Kashi 42 Na Ma’aikatan Jinya Na Niyyar Barin Afirka Saboda Rashin Albashi – WHO
Published: 12th, May 2025 GMT
Yayin da a wannan Litinin ake bikin ranar jami’an jinya ta Duniya ta shekarar 2025, hukumar lafiya ta Duniya WHO ta ce akwai kashi 42 cikin 100 na ma’aikatan jinya a Afirka, dake cike da burin ficewa daga nahiyar saboda rashin cikakkiyar kulawa da kuma albashi mara tsoka.
A jawabin da ya gabatar akan ranar ma’aikatan jiniya ta duniya, Daraktan riƙo na Hukumar ta WHO a Afirka, Chikwe Ihekweazu, ya ce ficewar tasu za ta nakasa harkokin kiwon lafiyar da ake riritawa a nahiyar.
Ihekweazu ya cigaba da cewa wannan ɓangare na masu aikin jinyar na da matuƙar muhimmanci ga ɗaukacin al’umma, don haka bashi kulawa, abu ne da ya dace, domin zai ba da gudunmawa ga cigaban ɓangaren lafiya, wanda kuma zai taka rawa wajen bunƙasar tattalin arzikin ƙasa da al’umarta.
Wannan rana na zuwa ne a yayin da jami’an jinyar da dama da na wasu sassan kiwon lafiya suka bar Najeriya, ƙasa mafi yawan al’umma a nahiyar Afirka, domin tafiya ƙasashen ƙetare da zummar samun kyakkyawar kulawa da tsarin da ya zarce wanda suke samu a kasarsu
rfi
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jami an jinya
এছাড়াও পড়ুন:
Putin Na Rasha Ya Gana Da Shugabannin Afirka Akan Batun Tsaro
Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin ya karbi bakuncin shugabannin kasashen Afirka da su ka hada na Zimbabwe da na Burkina Fasa, inda su ka tattaunawa hanyoyin karfafa alaka a tsakanin kasashen nasu.
Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa da na Burkina Faso Ibrahim Taraore sun isa birnin Moscow domin halartar bikin cika shekaru 80 da samun nasara akan ‘yan Nazi na Jamus a lokacin yakin duniya na 2.
Bugu da kari shugaban kasar ta Rasha ya kuma gana da shugaban gwamnatin kwarya-karyar Falasdinawa Mahmmud Abbas Abu Mazin,inda su ka yi musayar ra’ayi akan yadda za a kawo karshen kisan kiyashin da HKI take yi wa al’ummar Falasdinu.