniyya suke yi wa al’ummomin Falastinu da na Lebanon a daidai lokacin da kungiyoyin kasa da kasa da tarurrukan kasa da kasa suka yi shiru, yana mai cewa: A yau al’ummar yahudawan sahayoniyya ta zama wata babbar alama ta ta’addancin kasa a duniya. Birgediya Janar Nasirzadeh ya furta haka ne a ganawarsa da ministan tsaron Jamhuriyar Zimbabwe Uba Muchinguri Kashiri a lokacin ziyararsa a kasar Iran, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi kasashen biyu. A cikin wannan ganawar, ministan tsaron na Iran ya...
Jagoran kungiyar Ansarullahi ta kasar Yemen ya jaddada cewa: Suna tsaye kafada da kafada da kungiyar Hizbullah ta Lebanon kan duk wani yunkuri na kokarin tada zaune tsaye daga ‘yan sahayoniyya Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen, Sayyed Abdulmalik Badr al-Din al-Houthi, ya yi gargadin yadda yunwa ke barazana ga Falasdinawa sama da miliyan biyu a zirin Gaza, wadanda ke fuskantar yunwa a idon dukkanin bil’adama. Yana mai jaddada cewa: Wannan abin kunya ne ga kasashen duniya da kungiyoyin agaji na kasa da kasa. A jawabin da ya gabatar na zagayowar ranar shelar Falasdinawa kan neman taimakon Falasdinawa dangane da hare-haren wuce gona da irin yahudawan sahayoniyya, Sayyid Al-Houthi ya yi bayani kan sabbin abubuwa da suka shafi wuce gona...

Hamas Ta Yi Allah Wadai Da Matsayin Amurka Na Goyon Bayan Haramta Hukumar Kula Da ‘Yan Gudun Hijiran Falasdinawa Ta UN
Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta yi Allah wadai da matsayin Amurka na goyon bayan haramta hukumar kula da ‘yan gudun hijira falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA) Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta yi Allah wadai da matsayin Amurka na goyon bayan haramtacciyar kasar Isra’ila kan haramta hukumar kula da ‘yan gudun hijiran Falasdinawa da ayyukan ba da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya “UNRWA”, tana daukan wanan a matsayin Amurkia na ci gaba da nuna son kai da goyon bayan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ‘yar mamaya da kuma rashin mutunta dokokin kasa da kasa da yarjejeniyar jin kai. A cikin wata sanarwar manema labarai da ta fitar jiya Alhamis, kungiyar Hamas ta yi nuni da cewa: Shigar da Amurka...

Masifar Gobara Tana Kara Bunkasa A Haramtacciyar Kasar Isra’ila Tare Da Fara Raba Yahudawa Da Muhallinsu
Ana sa alamar tambayar cewa: Shin gobarar da ta tashi a birnin Kudus… shin sako ne na ranar tunawa da kafuwar gwamnatin ‘yan sahayoniyya? Gobarar da ta tashi a tsaunin Kudus da aka mamaye ta bazu zuwa manyan yankuna a cikin haramtacciyar kasar Isra’ila, inda ta kewaye wani sansanin soji tare da cinye filayen masu girma da tsayi. Hakan ya sa hukumomin gwamnatin mamayar Isra’ila suka kafa dokar ta baci tare da neman taimakon kasashen duniya. Yayin da Ministan tsaron cikin gidan Isra’ila Itamar Ben-Gvir yake neman dora wa Falasdinawa, alhakin tashin gobarar. Gobarar ta kunno kai ne a daidai lokacin da yahudawan sahayoniyya suka fara gudanar da bukukuwan cika shekaru 77 da kafuwar gwamnatinsu ta mamaya a kasar Falasdinawa,...
Iran ta sanar da cewa an dage tattauanwa ta karo na hudu da aka shirya gudanarwa tsakaninta Washington a ranar Asabar mai zuwa. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ne ya sanar da manema labarai da hakan a yammacin yau Alhamis yana mai cewa an sauya ranar da za a gudanar da tattaunawar ta gaba tsakanin Iran da Amurka da aka shirya gudanarwa a ranar Asabar 3 ga watan Mayu a birnin Rome na kasar Italiya. Esmail Baghai ya bayyana cewa, an dauki wannan matakin ne bisa bukatar ministan harkokin wajen kasar Oman, kuma Za a sanar da sabon lokaci nan gaba. Baghaei ya jaddada aniyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran na yin amfani da hanyar diflomasiyya wajen kare muradun al’ummar...
An ce shafin neman aikin zai kasance a buɗe har tsawon makonni biyu. Bayan haka, za a zaɓi waɗanda suka cancanta domin ganawa da su da kuma tantance su Hukumar ta shawarci duk masu sha’awar aikin da su gaggauta cike fom ɗin domin guje wa cunkoson mutane a ranar ƙarshe. Gwamna Fintiri ne, ya bayar.da umarnin buɗe shafin domin ɗaukar sabbin ma’aikata 4,000 a aikin gwamnati a jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A dai-dai lokacin da kasashen Amurka da JMI suke ci gaba da tattaunawa kan shirin makamashin nukliya ta Iran gwamnatin Amurka a jiya Laraba ta dorawa kamfanoni da mutanen da suke mu’amala da JMI a bangaren man Fetur takunkuman tattalin arziki. Da dama daga cikin wadannan kamfanoni na kasar China ne. Jaridar ‘the Nation’ ta Amurka ta ce tun farkon wannan shekarar ne shugaban Trump ta farfado da takurawar tattalin arziki mafi muni a ka kasar Iran da nufin tilasta mata dawowa teburin tattaunawa ko kuma ta wagaza cibiyoyin Nukliyar kasar. A halin yanzu dai kasashen biyu zasu ci gaba da tattaunawar ba kai tsaye ba, karo na hudu a birnin Roma na kasar Italiya a ranar Asabr mai zuwa....
