2025-05-02@22:24:41 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3381
«Gwamna Idris»:
Shugaban INEC ya jaddada muhimman ci gaban da ya samo asali daga sauye-sauyen da suka gabata da suka hada da fadada jaddawalin zabe, gyare-gyare don ba da damar kwanaki 180 tsakanin zaben fid da gwani na jam’iyya da zabe daga kwanaki 60 ya warware jinkirin kayan aiki. Ya ce wannan ya tabbatar da cewa an gudanar da babban zaben 2023 ba tare da jinkirta ba, a karon farko tun 2010. Ya ce wani ci gaba kuma ya hada da samar da kayan aiki na cikin gida, yana mai cewa a karon farko tun 1999, an buga dukkan kayan zabe masu muhimmanci a Nijeriya, Farfesa Yakubu ya bayyana kalubalen da ke bukatar kulawar majalisa, da suka hada da...
Babban darektan hukumar kula da tattara bayanai da yada su ta bangaren teku ta kasar Sin, Shi Suixiang, ya bayyana cewa, manufofin tallafi da aka bullo da su a matakai na tsakiya da na kananan hukumomi sun karfafa ci gaban yawon shakatawar. Ya kara da cewa, gwamnatin tsakiya ta inganta fadada hanyoyin jiragen ruwa da kayayyakin yawon shakatawa yayin da kuma ake kara daidaita tsarin rajistar jiragen ruwa da kuma shigar da su cikin hada-hada. Wasu manazarta dai sun bayyana cewa, a sa’ilin da lokacin goshin damina ke gabatowa, ana sa ran yawon shakatawa na bakin teku da tsibirai a yankin kudu maso gabashin kasar Sin ya bunkasa, tare da kara samun balaguro ta ruwa da nufin cin...
Ƙungiyar Yarabawa zalla ta Afenifere, ta shaida wa masu sukar Shugaba Bola Tinubu cewa zai yi wa’adi biyu ne a kan karagar mulki. Kungiyar ta kuma ce rashin adalci ne a hana Tinubu ya sake tsayawa takara a zaɓen 2027, ganin cewa jigo a Arewa, tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, a baya ya yi cikakken wa’adi biyu a ofishi shugaban ƙasa. Yadda aka yi bikin yaye sabbin matuƙa jiragen Rundunar Sojin Saman Najeriya An kama mutane 1,611 da ƙwato motoci 21, babura 51 da aka sace a Abuja Afenifere ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da sakataren ƙungiyar ta ƙasa Kole Omololu ya sanarwa manema labarai a ranar Juma’a, wadda Daily Trust ta samu. “An bar Buhari ya cika...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa gwamnatin JMI ba zata amince da tattaunawa tare da kara tsuge takunkuman tattalin arziki na koli da aka dorawa kasar ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a yau Jumma’a ya kuma kara da cewa yin haka sabawa dokokin kasa da kasa ne. Har\ila yau take hakkin mutanen kasar Iran ne da kuma shigar da shakku a cikin tattaunawar da Amurka take yi da kasar. Kafin haka dai gwamnatin kasar Amurka ta bada sanarwan kakabawa mutanen da kamfanoni 7 wadanda suke mu’amala da kasar Iran a kasashen UAE da Turkiya saboda sayan danyen man kasar Iran da kuma sinadaran manfetur na kasar. Har’ila...
Limamin da ya jagoranci sallar Jumma’a a nan Tehran Hujjatul Islam kazim Sadiki ya bayyana cewa kasar tana da kwararru wadanda suke da kwarewa a sanin fasahar nukliya da kuma hanyoyin dublomasiyya a tattaunawar da Iran take da Amurka dangane da shirin Nukliyar kasar. Tashar talabijin ta Al-alam a nan Tehran ta nakalto limamin yana fadar haka a khudubobinsa na sallar Jumm’a. Ya kuma kara da cewa, lalle tawagar kasar Iran a tattaunawar suna ci gaba da tattaunawa, sannan suna matukar iyawarsu don kare hakkin Iran na mallakar Fasahar Nukliya wacce take da matukar muhimmanci. Hujjatul Islam Sadiki ya kara da cewa tawagar Iran a wannan tattaunawar, suna amfani da tajruban da suke da shi a tattaunawar baya, sannan sauran...
Gwamnatin HKI ta kai farmaki kan tawaga masu rajin kare hakkin bil’adama dauke da kayakin agaji a cikin jirgin ruwa dauke da kayakin agaji zuwa zirin Gaza wacce ta hana shigar abinci cikinsa kimani watanni biyu da suka gabata. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto majiyar gwamnatin tsibirin Malta na cewa HKI ta kai hari kan jirgin agajin ne tare da amfani da jirgin yaki wanda ake sarrafashi daga Nesa, a ruwayen kasa da kasa. Labarin ya kara da cewa jirgin agajin ya tashi daga tsibirin Malta da nufin isa Gaza, saboda isar da kayakin agajin da suke dauke da su zuwa Gaza, wacce aka killace. Yahudawan saun kai hari da misalign karfe 12.23 a lokacin Malta...
Likitoci wadanda basa goyon bayan kissan kare dangi wanda HKI tare da taimakon Amurka suke yi a Gaza, sun fito zuwa majalisar dokokin kasar Capotol tare da bukatar a kawo karshen kisan kiyashi a Gaza. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta bayyana cewa likitocin sun bukaci majalisar dokokin kasar su gaggauta kawo karshen kissan kare dangin da ke faruwa a gaza, kuma a gaggauwa kawo karshen kissan falasdinawa da kuma bude kofofin shigar da agaji zuwa cikin yankin. Inda miliyoyin Falasdinawa daga ciki har da yara miliyon guda suke mutuwar yunwa ga kuma kissa da makami ta sama.
Jami’an tsaro a tarayyar Najeriya sun kama wani jami’in sojan kasar Burtania mai suna Manjor Micah Polo tare da zarginsa da shigo da makamai kasar sannan da kokarin fasa korinsu zuwa wajen kasar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa, an lama manjo polo ne da makamai wadanda suka hada da MK-47 50, bindiga mai jigida 6 da kuma manya-manyan albarusai har 3000. Labarin ya kara da cewa, Nigeria’s Department of State Services (DSS), ta bada labarin cewa ta kai sumame a wani wuri a birnin Asaba na Jihar Delta inda ake fama da yanbinga masu fasa bututan mai da kuma sace mutane don karban kudaden fansa inda suka kama makaman sannan sun kama Manjo Polo a...
Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta yaye sabbin matuƙa jiragen sama 35 bayan sun kammala samun horo. Babban Hafsan Rundunar, Iya Mashal Hassan Abubakar, ne ya sanya sabbin matuƙa jiragen anini a yayin bikin da aka gudanar a Makarantar Tukin Jirgi na rundunar (401 FTS) da ke Kaduna. Yayen nasu ya zo ne watanni kaɗan bayan rundunar ta mallaki sabbin jiragen yaki guda 12, waɗanda suka ƙara mata ƙaimi wajen ayyukan samar da tsaro da kuma ta’addanci. A wani taro da ya gudanar da tsofaffin sojojin rundunar a Kaduna, Iya Marshal Hassan Abubakar ya shaida musu cewa rundunar tana jiran karin jiragen yaƙi guda 34. Ya buƙaci waɗanda aka yayen nasu da su yi amfani da wannan dama wajen cika...
“Siyasar da na sani ba ita ce abin da ke faruwa a yau ba. Siyasar da na sani ita ce gwagwarmayar muradun jama’a don tabbatar da cewa suna da kyakkyawar rayuwa a duk fannoni kamar ilimi, ruwa, kiwon lafiya, da sauransu. “Na kasance a siyasa tsawon shekaru 48 da suka gabata,” in ji shi. Ya bayyana yanayin siyasa a matsayin wanda ke cike da rudani da son kai, yana mai jaddada cewa ‘yan siyasa da talakawa sun rikice. “Saboda wannan, akwai rudani ga masu nema da kuma wadanda ake nema. Masu neman suna makancewa, ba su da imani ko tausayi. Manufarsu kawai ita ce tabbatar da matsayi a gare su. A halin yanzu, talakawa sun tsunduma ciki yunwa, talauci, da...
Rundunar ’yan sandan birnin tarayya Abuja ta ce ta kama mutane 1,611 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban da suka haɗa da safarar miyagun ƙwayoyi tare da ƙwato motocin sata guda 21, babura 51 da kuma miyagun ƙwayoyi. Kwamishinan ’Yan sanda CP Ajoa Saka Adewale, wanda ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da motocin da aka ƙwato, baburan da sauran kayayyaki a gaban manema labarai a ranar Juma’a a Abuja. Sarki Sanusi II ya naɗa sabon Galadiman Kano da wasu 4 Ra’ayin Jama’a kan ziyarar Tinubu Katsina Ya ce an kama mutane 16 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban na satar mota. Ya kuma ce shida daga cikin motoci 21 da aka ƙwato an mayar wa...

Layukan Dogo Na Kasar Sin Sun Gudanar Da Sufurin Miliyoyin Fasinjoji A Ranar Farko Ta Hutun ‘Yan Kwadago
Layukan dogo na kasar Sin sun gudanar da sufurin kusan fasinjoji miliyan 23.12 a jiya Alhamis, ranar farko ta bikin ranar ‘yan kwadago ta duniya da aka saba yi duk shekara a watan Mayu, kamar yadda kamfanin sufurin layin dogo na kasar Sin ya bayyana. A cewar alkaluman da kamfanin ya fitar a yau Jumma’a, wannan adadi ya nuna karuwar kashi 11.7 cikin dari na adadin da ake samu a mizanin shekara-shekara. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Yunwa Ta Kazanta A Sansanonin ‘Yan Gudun Hijira Tun Bayan Da Majalisar Dinkin Duniya Ta Dakatar Da Ayyukanta
Ministan harkokin jin kai da rage radadin talauci na UNOCHA, Farfesa Nentawe Goshwe, ya sanar da yunkurin hukumar na ficewa daga Nijeriya. Ya shaida hakan ne a yayin taron kara wa juna sani kan tsarin da za a dauka a Nijeriya, wanda aka gudanar a cibiyar yaki da ta’addanci ta kasa, ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro a Abuja. A cikin wata wasika da aka yada a shafin intanet na hukumar a ranar 11 ga Afrilu, shugaban hukumar ta UNOCHA, Tom Fletcher ya ba da sanarwar yanke ayyuka sakamakon karancin kudade na kusan dala miliyan 60 a shekarar 2025. Hukumar ta ce za ta rage ayyukanta a Nijeriya, Kamaru, Kolombiya, Eritriya, Iraki, Libya, Pakistan, Turkiyya da Zimbabwe,...
