HausaTv:
2025-08-09@13:33:28 GMT

Gaza:Falasdinawa 7 Sun Yi Shahada Da Safiyar Yau Asabar

Published: 10th, May 2025 GMT

Da safiyar yau Asabar Falasdinawa 7 sun yi shahada sanadiyyar harin da HKI ta kai a yankin Gaza.

Sojojin HKI sun kai harin ne a kan sansanin ‘yan hijira na unguwar ” al-Sabrah” a cikin birnin Gaza, da hakan ya yi sanadiyyar shahadar Falasdinawa 5 a iyalai daya na Dulaibh. Shahidan su nel Saqar Ahmad Fu’ad dulaibh, da matarsa Hindu, da ‘ya’yansu Ahmad, Hamzah, da Abdulazizi.

Haka nan kuma ‘yan sahayoniyar sun kai wasu hare-haren ta jirgin sama maras matuki a unguwar “Tuffah” dake birnin Gaza, da ya yi sanadiyyar shahadar mutum daya.

Su ma jiragen ruwan HKI sun kai wasu hare-haren munanan a garin Rafah da ya yi sanadiyyar shahadar Muhammad Sa’id al-Burudawil.

A tsakiyar birnin Gaza, ma dai ‘yan sahayoniyar sun kai wasu hare-hare da manyan bindigogi da ya yi sanadiyyar shahadar karamin yaron Bafalasdine guda.

A wani gefen hukumar Gaza ta sanar da cewa yunwa, tana barazana ga rayuwar kananan yaran da sun kai 65,000 saboda ci gaba da hana shigar da kayan abinci cikin yankin na Gaza, da HKI take yi, na tsawonn watanni 2 a jere.

Tsawon kwanaki 40 kenan da dukkanin gidajen burodi a cikin yankin na Gaza su ka rufe kofofinsu saboda rashin fulawa.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: ya yi sanadiyyar shahadar

এছাড়াও পড়ুন:

Fashewar gurneti ya kashe yara uku a Borno 

Fashewar gurneti ya salwantar da rayukan yara mata uku a garin Pulka da ke Ƙaramar Hukumar Gwoza a Jihar Borno.

A wani rahoto da ma’aikacin Sibiliyan JTF Buba Yaga ya fitar, ya ce ɗaya daga cikin ƙananna yaran suna wasa da gurnetin da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne, suka yi watsi da su a lokacin da gurnetin ya tashi da misalin ƙarfe 2:20 na ranar Alhamis.

An garzaya da yaran zuwa Babban Asibitin Gwoza, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsu.

Daga nan ne aka miqa gawarsu ga iyalansu domin yi musu jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Yadda ma’aikatan gwamnati ke gina gidaje da kuɗin sata a Abuja Yadda ma’aikatan gwamnati ke gina gidaje da kuɗin sata a Abuja

Haɗaɗɗiyar tawagar ’yan sandan da suke tantance bama-bamai (EOD-CBRN), da dakarun Operation Hadin Kai, CJTF, da mafarautan yankin sun ziyarci wurin, inda suka gudanar da aikin share wasu na’urori.

Ba a samu ƙarin ko ɗaya ba, kuma an ayyana yankin a matsayin keɓantaccen wurin da za a kauce wa bi zuwa wani lokaci.

Hukumomin tsaron sun bukaci mazauna yankin da su gaggauta kai rahoton abubuwan da suke zargi ga jami’an tsaro domin hana afkuwar irin wannan bala’i.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Iran: ‘Yan Sahayoniyya Na Shari Share Falasdinawa Daga Kn Doron Kasa
  • Fashewar gurneti ya kashe yara uku a Borno 
  • An kashe manomi da dabbobi 39 a Bauchi
  • Isra’ila za ta mamaye ilahirin Zirin Gaza ya koma karkashinta – Netanyahu
  • Nijeriya Na Asarar Tiriliyan 3.2 Sanadiyyar Watsi Da Noma A Gandun Daji
  • Zamfarawa sun yi zanga-zanga kan hare-haren ’yan bindiga
  • Nazarin CGTN: Alummar Duniya Na Adawa Da Fadada Mamaya A Gaza
  • Hare-Haren Sojojin Mamayar Isra’ila Kan Gaza Sun Janyo Shahadan Falasdinawa Masu Yawa
  • Human Rights Watch Ta Ce: Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Rusa Makarantu Fiye Da 500 A Gaza
  • Gaza: Fararen hula 22 sun yi shahada a hare-haren Isra’ila a daren jiya