2025-12-06@21:54:26 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2293

«Firimiyar Ingila»:

    Rahotanni sun bayyana cewa dakarun tsaron kasashen pakistan da Afghanistan sun yi musayar wuta mai tsananin a iyakokin kasashensu, kuma yayi sanadiyar mutuwar mutane 5,  hakan na nuna irin rikicin dake tsakanin kasashen masu makwabtataka da juna, bayan sun cimma yarjejeniyar sulhu a kasar saudiya amma da alama babu ci gaban da aka samu. A...
    Fira ministan kasar Qatar shaikh mohammad bin Abdurrahaman al thani yayi gargadi game da ci gaba da kai hare-hare da kame falasdinawa da HKi ke yi a yankin gaza, ya jaddada cewa shirin da shugaban Amurka ya bullo da shi na zaman lafiya zai zama gaskiya ne idan isra’ila ta janye dukkan sojojinta a yankunan...
    Wasu mutane uku sun rasu yayin da suke tsaka da aikin yasar rijiya a garin Badume da ke Ƙaramar Hukumar Bichi a Jihar Kano.  A yayin da suke aikin haƙar rijiya, ɗaya daga cikinsu ya shiga domin yasowa biyu kuma na janyo ƙasar da aka haƙo. Ana cikin haka igiyar ta tsinke, inda nan take...
    Kotu ta yanke wa wani wanda ya yi wa wata yarinya ’yar shekara 12 fyaɗe hukuncin ɗaurin rai-da-rai a Ƙaramar Hukumar Guba ta Jihar Yobe. Babbar Kotun Jihar Yobe da ke zaune a ƙaramar hukumar Gujba ta yanke wa mutumin mai shekaru 31 mai suna Ali Kwano. An gurfanar da shi ne a kan zargin...
    Bayan da ƙasashen biyu maƙwabtan juna na Congo da Rwanda suka sanya hannu a yarjejeniyar zaman lafiya da Donald Trump ya bayyana a matsayin mai cike da tarihi, jagoron na Amurka ya jinjinawa shugabannin ƙasashen biyu waɗanda ya ce sun yi hangen nesa wajen amincewa da kawo ƙarshen zubar da jinin dubban mutane tsawon shekaru....
    Pars Today – Hanieh Rostamian, jarumar harbin bindiga ta Iran, za ta fafata a wasan karshe na gasar cin kofin duniya. Za a fara gasar cin kofin duniya ta 2025 gobe, Asabar, a Qatar. A cewar Pars Today, tunda manyan ‘yan wasan harbi na duniya suna shiga wannan gasar, Hanieh Rostamian—wanda a halin yanzu yana...
    Pars Today – Ziyarar da tawagar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kai Rasha a fannin sadarwa da fasahar sadarwa ta zamani ta haifar da sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin gwamnatoci guda 20, da kuma kwangiloli biyar tsakanin kamfanoni daga kasashen biyu. Meysam Abedi, Mataimakin Ministan Sadarwa da Fasahar Sadarwa ta Duniya kan Fasaha...
    Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ce gwamnatinsa ta kashe kusan Naira biliyan 100 a wannan shekara domin inganta tsaro a faɗin jihar. Ya bayyana haka ne lokacin da ya ziyarci Sarkin Uba, inda ya yi masa jaje kan hare-haren da suka yi sanadin mutuwar mutane da dama. Jami’an tsaro sun kama masu garkuwa...
    Rahotanni daga kasar Lebanon sun ambaci cewa da marecen yau jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai hare-hare a garuruwan Mahruna,jibaa, Bar-ishit da Majadil dake kudancin Lebanon. Hare-haren sun rusa gidaje da dama na garuruwan da su ka kai wa harin. Wannan harin dai yana faruwa ne kwana daya bayan da Lebanon ta aike da...
    Rundunar ’yan sandan jihar Borno ta kama matashin nan da ake zargi da kashe makwabciyarsa a unguwar Shuwari II, a garin Maiduguri babban birnin jihar, ta hanyar daba mata wuka. Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:00 na dare a ranar Talata. Amurka...