Gwamnatin kasar Iran ta bayyana cewa samar da kasar Falasdinu mai cikekken yenci , kuma da dukkan birnin Qudus a matsayin babban birnin kasar, hakkin Falasdinawa ne wannan babu tattaunawa a kansa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jakadan kasar Iran na din din din a MDD Amir Said Iravani yana fadar haka, a jiya laraba, a lokacinda yake gabatar da jawabi a gaban kwamitin tsaro na majalisar. Jakadan ya bukaci kungiyoyin Falasdinawa su hada kansu don duk wani sabani a tsakaninsu nasarace ga HKI. Iranvani ya ce HKI tana ci gaba da aikata laifukan yaki a yankin Gaza da kuma yankin yamma da kogin Jordan, tare da tallafin Amurka da wasu kasashen yamma. Kuma tallafin da...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Cututtuka da dama suna ƙamari a Najeriya wanda a mafi yawan lokuta mutanen da da7uke da irin cututtukan ba su da masaniyar suna dauke da su. Kamar yadda Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana, zaman lafiya, rashin matsalar kwakwalwa, da samun wadata na daga cikin abubuwan da ke tabbatar da lafiyar bil’adama. NAJERIYA A YAU: Dalilin karyewar farashin shinkafa a kasuwannin Najeriya DAGA LARABA: Asarar Da Hausawa Ke Tafkawa Sakamakon Bacewar Tatsuniya Wata cuta da ta addabi da yawa daga cikin al’umma itace Hawan jini wacce take daya daga cututtuakan da ke sanadiyyar mutuwar akalla mutum miliyan biyu a duk shekara a Najeriya. Domin sauke shirin, latsa nan

Kasar Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Najeriya Wajen Yin Watsi Da Kariyar Cinikayya Da Yin Adawa Da Danniya Da Cin Zarafi
Haka kuma Wang ya halarci taron ministocin waje na kasashe mambobin kungiyar BRICS da na kasashe kawayensu a wannan rana, inda aka tattauna game da yadda za a karfafa ra’ayin cudanyar bangarori daban daban. Wang ya bayyana cewa, mafitar matsalolin da ake fuskanta a duniya ita ce kiyayewa da aiwatar da ra’ayin cudanyar bangarori daban daban. Ya ce bayan da ta habaka mambobinta, ya kamata kungiyar BRICS ta ci gaba yayata manufar yin shawarwari da juna da tabbatar da ci gaban juna da cin moriya tare, da kiyaye muhimman ka’idojin huldar kasa da kasa, da kuma kare tsarin ciniki tsakanin bangarori daban daban. Wang ya jadadda cewa, amsar da Sin ta bayar game da yakin cinikayya a bayyane...
Kungiyar Tarayyar Afirka ta dage takunkumin da ta kakabawa kasar Gabon tare da maida ta a cikin cibiyoyinta. AU, ta sanar da hakan ne yayin taron kwamitin zaman lafiya da tsaro na kungiyar yau Laraba a Addis Ababa. Hakan dai ya karshen dakatarwar da aka yi wa kasar ta Gaban daga kungiyar, watanni 20 bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Agustan 2023. Kwamitin zaman lafiya da tsaro na AU, ya yi la’akari da mika mulki da ya hambarar da Ali Bongo “gaba daya cikin nasara,” saboda haka ya yanke shawarar dage takunkumin nan take. ‘’Tsarin siyasar Gabon yana da ” gamsarwa” inji sanarwar kungiyar. Wannan matakin na AU ya zo ne kwanaki uku gabanin rantsar da Janar...
Bayanai daga Falasdinu na cewa akalla Falasdinawa 35 dane suka hada da kananan yara aka kashe a wanisabon kisan kiyashi na Isra’ila a zirin Gaza. A cewar ma’aikatar lafiya ta Gaza, wadannan hare-haren sun yi sanadin mutuwar mutane 35 tare da jikkata 109 a cikin sa’o’i 24 da suka gabata. Adadin wadanda sukayi shahada sakamakon yakin kisan kare dangi da Isra’ila ke yi a yankin da aka yi wa kawanya ya zarce 52,400. Adadin wadanda suka jikkata kuma ya kai kusan 118,014 tun daga watan Oktoban 2023. Majalisar Dinkin Duniya dai ta yi gargadin barkewar ayyukan jin kai a Gaza. Hukumar samar da abinci ta duniya (WFP) ta fitar da wani kakkausan gargadi game da matsalar jin kai da ke...
Amurka ta sanar da kakaba takunkumi kan wasu kamfanoni 7 da ta ce suna da hannu wajen siyar da man kasar Iran, a wani mataki na kara matsin lamba duk da tattaunawar da aka yi kan shirin nukiliyar Iran. Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar ta ce, bangarorion da takunkumin ya shafa sun hada da kamfanonin kasuwanci guda biyar, hudu da ke Hadaddiyar Daular Larabawa, daya kuma a kasar Turkiyya, wadanda suka sayar da albarkatun man fetur na kasar Iran ga kasashe uku, da kuma wasu kamfanonin jigilar kayayyaki guda biyu. A cikin sanarwar da sakataren harkokin wajen kasar ta Amurka Marco Rubio ya fitar, ya ce “Matukar dai Iran na son samar da kudaden shiga na man...
Ya kara da cewa, shugaban kasa Bola Tinubu da sojojin Nijeriya suna aiki tukuru domin ganin an ga sauye-sauye a yaki da ta’addanci da ake yi, a fili kuma a bayyane. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnatin kasar Saudiya ta yi allawadai da HKI a kissan da take wa falasdinawa a Gaza, a jiya talata a gaban kutun ICJ. Saudiya ta bayyana cewa gwamnatin HKI ta sabawa dokokin kasa da kasa da dama a kissan kiyashin da take yi a Gaza. Wakilin kasar a gaban kotun Muhammad Saud Al-Nasser, ya kara da cewa, HKI ta ci gaba ta sabawa wadannan dokoki, amma kuma bata da dalilan saba masu. Banda kissan kiyashin da take yi a Gaza, Al-Nasser ya ce HKI ta maida Gaza kofai, ta rusa mafi yawan gine-ginen yankin, sannan ta hana shigowar abinci da ruwa da magunguna zuwa yankin, wadanda ko wane daya daga cikinsu take hakkin bil’adama ne wanda yake kaiwa ga laifin...
A yau Laraba sa jijjifin Safiya an sami shahidai 3 a Gaza da hakan ya kara yawan shahidai zuwa 40 a cikin sa’o’i 24. Bugu da kari, baya ga shahidan da suke faduwa a kowace rana, ana fama da matsananciyar yunwa a cikin yankin, bayan karewar kayan abincin HKI ta sake komawa yaki kwanaki 44 da su ka gabata. A cikin sansanin ‘yan hijira na “Nusairat” mutane 3 sun yi shahada da su ka hada da karamar yarinya sanadiyyar harin da sojojin na HKI su ka kai wa yankin. A gabashin birnin Khan-Yunus ma dai wasu Falasdinawa sun yi shahada. Daga ranar 7 ga watan Oktoba na 2023 zuwa yanzu adadin wadanda su ka yi shahada sun wuce 52,000,wadanda su...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tatsuniya wata hanya ce ta ilmantarwa da bayar da tarbiyya da kuma koyar da al’adu da halaye na gari a tsakanin Hausawa. Tatsuniyoyi na ɗauke da darussa na rayuwa, suna kuma koya wa yara da manya jarumta da tausayi da sauran dabi’u kyawawa. Sai dai a yayin da duniya take sauyawa, ba kasafai matasa suke sha’awar sauraron tatsuniya ba. NAJERIYA A YAU: Dalilin karyewar farashin shinkafa a kasuwannin Najeriya DAGA LARABA: Dalilan Rashin Wutar Lantarki A Wasu Jihohin Arewa Wannan ne batun da shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari a kai. Domin sauke shirin, latsa nan
Hukumar Fensho ta Jihar Jigawa da Kananan Hukumomin jihar ta shirya fara aikin tantance ‘yan fansho da ke cikin tsarin. Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar, Alhaji Muhammad K. Dagaceri ne ya bayyana haka yayin wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Gidan Fansho, inda shugabannin kungiyar ‘Yan Fansho ta Najeriya reshen Jigawa suka halarta. A cewarsa, an shirya fara aikin tantancewar ne daga ranar Litinin, 5 ga Mayu, 2025. Alhaji Dagaceri ya bayyana cewa, an shirya hakan ne da nufin sabunta tsarin biyan fansho tare da tabbatar da ingancin bayanai. Ya ce, aikin tantancewar zai gyara wasu ‘yan kura-kurai da suka kunno kai a cikin shekaru uku da suka gabata, da kuma tabbatar da ingantattun bayanai a jadawalin...
Aƙalla wasu mutum 10 mafarauta sun rasa rayukansu yayin aikin ceto a ƙauyen Kopire da ke Ƙaramar Hukumar Hong ta Jihar Adamawa. Shugaban ƙungiyar mafarautan Nijeriya reshen Arewa maso Gabas, Shawulu Yohanna ne ya tabbatar wa Aminiya hakan a ranar Talata. Wani abin fashewa ya kashe mutum 26 a Borno An dawo da wutar lantarki a Sifaniya da Portugal A cewarsa, ajali ya katse hanzarin mafarautan ne yayin wani arbatu da mayaƙan Boko Haram da suka yi musu kwanton ɓauna a jeji. Ya bayyana cewa, mafarautan sun tunkari maharan ne bayan samun bayanan sirri da ke nuna cewa suna shirin kai hari. “Abin takaicin shi yadda ake yi wa Gwamnan Borno ƙafar ungulu a ƙoƙarin da yake yi na ganin...
Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Umar Namadi, ya amince da nadin Aisha Shehu Mujaddadi a matsayin shugabar Hukumar Kula da Zuba Jari ta Jihar Jigawa (InvestJigawa). Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ya fitar ga manema labarai. Sanarwar ta ce “Aisha Mujaddadi ta samu digirinta na farko a fannin tattalin arziki a Jami’ar Maiduguri a shekarar 1996, ta kara inganta iliminta da samun digiri na biyu a fannin Gudanar da Kasuwanci (MBA) daga Jami’ar Bayero, Kano a shekarar 2011.“ Malam Bala Ibrahim ya bayyana cewa Aisha Mujaddadi ta samu gogewa na tsawon shekaru 19 a fannin aikin shawarwari na ci gaban kasa da kasa, inda ta yi aiki a kan muhimman...
“Lokacin da abubuwa suka fara lalacewa a lokacin shugaba Buhari, na fito na faɗi gaskiya. Lokacin da tsarin sauya fasalin Naira ya jefa jama’a cikin wahala, na ƙalubalanci gwamnati duk da cewa jam’iyyar APC ce ke kan mulki. Na fi biyayya ga Nijeriya fiye da kowane mutum,” in ji shi. El-Rufai ya ƙaryata jita-jitar cewa fushinsa da gwamnatin Shugaba Tinubu ne ya sa ya fice daga APC. Ya ce yana da shekaru 65, kuma babu wani abu da ya rage masa a siyasa da zai nema, sai dai kawai yana jin cewa matsalolin Nijeriya sun yi tsanani sosai wanda ba zai zauna ya yu shiru ba. “Zan iya yin ritaya cikin kwanciyar hankali, amma Nijeriya na fuskantar babbar barazana. Wannan...
Wakilin falasdinawa a kutun kasa da kasa ta ICJ da ke birnin Haque na kasar Nerthelands yace HKI tana amfani da hana kayakin agaji daga ciki har da abinci shiga gaza a matsayin makami kan Falasdinawa don kashesu. Tashar talabijib ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Ammar Hijazi jakadan kasar Faladinu a cibiyoyin MDD a kasashen Turai yana fadar haka a gaban alkalai a kotun ta ICJ a jiya litinin. Ya ce HKI tana kisa ta sama da makamai, sannan tana kisa ta kasa da yunwa banda haka tana ci gaba da korar Falasdinawa daga yankin yamma da kogin Jordan tun fiye da watanni 3 da sua habata. Kutun ta bude wannan zaman ne bisa bukatar MDD ta shekara...
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ƙaddamar da shirin rigakafin mahajjata na shekarar 2025 a yankin Hadejia da ke shiyyar arewa maso gabas ta jihar. Shugaban hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Hadejia. Alhaji Ahmed Umar Labbo ya jaddada kudirin hukumar na ba da fifiko ga lafiya da kuma tsaron mahajjatan jihar. Ya ce, kare lafiyar mahajjatan jihar nauyi ne da ya rataya a wuyan hukumar. “Shirin rigakafin da muka fara yana nuna shirinmu na tabbatar da nasarar aikin Hajjin shekarar 2025. Ina ƙarfafa mahajjata su ba da haɗin kai tare da bin ƙa’idojin lafiya yayin wannan tafiya mai albarka.” “Ina kuma ƙarfafa ku da ku zama masu bin doka da...
Bari mu dauki dala a matsayin misali, tattalin arzikin Amurka na dogara ne kacokan da girman dalar Amurka. Yayin da kasafin kudinta ke gazawa wajen biyan bukatunta na cikin gida, kuma tana da al’adar dogaro da kasashen waje kan kudaden da take kashewa da ke da alaka da jingina gazawar mulkinta ga sauran kasashen duniya, kamar yadda ta yi a lokacin rikicin hada-hadar kudi na duniya a shekarar 2008, ta yaya masana’antunta za su farfado bisa wannan tsarin? Hakazalika, babu yadda za a yi Amurka ta sake zama cibiyar masana’antun duniya bayan da ta yi watsi da matsalolin da ake fuskanta a zahiri kamar sauyin yanayi, wanda ayyukan masana’antu ne suka haifar da shi tun farko. Bari mu dauka...
Bankin Duniya ya yi hasashen cewa adadin waɗanda talauci ya yi wa katutu a Nijeriya zai ƙaru zuwa kaso 3.6 cikin ɗari a 2027. Wannan dai na ƙunshe ne cikin wani rahoto da Bankin Duniya ya fitar game da tattalin arziki da kuma yanayin tsadar rayuwa a Nijeriya. Ɗaukewar wutar lantarki ta tsayar da al’amura a Sifaniya da Portugal Talata ce ɗaya ga watan Zhul Qi’ida — Sarkin Musulmi Bankin Duniya ya fitar da rahoton ne bayan ganawa tsakanin wakilansa da na Asusun Bada Lamuni na Duniya IMF kamar yadda RFI ya ruwaito. Rahoton ya ce dogaro da Nijeriya ta yi gaba ɗaya kan man fetur na ɗaya daga cikin dalilin da zai sa haɓakar tattalin arzikinta ya ci gaba...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana a yau Litinin cewa, babu wata tattaunawa da aka yi ta wayar tarho tsakanin shugabannin kasashen Sin da Amurka a baya-baya nan, haka kuma bangarorin biyu ba su cimma wata yarjejeniya ko su tuntubi juna game da batun haraji ba. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Umar Namadi, ya amince da nadin Mai Martaba Sarkin Kazaure, Alhaji Dr Najib Hussaini Adamu, a matsayin Amirul Hajj na Jihar Jigawa, kuma shugaban tawagar Gwamnatin jihar domin gudanar da aikin Hajjin 2025. Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ya sanya wa hannu kuma aka raba wa manema labarai. Gwamnan ya kuma amince da nadin mambobin tawagar Amirul Hajjin. Malam Bala Ibrahim ya bayyana cewa, mambobin sun hada da Dr. Yusuf Abdurrahman, Babban Limamin Masarautar Hadejia da Alhaji Lawan Ya’u Roni, Talban Kazaure. Sauran su ne Dr. Mahmoud Yunusa, Sa’in Dutse da kuma Alhaji Adamu Dauda Zakar, Durbin Hadejia. Sanarwar ta bayyana cewa an yi wadannan...
