An Tabbatar Da Ficewar Sanata Sumaila Daga NNPP Zuwa APC A Majalisa
Published: 7th, May 2025 GMT
Sumaila, tsohon mataimaki na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harkokin majalisar dokokin kasar, ya bayyana jam’iyyar NNPP a matsayin “jam’iyyar da ke da rabe-rabe da tabarbarewar al’amura, inda ya ce, rikicin da ya dabaibaye Jam’iyyar a fili yake babu mai musantawa, wadanda suka hada da shari’o’i a kotuna da dama da kuma gwagwarmayar shugabancin jam’iyyar.
A karshe, Sumaila ya kafa uzuri a karkashin doka ta 42, inda ya bayyana godiyarsa ga takwarorinsa da jama’ar mazabarsa, inda ya yi alkawarin kara zage damtse wajen gudanar da ayyukansa na ‘yan majalisu domin yi wa kasa hidima.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Hafsan sojin sama ya umarci a yawaita yi wa ’yan ta’adda ruwan bama-bamai
Hafsan Sojin Sama na Najeriya, Air Marshal Sunday Aneke, ya umarci dukkanin kwamandojin rundunar da su ƙara ƙaimi wajen yi wa ’yan ta’adda ɓarin wuta ta sama
A yayin wani taron da suka gudanar da Abuja a ranar Laraba, Aneke, ya umarci kwamandojin da su kai hare-hare masu yawa domin kare rayuka da dukiyoyin ’yan ƙasa.
Za a gudanar da wasannin ƙwallon yashi a Abuja An amince da hukuncin yi wa malamai ɗaurin shekara 14 kan lalata da ɗalibaiYa ce, “Dole ne yayin kowane aiki a nuna ƙwarewa da ƙaunar ƙasa.”
Mai magana da yawun rundunar, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya ce taron ya mayar da hankali kan duba dabarun aiki da kuma ƙarfafa haɗin kai a tsakanin kwamandoji.
Ya ce, “Taron ya samar da dama don daidaita dabaru da tabbatar da cewa rundunar sojin sama tana ci gaba da zama ginshiƙi wajen tsaron ƙasa.”
Aneke, ya kuma jaddada muhimmancin haɗin kai a tsakanin sojin sama, sojin ƙasa, sojin ruwa da sauran hukumomin tsaro domin samun nasara tare.
Ya ce dole ne hare-haren su kasance bisa bayanan sirri da kuma tsari mai kyau don cimma sakamako mai ɗorewa.
Shugaban sojin sama ya tabbatar da cewa za su inganta walwalar jami’ai tare da ba su ƙarin horo da kayan aiki na zamani domin ƙara musu ƙwarewa a fagen fama.
Haka kuma ya yi alƙawarin bai wa ƙirƙire-ƙirƙire da fasaha muhimmanci a cikin ayyukan rundunar.
Hakazalika, Aneke ya tabbatar da cewa rundunar sojin saman za ta ci gaba da mara wa Gwamnatin Tarayya baya wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Ya ce rundunar za ta ci gaba da yin aiki cikin ladabi, mutunci da ƙwarewa.