    Ƙasar Amurka ta yi barazanar sanya takunkumin izinin shiga kasarta ga ’yan Najeriyar da aka gano suna ɗaukar nauyi ko goyon bayan ayyukan da ke take ’yancin yin addini da yi wa Kiristoci kisan kiyashi. Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ya bayyana haka a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafin X, inda...
    Hukuma ko kungiyar ‘The Guinness World Records organization’ ta bada sanarwan cewa daga yanzu ta daina karban duk wata bajinta ko wani al-amiri da ya shafeta daga HKI saboda ta’asan da take aikatawa a Gaza, wanda kuma kungiyoyin kare hakkin bil’adama a duniya sun tabbatar da cewa, kissan kare dangine. Kamfanin dillancin labaran IP na...
    Hukumar bada agaji da samar da ayyukan ga falasdinawa na majalisar dinkin duniya UNRWA ta fadi cewa isra’ila ta hana motoci makare da kayan agaji guda 6000 shiga yankin Gaza da suke dauke  da abinci magunguna da za su iya wadatar da yankin na tsawon watanni 3. Kakakin kungiyar ta UNRWA Adnan Abu Hasna ya...
    Daga Aliyu Muraki Hukumar Ilimi Matakin Farko ta Jihar Nasarawa (NSUBEB) ta yi barazanar kamawa tare da gurfanar da iyayen da  ‘ya’yansu ba sa zuwa makaranta a jihar. Shugaban Hukumar, Dr. Kasim Mohammed Kasim ne ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai a matsayin wani bangare na ayyukan babban  taron inganta ilimi da hukumar...
    Wani ya yi shigar mahaifiyarsa da ta mutu ya je karvar kuxin fanshonta Ana binciken wani tsohon ma’aikacin jinya a qasar Italiya bisa zargin ya yi shigar mahaifiyarsa da ta mutu kuma ya je ma’aikatar fansho a matsayin mahaifiyarsa don neman fanshonta. Haka kuma an gano ya voye gawarta a cikin gidansa har tsawon shekaru...
    Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar gwagwarmaya ta Hamas tayi tir da matakin da isra’ila ke dauka na tsauraran mataken shigar da kayan agaji zuwa yankin gaza musamman bangaren sansanin yan gudunn hijira da kuma tanti-tanti  da aka yi. Kakakin kungiyar hamas Hazem Qaseem ya jaddada cewa mafakar da suka rage a yankin tantuna ne da...
    Shugaban kungiyar kula da tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika kuma shugaban kasar saliyo Julius mada Bio yace ya tattauna da shugaban mulkin soji da ya yi juyin mulki a kasar Guinea Bissau , a kokarin da suke yi na ganin an yi aiki da kundin tsarin mulki a yankin na yammacin Afrika. A cikin jawabin...
    An gudanar da bikin cika shekaru 41 da kafa kungiyar hadin guiwa ta tatalin arziki ta ECO a nan birnin Tehran ne a jiya litinin  inda sakatare janar din kungiyar Eco Majeed khan da ministan aladu reza salihi –amiri suka gabatar da jawabai a wajen, da ya shafi irin ci gaba da kungiyar ta samu...
    Shugaban Ƙungiyar Iyaye na Jami’ar MAAUN, Alhaji Mustapha Balarabe, ya ƙaryata rahotannin da ke cewa jami’ar ta yanke wasu kuɗi masu yawa domin yaye ɗalibai. A wata sanarwa da ya fitar tare da sakataren ƙungiyar, Hajiya Habiba Sarki, ya ce koken da aka kai wa PCACC da kuma rahotannin da aka wallafa ba su da...
    Daga Ali Muhammad Rabi’u  ’Yan bindiga kimanin guda huɗu dauke da makamai sun kai hari a garin Eruku da ke ƙaramar hukumar Ekiti a jihar Kwara, inda suka sace wani manomi mai suna Mista Aasaru. Rediyon Najeriya ya ruwaito  cewa wannan hari shi ne na biyu da aka kai wa garin Eruku cikin wata guda,...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta bayyana cewa Isra’ila na jinkirta aiwatar da mataki na biyu na yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma. Mai magana da yawun Hamas, ya bayyana cewa duk da cewa kungiyar ta na girmama yarjejeniyar tsagaita wuta sosai, gwamnatin mamayar Isra’ila na jinkirta aiwatar da mataki na biyu na yarjejeniyar, wanda...