Majalisar Dinkin Duniya ta jaddada wajabcin komawa kan Shirin tsagaita bude wuta a Gaza Wakiliyar babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya na musamman ta jaddada a yau Litinin cewa: Akwai tsananin bukatar komawa ga Shirin tsagaita bude wuta a Gaza. A lokacin da take ba da shaida a zaman kotun kasa da kasa kan wajabcin da ya hau kan haramtacciyar kasar Isra’ila na kiyaye hakkokin mazaunan yankunan Falasdinawa, ta jaddada wajabcin isar da kayayyakin agajin na gaggawa ga Zirin Gaza, inda ta bayyana cewa: Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres na yin duk wani kokari na kawo karshen matsalar jin kai da fararen hula ke fuskanta a yankunan Falasdinawa da aka mamaye da yankunan Falasdinawa da ba a mamaye ba...
Tawagar jami’ai da ‘yan kasuwan kasar Tunisiya ta gana da mataimakin shugaban kasar Iran A yayin ganawarsa da ministan kasuwanci da fitar da kayayyaki na kasar Tunisiya Samir Ben Salem Obeid, mataimakin shugaban kasar Iran na farko na Jamhuriyar Musulunci ta Iran Mohammad Reza Aref ya jaddada cewa: Lokaci ya yi da za a dauki kwararan matakai wajen fadada dangantakar tattalin arziki tsakanin Iran da Tunusiya. A yayin taron, wanda aka gudanar a ofishinsa tare da halartar jakadan kasar Tunisiya a Iran Imed Rahmouni da tawagar da ke tare da shi, Aref ya bayyana cewa, dangantakar siyasa da ke tsakanin al’ummar Iran da Tunisiya na tafiya cikin wani yanayi mai ma’ana, amma hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya ya kasance...
Shugaban kasar Siriya ya ki amincewa da bukatar kurdawan kasar daga dakarun Democradiyyan kurdawa wato (SDF), na samar da tsarin tarayya a kasar bayan kifar da gwanatin Basshar Al-Asab. Jaridar The Nation ta nakalto shuga Al-Ahmad Sharaa yana fadar haka a jiya Lahadi ya kuma kara da cewa tsarin tarayyar barazana ce ga hadin kan kasar ta Siriya sannan tsarin tarayya ya sabawa yarjeniyar da aka kulla da kurdawan a baya-bayan nan. A wani taron da suka gabatar a makon da ya gabata, jam’iyyar kurdawan kasar ta Siriya (SDC) ta fadawa “ The National ” bayan taron kan cewa suna bukatar tsarin tarayyar a kasar Siriya don shi ne kadai zai tabbatar da hakkinsu a kasar. A cikin watan maris...
A nasa jawabin, Gwamna Dauda Lawal ya yaba da ziyarar da cibiyar ta kai Zamfara domin duba ƙoƙarin gwamnati na magance matsalar rashin tsaro a jihar. “Ina yawan cewa, idan ku ka yi ƙoƙarin shawo kan Zamfara yadda ya kamata ta fuskar rashin tsaro, za ku magance kashi 80 na matsalolin tsaro a Arewa. “Daga dukkan tsare-tsaren da na gani ya zuwa yanzu, mun mallaki abin da ake buƙata domin tunkarar waɗannan ƙalubale bisa tuntubar juna da haxin gwiwa tsakanin jihar Zamfara da ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, wannan abin a yaba ne. “Na yi farin ciki da jin cewa Tarayyar Turai ta ware wasu kuɗaɗe, duk da cewa za mu samar da...
Mataimakin ministan harkokin waje mai kula da bangaren siyasa, ya bayyana cewa; Ko kadan ba a bijiro da batun dakatar da tace sanadarin uranium a Iran ba, ko kuma batun makamanta masu linzami. Mataimakin ministan harkokin wajen na Iran ya tabbatar da cewa, wadannan abubuwan biyu wato dakatar da ci gaba da tace sanadarin uranium da kuma makamai masu linzami, jan layi ne da jamhuriyar musulunci ta Iran ba za ta bari a ketara su ba ba kuma za ta bari a bude tattaunawa akansu ba. Kwamitin da yake kula da tsaron kasa da kuma siyasar waje a majalisar shawarar musulunci ta Iran a karkashin jagorancin dan majalisar Ibrahim Ridhazi ya yi taro a ranar Lahadin da ta gabata, inda...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ƴan ta’adda da ake zargin Boko Haram ne sun kashe mutane 10 na yawucin dabbobi da kuma mambobin jami’an tsaron sa kai (CJTF) a garin Kwapre, dake cikin ƙaramar hukuma ta Hong a Jihar Adamawa. Shugaban ƙaramar hukuma, Hon Usman Wa’aganda, ya tabbatar da wannan lamarin ga LEADERSHIP ta waya a ranar Lahadi a Yola, inda ya bayyana cewa wani mutum da ya samu raunuka daga harin ‘yan ta’addan yana samun kulawar likita a wani asibiti da ba a bayyana sunansa ba. Daidaikun Kasashe Za Su Kara Karfi Idan Suka Hada Hannu Tare ‘Yansanda Sun Kama Wani Kato Bisa Zargin Cin Zarafin Wata Mata A Adamawa Wa’aganda ya ce ‘yan ta’addan sun ƙone gidaje da dama da kuma amfanin gona,...
Hakimin Kafin Hausa, Dan Amar na Hadejia, Alhaji Aliyu Usman Ginsau, ya yaba wa Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, bisa aiwatar da jerin manyan ayyuka a fadin jihar cikin shekaru biyu da suka gabata. Hakimin ya yi yabon ne yayin bikin kaddamar da wani littafi a garin Kafin Hausa. A jawabinsa yayin taron, Gwamna Umar Namadi ya yi jinjina ga marubucin littafin bisa rubuta cikakken tarihi da zai amfani al’umma, musamman matasa masu tasowa. Malam Umar Namadi ya kuma yi alkawarin umurtar ma’aikatar ilimi ta jihar da ta sayi kwafin littafin domin amfanin ɗalibai a makarantun gwamnati. Gwamna Umar Namadi ya kuma sayi kwafi bakwai na littafin a madadin iyalinsa kan kudi naira miliyan daya, yayin da...
A wani hari da jirgin sama maras matuki da dakarun kai daukin gaggawa su ka kai akan sansanin ‘yan hijira a Jahar ” Nahrun-Nil” a Arewacin Sudan sun kashe mutane da dama da kuma jikkata wasu, haka nan kuma sun yi sanadiyyar yanke wutar lantarki a yankin. Kafar watsa labaru ta “al-muhakkak” ta ce; Dakarun kai daukin gaggawar sun kai hari da jirgin sama maras matuki akan sansanin ‘yan hijira da ya yi sanadiyyar mutuwar da dama daga cikinsu da kuma yanke wutar lantarki a garin Atbarah, a jihar “Nahrun-Nil” ta arewa. Hukumar dake samar da wutar lantarki ta Sudan ta tabbatar da yankewar samar da wuta a wannan yankin saboda harin da mayakan na rundunar daukin gaggawa su ka...
