Jami’an tsaro na ba da gudunmawar aikata miyagun laifuka a Nijeriya — Zulum
Published: 7th, May 2025 GMT
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya yi zargin cewa sojoji da sauran jami’an tsaro na bayar da gudunmawar aikata miyagun laifuka da cin zarafin jama’a a Nijeriya.
Zulum ya faɗi hakan ne yayin da yake haramta sayar da barasa a birnin Maiduguri da kewaye.
Ka-ce-na-cen da ya biyo bayan ziyarar Tinubu a Katsina DAGA LARABA: Ɓoyayyun Dalilan Da ke Sa Faɗuwa Jarabawa A NajeriyaGwamnan ya bayyana haka ne a ranar Talata a wajen ƙaddamar da wani kwamitin da aka kafa don “ƙwace haramtattun otal-otal da gidajen karuwai da gidajen kwana da maɓoyar miyagun laifuka da kuma daƙile illolin munanan ɗabi’u.
Gwamnan ya ce tsofaffin jami’an tsaron Nijeriya da na yanzu da suke aiki sun taka rawa wajen jawo jama’a cikin aikata miyagun laifuka kamar tsaurin ra’ayi da karuwanci da sauran munanan ɗabi’u, lamarin da ke kara ta’azzara barazanar ta’addanci a jihar.
“Na yi farin ciki da sanin cewa jami’an soji suna wajen nan, musamman sojoji, ‘yan sanda, da sauran su, domin yawancin waɗannan ayyukan wa ke yin su?
“Wasu daga cikinsu akwai jami’an soji da aka kora da masu ci a yanzu har da fararen hula.
“Don haka, bai kamata a ƙi sukar kowane ɓangare ba a cikin wannan lamarin idan har muna son babban birnin Maiduguri da kuma jihar ta kawar da ta’addanci da sauran laifuka,” in ji Zulum.
A takaitaccen taron, Zulum ya sake kafa kwamitin tare da sake ba wa kwamitin damar kawar da duk wani nau’i na miyagun laifuka da munanan ɗabi’u a cikin birnin Maiduguri da kewaye.
Dokar hana sayar da barasa da kayan maye, a cewar gwamnan, ta samo asali ne daga yadda ake ta samun tashe-tashen hankula a tsakanin ƙungiyoyin da ke gaba da juna da ƙungiyoyin asiri da karuwanci da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da ‘yan fashi da sata, waɗanda suka haddasa asarar rayuka da dukiya.
Gwamnan ya haɗa hannu da sojoji, ‘yan sanda, sibil difens da wasu jami’an tsaro da dama da suka haɗa da ’yan sa-kai domin shiga cikin kwamitin domin gudanar da cikakken bincike.
Da yake amincewa da aikin da ke gaban kwamitin da aka sake kafawa, shugaban kwamitin ya yi tir da tabarbarewar harkokin tsaron cikin gida a Maiduguri tare da bayyana matakin da kwamitin zai ɗauka nan take.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: cin zarafi Jami an Tsaro jihar Borno Miyagun Laifuka miyagun laifuka
এছাড়াও পড়ুন:
Jami’an Alhazai Sun Karrama DG Labbo Bisa Nasarar Hajjin 2025
Jami’an Alhazai na shiyya-shiyya sun karrama Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa Alhaji Ahmed Umar Labbo bisa nasarorin da aka samu a aikin hajjin shekarar 2025.
Shugaban jami’an alhazai na shiyya-shiyya, Alhaji Sale Haruna Kafin Hausa ya tabbatar da hakan a wani kwarya-kwaryan biki da aka gudanar a shelkwatar hukumar dake Dutse Babban Birnin jihar.
Ya ce karrama Ahmed Labbo, na da nasaba da gudunmawar da ya bayar da kuma samun nasarar aikin hajjin bana a gida da kuma kasar Saudi Arabia.
Yace wadannan nasarorin sun sanya hukumar ta samu lambobin yabo da kyautuka da dama a kasa mai tsarki.
Alhaji Sale Haruna Kafin Hausa, yana mai cewar jami’an alhazai na shiyya-shiyya suna alfahari da Alhaji Ahmed Umar Labbo bisa yadda yake kula da su da kuma tafiya da kowa wajen gudanar da aikin hajji.
Da yake maida jawabi, Darakta janar na hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ya yaba ma jami’an bisa wannan karamci da kuma gode musu bisa kokarin su wajen kula da alhazai a aikin hajjin bana.
Shima a nasa tsokacin, Mai bai wa Gwamna Umar Namadi shawara akan aikin hajji, Alhaji Isa Idris Gwaram ya bayyana Alhaji Ahmed Umar Labbo a matsayin Shugaba abun koyi da hukumar alhazai ta jihar take alfahari da shi.
Wakilinmu, ya shaida mana cewar, a yayin bikin an kuma karrama Daraktan kudi da mulki na hukumar, Alhaji Jamilu Ilu Kazaure wanda ya yi ritaya daga aiki.
Usman Mohammed Zaria