114-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na Kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin Alkur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Murtadha Mutahhari ko cikin littafin Mathnawa na maulana jalaluddin Romi ko kuma cikin wasu littafan, da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a wannan shirin. //… Masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin kisser Imam Al-Hassan limami na biyu daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All…(s) kuma da na farko ga Fatimah (S) diyar manzon All..(s) kuma jakansa na farko da muke kawo maku, a shirimmu da ya...
Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya naɗa Alhaji Munir Sanusi Bayero a matsayin sabon Galadiman Kano, tare da wasu manyan muƙamai guda huɗu. Sauran waɗanda aka naɗa sun haɗa da Alhaji Kabir Tijjani Hashim, Hakimin Nassarawa, wanda ya zama sabon Wamban Kano; Alhaji Mahmud Ado Bayero Hakimin Gwale, wanda aka naɗa a matsayin Turakin Kano; Adam Lamido Sanusi a matsayin Tafidan Kano; da Alhaji Ahmad Abbas Sanusi a matsayin Yariman Kano. Ra’ayin Jama’a kan ziyarar Tinubu Katsina Gobarar rumbum makamai Maiduguri da Matakan da ya kamata a ɗauka — Ƙwararru Da yake jawabi yayin bikin naɗin sarautar, Sarki Sanusi ya buƙaci sabbin masu riƙe da muƙaman da su kasance masu koyi da shugabanni da kuma ci gaba da...
Wata ƙungiyar matasa mai suna “North-East Coalition Against Terrorism” ta yi maraba da Major General Abdulsalam Abubakar, sabon kwamandan yakin Operation HADIN KAI (OPHK), inda ta bayyana cewa tana fatan zaman lafiya ya dawo yankin. A cikin wata sanarwa da Ismail Mustapha da Sakatare Danlami Bukar suka rattaba hannu, ƙungiyar ta ce Sojojin Nijeriya a ƙarƙashin babban Hafsan Soja Janar Chris Musa za su ci gaba da matsa lamba kan mayakan. Ta kuma yi kira ga al’ummar yankin su ba sabon kwamandan goyon baya. Boko Haram Sun Kashe Masu Kamun Kifi 18 A Borno Sojoji Sun Harbe Mutane Biyu Har Lahira Da Ake Zargi Ɓarayin Mota Ne A Filato Ƙungiyar ta gargadi matasa su ƙi tayin shiga ƙungiyoyin da ba...
Wuta ta tashi da safiyar yau Juma’a inda ta ƙone shaguna uku da wasu kayayyaki masu yawa a unguwar Sango da ke cikin babban birnin jihar Oyo, Ibadan. Manaja Janar na hukumar kashe gobara ta Jihar Oyo, Akinyemi Akinyinka, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya bayyana cewa wutar ta tashi a bayan wani gidan man da ke Sango. Akinyinka ya ce an ba da rahoton faruwar gobarar da karfe 4:41 na safe ta wayar tarho, kuma ma’aikatan hukumar, ƙarƙashin jagorancin ACFS Adedeji (Mrs.), sun isa wurin nan da nan. “Lokacin da muka isa, mun gano cewa shaguna uku daga cikin goma na shagunan sun ƙone. Mun yi sauri mu kawar da wutar kuma mun hana ta yaɗuwa zuwa sauran...
A yau Juma’a 2 ga watan Mayu, 2025 Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ke ziyartar Jihar Katsina a karon farko tun bayan hawansa kujerar mulki. Kamar yadda gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Malam Dikko Umar Raɗɗa ta ce, shugaban zai duba wasu muhimman ayyukan da gwamnan ya aiwatar da waɗanda ake cikin yi. Wakilin mu ya tuntuɓi wasu daga cikin al’ummar jihar domin jin ra’ayoyinsu akan wannan ziyara. Ya zo ɗaurin auren ’yar gwamna ne — Sabo Musa Alhaji Sabo Musa shi ne mai bai wa Gwamna Raɗɗa shawara a kan wayar da kan al’umma a harkokin gwamnati, ya bayyanawa wakilinmu cewar, Shugaba Tinubu zai zo Katsina ne domin halartar ɗaurin auren ’yar Gwamna Raɗɗa wanda za a yi a ranar Asabar,...
Masana harkokin tsaro sun ja hankalin hukumomi su ɗauki matakan da suka dace bayan gobarar ma’ajiyar makamai a babban Barikin Sojoji na Giwa da ke Maiduguri, babban birnin Jihar Borno. Sun bayyana damuwa game da mummunan abin da ke iya biyo baya ta fuskoki daban-daban, tare da bayar da shawarar matakan da ya kamata a ɗauka domin daƙile ayyukan miyagu da ke iya ƙoƙarin cin gajiyar yanayin a matsayin wata dama ta aikata mugun laifi ko ta’addanci. Damuwar ƙwararru kan ƙarsashi da karfin sojoji Wani ƙwararre kan harkokin tsaro, Kabiru Adamu, ya ce illar wannan lamari ta wuce ɓarnar zahiri da kuma yiwuwar asarar rayuka. Ya ce, “Lalacewar makamai, harsasai, da sauran muhimman kayan aikin soja a barikin babban asarar...
Sai dai kuma, idan Atiku da sauran ‘yan adawa suka ji tsoro, wanda hakan mai yiwuwa ne, kuma Tinubu ya sake cin zaven 2027, wanda shi ma zai iya yiwuwa, hakan ba zai zama saboda sauya sheka ba ne; domin kuwa tuni Atiku ya share fagen ruguza PDP, don kuwa ya nuna shi ne yake da jam’iyyar, abin da ba a cika fada ba, saboda yana jin dadin qalubalantar Tinubu. *Damar Da Ta Kuvuce Misali, jigo a jam’iyyar PDP, Sule Lamido a ranar Talata ya bayyana cewa; “Ya kamata shugaban qasa ya yi adalci, ya ceci ‘yan adawa daga murkushewa. Ba ni da tabbacin nawa Lamido zai biya Tinubu, saboda zaluntarsa.Wani abin mamaki shi ne, xaya daga cikin wadanda suka...
Masana harkokin tsaro sun ja hankalin hukumomi su ɗauki matakan da suka dace, lura da abin da ke iya biyo bayan gobarar ma’ajiyar makamai a babban Barikin Sojoji na Giwa da ke Maiduguri, babban birnin Jihar Borno. Sun bayyana damuwa game da mummunan abin da ke iya biyo baya ta fuskoki daban-daban, tare da bayar da shawarar matakan da ya kamata a ɗauka domin daƙile ayyukan miyagu da ke iya ƙoƙarin cin gajiyar yanayin a matsayin wata dama ta aikata mugun laifi ko ta’addanci. Damuwar ƙwararru kan ƙarsashi da karfin sojoji Wani ƙwararre kan harkokin tsaro, Kabiru Adamu, ya ce illar wannan lamari ta wuce ɓarnar zahiri da kuma yiwuwar asarar rayuka. Ya ce, “Lalacewar makamai, harsasai, da sauran muhimman...
A sanarwar manema labarai da kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Bauchi, Babban Sufuritendan dansanda, CSP Ahmed Mohammed Wakil, ya tabbatar da cewa, cikin gaggawa aka yi tura jami’an ‘yansanda wanda hakan ya kai ga kamo Amusu. Wakil ya ce an kai yarinyar zuwa babban asibitin Bayara domin likita ya dubata kuma wanda ake zargin ya amsa laifinsa a lokacin da ake masa tambayoyi. A wani labarin kuma, rundunar ‘yansandan ta cika hannunta da wani matashi mai shekara 26 a duniya, Johnson John, mazaunin unguwar Gwallameji, bisa zarginsa da yin safarar wata budurwa ‘yar shekara 19 a duniya, Cecelia Cosmos, zuwa kasar Burkina Faso domin karuwanci. A cewar ‘yansanda, Johnson ya yaudari Cecelia ne a ranar 12 ga watan...
Amurka ta kawo ƙarshen cire haraji kan wasu kayayyaki da ba ma su tsada ba da ake shiga da su ƙasar daga China. A baya Amurkawa na iya sayan kayayyakin China da ba su haura dala 800 ba, idan za su yi oda ta intanet ba tare da wani haraji ba, amma yanzu za su biya kashi 120. Ana sa ran harajin zai fara aiki nan take, kuma wasu Amurkawa masu sayayya za su ji a jikinsu. Hakazalika su ma yawancin kamfanonin China da ke samar da kayan da shigar da su can.
Kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC reshen jihar Kano ta yabawa gwamnatin jihar Kano kan kudirin ta na daidaita bashin da ake bin ‘yan fansho da ya haura naira biliyan 16. Da yake jawabi yayin bikin ranar ma’aikata da aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha da ke kofar Mata a Kano, shugaban kungiyar kwadago ta NLC, Kwamared Kabiru Inuwa, ya bukaci ma’aikatan Nijeriya da su jajirce wajen tabbatar da adalci da walwala. Kwamared Inuwa ya bayyana cewa duk da nasarorin da gwamnatin ta samu wajen horas da ma’aikata, har yanzu akwai bukatar karin ma’aikata masu tallafawa a ma’aikatun gwamnati da na kananan hukumomi. Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jaddada kudirin gwamnatin sa...
Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya ce gwamnatinsa ta himmatu wajen gina jihar da ma’aikata za su bunkasa, samar da ayyukan yi masu nagarta, da baiwa kowane bangare damar bayar da gudunmawa mai ma’ana ga ci gaban jihar. Gwamna AbdulRazaq a cikin sakonsa na bikin ranar ma’aikata ta duniya na shekarar 2025, a Ilorin, ya mika sakon gaisuwa ga maza da mata da jama’a da kungiyoyi masu zaman kansu wadanda kokarinsu ke karfafa tattalin arziki da samar da makomar al’ummarmu. Ya yaba da gagarumar gudunmawar da ma’aikata ke bayarwa a kowane fanni na sadaukarwa, juriya, da fasaha wanda ya sa su zama ginshiƙan girma da ci gaba. Gwamnan ya jaddada kudirin gwamnatin na aiwatar da manufofin da...

Zamfara Ta Biya Sama Da Naira Biliyan 13 A Matsayin Bashin Garatuti Da Aka Gada – Mataimakin Gwamna.
Gwamnatin jihar Zamfara ta kammala biyan sama da naira biliyan 13 na garatuti, wanda ke nuna wani gagarumin mataki na inganta jin dadin ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya a jihar. Mataimakin gwamnan jihar, Mani Malam Mummuni, ya bayyana hakan a yayin bikin ranar ma’aikata na shekarar 2025 da aka gudanar a Gusau, babban birnin jihar. A cewar Mummuni, gwamnatin Gwamna Dauda Lawal ta jajirce wajen ganin ta magance kalubalen da ma’aikata da masu ritaya ke fuskanta a jihar. Ya bayyana cewa, gwamnatin jihar tana sane da korafin ma’aikatan da aka yi kuskuren cire su daga lissafin albashin sakamakon aikin tantance ma’aikatan da aka kammala. “Gwamnati ta riga ta kafa wani kwamiti a karkashin jagorancin shugaban...
Gwamnatin jihar Kebbi, ta baiwa ma’aikatan jihar tabbacin ci gaba da jajircewa wajen kyautata jin dadin su da kuma kare hakkokinsu. Gwamna Nasir Idris wanda ya ba da wannan tabbacin a lokacin da yake jawabi ga ma’aikata domin bikin ranar watan Mayu a Birnin Kebbi, ya jaddada cewa ma’aikata aminai ne masu kima wajen ci gaban jihar Kebbi, kuma su kasance masu ruwa da tsaki da ba za a yi watsi da su ba. Gwamna Idris, wanda ya bayyana bikin ranar Mayu a matsayin wani muhimmin lokaci, ya yabawa ma’aikatan bisa jajircewarsu da irin gagarumar gudunmawar da suke bayarwa wajen ci gaban jihar. “Kwazonku da jajircewarku sune kashin bayan tattalin arzikinmu. Ina yaba muku kan kokarinku na...
Gwamna Umar Namadi ya bi sahun kungiyoyin kwadago domin tunawa da irin gudunmawar da ma’aikata ke bayarwa wajen ci gaban jihar Jigawa. Da yake gabatar da jawabinsa, Gwamna Namadi ya yaba da jajircewar ma’aikatan Jigawa, inda ya bayyana ma’aikata a matsayin masu kawo ci gaba. Ya bayyana cewa, ma’aikata a dukkan bangarori suna aiki da gaske a matsayin injin da ke ba da kuzarin motsa al’umma zuwa ga ci gaba. Ya kuma kara jaddada kudirin gwamnatinsa na samar da walwalar ma’aikata, inda ya bayar da misali da nasarorin da aka samu da suka hada da aiwatar da mafi karancin albashi na Naira 70,000, gina gidaje masu saukin kudi ga ma’aikatan gwamnati, da kuma shigar da sama da...
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umar Bago ya bayyana dangantakarsa da mataimakinsa, Kwamared Yakubu Garba a matsayin cikakkiya da jituwa. Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai kan dangantakarsa da mataimakinsa bayan bikin ranar ma’aikata a Minna. A cewarsa, “mu kungiya ce, ba za su iya karya mu ba, hankalinmu yana kan manufa, kuma za mu cimma ta.” Gwamnan ya bukaci al’ummar jihar da su ci gaba da marawa gwamnatinsa baya, tare da tabbatar da cewa wata sabuwar Nijar za ta yiwu. Binciken da aka gudanar ya nuna cewa mataimakin gwamnan jihar Neja, Kwamared Yakubu Garba bai halarci bikin ranar ma’aikata ta bana a Minna ba wanda wasu al’ummar Nejar din...
Jami’an tsaron sa kai sun kama wasu abokai biyu masu sana’ar acaba, bisa zargin yin fyaɗe ga wata Bafulatana mai tallar fura da nono a Yankin Babban Birnin Tarayya Abuja. Wani jami’in tsaron sa kai, Usman Dantala, ya ce abokan biyu sun yi wa Bafulatanar fyade ne da tsakar rana a yankin Ikwa da ke Ƙaramar Hukumar Gwagwalada. Ya bayyana cewa ranar Asabar da misalin karfe 2:12 na rana ne abokan biyu suka yaudari mai faurar ’yar kimanin shekaru 19 zuwa daƙin wani abokinsu inda suka yi mata fyade. Jami’in ya ce, sun kira Bafulatanar ne da cewa za ta sayar musu da nono a gidan wani abokinsu. A can ne suka yaudare ta shiga daƙin suka kuma yi mata...
“Murkushe ‘yan adawa tare da musguna musu, musamman jam’iyyar PDP, wata alama ce karara da ke nuna cewa; zangon karshen mulki na karatowa; domin kuwa tarihi ya sha nuna hakan”, in ji Lamido a tattaunawarsa da BBC Hausa. “Ya kamata Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, ya kasance mai adalci, domin shi ne shugaban dukkanin ‘yan Nijeriya. Dole ne ya bar ‘yan adawa su yi takara a siyasance da jam’iyyar APC, idan kuma bai yi taka-tsan-tsan ba, abin zai iya komawa kansa”, in ji shi. A ranar Litinin ne, Gwamnan Jihar Delta Sheriff Oborebwori da da wanda ya gaji kujerar daga wajensa, Dakta Ifeanyi Okowa da daukacin tsarin ‘yan siyasar da ke jam’iyyar PDP a jihar, suka sauya sheka...
An kama wani matashi ɗan shekaru 33 bisa zargin yin garkuwa da ’yar maƙwabcinsa mai shekaru 21 a ƙauyen Paikon Bassa da ke Ƙaramar Hukumar Abaji a yankin Babban Birnin Tarayya. Wani ɗan banga a yankin, Dangana Bala, ya ce an kama wanda ake zargin ne bayan samun ƙorafi daga iyayen matashiyar da ta ɓace na wasu makonni. Ya ce iyayenta sun yi zargin mutumin, wanda suka ce ya daɗe yana soyayya da ita a ɓoye. Ya ƙara da cewa da samu wannan bayanin, ’yan sintirin suka sanar da abokan aikinsu a ƙauyen Dafa da ke makwabta da su, kuma an gano matashiyar a ƙauyen Tukurwa da ke Ƙaramar Hukumar Kwali a ranar Lahadin da ta gabata. Wulaƙancin da ake...

Ranar Maleriya Ta Duniya: ‘Yan Nijeriya Na Kashe Naira Tiriliyan 1.156 Duk Shekara Wajen Sayen Magunguna
Binciken LEADERSHIP ya nuna cewa, duba mara lafiya guda daya tak da ke dauke da cutar Maleriyar da ba ta yi karfi sosai ba a asibitin gwamnati, na lashe kimanin Naira 17,000, tsakanin ganin likita, yin gwaje-gwaje da kuma magunguna. Wadannan kudade sun kai kimanin Naira tiriliyan 1.156 da ake kashewa a kan wannan cuta, amma asalin kudaden sun zarta haka, musamman idan Maleriyar ta yi kamari, za a iya kashe ninki uku ko sama da haka na wannan kudi. Yayin da duniya ke yin wannan biki na ranar Maleriya, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta nanata cewa, cutar na ci gaba da zama barazana, musamman a yankuna masu fama da zafi, duk da cewa; cuta ce da...

Sabon Tsarin Ci Gaba Na Sin Ya Kawo Sauyi Daga Samar Da Takalma Miliyan 100 Zuwa Kera Mattarar Bayanai Ta Microchip
Kamar yadda firaministan kasar Malaysia Anwar bin Ibrahim ya fada a kwanan baya cewa, yayin da kasa da kasa ke fuskantar mawuyacin hali, suna bukatar samun tabbaci da wani nagartaccen shiri na samun ci gaba. Don haka, ana ganin yadda kasar Sin ta samu nasarori, an nuna yabo ga kasar ta Sin, kasar Sin ta kawo tabbaci da kuma kyakkyawar makoma ga duniya. (Zainab Zhang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Al’ummar Arewa mazauna yankin Obalande da ke Jihar Legas sun yunƙura domin tunkarar matsalolin da ke ci musu tuwo a ƙwarya, musamman yadda suka ce ’yan ƙasa ke musu cin kashi. Sun ce sun gaji da irin tsangwama da ƙasƙanci da ’yan ƙasa a yankin ke nuna wa ’yan Arewa, musamman Hausawa mazauna. Sun bayar da misali bisa yadda samarin Yarabawa daga wasu unguwanni suka mayar da unguwar tasu filin ƙwallon ƙafa, inda suke tilasta musu rufe rumfunansu na kasuwa, har sai an gama buga ƙwalon kafin su ci gaba da sana’arsu. A kan haka ne suka yi wani zama da Shugaban Karamar Hukumar Ikoyi Obalande (LCDA) Fu’ad Lawal Atanda da shugabannin siyasa ’yan Arewa a jihar, da nufin cire...

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ya Ce Kasar Oman Ce Ta Bukaci Dage Zaman Tattaunawan Iran Da Amurka
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: An dage zaman tattaunawan Iran da Amurka ne bisa shawarar kasar Oman Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi nuni da cewa: Ministan harkokin wajen kasar Oman ne ya sanar da sauyin lokacin zaman tattaunawan ba na kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka, yana mai bayanin cewa, dage shawarwarin ya zo ne bisa shawarar ministan harkokin wajen kasar, kuma za a sanar da wata sabuwar rana daga baya. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya sanar da manema labarai cewa: An canja ranar da za a gudanar da zaman shawarwarin ba na kai tsaye ba na gaba tsakanin Iran da Amurka, wanda aka shirya gudanarwa a...