A cikin sa’o’i 24 da su ka gabata an sami shahidai 39 sanadiyyar hare-haren wuce gona da iri da sojojin mamaya su ka kai a sassa mabanbanta na zirin Gaza. A birnin Khan-Yunsu Falasdinawa 3 sun yi shahada, daga cikinsu da akwai karamin yaro, yayin da wasu da dama su ka jikkata. Majiyar kiwon lafiya ta Falasdinawa ta ambaci cewa, wani masunci ya yi shahada saboda harin da ‘yan sahayoniya su ka kai masa a gabar ruwan garin Khan-Yunus. A wani labarin daga yankin na Gaza, sojojin HKI suna ci gaba da rusa gidajen fararen hula a arewacin birnin Rafah dake kudancin zirin Gaza. Tun da HKI ta sake komawa yaki gadan-gadan akan al’ummar Falasdinu a ranar 18 ga watan...
Mai magana da yawun Gwamnan, Mamman Mohammed ya bayyana sakon a matsayin kirkirarre kuma marar tushe da makama, wanda yayi hannun riga da gaskiya, ta wane bangare a cikin wannan shaci-fadi. Ya ce ba a taba yin makamancin wannan sakon ba, kuma mai wannan maganar bai taba zama makusancin Gwamna ba, ballantana ya iya gano ra’ayinsa ko ya iya hasashen yanayin siyasarsa. “Gwamna Buni bai tsaya kawai dan jam’iyyar APC ba; ko kawai gwamnan APC ba. Shi ne APC gaba dayanta, saboda sanannen abu ne cewa APC ta ratsa jijiyoyin jininsa. “Sannan gudunmawar da ya bayar wajen gina APC a matsayinsa na Sakatarenta na kasa sau biyu, kuma ya rike ragamar Shugaban kwamitin tsara taron jam’iyyar; ya...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu ya yaba da yadda tattaunawa da Amurka kan shirin Nukliyar kasar yana tafiya kamar yadda ta dace. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya nakalto Aragchi yana fadar haka bayan, bayan ya fito daga taron tattaunawa ta ukku wanda aka gudanar a birnin Mascat na kasar Omman. Ya ce bangarorin biyu a shirye suke su ci gaba da tattaunawa, ya kuma kara da cewa tawagra tattaunawa a wannan karon sun dan kara yawa, don akwai bukatar kwararrun a bangaren siyasa, sannan a zama mau zuwa a ranar Asabar mai zuwa zai hada kwararru a fanni makamashin nukliya. Ministan ya kammala da cewa idan Amurka da gaske...
Kungiyar Hamas a Gaza, ta yi allawadai da ma’aikatar sharia ta kasar Amurka wacce ta cire rigar kariya ga ma’aikatan hukumar bada agaji ta falasdinwa wanda MDD take kula da ita. Kungiyar UNRWA ta na bada agaji ga falasdinawa ne tun bayan kafa HKI da kuma korar Falasdinawa a karon farko daga kasarsu a shekara 1947. Gwamnatin kasar Amurka ta dade tana ganin an dade ba’a wargaza hukumar ba. Kungiyar ta kara da cewa wannan matakin ya nuna irin nuna son kai ga HKI wanda Amurka ta dade taba yi. Kuma ta bukaci kasar Amurka ta yi sauri ta maiha wannan rigar kariyar ga wadannan ma’aikata.
Alkaluman zuba jari na kasashen waje sun hau kan mizani mai kyau a rubu’i na farko, a kan hakan kuwa, kasar Sin za ta kara bude kofarta domin maraba da jarin waje na duniya. Har ila yau ana sa ran karin kamfanonin waje za su zuba jari da gudanar da kasuwanci a wannan kasa mai albarka. Lokaci zai tabbatar da cewa, kasar Sin ta taba zama kyakkyawan wurin saka jari da ya dace, kuma tana kasancewa haka ma a yanzu, kana babu makawa a nan gaba za ta ci gaba da zama hakan ga ‘yan kasuwa na kasashen waje. (Mai fassara: Bilkisu Xin) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin...
Mazauna Ƙauyen Batakashi da ke ƙaramar hukumar Garki a Jihar Jigawa sun yaba wa Gidauniyar Aliko Dangote bisa tallafin abinci da ta kai musu. Wasu daga cikin mazaunan da suka tattauna da wakilinmu sun bayyana farin cikinsu kan wannan karamci, tare da fatan alheri ga gidauniyar. Daya daga cikin waɗanda suka amfana da tallafin, Malam Umar Abdullahi, ya ce gidauniyar ta kawo sassauci ga al’umma bayan iftila’in gobara da ya cinye gidaje kusan 45 a kwanan nan. Haka shi ma Malam Usman Auwal, ya nuna farin cikinsa, inda ya yaba da gwamnatin jihar Jigawa da kuma Gidauniyar Dangote, bisa tallafinsu ga al’umma. A jawabinsa yayin kaddamar da rabon tallafin na buhunan shinkafa guda 500 masu nauyin kilogiram10, Shugaban ƙaramar...
Jiragen yakin HKi sun kai hare-hare da safiyar yau Asabar a birnin Gaza da hakan ya yi sanadiyyar samun shahidai da dama. Mutane 4 sun yi shahada a harin na jiragen ‘yan sahayoniyar akan wani gida dake unguwar “al-Sabrah’ a kudancin birnin Gaza. Haka nan kuma jiragen yakin na HKI sun kai wani harin da asubahin yau Asabar akan wani gidan da yake a sansanin ‘yan hijira da “Mukhayyam-Shati’i.” da hakan ya yi sanadiyyar samun shahidai 3 da jikkata wasu da dama. Majiyar Falasdinawa ta kuma ambaci cewa, da asubahin yau Asabar sojojin HKI sun tarwatsa wasu gidaje a yankunan da suke gabashin birnin Kudus. Dama a jiya Juma’a jiragen yakin HKI sun kai hari akan wata makaranta da take...

Kasar Sin Ta Goyi Bayan Rawar Da Hukumar IAEA Ke Takawa Wajen Warware Batun Nukiliyar Iran Ta Hanyar Diflomasiyya
Li ya kara da cewa, Sin da Rasha sun bayyana goyon baya ga Iran wajen karfafa tattaunawa da hadin gwiwa da hukumar IAEA. (Mohammed Yahaya) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Muscat Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Kama Hanyar Zuwa Birnin Domin Ci Gaba Da Tattaunawa Da Amurka
Ministan harkokin wajen Iran ya nufi birnin Muscat na kasar Oman a yau domin gudanar da zaman tattaunawa ba na kai tsaye ba da Amurka Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya sanar da cewa: A yau ne ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya nufi birnin Muscat na kasar Oman a karkashin jagorancin tawagar diflomasiyya da fasaha don shiga zagaye na uku na shawarwarin da ba na kai tsaye ba da Amurka ta hanyar shiga tsakanin mahukuntan Oman. Baqa’i ya bayyana cewa: Bangarorin biyu sun amince da gudanar da tarukan fasaha tare da halartar manyan jami’an shawarwari, yana mai bayanin cewa “bisa tsarin da Oman ta shirya da kuma hadin gwiwa tsakanin Iran da Amurka, za a gudanar da tarukan...

