Gwamnatin kasar Pakisatan ta basa sanarwan kai hare-haren maida martani kan kasar Indiya, inda tayi amfani da makamai masu linzami wadanda suka fada kan rumbun ajiyar makaman kasar ta Indiya da wani filin tashin jiragen.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar sojojin kasar Nacewa daga wadannan wurare biyu ne makaman kasar Indiya suka tashi suka kuma yi sanadiyyar kashe mutane fararen hula a cikin kasar Pakisatan a makon da ya gabata.

Labarin ya kara da cewa sojojin Pakisatan sun bawa wannan farmakin maida martani suna [Bunyanun Marsus) inda suka dauki aron Kalmar daga wata ayar al-kur’ani mai girma.

Hare-haren maida martanin sun auku ne a safiyar yau Asabar, don haka har yanzun bamu ta bakin kasar Indiya ba.

Yaki a tsakanin kasashen biyu ya soma ne daga ranar 22 ga watan Afrilun da ya gabata, inda kasar Indiya ta zargi Pakistan da hannu a cikin hare-haren da wasu yan ta’adda suka kai a yankin Pahalgam na yankin Kashmir da ke karkashin ikon kasar Indiya inda mutane 26 masu yawan shakatawa ko bude ido suka rasa rayukansu.

Ba tare da bata lokaci ba sojojin kasar Indiya suka fara cilla makamai kan kasar Pakistan, daga ciki har da farmakin da ta kira “sindoor”.

Da farko kasar Pakisatan ta musanta zargin ta kuma yi allawadai da hare-haren na ta’addanci a cikin kasar Indiya. Sai dai tunda kasar Indiya bata saurareta ba, bata da zabi in banda maida martani a safiyar yau Asabar.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: kasar Indiya

এছাড়াও পড়ুন:

Yemen ta sake kai hari kan filin jirgin saman Isra’ila da makami mai linzami

Dakarun Yeman sun sanar da sake kai hari kan filin jirgin saman Isra’ila na Ben Gurion da ke kusa da birnin Tel Aviv da makami mai linzami mai linzami.

Bayanai sun ce ko wannan karo tsarin garkuwa daga hare haren sama na Amurka samfarin THAAD ya gaza kakkabo harin.

Sanarwar da rundunar ta fitar ta hannun mai magana da yawunta Birgediya Janar Yahya Saree ta bayyana cewa, an kai harin ne yau Juma’a.

Kakakin rundunar ‘yan Houthi Yahya Saree ya ce, sun yi amfani da makami mai linzami mai gudun tsiya,”

Isra’ila dai ta sha alwashin mayar da martani mai karfi kan harin.

Kasar Yemen dai na mai kai hari kan kaddarorin Isra’ila domin nuna goyan baya ga al’ummar Gaza da ke fuskantar hare-hare daga Isra’ila.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yemen ta sake kai hari kan filin jirgin saman Isra’ila da makami mai linzami
  • ’Yan kungiyar asiri sun kashe masu shirin tafiya NYSC a Bayelsa
  • Gwamna Buni ya tallafawa iyalan sojojin da suka mutu 
  • Aragchi: Muna Bukatar Rage Zaman Daradar Da Kuma Tabbatar Da Zaman Lafiya A Tsakanin Pakisatan Da Indiya
  • An Gano Sunan Bayahuden Da ya Kashe Yar Jaridar Tashar Talabijin Ta Aljazeera Shirin Abu Akila
  • Sojoji sun kama mutum 4 kan zargin ta’addanci a Taraba
  • Falasdinawa Sun Yi Shahada A Hare-Haren Da Sojojin Isra’il Suka Kai Gidan Cin Abinci Da Kasuwa A Gaza
  • An Tabbatar Da Ficewar Sanata Sumaila Daga NNPP Zuwa APC A Majalisa
  • Duniya Ta Gano Damammaki Masu Kyau Daga Kasuwar Kasar Sin A Yayin Hutun Ranar Ma’aikata Ta Duniya