Ministan Tsaron kasar Iran ya bayyana cewa: Gwamnatin yahudawan sahayoniyya ta zama babbar alamar ta’addanci a duniya Ministan tsaron kasar Iran Birgediya Janar Aziz Nasirzadeh, yayin da yake yin Allah wadai da kisan gillar da yahudawan sahayoniyya suke yi wa al’ummomin Falastinu da na Lebanon a daidai lokacin da kungiyoyin kasa da kasa da tarurrukan kasa da kasa suka yi shiru, yana mai cewa: A yau al’ummar yahudawan sahayoniyya ta zama wata babbar alama ta ta’addancin kasa a duniya. Birgediya Janar Nasirzadeh ya furta haka ne a ganawarsa da ministan tsaron Jamhuriyar Zimbabwe Uba Muchinguri Kashiri a lokacin ziyararsa a kasar Iran, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi kasashen biyu. A cikin wannan ganawar, ministan tsaron na Iran ya...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Kimanin Naira biliyan ɗaya ce aka ƙiyasta ta salwanta sakamakon gobarar da ta ƙone wani sashe na babbar kasuwar da ke tsakiyar garin Jos, babbar birnin Jihar Filato. An rawaito cewar gobarar ta laƙume shaguna fiye da ɗari biyar, galibinsu na masu sayar da kayan gwanjo. Mutane da dama dai sun rasa hanyar cin abincinsu, kasancewar galibinsu sun dogara ne da samun da suke yi a kullum a wannan kasuwa don ciyar da iyalansu. Ko a wane hali waɗanda suka tafka wannan asara suke ciki bayan wannan ibtila’i? NAJERIYA A YAU: Dalilan Kamuwa Da Cutar Hawan Jini Da Hanyoyin Magance Ta DAGA LARABA: Asarar Da Hausawa Ke Tafkawa Sakamakon Bacewar Tatsuniya Wannan na...

Masifar Gobara Tana Kara Bunkasa A Haramtacciyar Kasar Isra’ila Tare Da Fara Raba Yahudawa Da Muhallinsu
Ana sa alamar tambayar cewa: Shin gobarar da ta tashi a birnin Kudus… shin sako ne na ranar tunawa da kafuwar gwamnatin ‘yan sahayoniyya? Gobarar da ta tashi a tsaunin Kudus da aka mamaye ta bazu zuwa manyan yankuna a cikin haramtacciyar kasar Isra’ila, inda ta kewaye wani sansanin soji tare da cinye filayen masu girma da tsayi. Hakan ya sa hukumomin gwamnatin mamayar Isra’ila suka kafa dokar ta baci tare da neman taimakon kasashen duniya. Yayin da Ministan tsaron cikin gidan Isra’ila Itamar Ben-Gvir yake neman dora wa Falasdinawa, alhakin tashin gobarar. Gobarar ta kunno kai ne a daidai lokacin da yahudawan sahayoniyya suka fara gudanar da bukukuwan cika shekaru 77 da kafuwar gwamnatinsu ta mamaya a kasar Falasdinawa,...
Ma’aikatan jihar Ribas sun hallara a sakatariyar kungiyar kwadago ta kasa, NLC da ke Fatakwal domin bikin ranar ma’aikata ta 2025 a ranar Alhamis. Dama kungiyar ta NLC, tuni ta sanar da cewa, ba za ta gudanar da bikin murnar ranar ma’aikata ba kamar yadda aka saba yi a filin shakatawa na Isaac Boro, inda a al’adance kungiyoyin kwadago daban-daban ke gudanar da tattaki a filin domin murnar wannan rana ta 1 ga watan Mayu. Gobara A Haramtacciyar Wurin Ajiye Man Fetur Ta Ci Rayukan Mutane 5 A Jihar Ribas Aikin Gina Tashar Jirgin Ƙasa A Kano Yana Ci Gaba Gadan-gadan A maimakon haka, ma’aikatan sun taru ne domin nuna goyon bayansu ga Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakinsa da ‘yan...
Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya yaba wa takwarorinsa na gwamnonin Jihohin Borno, Bauchi, Adamawa, Gombe da Taraba a bisa ga samun damar da suka yi na halartar taron ƙungiyarsu ta Arewa maso Gabas (NEGF) karo na 11 a garin Damaturu. Ya yi wannan yabo ne a ranar Alhamis a ɗakin taro na gidan gwamnati da ke Damaturu yayin jawabinsa na maraba yadda ya bayyana fatansa cewa, taron zai samar da sabbin dabarun yaƙi da rashin tsaro da taɓarɓarewar tattalin arziki. Sojoji sun ceto fasinjoji 99 daga hatsarin kwale-kwale a Ribas Gobara ta lalata shagunan kasuwar waya a Kwara Buni ya bayyana wannan ƙungiyar a matsayin wani muhimmin dandali na haɗin gwiwa da daidaita manufofi, musamman yadda yankin ke fama da...
Cibiyar cinikayyar kasashen waje ta kasar Sin, mai shirya bikin, ta ba da sanarwar cewa, baya ga wuraren baje kolin da suka shafi farfado da yankunan karkara da za a ba su rumfuna kyauta, sauran masu baje kolin kayayyakin da ake fitarwa zuwa kasashen waje su ma za a rage musu kudaden rumfunansu da kashi 50 cikin dari a wajen bikin Canton Fair karo na 137. Ana gudanar da bikin Canton Fair karo na 137 ne a matakai uku, daga ranar 15 ga Afrilu zuwa 5 ga Mayu. Kashi na farko da na biyu sun jawo hankulan masu sayayya fiye da 220,000 daga kasashe da yankuna 219 na duniya, inda suka kafa sabon tarihi a lokaci guda. Wannan...
Haka kuma, kasar Sin ta yi nuni da cewa, matakan kasar Amurka kan harajin kwastam sun kawo illa ga cinikayyar duniya, da moriyar kasashe masu tasowa, amma kasar Sin a nata bangaren kokari take yi wajen tabbatar da bunkasar cinikayya ta duniya, da kuma tsayawa tare da kasashe masu tasowa. (Zainab Zhang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Faɗin ginin, wanda ya haura sukwaya mita 13,000, ya ƙunshi babban ginin tashar da ababen da ke tattare da shi, kuma zai kasance tashar da ta fi kowace girma a layin dogon da ake kira Kaka Reluwe. Kaka Reluwe na nufin hanyar dogo daga KAduna zuwa KAno. Kamfanin CCECC ya ce idan an gama aikin, zai taimaka gaya wajen haɓaka harkokin sufuri kuma ya kawo matuƙar sauƙi ga miliyoyin matafiya a ɓangaren Kano na hanyar jirgin. Shi dai wannan layin dogo na Kaka Reluwe, hanya ce mai tsawon kilomita 204. Ta tashi daga Kaduna, ta bi ta Zariya, zuwa Kano. Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ne ya ƙaddamar da ita a ranar 15 ga Yuli, 2021, sannan...
A ranar Laraba ne jami’an sojojin ruwa na Najeriya da ke Fatakwal suka ceto fasinjoji 99 daga wani hatsarin kwale-kwale da ya rutsa da su a kogin Bukuma da ke ƙaramar hukumar Degema a Jihar Ribas. Jirgin ruwan, wanda yake na jigilar fasinja yana kan hanyarsa ta daga Fatakwal zuwa Ƙaramar hukumar Akuku-Toru, inda ya yi karo da wani jirgin ruwa a tsakiyar kogin. Gobara ta lalata shagunan kasuwar waya a Kwara Dalilin da ya sa aka samu fashewar abubuwa a barikin Maiduguri – Sojoji Jami’ar yaɗa labarai na sansanin, Laftanar Kwamanda Bridget Bebia, a wata sanarwa da ta fitar a Fatakwal, ta ruwaito Kwamandan sojojin masu aikin bincike, Commodore Cajethan Aniaku, ya tabbatar da faruwar lamarin. A cewar Aniaku,...
Jakadan kasar Sin ya bayyana cewa, kasar tana kiran a samar da hanyar kawar da makaman nukiliya wacce a karkashinta ba za a iya raba tsaro na kashin kai da tsaro na bai daya ba, tare da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya. Babban darektan sashen kula da makamai na ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Sun Xiaobo, ya shaida wa babban taron muhawara na 3 na kwamitin shirya taron koli na yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT) na shekarar 2026 cewa, kasar Sin tana nan a kan bakanta game da kin raba ‘yancin kiyaye tsaro da na sauke nauyin da ya rataya a wuyan kasashe na tsaro, da kafa shugabanci na adalci a kan hana yaduwar makaman...
Gwamnan ya kara da bayyana biyan Biliyan 16 na basussukan fansho, da kuma sauya mafi karancin fansho daga ₦5,000 zuwa ₦20,000, da kuma fitar da Naira miliyan 100 domin tallafawa ayyukan ’yan fansho. A wani mataki makamancin haka, gwamnan ya sanar da kafa sabbin ma’aikatu 4 da hukumomi 2 da za su zaburar da samar da ayyukan yi da kirkire-kirkiren fasaha a jihar. Wadannan sun hada da ma’aikatun raya gidaje, tsaron cikin gida, daskararrun ma’adanai, da wutar lantarki da makamashi mara illa, sannan kuma ya kafa hukumomar bunkasa ICT ta jihar Kano da hukumar kula da kanana da matsakaitan masana’antu. Gwamna Yusuf ya kuma ba da sanarwar umarnin fara aiwatar da shirin mafi karancin albashi na ₦71,000...
Kasashen Iran da Nijar sun gudanar da taron kwamitin hadin gwiwa kan tattalin arziki. An gudanar da taron ne a gefen taron baje koli na Iran 2025, karo na bakwai na Jamhuriyar Musulunci ta Iran, wanda aka fara a birnin Tehran a ranar Litinin. Mohammad Atabak, ministan masana’antu, ma’adinai, da kasuwanci na Iran; da Mohammad Ali Dehghan Dehnavi, shugaban kungiyar bunkasa kasuwanci ta Iran; da Sahabi Oumarou, ministan mai na Nijar, ne suka halarci taron. Da yake jawabi a wajen taron, Atabak ya ce, bayan shafe shekaru 13 da aka shafe ana aikin kwamitin hadin gwiwa tsakanin Iran da Nijar, “Muna fatan inganta dangantakar tattalin arziki tsakanin kasashenmu biyu ta hanyar wannan takardar hadin gwiwa.” Dehghan Dehnavi ya jaddada cewa,...