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ya Yi Gargadin Munanan Sakamakon Da Zai Biyo Bayan Kashe Falasdinawa
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran yayi kashedin kan illar ci gaba da killace Gaza da kuma hare-haren ta’addancin ‘yan mamaya Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Ci gaba da rashin hukunta ‘yan sahayoniyya kan kisan gillar da suke yi a zirin Gaza da Gabar yammacin kogin Jordan, da kuma mamayar wasu yankunan kasar Labanon da Siriya yana da matukar barazana ga zaman lafiya da tsaro a yankin. A cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Juma’a, Isma’il Baqa’i ya yi kakkausar suka kan ci gaba da ayyukan wuce gona da iri da na ta’addancin yahudawan sahayoniyya a Gaza da Lebanon.
Haka zalika, mazauna jihohin da abin ya shafa, sun koka kan wasu abubuwan more rayuwa, kamar ruwan sha da sauran makamantansu. Masu Sayar Da Ruwa Sun Kara Farashi A Kano A Jihar Kano, wani mazaunin unguwar Hotoro ta Arewa, a Karamar Hukumar Nassarawa, Malam Gambo Muhammad, ya ce; ana sayar da kowacce jarka daya kan Naira 70, kafin samun wannan karancin wutar lantarki, wanda a halin yanzu kuma ake sayar da ita kan Naira 120. “Muna wahalar samun ruwan sha da arha a wannan yanki namu, manyan hanyoyin samun ruwa a Kano su ne, ta hanyar rijiyoyin burtsatsai (Boreholes), sannan ana iya samun ruwan ne ta hanyar amfani da wutar lantarki. Don haka, da zarar an ce babu wutar lantarki,...
Kungiyar Shugabannin Arewa (NEF) ta zargi Shugaba Bola Tinubu da nadin mukaman gwamnati ba tare da daidaito tsakanin yankunan Nijeriya ba, wanda ta ce yana fifita yankin Kudu maso Yamma a kan sauran yankuna shida na kasar. Mai magana da yawun kungiyar, Farfesa Abubakar Jiddere, a cikin wata sanarwa a yau Juma’a a Abuja, ya bayyana cewa nadin da aka yi sun karkata ne wajen goyon bayan Kudu maso Yamma, yayin da sauran yankunan suka samu kadan ko kuma aka danne su. Gazawar Gwamnatin Tinubu Ce Ke Haddasa Zubar Da Jini A Filato – Ƙungiyar Dattawan Arewa Rurum Ya Shawarci Mafarautan Arewa Da Su Daina Zuwa Kudu Farauta NEF ta bayyana cewa wannan lamari ya sabawa tsarin hadin kan kasa,...
Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Jigawa ta bullo da tsarin da kowanne maniyyaci zai san masaukinsa a kasa mai tsarki tun daga nan gida najeriya. Shugaban hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana haka a lokacin taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a shalkwatar hukumar dake Dutse. Yana mai cewar, wannan shi ne karon farko da hukumar ta bullo da tsarin domin maniyyaci ya san masaukinsa a nan gida kafin zuwa kasa mai tsarki. Game da batun kudade kuwa, Alhaji Ahmed Umar Labbo ya kuma kaddamar da kwamitin canjin kudaden guzuri na maniyyata domin samun saukin canji yayin aikin Hajjin. Ya ce an kafa kwamitin ne domin bibiyar maniyyata kan canjin kudin guzuri, kasancewar wasu batagari na...
Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya ce gwamnatinsa na shirin bayar da gudunmawar kashi 50 na shinkafar da Najeriya ke bukata nan da shekara ta 2030. Ya bayyana haka ne a lokacin da yake karbar tawagar hukumar tattara kudaden shiga da kasafi (RMAFC) karkashin jagorancin shugaban kwamitin inganta kasafin kudi da kasafin kudi, Ambasada Desmond Akawor, yayin ziyarar ban girma da suka kai a gidan gwamnati dake Dutse. Ya bayyana cewa, suna noman shinkafa sau biyu a shekara, inda ya nuna cewa, a shekarar 2024 kadai, sun noma sama da hekta 200,000 na shinkafa. Ya yi nuni da cewa, a bana, suna son noma sama da hekta 250,000 wanda a shekarar 2030, burinsu ya kai kadada...
Gwamna Dauda Lawal ya amince da nadin Amirul Hajj karkashin wani kwamiti don sa ido kan ayyukan Hukumar Alhazai ta Jiha a Saudiyya don tabbatar da bin ka’idojin gida da na Saudiyya gaba daya a duk lokacin gudanar da aikin Hajjin 2025. Sakataren gwamnatin jihar, Malam Abubakar Mohammad Nakwada ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai Sulaiman Ahmad Tudu ya raba wa manema labarai, ya ce kwamitin zai fara aiki cikin gaggawa. A cewar sanarwar, mambobin kwamitin sune mai martaba Sarkin Maradun a matsayin shugaban tawagar yayin da Alhaji Habibu Balarabe aka nada a matsayin Sakatare. Sauran wakilan sune Sulaiman Adamu Gummi, Bello Isah Almufty,...
Assalamu alaikum masu sauraro sharhin bayan labarammu zai yi magana a kan ‘wani makircin da kasar faransa ta kullawa falasdinawa a gaza’ don su amfana da kwararrunsu’ wanda ni tahir amin zan karanta. ///… Shugaba kungiyar kare hakkin bil’adama masi suna [the Euro-Mediterranean Human Rights Monitor] ta fallasa wani shiri tsakanin gwamnatin kasar faransa da HKI na fitar da kwararru da kuma masana falasdinawa da suka rage a Gaza, zuwa wajen yankin, kafin HKI ta fa wani gagarumin kissan kiyashi a yankin kashe falasdinawa da suka rage a yankin. Kamfanin dillancin labaran Parstoday na kasar Iran ya nakalto Ramy Abdu shugaban kungiyar na fadar haka, ta kuma kara da cewa, offishin jakadancin kasar Faransa da ke birnin Qudus da aka...
Kasar faransa ta jaddada anniyar na ci gaba da tattaunawa kan shirin nukiliyar iran. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Faransa ya bayyana a ranar Alhamis cewa, Faransa na ci gaba da jajircewa wajen ganin an warware matsalar nukiliyar Iran ta hanyar diflomasiyya, kuma a shirye take ta ci gaba da tattaunawa da Tehran. A yayin taron manema labarai na mako-mako a birnin Paris, Christophe Lemoine ya jaddada cewa: “Muna ci gaba da jajircewa wajen warware matsalar nukiliyar Iran ta hanyar diflomasiyya, kuma a shirye muke mu ci gaba da tattaunawa da Tehran.” Wannan bayanin na zuwa ne bayan da ministan harkokin wajen Iran Seyyed Abbas Araghchi ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na X cewa, Tehran a shirye ta ke...
