Kotu Ta Ɗage Shari’ar Yahaya Bello Zuwa 26 Ga Yuni Don Yanke Hukunci
Published: 9th, May 2025 GMT
Kotun tarayya da ke Abuja ta ɗage ƙarar tuhumar tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello kan zargin badaƙalar kuɗi da hukumar EFCC ta gabatar zuwa ranakun 26, 27 ga Yuni da 4, 5 ga Yuli don yanke hukunci kan buƙatar masu gabatar da ƙara ta “yi wa shaidar tambayoyi” da kuma ci gaba da shari’ar.
Alkali Emeka Nwite ya ɗage shari’ar bayan ya saurari hujjojin daga ɓangaren masu gabatar da ƙara da na masu kare Yahaya Bello.
Wani shaidar hukumar EFCC, Nicholas Ojehomon, wanda ya faɗi a kotun cewa ba a tura kuɗin karatar ƴaƴan gidan Yahaya Bello daga gwamnatin jihar Kogi ko wata ƙaramar hukuma zuwa asusun makarantar AISA ba, ya kuma karanta wani ɓangare na hukuncin da kotun FCT ta yanke cewa babu umarnin kotu da ya umarci makarantar AISA da ta mayar da kuɗaɗen zuwa hukumar EFCC.
Al’ƙalin ya yanke shawarar ɗage shari’ar don yanke hukunci kan bukatar EFCC ta yi wa shaidar tambayoyi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Yahaya Bello
এছাড়াও পড়ুন:
Hatsarin mota ya yi ajalin mutum 4, 16 sun jikkata a Yobe
Aƙalla mutum ne sun rasu, yayin da wasu 16 suka jikkata a wani hatsarin mota da ya auku a Ƙaramar Hukumar Karasuwa, a Jihar Yobe.
Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Yobe, SP Dungus Abdulkareem ne, ya tabbatar da faruwar hatsarin ya faru a ranar Asabar da misalin ƙarfe 2:50 na rana a ƙauyen Zangon Kanwa.
Gwamnan Gombe ya bai wa maharba kyautar motoci da babura don bunƙasa tsaro An sanya tukwicin N10m domin kama makasan limamin coci a EnuguHatsarin ya rutsa da mota ƙirar Toyota Hiace wadda ke ɗauke da fasinjoji daga Jakusko zuwa kasuwar Jajimaji da kuma mota ƙirar Volvo daga garin Azare.
Rahoto ya nuna cewa mota ƙirar bas ce ta ƙwace ta buga wani Keke Napep sannan ta ci karo da babbar motar.
Sakamakon haka, direban bas ɗin, Ibrahim Makeri, tare da fasinjoji biyu; Adamu Isiya da Alhaji Shaibu sun rasu nan take.
Daga baya kuma wani daga cikin waɗanda suka ji rauni ya rasu, wanda ya kawo adadin waɗanda suka mutu zuwa huɗu.
An kai gawarwakin da kuma waɗanda suka jikkata zuwa Asibitin Gashuwa da ke Ƙaramar Hukumar Bade.
Likitoci suka tabbatar da mutuwar waɗanda suka rasu, sauran kuwa suna samun kulawa.