Hukumar lafiya ta Duniya WHO, ta nuna matukar kaduwa game da halin da ake ciki a Gaza. Abin da ke faruwa a Gaza “ba abinda za’a lamunta da shi ne ba,” in ji Mike Ryan, mataimakin darekta-janar na Hukumar Lafiya ta Duniya, yayin wani taron manema labarai. Mista Ryan, ya nuna fushinsa matuka game da rashin tabaka komai na taimaka wa jama’a a zirin Gaza. “Muna wargaza tunani da jikin yaran Gaza, ga yunwa ga yaran Gaza, idan ba mu dauki mataki ba, za mu shiga cikin abin da ke faruwa a idanunmu,” in ji shi. A gobe Juma’a ne za a cika watanni biyu na hana shigar da kayan agaji da sojojin Isra’ila suka yi a zirin Gaza baki...
Iran ta sanar da cewa an dage tattauanwa ta karo na hudu da aka shirya gudanarwa tsakaninta Washington a ranar Asabar mai zuwa. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ne ya sanar da manema labarai da hakan a yammacin yau Alhamis yana mai cewa an sauya ranar da za a gudanar da tattaunawar ta gaba tsakanin Iran da Amurka da aka shirya gudanarwa a ranar Asabar 3 ga watan Mayu a birnin Rome na kasar Italiya. Esmail Baghai ya bayyana cewa, an dauki wannan matakin ne bisa bukatar ministan harkokin wajen kasar Oman, kuma Za a sanar da sabon lokaci nan gaba. Baghaei ya jaddada aniyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran na yin amfani da hanyar diflomasiyya wajen kare muradun al’ummar...
Jiragen yakin Amurka sun sake kai hare-hare da dama kan lardunan Saada da Hudaidah na kasar Yemen yau Alhamis. Wata majiyar tsaro a Yemen ta kara da cewa, an kai wasu hare-hare uku a yankin Kataf da ke lardin Saada, yayin da wani kuma ya afkawa gundumar al-Houk da ke lardin Hudaidah a gabar tekun yammacin Yeman, lamarin da ya janyo hasarar kayayyaki na fararen hula. Dama a cewar kafar yada labaran kasar Yemen Al-Masirah, jiragen yakin Amurka sun kai hari a gundumar al-Sayl da ke lardin al-Jawf a arewacin kasar Yemen ranar Laraba. Tun a ranar 15 ga watan Maris da ya gabata ne, kawencen Amurka da Birtaniya ke kai hare-hare ta sama kan kasar Yamen, domin nuna goyon...
Gwamnan Zulum ya yi tsokaci dangane da yadda tabarbarewar harkokin tsaro ke ci gaba da zafafa a yankin, yayin da kuma ya yaba wa kokarin sojojin Nijeriya, inda ya ce, “Ina kira gareku, ku ci gaba da yaki da yan ta’adda har sai mun kawo karshen wannan matsalar.” “Dawowar hare-haren yan ta’adda a cikin jihohinmu wani al’amari ne mai matukar tayar da hankali wanda hakan zai iya wargaza nasarorin da aka samu a fagen yaki da matsalolin tsaro a yankin. Ina mai bayar da shawarar cewa, sojojinmu su fadada sabbin dabarun da suke dasu wajen dakile farmakin yan ta’adda.” Gwamna Zulum ya ce, “kangin talaucin da yankinmu yake fuskanta, abin tsoro ne, kuma ya zama dole mu dauki...
Iran ta yi tir da Allah-wadai da sabbin takunkuman da Amurka ta lafta mata. Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta bakin kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta ce matakin wata babbar alama ce da ke nuna cewa Washington ba ta da kyakyawar niyya, hasali ba abar yarda ce ba. Sanarwar ta bayyana karara cewa Iran ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen matsin lamba na Amurka kuma ta dage kan yin shawarwari a karkashin sharudda guda. Iran na cewa takunkuman da Amurka ke bayyanawa da matsin lamba mafi girma, tun zuwa gwamnatin Trump, ba zasu tankwaso Tehran ba game da hakokkinta. Kalaman na zuwa ne jim kadan bayan da sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya sanar da kakaba...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A ranar Alhamis ɗin nan ne rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da cewa, an samu fashewar wani abu a wurin ajiyar makamai da ke barikin Giwa a Maiduguri wanda ya faru sakamakon tsananin zafi da aka samu a yankin. A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Alhamis mai ɗauke da sa hannun muƙaddashin daraktan hulɗa da jama’a na rundunar, Kaptin Reuben Kovangiya, a hedkwatar rundunar haɗin gwiwa ta shiyyar Arewa maso gabas ta Operation HAƊIN KAI. ’Yan fashin teku sun sace mata 4 a hanyar ruwa ta Bayelsa NAJERIYA A YAU: Dalilan Kamuwa Da Cutar Hawan Jini Da Hanyoyin Magance Ta Ya fayyace cewa fashewar ta faru ne ba sakamakon wani harin maƙiya ba, illa dai lamarin ya faru...
Wasu ’yan bindiga da ake zargin ’yan fashi ne sun kai hari kan wani jirgin ruwa da ke jigilar mata ’yan kasuwa zuwa Ƙaramar hukumar Ijaw ta Kudancin Jihar Bayelsa, a kan hanyar ruwan Lobia/Foropa. Rahotanni sun ce maharan sun yi garkuwa da wasu mata huɗu a lokacin da lamarin ya faru a ranar Talata. NAJERIYA A YAU: Dalilan Kamuwa Da Cutar Hawan Jini Da Hanyoyin Magance Ta Najeriya za ta karɓi baƙuncin Gasar Karatun Alkur’ani ta Duniya a karon farko Wata majiyar unguwar da lamarin ya faru ta shaida wa Daily Trust a safiyar ranar Alhamis, maharan sun kai harin ne ’yan mintuna kaɗan bayan jirgin ruwan fasinjan ya tashi daga gaɓar ruwan Swali a Yenagoa, babban birnin jihar....
Zargin sabani tsakanin Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, da mataimakinsa, Kwamred Yakubu Garba, ya karu a yau Alhamis bayan da mataimakin gwamnan ya kaurace wa bikin Ranar Ma’aikata a birnin Minna, babban birnin jihar. LEADERSHIP ta ruwaito cewa Kwamred Garba, wanda shi ne tsohon shugaban reshen jihar na ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC), bai taɓa kin halartar bikin Ranar Ma’aikata ba tun bayan da ya zama mataimakin gwamna. Sabanin shekarar da ta gabata, Kwamred Garba bai bayyana a wannan shekarar ba duk da cewa Gwamna Bago da Sanata mai wakiltar mazabar Neja ta Gabas, Sani Musa, sun halarta, lamarin da ya ƙara zafafa zargin rikici tsakaninsa da gwamnan. Wasu majiyoyi sun ce yana wajen gari, yayin da wasu ke...
An tashi 3-3 tsakanin Barcelona da Inter Milan a wasan farko zagayen daf da karshe a Champions League da suka kara a Sifaniya ranar Laraba. Inter Milan ce ta fara cin ƙwallo a daƙiƙa 30 da take leda ta hannun Marcus Thuram, ya zama na farko da ya ci ƙwallo a ƙanƙanin lokaci a daf da karshe a Champions League. Daga nan Inter ta kara na biyu ta hannun Denzel Dumfries, wanda ya zama na farko daga Netherlands da ya ci ƙwallo ya kuma bayar aka zura a raga a daf da karshe a Champions League, tun bayan Wesley Sneijder a Inter a karawa da Barcelona. Dumfries shi ne ya bai wa Thuram ƙwallon farko da Inter Milan ta zura...
Gwamnatin tarayya ta kaddamar da wayar da kan al’umma kan kare lafiyar ruwa tare da raba riguna a wasu zababbun Jihohin Najeriya. Ministan Tattalin Arzikin Ruwa, Adegboyega Oyetola wanda ya kaddamar da taron a gidan gwamnati, Minna ya ce wannan ra’ayin ya yi daidai da jajircewar Gwamnatin Tarayya na kare rayuka da dukiyoyin al’umma da rayuwar ’yan Najeriya da ke dogaro a kullum kan hanyoyin ruwa na cikin kasa wajen sufuri da kasuwanci. Ya amince da dimbin karfin tattalin arzikin magudanan ruwa a kasar nan da ke fama da tashe-tashen hankula sakamakon yawaitar hadurra na kwale-kwalen da ke bukatar hada kai, da kuma daukar matakai bisa dabaru don haka aka fara raba riguna 3,500 a matakin farko ga...
An ce shafin neman aikin zai kasance a buɗe har tsawon makonni biyu. Bayan haka, za a zaɓi waɗanda suka cancanta domin ganawa da su da kuma tantance su Hukumar ta shawarci duk masu sha’awar aikin da su gaggauta cike fom ɗin domin guje wa cunkoson mutane a ranar ƙarshe. Gwamna Fintiri ne, ya bayar.da umarnin buɗe shafin domin ɗaukar sabbin ma’aikata 4,000 a aikin gwamnati a jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Majalisar zartaswar jihar Kano ta amince da kashe Naira biliyan 51.5 wanda ba a taba ganin irinsa ba, domin muhimman ababen more rayuwa da ayyukan yi wa al’umma hidima a fadin jihar, a wani bangare na tsare-tsare na gwamnatin na bunkasa zamantakewa da tattalin arziki. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar bayan taron majalisar zartarwa karo na 27 da aka gudanar a gidan gwamnatin Kano. A cewar sanarwar, majalisar ta ba da haske ga manyan ayyuka da yawa, da suka hada da manyan gyare-gyaren hanyoyi, shigar da tsarin zirga-zirga, fadada gine-ginen jama’a, da inganta wutar lantarki. Wani abin lura a cikin amincewar akwai fitar...