Ya kara da cewa, “Za mu gwabza yaki, idan yakin ya zama dole, amma kofofinmu a bude suke idan Amurka tana son a tattauna,” kana ya ce, Sin na neman hawa teburin tattaunawa da yin shawarwari ne kawai bisa daidaito, da mutuntawa da kuma samun moriyar juna. (Abdulrazaq Yahuza Jere). Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ya ƙara da cewa IEDs guda biyu da aka gano an birne su ne yankunan ƙaramar hukumar Hong, kuma an fashe su. Morris ya kuma ce ‘yansandan sun ceto wasu da aka sace guda shida tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro. Ya jinjina wa jami’an tsaron da suka taka rawar gani wajen wannan aiki, kuma ya tabbatarwa da jama’a cewa rundunar za ta ci gaba da ɗaukar matakai don tabbatar da tsaro a jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Kasar Iran Ta Bayyana Cewa Kakaba Takunkumi Kan Kasarta Ya Sabawa Hikimar Gudanar Da Zaman Tattaunawa Da Ita
Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ta bayyana cewa; Kakaba takunkumi kan kasarta ya sabawa ikirarin Amurka na yin shawarwari da ita Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi kakkausar suka kan matakin da Amurka ta dauka na kakabawa wasu gungun mutane masu alaka da bangaren makamashi, man fetur da iskar gas da kuma wasu mutane da dama masu fafutuka a shirin nukiliyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran na lumana takunkumi. A cikin wata sanarwa da ya fitar, Baqa’i ya bayyana manufar takunkuman da Amurka ta kakabawa al’ummar Iran da cewa; A fili take nuna kyama ga masu yanke shawaran Amurka kan al’ummar Iran da kuma nuna rashin mutunta doka da hakkin dan Adam ne. Ya kara da cewa: Dogaro...
Munanan azabtarwa kan fursunonin Falasdinawa a gidajen kurkukun haramtacciyar kasar Isra’ila da suka hada da fyade da dangogin azaba Rahoton da Hukumar Kula da Fursunoni Falasdinawa dakungiyar Fursunonin Falasdinawa da aka saka daga gidan kurkukun haramtacciyar kasar Isra’ila sun fiyar da rahoton hadin gwiwa a yau Alhamis, 24 ga watan Afrilun shekara ta 2025, da ya kunshi munanan shaida daga fursunonin Zirin Gaza da ke tsare a gidan yarin Negev da sansanin Ofer na gwamnatin haramtaciyar kasar Isra’ila. Rahoton ya bayyana yadda ake ci gaba da yin fyade da cin zarafi ga wadanda ake tsare da su a Gaza. Wanda ake tsare da shi a sansanin Ofer ya bayyana cewa da gangan masu gadin sansanin suke kara radadin yadda wanda...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jinjinawa kasashen Sin da Rasha a matsayin abokan hulda na kut-da-kut da kasar, yayin da ya isa birnin Beijing domin yin shawarwari da manyan jami’an kasar Sin, gabanin yin tattaunawa zagaye ta uku da Amurka kan shirin nukiliyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Abbas Araghchi ya shaida wa kafar yada labaran Iran a babban birnin kasar Sin a ranar Laraba cewa, “Sin da Rasha abokan hulda ne na kut da kut da suka tsaya tare da mu a lokutan wahala, don yana da kyau da ma’ana mu ci gaba da tuntubar juna tare da su a bangarori daban-daban, musamman ma yanzu da ake tattaunawa da Amurka.” “Ya zama dole mu sanar da abokanmu a kasar...
Jami’in ya kara da cewa, kasar Sin ba ta son gwabza yakin kasuwanci da karin harajin kwastam, amma kuma ba za ta rungume hannu ta zuba ido ba idan yakin ya kaure, yana mai nuni da cewa, idan har Amurka ta zabi fafata yakin kasuwanci, Sin za ta sha damarar yakin har sai ta ga abin da ya ture wa buzu nadi. Sai dai kuma duk da haka, ya ce idan Amurka na son a tattauna, Sin za ta bar kofarta a bude domin yin hakan. Bugu da kari, dangane da batun yadda a baya-bayan nan kafafen yada labarun kasar Panama suka soki Amurka kan yin katsalandan da nuna babakere a kasashen yankin tsakiyar Amurka, musamman a kasar ta...
Rashford ya yi watsi da yiwuwar komawa Landan, inda yace ba lallai bane ya cigaba da wasa a karkashin Ruben, inda yake da burin zama a kungiyar da zata buga gasar Zakarun Turai a badi, majiyoyi na kusa da dan wasan sun tabbatar Rashford har yanzu bai tattauna kan makomarsa ba kuma baya shirin yin hakan har zuwa tsakiyar watan Yuni. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ministan harkokin wajen Iran wanda ya ziyarci kasar China, ya bayyana cewa, tattaunawa da mahukunta wannan kasa ta yi kyau, kuma ba da jimawa ba, shugaban kasar Iran zai kai Ziyara can kasar. Ministan harkokin wajen na Iran Abbas Arakci bayan ganawa da takwaransa na China ya ce; Na yi doguwar ganawa da ministan harkokin wajen China, wacce take mai muhimmanci, kuma kusan dukkanin bangarorin da suka shafi alakar tsakanin kasashenmu biyu mu ka tattauna, haka nan kuma batutuwa da su ka shafi siyasar kasa da kasa.” Arakci ya kara da cewa; Da akwai fahimtar juna a tsakaninmu, musamman abinda ya shafi batun makamashin Nukiliyar Iran na zaman lafiya, da tataunawar da ake yi da Amurka.” Haka nan kuma ya...
Ministan harkokin wajen Iran ya jaddada cewa; Iran ba za ta taba gudanar da shawarwari kan tsaronta ba A cikin jawabinsa na shirye-shiryen shirin zaman taron Carnegie kan manufofin nukiliya na kasa da kasa da aka soke a yanzu, ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa kamfanonin Amurka za su iya cin gajiyar damar dala tiriliyan da tattalin arzikin Iran ke samarwa kuma kasuwar Iran za ta iya farfado da masana’antar nukiliyar Amurka da ta tsaya cak. Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana ta shafinsa na Twitter a takaitaccen jawabin da aka shirya yi a taron manufofin nukiliya na kasa da kasa na Carnegie, yana mai jaddada cewa, “Iran sam ba ta da niyyar yin...

Al’ummar Gaza Suna Tsananin bukatar Agaji Da Kiran A Tilastawa Gwamnatin Mamayar Isra’ila Bude Mashigar Yankin
Al’ummar Gaza sun bukaci kasashen duniya da su tilasta daukan matakin shigar da kayan agaji cikinsu Al’ummar Falasdinawa a Zirin Gaza sun yi kira ga hukumomin kasa da kasa da na Larabawa da su tilasta shigar da kayan agaji cikin yankin, duba da munanan bala’in jin kai da al’ummar yankin ke fuskanta. A cikin wata sanarwa da ya fitar, Akif al-Masri, kwamishinan hukumar koli ta al’amuran da suka shafi Falasdiwa a Gaza, ya ce: “Matsalar yunwa tana barazana ga rayuwar dubban daruruwan mutanen Gaza, yana mai cewa: Mafi yawan gidaje kusan babu kayan abinci, kuma iyalai ba za su iya samun abincinsu na yau da kullum ba.” Al-Masry ya tabbatar da cewa: Sojojin mamayar Isra’ila sun ketare dukkan iyakokin kasa...