    A daidai lokacin ziyarar Paparoma Leo na XIV  shugaban Katolika na duniya a kasar Lebanon, kungiyar Hezbollah ta fitar da wata sanarwa a hukumance da aka aike masa. Kungiyar ta yi maraba da ziyarar Paparoma, ta kuma jaddada muhimmancin Lebanon a matsayin kasa mai bambance-bambance na addini da kabilu da akidu, wadda al’ummominta suke bukatar...
    A birnin Dublin na kasar Ireland an cire sunan tsohon sugaban “Isra’ila” Chaim Herzog,daga wata lambu na shakatawa a unguwar Ratgar, tare da maye gurbinsa da sunan Shahida Hind Rajab. Jaridar “Vadiot-Ahranot” ta ‘yan sahayoniya ta buga labarin cewa, hukumar birnin Dublin a Ireland ta amince da a sauya sunan shugaban “Isra’ila” ta shida Chaim...
    Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Ƙwarewa ta Najeriya (NARD) ta dakatar da yajin aikin da ta shafe kwanaki 29 tana yi, bayan wani taron gaggawa da Majalisar Koli ta ƙungiyar ta gudanar a ranar Asabar. Shugaban NARD, Muhammad Suleiman, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya wallafa, inda ya bayyana cewa an dakatar da...
    Wata fitacciyar sinima a Faransa, Cinematheque Francaise, ta rufe ɗakunan kallonta na tsawon wata guda saboda yaɗuwar kuɗin cizo da aka gano a cikinta Cibiyar wadda ke gabashin birnin Paris ta ce rufe sinimar zai ba ta damar tabbatar da cewa masu kallo sun samu “aminci da kwanciyar hankali” bayan ƙorafe-ƙorafen da aka yi na...
    Rahotanni sun bayyana cewa iran ta yi tir da sanarwar da shugaban Amurka ta fitar na rufe sararin samaniyar kasar venuzuwela kuma ta bayyana shi a matsayin keta dokokin kasa da kasa, da kuma dokokin kula da zirga –zirgar jiragen sama. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Isma’ila Baghae ne ya fitar da wannan sanarwa...
    Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bada sanarwan rufe zirga zirgan jiragen sama kwata-kwata a kan sararin samaniyar kasar Venezuel daga yau, a cikin shirinsa na fara mamayar kasar. Tashar talabijan ta Al-Mayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto Trump yana fadar haka a shafinsa na sadarwa True Social. Ya kuma bayyana cewa wannan sako ne...
    Pars Today – Sakataren Majalisar Tsaron Ƙasa ta Iran ya jaddada cewa ayyukan Isra’ila, ciki har da kisan kai da ayyukan ta’addanci, ba komai ba ne illa wauta, domin “muna da dubban ƙwararrun nukiliya a Iran.” Ali Larijani, Sakataren Majalisar Tsaron Ƙasa ta Iran, ya ce a ranar Juma’a a wata hira da HUM News...
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar Pakistan ta bayyana ziyara da babban sakatare tsaron kasar Iran Dr Ali Larijani ya kai kasar a matsayin babban ginshiki a alakar dake tsakanin Tehran da kuma Islam Abad , domin ya kara karfafa danganatar dake tsakanin a bangarorin siyasa, tattalin arziki, da kuma tsaro dake tsakanin kasashen makwabtan juna. Kasashen...
    Asibitin Kula da masu lalurar kwakwalwa da ke Kaduna na Jagorantar Sauye-Sauren Lafiyar ƙwaƙwalwa a Arewacin Najeriya — Farfesa Aishatu Armiya’u Ta Bayyana Muhimman Nasarori a Shugabanci da Ayyuka da Hadin Gwiwa Shugabar gudanarwa kuma daraktar lafiya ta Asibitin kula da masu lalurar ƙwaƙwalwa dake Kaduna, Farfesa Aishatu Yusha’u Armiya’u, ta tabbatar da kudirin asibitin...