Gwamnatin jihar Kwara ta sake jaddada kudirinta na kara bude kofa ga al’umma domin ci gaba da kuma sanya jihar ta yadda za ta yi tasiri a duniya ta hanyar sanya hannun jari mai inganci. Kwamishinan Ayyuka na Jiha Injiniya. Abdulquawiy Olododo, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da ayukkan ma’aikatar a taron manema labarai na wata 3 na farkon shekara ta 2025, wanda aka gudanar a dakin taro na ma’aikatar kudi, Ilorin. A cewarsa jimillar ayyuka 46 da ake ci gaba da gudanarwa a cikin kwata na farko na shekarar 2025, daga cikin su 33 an kammala su baki daya, inda a yanzu haka ayyuka 11 ke ci gaba da gudana. Ya kara...
Gwamnatin kasar Iran ta bayyana cewa samar da kasar Falasdinu mai cikekken yenci , kuma da dukkan birnin Qudus a matsayin babban birnin kasar, hakkin Falasdinawa ne wannan babu tattaunawa a kansa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jakadan kasar Iran na din din din a MDD Amir Said Iravani yana fadar haka, a jiya laraba, a lokacinda yake gabatar da jawabi a gaban kwamitin tsaro na majalisar. Jakadan ya bukaci kungiyoyin Falasdinawa su hada kansu don duk wani sabani a tsakaninsu nasarace ga HKI. Iranvani ya ce HKI tana ci gaba da aikata laifukan yaki a yankin Gaza da kuma yankin yamma da kogin Jordan, tare da tallafin Amurka da wasu kasashen yamma. Kuma tallafin da...
Ministan Kasafin Kudi da Tsare Tattalin Arziki, Sanata Atiku Bagudu tare da hadin guiwar Kyakyawar Gate Handicapped Centre Jos, sun bayar da tallafin keken guragu guda dari da talatin ga masu bukata ta musamman a Birnin Kebbi na jihar Kebbi. Kakakin Ministan, Sadiq Nura Maiyaka, ya ce Ministan ya kuduri aniyar taimakawa masu bukata ta musamman don gudanar da ayyukansu na yau da kullun da sauran jama’a. Ya shawarci wadanda suka amfana da su yi amfani da keken guragu kada su sayar da su domin su rika zagayawa da ayyukansu ba tare da wata damuwa ba. Daraktan yada labarai na Kyawawan Gate Handicapped Centre Jos, Sandra Riliwan, ta ce wannan ba shi ne karon farko da cibiyar...

An Bukaci Masu Yiwa Kasa Hidima Su Yi Amfani Da Kafofin Sadarwa Na Zamani Don Inganta Hadin Kan Kasa.
Babban daraktan hukumar yi wa kasa hidima ta kasa (NYSC), Birgediya-Janar Olakunle Oluseye Nafiu, ya yi kira ga mambobin kungiyar a fadin kasar nan da su yi amfani da kafafen sada zumunta na zamani cikin gaskiya da kuma bayar da gudunmawa mai ma’ana ga ci gaban kasa. Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga matasa masu yiwa kasa rukunin A na 2025 Batch a sansanin ‘yan gudun hijira na wucin gadi da ke Gusau babban birnin jihar Zamfara. Birgediya Janar Nafiu ya kuma shawarci matasan su guji bibiyar shaharar shafukan sada zumunta na zamani, maimakon haka su mayar da hankali wajen samar da bayanai masu ma’ana da tasiri. “Bari in yi magana da ku...
Rear Admiral Alireza Tangsiri babban kwamandan sojojin ruwa na dakarun IRGC ya bayyana haka ne a jiya a bikin ranar “Tekun farisa’ ta kasa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa kwale-kwalen mai sauran kilomita Knots 116 na ruwa wanda yayi dai-dai da kilomita 215 / a ko wace sa’a yana da kayan aikin cilla makamai masu linzami. Kwamandan ya kara da cewa, wannan yana daga cikin shirin JMI na karfafa tsoron kasar, kuma sako ne ga makiya su san da haka, sannan sakon zaman lafiya ga makobta da abokai. An sanya ranar da turawan Portigal suka fice daga tekun farisa da mashigar ruwa ta Hurmus shekaru 1622 da suka gabata, a matsayin ranar tekunfarisa ta kasa....
Ya kai wannan mataki ne bayan lashe Copa del Rey a wasan ƙarshe da Real Madrid a filin wasa na La Cartuja a Seville. Yamal ya fara buga wasa a Barcelona a shekara ta 2023, inda ya fara a gasar La Liga a wasan da suka buga da Betis, yana da shekaru 15 da watanni tara a lokacin. Tun daga wannan rana, ya ci gaba da kafa tarihi a ƙungiyar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Cututtuka da dama suna ƙamari a Najeriya wanda a mafi yawan lokuta mutanen da da7uke da irin cututtukan ba su da masaniyar suna dauke da su. Kamar yadda Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana, zaman lafiya, rashin matsalar kwakwalwa, da samun wadata na daga cikin abubuwan da ke tabbatar da lafiyar bil’adama. NAJERIYA A YAU: Dalilin karyewar farashin shinkafa a kasuwannin Najeriya DAGA LARABA: Asarar Da Hausawa Ke Tafkawa Sakamakon Bacewar Tatsuniya Wata cuta da ta addabi da yawa daga cikin al’umma itace Hawan jini wacce take daya daga cututtuakan da ke sanadiyyar mutuwar akalla mutum miliyan biyu a duk shekara a Najeriya. Domin sauke shirin, latsa nan
Ya kai wannan mataki ne bayan lashe Copa del Rey a wasan ƙarshe da Real Madrid a filin wasa na La Cartuja a Seville. Yamal ya fara buga wasa a Barcelona a shekara ta 2023, inda ya fara a gasar La Liga a wasan da suka buga da Betis, yana da shekaru 15 da watanni tara a lokacin. Tun daga wannan rana, ya ci gaba da kafa tarihi a ƙungiyar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Syria ta nuna kin amincewarta da tsoma bakin kasashen waje a rikicin da kasar take fuskanta. Sanarwar ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Syria ta kuma ce; gwamnatin kasar za ta kare dukkanin ‘yan kasar. Kasar Syria tana fuskantar fada a tsakanin ‘yan Duruz da kuma sojojin gwamnatin kasar a yankin Sahanaya da Ashrafiyyah a yankin Suwaida. Ya zuwa yanzu dai adadin wadanda su ka rasa rayukansu sun kai 70.
Kwanaki kadan bayan wani furuci daga babban jami’in sojan Amurka a Afirka akan shugaban kasar ta Burkina, dubban mutanen kasar sun yi gangami na nuna goyon bayan Kaftin Ibrahim Traore Gangamin na mutanen kasar Burkina Faso, ya biyo bayan maganganun da su ka fito daga kwamandan sojojin Amurka a Afirka Janar Michael Langley wanda ya zargi sojojin dake Mulki da amfani da ma’adanan kasar saboda kashin kansu maimakon yi wa mutane aiki. Mahalarta gangamin sun daga kwalaye dake dauke da rubutun yin tir da furucin jami’in sojan na Amurka da kuma nuna goyon baya ga shugaban kasar. Daga cikin mahalarta gangamin da akwai fitaccen mawakin kasar, Ocibi Joan,wanda ya siffata jami’in sojan Amurkan da dabbar daji mai cin mutane yana...
Mataimakin shugaban kasar Iran na farko Muhammad Ridha Arif ya bayyana cewa; Da akwai bukatar fadada da bunkasa alakar dake tsakanin Iran da Sudan, sannan ya kara da cewa; Iran din a shirye take ta yi aiki da Sudan domin bunkasa sana’o’inta. Mataimakin shugaban kasar ta Iran ya furta haka ne dai a lokacin da ya gana da ministar masana’antu ta Sudan Mahasin Ali Yakub da ta kawo Ziyara Iran. Muhammad Ridha Arif ya yi wa Sudan fatan alheri da son ganin zaman lafiya ya dawo, sannan kuma ya bayyana sake bude ofishin jakadancin Sudan a Tehran a shekarar da ta gabata a matsayin alamar kyautatuwar alaka a tsakanin kasashen biyu. Mataimakin shugaban kasar ta Iran ya zargi kasashen turai...
Sakataren Majalisar koli ta tsaron kasar Iran wanda ya halarci taron kungiyar “Brics” a kasar Brazil ya bayyana cewa; Makaman Nukiliya ba su cikin akidar tsaron kasar Iran. Ali Akbar Amhadiniyan ya kuma kara da cewa; Iran ba za ta amince da kin aiki da hakkokinta na cin moriyar fasahar makamashin Nukiliya a fagagen zaman lafiya ba. Da yake Magana akan Falasdinu kuwa, sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran ya ce: “Amfani da karfi domin kai wa ga sulhu” da “Diflomasiyya ta dole” akidun siyasa ne masu hatsarin gaske, yana mai kara da cewa; ta hanyar shimfida adalci ne ake kai wa ga sulhu,haka nan kuma yin furuci da hakokin da suke halartattu. Akan barazanar da wasu kasashe suke...
Masana Alkur’ani daga ƙasashe 20 ne za su shiga Gasar Karatun Alƙur’ani ta Duniya da za gudanar a karon farko a Najeriya. Gasar wadda za ta gudana a watan Agustan wannan shekarar, za a fara ta ne a Birnin Jos na Jihar Filato, sannan a kammala a Babban Birnin Tarayya Abuja Tsohon Ɗan Majalissar Wakilai Mai wakiltar Mazaɓar Bassa da Jos ta Arewa a Jihar Filato, Honorabul Muhammad Adam Alkali, ya ɗauki nauyin shiryawa. A lokacin gagarumin taron kaddamar da kwamitocin shirye-shiryen gasar ta duniya, wanda Gwanayen Alƙur’ani daga faɗin kasar nan suka halarta, Honourable Alkali ya ce tuni an sanar da cibiyar bunƙasa karatun addinin Musulunci ta Jami’ar Usmanu Ɗan Fodiyo ta Sakkwato kuma ta goyi bayan ƙudirin. Ya...
Ƙarar wani abin fashewa mai ƙarfi ya girgiza Barikin Sojoji na Giwa da ke Maiduguri a Jihar Borno da sanyin safiyar Alhamis ɗin nan. Tashin abin fashewan ya jefa mazauna unguwannin Polo, Fori, GRA da Jami’ar Maiduguri cikin tashin hankali. Ƙarin bayani na nan tafe.
Ministan ya ce sabon gidan yanar na intanet zai taimaka wajen shawo kan matsalolin da suka daɗe suna dagula harkokin sayayya a gwamnati, kamar yadda ake fama da rashin ingantattun tsare-tsare, ƙarancin ƙwararru da rashin tsarin horaswa na dindindin. Ya ce: “Ƙaddamar da wannan sabon shafin ba kawai cigaba ba ne a fannin fasaha; wata babbar hanya ce ta sauya fasalin aiki gaba ɗaya wadda ke magance manyan ƙalubale a tsarin sayen kaya na gwamnati, irin su cikas da ke yawan faruwa, rashin ingantattun hanyoyin sayayya, ƙarancin ma’aikatan da suka dace, da kuma rashin ingantaccen tsarin gina ƙwarewa. “Waɗannan matsaloli sun daɗe suna hana a yi amfani da dukiyoyin gwamnati yadda ya kamata tare da kawo cikas ga...
Gwamnatin Nijeriya ta ayyana gobe Alhamis 1 ga watan Mayu a matsayin ranar hutu ga ma’aikatan ƙasar albarkacin bikin murnar Ranar Ma’aikata ta Duniya. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Ministan Harkokin Cikin Gida na ƙasar, Olubunmi Tunji-Ojo, ya fitar a yammacin wannan Larabar. AU ta janye takunkumin da ta ƙaƙaba wa Gabon Tsoffin ma’aikatan NECO na neman a biya su bashin haƙƙoƙinsu Sanarwar ta ambato ministan yana yaba wa ma’aikatan ƙasar kan sadaukarwa da jajircewar da suke yi wajen gudanar da ayyukansu. Ministan ya kuma yaba musu kan gudunmawar da suke bayarwa wajen ciyar da Nijeriya gaba. Ana dai gudanar da bikin Ranar Ma’aikata a ranar 1 ga watan Mayun kowace shekara a sassan duniya.
Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta janye takunkuman da ta ƙaƙaba wa Gabon bayan dakatar da ƙasar ta Tsakiyar Afirka saboda juyin mulkin da aka yi a watan Agustan 2023. Wani taro da aka yi na Kwamitin Zaman Lafiya da Tsaro kan sauyin siyasa a Gabon “ya yi nazari kan ayyukan tare da gano cewa sun yi nasara,” in ji shashen Siyasa da Zaman Lafiya da Tsaro na AU a shafin X a ranar Laraba. Dokta Bashir ya zama shugaban Majalisar Shari’ar Musulunci ta Nijeriya Dalilin da manyan ’yan siyasa ke barin NNPP — APC Sanarwar ta ce za a yi maraba da Gabon “ta dawo nan da nan, ta ci gaba da shiga ayyuka” a sakatariyar Tarayyar Afirka. An dakatar...

Kwastam Ta Kama Jirage Marasa Matuka Da Sauran Kayayyaki Da Darajarsu Ta Haura Naira Biliyan 921 A Legas
Ya bayyana cewa, ziyarar da ya kai a tashar ruwa ta PTML da Tin Can na da nufin sanin irin kalubalen da jami’an sa ke fuskanta wurin amfani da sabuwar na’urar zamani domin binciken kayayyakin da ake shigowa da su kasar. Ya kuma kara gargadin jama’a game da karuwar kwararowar magunguna kasar da ba su da rajista, musamman magungunan inganta jima’i, inda ya yi gargadin cewa irin wadannan abubuwa na da matukar barazana ga kiwon lafiyar jama’a. Ya yi gargadin cewa, yin amfani da wadannan magungunan ba tare da kulawar likitoci ba zai iya haifar da mummunar illa ga lafiyar jiki, ciki har da haɗarin cututtukan zuciya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da...
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce za a yi taro karo na hudu na shawarwari tsakanin Tehran da Washington kan shirin nukiliyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a birnin Rome na kasar Italiya a ranar Asabar mai zuwa. M. Araghchi ya fadawa manema labarai a gefen taron majalisar ministocin gwamnatin kasar na mako-mako yau Laraba cewa, inda ya ce taron na Rome zai kasance gabanin wani taro a ranar Juma’a na tsakanin Tehran da kasashen Turan nan uku da ake wa lakabi da E3 wato – Ingila, Faransa da kuma Jamus wadanda suka sanya hannu kan yarjejeniyar nukiliyar Iran ta 2015. Ya ce rawar da kasashen Turai uku ke takawa ta ragu sakamakon manufofinsu a tattaunawar da aka dade...
Iran ta sha alwashin ci gaba da aiwatar da manufofinta na raya dangantakarta da Jamhuriyar Nijar. Mataimakin shugaban kasar na farko Mohammad-Reza Aref ya ce Iran na ci gaba da aiwatar da manufofinta na raya dangantakarta da Nijar da sauran kasashen nahiyar Afirka bisa tsarin juyin juya halin Musulunci. Aref ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da ministan man fetur na kasar Nijar Sahabi Oumarou wanda ke Tehran, inda yake jagorantar wata tawaga, domin halartar taron hadin gwiwar tattalin arzikin Iran da Afirka karo na uku. Ya ce da gaske ne gwamnatin Iran mai ci a yanzu tana son raya dangantakar da ke tsakaninta da kasashen Afirka ciki har da Nijar dangane da batutuwan da suka dace....
To, bayanai a sama sun nuna ra’ayi iri daya na gwamnatocin dimbin kasashe masu tasowa. Ban da haka, wani binciken jin ra’ayin jama’a da kafar yada labarai ta Sin CGTN, da jami’ar Renmin ta kasar Sin suka gudanar a kasashe 38, ya nuna cewa, matakan ramuwar gayya da kasar Sin ta dauka kan kasar Amurka suna samun goyon baya tsakanin al’ummun kasashe daban daban, inda a dimbin kasashe masu tasowa da suka hada da Najeriya, da Kenya, da Masar, da Ghana, da Afirka ta Kudu, da Turkiya, matakan kasar Sin suka samu goyon baya daga mutane fiye da kaso 70% da aka gudanar da bincike kansu. Kana a kasashen yamma da suka hada da Faransa, da Jamus, da Canada,...
Bayanai daga Falasdinu na cewa akalla Falasdinawa 35 dane suka hada da kananan yara aka kashe a wanisabon kisan kiyashi na Isra’ila a zirin Gaza. A cewar ma’aikatar lafiya ta Gaza, wadannan hare-haren sun yi sanadin mutuwar mutane 35 tare da jikkata 109 a cikin sa’o’i 24 da suka gabata. Adadin wadanda sukayi shahada sakamakon yakin kisan kare dangi da Isra’ila ke yi a yankin da aka yi wa kawanya ya zarce 52,400. Adadin wadanda suka jikkata kuma ya kai kusan 118,014 tun daga watan Oktoban 2023. Majalisar Dinkin Duniya dai ta yi gargadin barkewar ayyukan jin kai a Gaza. Hukumar samar da abinci ta duniya (WFP) ta fitar da wani kakkausan gargadi game da matsalar jin kai da ke...
Amurka ta sanar da kakaba takunkumi kan wasu kamfanoni 7 da ta ce suna da hannu wajen siyar da man kasar Iran, a wani mataki na kara matsin lamba duk da tattaunawar da aka yi kan shirin nukiliyar Iran. Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar ta ce, bangarorion da takunkumin ya shafa sun hada da kamfanonin kasuwanci guda biyar, hudu da ke Hadaddiyar Daular Larabawa, daya kuma a kasar Turkiyya, wadanda suka sayar da albarkatun man fetur na kasar Iran ga kasashe uku, da kuma wasu kamfanonin jigilar kayayyaki guda biyu. A cikin sanarwar da sakataren harkokin wajen kasar ta Amurka Marco Rubio ya fitar, ya ce “Matukar dai Iran na son samar da kudaden shiga na man...
Gwamnatin jihar ta ce, matakin na daya daga cikin kokarin gwamnati mai ci na inganta ayyukanta domin samar da romon dimokuraɗiyya ga al’ummar jihar Sokoto. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A ganin gwamnatin Amurka, manufar ramuwar haraji za ta taimaka wajen farfado da masana’antu a kasar da kara samar da guraben aikin yi, amma yadda ta daidaita matsalolin tattalin arzikinta ba ta hanyar da ta dace ba, da kuma gazawa wajen bin ka’idojin tattalin arziki, ya haifar da damuwa a zukatan al’umma da kuma tsoro a kasuwanni, lamarin da ya sa Amurka ta kara shiga mawuyacin hali. Cikin kwanaki 100 da suka shude, wasu kasashen duniya sun ki mika wuya ga cin zalin Amurka ta fuskar manufar ramuwar haraji. Misali, kasar Sin ta fara mayar da martani, a kokarin kiyaye halastattun hakkokinta da tsarin tattalin arziki da cinikayya da ma na adalci a duniya. Kana kuma kungiyar tarayyar Turai...
Rayukan al’umma gami da dukiya musamman na ababen hawa na ci gaba da salwanta a Mahadar hanya ta yankin Tipper-garage da ke Dutse-Baupma, da ke kan titin da ya tashi daga garin Dutsen-Alhaji ya nufi garin Bwari, a yankin Birnin Tarayya Abuja. Titin da ke mastayin tagwaye ya haɗa yankin da garin Jere da ke Jihar Kaduna. Hanyar na ci gaba da ganin ƙaruwar kwararan motoci a sakamakon ingancinta da kuma karancin matsalar tsaro, idan a ka kamanta ta da babban titi Abuja zuwa Kaduna. Rawar da Arewa za ta taka a Zaɓen 2027 An ɗaure ’yar shekara 80 a kurkuku saboda dukan jikarta da silifas Adadin motoci da ke bin titin ya kara dagawa a bayabayan nan a dalilin...