Adadin Falasdinawa da suka yi shahada sakamakon hare-haren wuce gona da irin sojojin mamayar Isra’ila kan Gaza ya kai shahidai 51,266 Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta sanar da cewa: An isar da gawawwakin shahidai 26 da kuma wasu 60 da suka jikkata a asibitocin zirin Gaza cikin sa’o’i 24 da suka gabata. Ma’aikatar ta bayyana a cikin wata sanarwa a jiya Talata cewa adadin wadanda suka yi shahada da wadanda suka jikkata tun ranar 18 ga Maris, shekara ta 2025 ya kai shahidai 1,890 da kuma jikkata wasu 4,950 na daban. An tabbatar da cewa adadin wadanda suka yi shahada a sakamakon harin ta’addancin ‘yan sahayoniyya ya karu zuwa shahidai 51,266 da jikkatan wasu 116,991 tun daga ranar 7 ga...
Gwamnatin Amurka ta kakabawa kamfanonin kasar Iran sabbin takunkumi, duk da tattaunawar da ake yi kan shirin nukiliyar. Ofishin kula da kadarorin waje na ma’aikatar baitul malin Amurka (OFAC) ya sanar a cikin wata sanarwa jiya Talata cewa, ya kara sunan wani dan kasuwa dan kasar Iran, Seyyed Assadollah Emamjomeh da kamfaninsa cikin jerin takunkumin da aka kakabawa Iran bisa zarginsu da hannu wajen fitar da danyen mai da iskar gas a Iran. Amurka ta yi zargin cewa Emamjomeh da mukarrabansa ne ke da alhakin jigilar danyen mai na iran da aka kiyasta ya kai daruruwan miliyoyin daloli zuwa kasuwannin kasashen waje. Ma’aikatar Baitulmali ta Amurka ta yi zargin cewa kamfanin Emamjomeh ya fitar da dubunnan kayayyaki daga...
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima ya bayyana farin cikisa bisa da shirye-shiryen da Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa NAHCON, ta gudanar ya zuwa yanzu, domin aikin Hajjin shekarar 2025. Shugaban Hukumar, Farfesa Abdullahi Saleh Usman ne ya bayyana hakan ne a ranar Talata, yayin tattaunawa da manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa, bayan da ya jagoranci membobin hukumar ta NAHCON domin gabatar wa Mataimakin Shugaban Ƙasa bayanai kan shirye-shiryen aikin Hajjin 2025. Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa ne ke sa ido kan ayyukan NAHCON, kuma Hukumar ta shaida wa Sanata Kashim Shettima cewa an kammala dukkan shirye-shiryen da suka wajaba domin fara aikin Hajjin 2025 da jigilar mahajjata zuwa ƙasar Saudiyya daga ranar 9 ga Mayu, 2025. A...
A yayin ziyarar, mataimakin shugaban kamfanin LEADERSHIP Mike Okpere, ya bayyanawa uwargidan shugaban kasa irin ayyukan agaji da Kamfanin LEADERSHIP ke gudanarwa tare da yin fatan hada hannu da shirin tallafin fata na gari ‘Renewed Hope Initiative (RHI)’ da nufin karfafawa mutane 1,000 da ayyukan yi. A cewar Okpere, shirin zai mayar da hankali ne wajen samar da sana’o’in dogaro da kai a sassa daban-daban na tattalin arziki da suka hada da rini, kamun kifi, dinki da dai sauransu. Ya yi nuni da cewa, manufar ita ce a taimaka wa daidaikun mutane su samu ‘yancin cin gashin kansu da kuma zama masu amfani a cikin al’umma. Uwargidan shugaban kasar, wacce ta yi marhabin da shirin tallafin, ta...
Kamfanoni da masana’antun America da dama sun dakatar da harkokinsu, dubban mutane sun rasa aikin yi. Don haka wannan mataki bai haifar da sakamakon da Mr. Trump ke bukata ba, musamman idan aka yi la’akari da yadda kasuwar hannayen jari ta shiga cikin rudani, gami da hali na rashin tabbas da manoman America suka samu kansu biyo bayan maida martani da China tayi na ramuwar gayya. Domin kuwa sai da gwamnatin America ta kashe kimanin dala biliyan 30 wajen tallafawa manoman kasar kan asarar da suka tafka, biyo bayan harajin da China ta kakabawa wasu daga cikin amfanin gonar America da ake shigar da su China. Sabo da haka a nan za mu iya bugun gaba mu ce “Kwalliya...
Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: A shirye suke su cimma yarjejeniya yayin da suke kiyaye muradun kasarsu Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Iran a shirye take ta cimma matsaya bisa kayyade tsare-tsare tare da kiyaye moriyar kasarta, amma idan ba ta son yin shawarwari da ta daga kan matsayinta, tare da ci gaba a kan tafarkinta. Kamar yadda Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ce: Babu kyakykyawan fata kuma ba za a fitar da rai ba. Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian da yake jawabi a taron da gwamnonin kasar suka yi a ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar a yau, ya yi jawabi kan shirin tattaunawa ba na kai tsaye ba da Amurka, yana mai cewa: Tun...
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Ba su da niyyar gudanar da tattaunawa da Amurka a fili Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana ta shafinsa na Twitter a takaitaccen jawabin da aka shirya yi a taron manufofin nukiliya na kasa da kasa na Carnegie, yana mai jaddada cewa, “Iran sam ba ta da niyyar yin shawarwari da Amurka a fili a bainar jama’a.” Araghchi ya rubuta a shafinsa na Twitter da safiyar yau Talata cewa, “Lokacin da ya amince da gabatar da muhimmin jawabi a taron manufofin nukiliya na kasa da kasa na Carnegie, har yanzu Iran da Amurka ba su sanya ranar da za a yi shawarwarin zagaye na gaba ba, wanda za a fara...
Jamuhuriyar Musulunci ta Iran ta jaddada matsayinta kan batun tace sinadarin yuraniyo. Mai magana da yawun gwamnatin Iran Fatemeh Mohajerani ta bayyana cewa, Iran na kokarin yin shawarwari ne domin samar da amana da samar da gaskiya game da shirinta na nukiliya domin dage takunkumi kanta. A cikin taron manema labarai na mako-mako da ta gudanar a jiya litinin, Mohajerani ta mayar da martani ga wata tambaya game da tattaunawar da ake yi tsakanin Iran da Amurka, inda ta ce, shin bangarorin biyu sun cimma matsaya dangane da kasar da za a aike da hajojin uranium da Iran ta inganta? Shin Iran ta amince ta mika wadannan haja zuwa Rasha? Ta ce: Ina so in bayyana dangane da kashi na...