    Hukumar ƙwallon ƙafa ta Afrika (CAF), ta sanar da cewa daga yanzu kowace ƙasa da za ta taka leda a Gasar Cin Kofin Afrika za ta je da ’yan wasa 28, maimakon 23 da ake amfani da su a baya. CAF, ta ce ta ɗauki wannan matakin ne domin rage matsalar samun raunin da ’yan...
    Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayar da umarnin a fara tsara yadda za a shigar da kungiyar “Muslim Brotherhood” a cikin jerin kungiyoyin ta’addanci na waje. Kungiyar ta ce, babu wani dalili da Amurkan za ta iya samu da zai tabbatar mata da cewa kungiyar tana ayyukan ta’addanci. Haka nan kuma kungiyar ta ce,...
    Ana fargabar cewa wata mata mai suna Success ta kashe wata yarinya mai shekaru bakwai, Alicia Olajumoke, a unguwar Rumueme da ke birnin Fatakwal na Jihar Ribas. Mazauna yankin sun shaida wa Aminiya cewa matar da ake zargin tana da kusanci da dangin mahaifiyar yarinyar, wacce ita kaɗai ce a wurin iyayenta. El-Rufai ya koma...
    Ɗan wasan gaban ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid, Kyalian Mbappe ya samu nasarar zura kwallaye huɗu rigis a ragar Olympiacos a wasan mako na biyar na kofin zakarun nahiyyar turai da suka buga a yammacin jiya Laraba. Real Madrid dai caskara Olympiacos 4-3 ne a wasan, lamarin da ya ba ta damar haɗa...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ta gano harsasai 210 da aka jefar a kan babbar hanyar Zariya zuwa Funtuwa, a unguwar Dogo Itace da ke Samaru, Zariya. Lamarin ya faru ne lokacin da DPO na Samaru tare da tawagarsa suke sintiri a kan hanyar. Allah Ya yi wa Sheikh Dahiru Bauchi rasuwa Juyin mulki ya...
    Ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ta bada sanarwan cewa yawan Falasdinawa wadanda sojojin HKI suke kashewa a Gaza yana karuwa duk tare da abinda suka kira tsagaiya budewa Juna wuta. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta nakalto ma’aikatar na cewa a cikin sa’oii 24 da suka gabata sojojin HKI sun kashe Falasdinawa 2...
    Kungiyar ta kasa da kasa mai gudanar da a ayyukan agaji, ta sanar da janye ma’aikatanta daga asibitin Darfur, bayan da aka bude musu wuta, ya kuma kai ga kashe daya daga cikin masu aikin agaji. Kungiyar ta yi kira ga rundunar kai daukin gaggawa RSF da ta tabbatar da tsaro da kuma kiyaye lafiyar...
    Babbar Mai Shari’ar ta kasa , Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun, ta jaddada cewa alkalai suna da nauyin tabbatar da adalci cikin gaskiya da daidaito a lokacin da matsalolin tattalin arziki ke kara tsananta wa al’umma. Ta bayyana haka ne a Taron Alkalai na Shekara-shekara Karo na 26, wanda Cibiyar Nazarin Shari’ar Musulunci ta Jami’ar Ahmadu...
    Kungiyar Hizbollah ta kasar Lebanon ta bayyana cewa Isra’ila na yin kuskure idan ta na tunanin kashe-kashe da kisan gillar da ake wa mambobi da kwamandojinta zai kawo karshen kungiyar. Wannan na zuwa ne bayan kisan gillar da Isra’ila ta yi wa babban kwamandan sojin kungiyar da wasu makusantansa a ranar Lahadi, a wani hari...
    Gwamnonin jihohin  Arewa 19 za su gudanar da muhimmin taro a ranar Asabar, 29 ga Nuwamba, domin tattauna matsalolin tsaro da suka addabi yankin. Mai bai wa Gwamnan Nasarawa shawara na musamman kan harkokin jama’a, Peter Ahemba, ne ya sanar cewa, taron gwamnonin Arewa da aka shirya a Kaduna zai samu halartar manyan sarakunan gargajiya....