Sun ce suna tafiya daga Yola zuwa Lafia ne lokacin da wasu mutane da ake zargin ‘yan fashi ko masu garkuwa da mutane ne suka kai musu hari, lamarin da ya sa suka tsere zuwa daji don tsira rayukansu. Sojojin sun taimaka wajen gyara tayar motar sannan suka tabbatar da cewa fasinjojin sun ci gaba da tafiyarsu cikin tsaro. Shugaban Runduna ta 6, Birgediya Janar Kingsley Uwa, ya yaba wa sojojin bisa saurin ɗaukar mataki da kuma tsayin daka kan aiki. Ya kuma buƙaci jama’a da su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro haɗin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanai a kan lokaci domin taimakawa wajen yaƙi da laifuka. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun...
’Yan siyasar yankin Arewa na ganin dole sai da goyon bayansu ɗan takara zai yi nasara a zaben Shugaban ƙasa. Hakan na zuwa ne bayan tsohon maitaimaka wa shugaban ƙasa a fannin siyasa, Alhaji Hakeem Baba-Ahmed ya yi wata hira, inda yake cewa, nan da wata shida yankin zai fitar da matsayarsa. An ɗaure ’yar shekara 80 a kurkuku saboda dukan jikarta da silifas Dalilin da manyan ’yan siyasa ke barin NNPP — APC Duk da cewa Hakeem ba shi ne mai magana da yawun al’ummar yankin ba, amma ana kallon sa a matsayin daya daga cikin manya a yankin, saboda tsohon matsayinsa na mai magana da yawun Kungiyar Dattawan Arewa (NEF). Tsarin siyasar kasar nan ya sa dole ne...
Kakakin ma’aikatar sharia a nan JMI ya bada sanarwan cewa,ma’aikatar za ta bayyanawa mutanen sakamakon bincken da suka gudanar kuma suke ci gaba da yi, dangane da fashewa da kuma gobatar da ta tashi a tashar jiragen ruwa ta Shahid Rajaee a cikin yan kwanakin da suka gabata. . Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran, ya bayyana cewa, Asgar Jahangir kakakin ma’aikatar sharia da kuma Zabihullah Khudayiyan shugaban hukumar bincike ta kasa, sun gudanar da taron hadin guiwa da yan jaridu da kafafen yada labarai na cikin gida da waje a safiyar, dangane da fashewa da kuma gobarar da ta biyo baya a tashar jiragen ruwa na Shahid Rajaee. Banda haka jami’an sun amsa tambayoyin yan jarida bayan jawabansu...
A wani taro wanda ya hada ministan riko na tattalin arziki da kudade na JMI da kuma mai bawa firai ministan kasar Iraki shawara, bangarorin biyu sun tabbatar da cewa an kammala aikin shimfida layin dogo tsakanin garin Shalamcheh na kasar Iran da kuma birnin Basra a kasar Iraki. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto jami’an gwamnatocin kasashen biyu na fadar haka, sun kuma jaddada muhimmancin layin dogon da kuma samar da kasuwar babu kudaden fito a kan iyakokin kasashen biyu. Labarin ya kara da cewa harkokin kasuwanci tsakanin kasashen biyu ya zuwa yanzu ya kai dalar Amurka biliyon $11a ko wace shekara kuma anan saran nan gaba zai iyakaruwa zuwa dalar Amurka biliyon $25. Rahmatollah Akrami,...
A Kaduna, an kama wasu mutane uku da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, ciki har da wani da ya ce ya koma jihar ne domin kafa sabuwar ƙungiya bayan an kama abokan aikinsa a Kwara. Haka kuma, an kama wasu biyu da ke ɗauke da bindigogi. ‘Yansanda sun gano makamai da dama, ciki har da bindigogi ƙirar AK-47 da AK-49, da kuma wasu makamai da aka ƙera a gida. Wannan aiki na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na yaƙar garkuwa da mutane da safarar makamai a faɗin ƙasar. Kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ya ce ana ci gaba da bincike, kuma za a gurfanar da waɗanda ake zargi a kotu da zarar an kammala binciken. Ya kuma yaba da goyon...
A yammacin ranar Talata Arsenal ta karbi bakuncin PSG a matakin wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin zakarun Turai na bana. An dai barje gumi ne a filin wasa na Emirates, inda PSG ta yi wa Arsenal ci daya mai ban haushi har gida. DAGA LARABA: Asarar Da Hausawa Ke Tafkawa Sakamakon Bacewar Tatsuniya ISWAP ta ɗauki alhakin kashe mutum 26 a Borno PSG ta fara cin ƙwallo ta hannun Ousmane Dembele a minti na huɗu da take leda, haka suka je hutu har da zagaye na biyu, amma Gunners ba ta farke ba. Wannan shi ne karo na biyu da suka fuskanci juna a Champions League a kakar nan, inda Gunners ta yi nasarar cin 2-0...
Ƙungiyar matasan jam’iyyar APC reshen Jihar Kano ta ce guguwar sauyin sheƙa ta jiga-jigan ’yan siyasa da ke ficewa daga jam’iyyar NNPP alama ce da ke nuna cewa tasirin tsohon Gwamnan Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso a siyasance na ƙara disashewa. Cikin wata sanarwa da ƙungiyar matasan ta KASASCO ta fitar a ranar Talata, ta ce a halin yanzu jam’iyyar APC ba ta buƙatar dawowar Kwankwaso cikinta saboda tasirinsa a siyasance na ci gaba da gushewa. DAGA LARABA: Asarar Da Hausawa Ke Tafkawa Sakamakon Bacewar Tatsuniya ISWAP ta ɗauki alhakin kashe mutum 26 a Borno Darekta Janar na KASASCO, Kwamared Yahaya Usman Kabo, ya ce jam’iyyar APC a ƙarƙashin jagorancin Abdullahi Abbas ta yi tsayuwar daka da kafa tubalin samun nasara...
Manyan malaman addinin darikar Roman Katolika za su fara Shirin zabar shugaban darikar tasu a fadar Vatican Adadin manyan malaman addinin masu mukamin “Cardinal” 130 ne za su taru a fadar Vatican, domin su zabi wanda zai maye gurbin Paparoma Farancis da ya rasu. Sai dai masu kusancin da fadar ta Vatican suna bayyana cewa, da akwai batutuwa da dama da su ka raba kawunan manyan malaman addinin na Roman Katolika da su ka batun auren jinsi, da rawar da mata za su taka a karkashin inuwar cocin. Sai dai kuma wani mai sharhi akan abubuwan da su ka shafi cocin, Reese ya bayyana cewa, masu zaben za su mayar da hankali ne akan wanda zai kare ayyukan da mamacin...
Kakakin kwamitin tsaron kasa a majalisar shawarar musulunci ta Iran ya bayyana cewa; ” Ya zuwa yanzu ba za mu iya yin hukunci akan dalilan da su ka haddasa fashewar abubuwa a tashar ruwa ta Shahid Raja’i ba, amma za mu iya cewa babu hannu waje a ciki. Kakakin kwamitin tsaron kasar ta Iran Ibrahim Rizai wanda ya halarci taron da aka yi a Majalisa akan fashewar da aka samu a tashar ruwan ta shahid Raja’i, ya kuma kara da cewa; Fahimtata da abinda na ji daga abokan aikina dangane da abinda ya faru a tashar ruwa ta Shahid Raja’i, da kuma rahotannin da su ka iso mana, shi ne cewa abinda ya farun ba shi da alaka da waje.”...
Wani bon kirar hannu da aka dasa akan hanyar dake hada Rann da Gamboru a jihar Borno ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 6. Daga cikin wadanda su ka rasa rayukansu sanadiyyar tashin bom din sun hada mata da kananan yara kamar yadda majiyar ‘yan sanda ta sanar. Kungiyar nan mai suna; gwamnatin musulunci a yammacin Afirka ce ta sanar da daukar alhakin kai hari na ranar Litinin din da ta gabata. Bugu da kari sauran wadanda su ka rasa rayukan nasu manoma ne da suke cikin motar a-kori-kura da ta taka nakiya. Baya ga wadanda su ka rasa rayukansu, wasu mutanen su 3 sun jikkata,kuma tuni an dauke su zuwa asibiti domin yi musu magani. Wani dan sintiri da yake...
A yau Laraba sa jijjifin Safiya an sami shahidai 3 a Gaza da hakan ya kara yawan shahidai zuwa 40 a cikin sa’o’i 24. Bugu da kari, baya ga shahidan da suke faduwa a kowace rana, ana fama da matsananciyar yunwa a cikin yankin, bayan karewar kayan abincin HKI ta sake komawa yaki kwanaki 44 da su ka gabata. A cikin sansanin ‘yan hijira na “Nusairat” mutane 3 sun yi shahada da su ka hada da karamar yarinya sanadiyyar harin da sojojin na HKI su ka kai wa yankin. A gabashin birnin Khan-Yunus ma dai wasu Falasdinawa sun yi shahada. Daga ranar 7 ga watan Oktoba na 2023 zuwa yanzu adadin wadanda su ka yi shahada sun wuce 52,000,wadanda su...
Shugaban tawagar baƙin, Alhaji Ibrahim Abdullahi Yar’adua, ya ce sun zo Yobe domin nazarin halin tsaro da tattara bayanai da za su taimaka wajen tsara manufofin tsaron ƙasa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Mista Mark Joseph Carney murna bisa zaɓensa a matsayin Firaiminista na 24 na ƙasar Kanada, bayan nasarar jam’iyyar Liberal a zaɓen majalisar dokokin da aka kammala kwanan nan. A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga, ya fitar, Shugaba Tinubu ya bayyana zaman Carney a wannan matsayi a matsayin wani muhimmin ci gaba, musamman a wannan lokaci da Kanada ke bukatar gogaggen shugaba domin fuskantar ƙalubale da dama. Carney, wanda fitaccen masani ne a fannin tattalin arziki, ya taba rike mukamin Gwamnan Babban Bankin Kanada daga shekarar 2008 zuwa 2013, sannan ya ci gaba da zama Gwamnan Babban Bankin Ingila daga 2013...