HausaTv:
2025-08-08@08:50:00 GMT

Ministan harkokin wajen Iran zai Ziyarci Saudiyya da Qatar

Published: 9th, May 2025 GMT

A wani lokaci a gobe Asabar ne ake sa ran ministan harkokin wajen Iran zai fara wata ziyara a kasashen Saudiyya da kuma Qatar.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa, ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi zai ziyarci Saudiyya da Qatar a, bayan rahotannin da ke cewa akwai yiwuwar yin wata sabuwar tattaunawa tsakanin Tehran da Washington.

M. Baghai ya bayyana cewa ziyarce ziyarce da Araghchi zai yi na daga cikin manufofin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na ci gaba da karfafa alakarta da makwabtanta.

“Ministan harkokin wajen kasar ta Iran, zai fara tafiya birnin Riyadh don ganawa da manyan jami’an Saudiyya, sannan kuma zai tafi Doha don halartar taron tattaunawa tsakanin Iran da kasashen Larabawa.”

Bayanin hakan ya biyo bayan rahoton da kafar yada labaran Amurka Axios ta bayar cewa, ranar Lahadi ne ake sa ran za a gudanar da zagaye na hudu na tattaunawar tsakanin Iran da Amurka a birnin Muscat na kasar Omani.

Tun da farko dai an shirya gudanar da taron ne a ranar 3 ga watan Mayu, amma aka dage.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: harkokin wajen

এছাড়াও পড়ুন:

Duk wanda ya haka rijiyar burtsatse a Lekki ruwan masai yake sha – Gwamnatin Legas

Gwamnatin jihar Legas ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar duk wanda yake haka rijiyar burtsatse a unguwar masu hannu da shuni ta Lekki da ke jihar, ruwan masai yake sha.

Babban Sakatare a ofishin da ke kula da magudanun ruwa da tsaftar ruwan sha a jihar, Mahmood Adegbite ne ya bayyana haka yayin wani taron masu ruwa da tsaki kan samar da ruwan sha a jihar a kwanakin baya.

DAGA LARABA: Me Ke Sa Matasa Zama Karnukan Farautar ‘Yan Siyasa A Kafafen Sadarwa Na Zamani? ‘Za a yi ambaliyar kwana 5 a jihohi 19 na Najeriya’

Mahmood ya kuma ce gurbataccen ruwan sha a unguwar zai iya haifar da barazanar lafiya matukar ba a bi hanyoyin da suka dace wajen tsaftace shi ba.

Ya ce, “Game da batun kula da tsaftar muhalli kuwa, zan iya cewa duk wanda ya haka burtsatse a yankin unguwar Lekki, watakila yana shan ruwan da zan iya kira da ruwan masai ne.

“Amma idan muka yi kokari wajen sarrafa dattin da yake fitowa daga yankin kamar yadda muke yunkurin yi a yanzu haka, za mu dakile duk wata cuta da za ta iya yaduwa sanadiyyar rashin tsafta,” in ji shi.

Sai dai ya ce akwai jan aiki a gaban jihar wajen magance matsalar ambaliyar ruwa, yana mai cewa ko a watan da ya gabata sai da aka samu ambaliyar a wasu sassan jihar, sabanin a watan Agustan da aka saba gani a shekarun baya.

“Maganar gaskiya a bangaren ambaliya, duk da muna namijin kokari wajen magance ta, amma har yanzu akwai jan aiki a gabanmu kafin mu iya magance matsalar baki daya,” in ji Babban Sakataren.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kasar Masar Tana Ta Zama Mai Shiga Tsakanin Iran Da IAEA Da Kuma Amurka
  • Araqchi: Ba a kayyade wani lokacin shiga wata sabuwar tattaunawa da Amurka ba
  • Shugaban Kasar Iran Ya Jaddada Wajabcin Haduwar Kasashen Musulmi Wajen Hana Laifukan Gaza
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Taya Ali Larijani Murnar Nada Shi Sakataren Majalisar Kolin Tsaron Kasar Iran
  • Ministan tsaron Ghana da wasu sun rasu a hatsarin jirgin sama
  • Iran Ta Ce Babu Wani Da Zai Kusanci Cibiyoyin Tashe Makamashin Uranim Na Kasar
  • Kwamishinan ‘Yan Sanda Na Jihar Kano Ya Sha Alwashin Kawar Da Badala A Harkokin Fina-finai
  • Iran Ta Ce Babu Wani Da Zai Kusanci Cibiyoyin Tashe Makamashin Uranim Na Kasar Iran
  • Duk wanda ya haka rijiyar burtsatse a Lekki ruwan masai yake sha – Gwamnatin Legas
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Ce; Hadin Kai Tsakanin Cibiyoyi  Na Tabbatar Da Karfi Da Ci gaba