    Kakakin kungiyar Hamas yayi Tir da ci gaba da kai hare haren da Isra’ila ke yi a fadin yankin Gaza, yayi gargadin cewa wadannan matakai suna barazana sosai ga yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma tsakaninta da Isra’ila a kasar masar a watan Jiya. A cikin wani bayani da Hazem qassem yayi gargadin...
    Kociyan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool, Arne Slot, na fuskantar matsin lamba saboda rashin kataɓus da ƙungiyar ke fama da shi a bayan nan. A yammacin jiya Lahadi ne Nottingham Forest ta je har filin wasa na Anfield, inda ta lallasa Liverpool da ci 3-0 a wasan mako na 12 na gasar Firimiyar Ingila. Mayaƙan...
    A dare na uku na makokin shahadar Fatiman Azzahra (s) diyar manzon All.. (s) shuwagabannin bangarorin gwamnati 3 a nan Iran sun sami halattan makakinta (s) a Husainiyyar Imam Khomanin(q) dake nan Tehran. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayyana cewa, shugaban kasa Dr Masoud Pazeshkiya, Alkalin alkalai Hujjatul Islam Sheikh Ibrahim Ijeyi...
    Yayan kungiyar yan ta’adda ta ‘the Islamic State West African Province (ISWAP) ta bada sanarwan kamawa da tsare yan mata 13 a karamar hukumar Askira-Uba na jihar Borno a jiya Lahadi. Jaridar Daily Trust ta Nageriya ta nakalto Abdullahi Askira dan majalisar dokokin jihar Borno mai wakiltan Askira yana tabbatar da labarin ya kuma kara...
    Ofishin Yada Labarai na Gwamnatin Gaza ya ce Isra’ila ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta ta Gaza da Amurka ta shiga tsakani akalla sau 497 cikin kwanaki 44, inda ta kashe daruruwan Falasdinawa tun lokacin da yarjejeniyar ta fara aiki a ranar 10 ga Oktoba. Ofishin ya ce Isra’ila ce ke da alhakin dukkan tabarbarewar al’amuran...
    Babban magatakardar MDD Antonio Guterres ya yi kira ga shugabannin kasashen duniya da suke taro a birnin  Johannesburg na kasar Afirka Ta Kudu da su warware matsalar rashin daidaito a cikin harkokin kasuwanci a tsakanin kasashe. Babban magatakardar MDD wanda ya gabatar da jawabi a wurin taron na G 20 ya yi Ishara da gibin...
    Shugabannin kasashen duniya da su ka halarci taron kungiyar G 20 sun amince da kudurin akan hanyoyin bunkasa tattalin arziki, sai dai ba a fitar da da cikakken bayani akan abinda ya kunsa ba. Gwamnatin Donald Trump ta ki halartar taron na kungiyar G 20 da aka bude jiya a kasar Afirka Ta Kudu, da...
    Kasashen Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Habasha sun rattaba hannu ne akan yarjejeniyar aikin soja a tsakaninsa a wurin baje kolin jiragen sama na wannan shekara ta 2025 a birnin Dubai. A bangaren Hadaddiyar Daular Larabawa, wanda ya wakilce ta shi ne Janar Ibrahim Nasir al-Alawi, wanda wakilin ma’aikatar tsaro ne, sai kuma janar Rashid...
    Ƙungiyar Ƙwadago ta Ma’aikatan Wutar Lantarki ta Ƙasa (NUEE) ta yi barazanar dakatar da dukkan ayyukan samar da wutar lantarki a faɗin Najeriya, sakamakon harin da ta ce jami’anta sun fuskanta a Jihar Imo. Ƙungiyar ta bayyana cewa wasu jami’an ’yan sanda ɗauke da makamai ne suka kai wa ma’aikatanta hari a Egbu 132/33kB Transmission...
    Shuwagabannin kasashen duniya a kungiyar G20 sun gabatar da jawabin bayan taro da kuma matsayin kungiyar a cikin al-amura da dama a duniya, duk tare da kauracewa taron wanda  shugaban kasar Amurka Donal Trump yayi. Shafin yanar gizo na labarai AfricaNews ya nakalto shugaban afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa  yana gabatar da jawabi bayan taron...