Xi Da Putin Sun Rattaba Hannu Kan Sanarwar Hadin Gwiwa A Sabon Zamani
Published: 9th, May 2025 GMT
A yau Alhamis ne shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Rasha Vladimir Putin suka rattaba hannu kan wata sanarwa ta hadin gwiwa game da kara zurfafa hadin gwiwar abokantaka bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni tsakanin Sin da Rasha a sabon zamani. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare.
এছাড়াও পড়ুন:
An Fara Gabatar Da Shirin “Kalaman Magabata Dake Jan Hankalin Xi Jinping” A Rasha
An gabatar da shirin talabijin na kasa da kasa mai taken “Kalaman Magabata dake Jan Hankalin Xi Jinping” jiya Laraba a kasar Rasha, yayin da shugaban Sin Xi Jinping ya isa birnin Moscow domin ziyarar aiki a kasar da kuma halartar bukukuwan cika shekaru 80 da samun nasarar yakin ceton kasa na tsohuwar tarayyar Soviet.
Sama da mutane 200 daga Sin da Rasha ne suka halarci bikin kaddamar da shirin a Moscow. Da yake bayyana kaddamar da shirin a matsayin irinsa na 4 da aka yi a Rasha, shugaban CMG Shen Haixiong ya ce shirin na wannan karo ba amfani da dadaddun labarai wajen gabatar da falsafar shugabanci na gari na Xi Jinping da dabi’un dan adam ga duniya kadai ya yi ba, har da gabatar da wani sabon tsarin kare muhalli da raya fasahohi da bayyana muhimmancin iyali da ilimi. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp