2025-05-12@10:57:57 GMT
إجمالي نتائج البحث: 20
«da shawarar»:
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya ba da shawarar yin tattaunawa “kai tsaye” ba tare da sharadi ba” tsakanin kasarsa da Ukraine a ranar 15 ga Mayu a Istanbul. A martanin da ya mayar, shugaban na Ukraine ya ce a shirye ya ke don tattaunawa kai tsaye, amma ya zama dole a tsagaita bude wuta a gabanin haka, yana mai nuni da shawarar da kawayensa na yammacin duniya suka bayar na tsagaita bude wuta na kwanaki 30 ba tare da sharadi ba daga ranar Litinin. Ba tare da yin tsokaci a kai tsaye kan shawarar kasahen ba, shugaban na Rasha ya caccaki turawan da ya ce sun yi wa Rasha “rashin ladabi da kakkausan lafazi” ya kuma ce ya kamata...
Wata muhawara ta kunno kai a Jihar Kano da ma wajenta bayan gwamnatin jihar ta ba da umarni a cire naira miliyan 670 daga asusun ƙananan hukumomin jihar domin saye da kuma gyaran motocin Mai Martaba Sarkin Kano, Muhanmmadu Sanusi II. Gwamnatin jihar ta bayyana cewa za a kashe naira miliyan 50 daga cikin kudin wajen gyaran wasu motoci biyu na sarkin, ragowar kuma za a sayo wasu sababbin motoci huɗu. Shekara 10: Me ya sa Kofin Zakarun Turai ya gagari Barcelona? Za a kwaso ’yan Nijeriya 15,000 da ke gudun hijira a ƙetare Ɓullar takardar da ke ɗauke da umarnin ta haifar da ce-ceku-ce, amma gwamnatin jihar ta hannun Kwamishinan Watsa Labarai, Ibrahim Waiya, ta kare matakin da cewa...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ya Ce Kasar Oman Ce Ta Bukaci Dage Zaman Tattaunawan Iran Da Amurka
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: An dage zaman tattaunawan Iran da Amurka ne bisa shawarar kasar Oman Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi nuni da cewa: Ministan harkokin wajen kasar Oman ne ya sanar da sauyin lokacin zaman tattaunawan ba na kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka, yana mai bayanin cewa, dage shawarwarin ya zo ne bisa shawarar ministan harkokin wajen kasar, kuma za a sanar da wata sabuwar rana daga baya. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya sanar da manema labarai cewa: An canja ranar da za a gudanar da zaman shawarwarin ba na kai tsaye ba na gaba tsakanin Iran da Amurka, wanda aka shirya gudanarwa a...
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ya bayyana kalaman gwamnatin ‘yan sahayoniyya a matsayin wani rudu da ba shi da amfani da har zai yi tasiri a zaman tattaunawan Iran da Amurka Wanda ba na kai tsaye ba, yana mai cewa duk wani hari ko da karami ne za a kai kan Iran zai zama tamkar tartsatsin wuta da zai iya janyo tashin gobara da zai iya kona yankin gaba daya. A jawabin da ya gabatar yayin taron kolin majalisar shawarar Musulunci ta Iran a yau Talata, Muhammad Baqir Qalibaf ya bayyana cewa: Firai ministan gwamnatin yahudawan sahayoniyya mai laifi ne mai zubar da jinin fararen hula, saboda neman hana mutuwarsa a fagen siyasa, kuma yanzu yana yin barazana ga al’ummar Iran...

Shawarar Tabbatar Da Tsaro A Duniya Ta Samar Da “Kyakkyawan Fata” Ga Duniya Mai Fama Da Tashin Hankali
Na uku, ba da ra’ayin samun tsaro kafada da kafada, inda aka jaddada cewa, ya dace kasa da kasa su yi fatali da ra’ayin nuna wa juna fito-na-fito, kana, su fuskanci dimbin kalubalen tsaro cikin hadin-gwiwa. Na hudu wato na karshe, tallata ra’ayin tabbatar da tsaro mai dorewa, wato a maida hankali kan dorewar tsaro na wani dogon lokaci. Alal misali, yayin da ake daidaita rikicin wani yanki, bai dace a dogara kan matakan soja kadai ba, ya kamata a nemo mafita tun daga asalin rikicin. Wannan shawarar tsaron da shugaba Xi Jinping ya gabatar, ta samu amincewa sosai daga mutanen kasa da kasa, inda ya zuwa yanzu, ta riga ta samu goyon-baya daga kasashe da yankuna da kungiyoyin kasa...
Yayin ziyararsa kasar Sin kwanan nan, babban mashawarcin gwammatin wucin-gadi ta kasar Bangladesh, Muhammad Yunus, ya tattauna da wakiliyar CMG, wato babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin, inda a cewarsa, a matsayin kasa ta farko a kudancin nahiyar Asiya, wadda ta rattaba hannu tare da kasar Sin kan takardar bayanin hadin-gwiwa game da raya shawarar “ziri daya da hanya daya”, Bangladesh na matukar bukatar shawarar nan, ganin yadda aikin raya shawarar ke da muhimmanci sosai. Muhammad Yunus ya ce, Bangladesh na matukar bukatar cudanyar sassa daban-daban. Hanyoyin mota na taka rawar gani wajen jigilar hajoji, don haka kasar na bukatar kara shimfida hanyoyin mota. Hanyoyi su ne tamkar manyan jijiyoyin tattalin arzikin kasa, shi ya sa ya...
Kungiyar Hamas ta yi Allah-wadai da matakin hadin gwiwa da Amurka da Tarayyar Turai suka dauka na hana watsa tashar talabijin ta Al-Aqsa ta Larabci ta Falasdinu da ke da alaka da kungiyar gwagwarmayar. Kungiyar ta bayyana hakan a matsayin wani yunkuri na toshe muryar Falasdinawa. Sanarwar da Hamas ta fitar ta kara da cewa, wannan shawarar toshe ‘yancin watsa labaru ne da kuma hakki na al’ummar Falasdinu na a ji muryarsu a duniya.” Hamas ta yi kira ga cibiyoyin yada labarai na kasa da kasa da su yi Allah wadai da wannan shawarar, kuma kada su yi shiru dangane da cin zarafin da gwamnatin sahyoniya ta ke yi wa dokokin kasa da kasa da ka’idojin jin kai. Bisa shawarar...
Shugaban Majalisar shawarar musulunci ta Iran Muhammad Bakir Kalibaf, ya bayyana cewa; Babu yadda za a yi Iran ta zauna teburin tattaunawa da gwamnatin Amurka alhali tana yi ma ta barazana. Har ila yau ya ce zancen bayan nan na shugaban kasar Amurkan akan tattaunawa manufarsa ita ce yaudara da kuma kokarin raba Iran da karfinta. A yau Lahadi ne shugaban majalisar shawarar musuluncin ta Iran ya bayyana haka, yana mai kara da cewa; Kasarsa ba ta jiran wani sako daga Amurka, kuma za ta dakile dukkanin takunkuman da ta kakaba mata ta hanyar dogaro da karfin tattalin arzikinta da kuma alakarta ta kasa da kasa. Shugaban majalisar shawarar musuluncin ta Iran ya kuma ce; Yadda Donald Trump ya yi...
Manyan kasashen Turai, da suka hada da Burtaniya, Faransa, Jamus, da Italiya, sun goyi bayan shawarar Masar na sake gina Gaza a matsayin mai adawa da shirin “riviera” na shugaban Amurka Donald Trump wanda ke ba da shawarar korar Falasdinawa da karfi daga yankin. Duk da goyon bayansu da kuma wanke ayyukan kisan kare dangi da Isra’ila ke yi a zirin Gaza tun farkon yakin a watan Oktoban 2023, ministocin harkokin wajen Birtaniya, Faransa, Jamus, da Italiya sun sanar a cikin wata sanarwa a ranar Asabar cewa sun amince da shirin Masar wanda zai inganta “mummunan yanayin rayuwa da Falasdinawa suke ciki a Gaza.” Sanarwar ta kara da cewa, “Shirin ya nuna wata hanya ta sake gina Gaza idan aka...
Kwamitin Majalisar Dattawa ya bayar da shawarar a dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, na tsawon watanni shida. Kwamitin ladabtarwa da ɗa’a ne, ya bayar da shawarar biyo bayan zargin da ta yi wa Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio, kan cin zarafinta. Sheikh Sa’idu Hassan Jingir ya rasu A yi adalci a binciken mutuwar dan kwallon Nijerirya a Uganda —Gwamnatin Sakkwato A zaman Majalisar Dattawa na ranar Alhamis, Shugaban kwamitin, Neda Imasuen, ya gabatar da rahoton kwamitin, inda ya bayyana cewa Natasha ta ƙi bayar da haɗin kai wajen binciken da aka yi. Kwamitin ya kuma bayar da shawarar a dakatar da biyanta albashi tare da janye mata jami’an tsaron da ke kula da ita. Rikicin ya...
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce Paris da London na aiki kan shirin tsagaita wuta na wata guda a Ukraine. A wata hira da jaridar Le Figaro ta Faransa, Emmanuel Macron ya ce London da Paris suna ba da shawarar tsagaita wuta na wata guda da kuma samar da makamashi.” Daga baya a cikin jawabin nasa, Macron ya ba da shawarar cewa kasashen Turai su kara yawan kudaden da suke kashewa a fannin tsaro da kashi 3 zuwa 3.5 na GDP don mayar da martani ga canje-canjen abubuwan da Washington ta sa a gaba. “Tsawon shekaru uku, Rashawa suna kashe kashi 10% na GDPn su a fannin tsaro; Don haka dole ne mu shirya don abin da ke gaba. »
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi watsi da shawarar da Isra’ila ta gabatar na tsawaita matakin farko na yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza, inda ta yi kira ga kasashen duniya da su matsa wa gwamnatin mamayar lamba don ci gaba da mataki na biyu na yarjejeniyar kamar yadda aka tsara tun farko. Yau Asabar ne dai matakin farko na yarjejeniyar ke kaow karshe. Kakakin kungiyar Hamas Hazem Qassem ya bayyana a wata hira da gidan talabijin na Al Araby cewa, ba za a amince da tsawaita matakin farko na yarjajjeniyar kuma gwamnatin mamaya na da cikakken alhakin gazawar fara shawarwari a mataki na biyu na tsagaita wuta a zirin Gaza. Qassem ya kuma lura da cewa, maganar da...
Masar ta yi watsi da shawarar da jagoran ‘yan adawar Isra’ila Yair Lapid ya gabatar na cewa Alkahira, maimakon kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta karbi ragamar zirin Gaza na wucin gadi, tana mai danganta irin wadannan tsare-tsare da cewa “ba za a amince da su ba.” Kamfanin dillancin labarai na MENA ya nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen Masar Tamim Khalaf yana cewa, “Duk wani ra’ayi ko shawarwari da suka saba wa matsayar Masar da Larabawa (a kan Gaza) an yi watsi da su kuma ba za a amince da su ba.” Kakakin ya nanata kiran da Masar ta yi na janyewar Isra’ila daga yankunan Falasdinawa da ta mamaye, da kuma goyon bayanta ga kafa kasar Falasdinu mai cin gashin...
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Iran ce zata yanke shawara a nan gaba kan matsayin kasarta, ba Trump ba Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian a yammacin jiya Alhamis ya jaddada cewa: Iran ce take da hakkin yanke shawara kan makomarta ba Trump ba, yana mai jaddada wajabcin sauya ra’ayi domin dakile duk wani takunkumin da Trump ya kakabawa kasarsa. A jawabin da shugaba Pezeshkian ya gabatar a wajen taron shugabannin lardin Tehran ta yamma da majalisar gudanarwa ta garuruwan Mallard, Shahriar da Quds, shugaba Pezeshkian ya bayyana cewa, ma’anar gudanarwa ita ce sanin damammaki da barazana a ciki da wajen kasar da kuma sanin irin karfi da ake da shi. Shugaban kasar ya jaddada cewa: Trump na fadin wani...

Trump Ya Bukaci Ukirain Ta Bada Ma’adinanta Ga Kasar Amurka Idan Tana Son Ta Taimaka Mata Da Kayakin Yaki
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ce, Amurka ta na son mallakar ma’adanan na kasar Ukiraniya, wadadensu ya kudadensu ya kai dalar Amurka biliyan 500, a matsayin mayar da kwaryar taimakon Amurkan ta fuskar soja da makamai. A wata hira da tashar talabijin ta “FOX NEWS” ta yi da shi, shugaban kasar ta Amurka Donald Trump ya ce, ya na son Amurka ta mallaki ma’anadai na kasar Ukiraniya a matsayin ladar da tallafin sojen da take bukata daga Amurka. Gwamnatin Donald Trump ta gabatar wa da Kiev shawarar yin musayar ma’adanai na musamman da irinsu sun yi karanci a duniya, da take da su, na kaso 50% da hakan zai zama abinda take biyan Amurka da su, madadin taimakon soje...

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Ta Iran Ya Ce; Kasashen Iran Da Iraki Zasu Kare Kungiyoyin Gwagwarmaya
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya jaddada cewa: Iran da Iraki sun kuduri aniyar kare kungiyoyin gwagwarmaya Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf ya jaddada cewa: Iran da Iraki sun kuduri aniyar kare wannan gwagwarmaya da ta hana makiya numfasawa a yankin. Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf a wani taron manema labarai da ya yi da takwaransa na Iraki Mahmoud al-Mashhadani, ya bayyana cewa: Kasashen Iran da Iraki sun kuduri aniyar kare gwagwarmaya, yana mai jaddada cewa: Iran da kawarta Iraki sun kuduri aniyar marawa bangaren gwagwarmaya baya domin kare Musulunci da martabar al’ummar musulmi. Baqir Qalibaf ya kara da cewa: Sun ba da muhimmanci wajen raya hanyar layin dogo, musamman sabuwar...
Kungiyar Hamas ta yi Allah-wadai da kalaman shugaban Amurka Donald Trump kan mayar da mazauna Gaza zuwa kasashen Masar da Jordan dake makwabtaka da ita. A cikin wata sanarwar da ya fitar, shugaban kungiyar Hamas Sami Abu Zuhri ya yi tir da irin wadannan shawarwari a matsayin “abin dariya kuma maras amfani,” yana mai cewa, “Abin da mamayar Isra’ila ta kasa cimma da karfi, ba zai samu ta hanyar makircin siyasa ba.” Abu Zuhri ya kara da cewa, “Sanarwar da Amurka ta nanata na raba Falasdinawa da gidajensu da nufin sake gina yankin zirin Gaza na nuni da yadda kasar ke da hannu wajen aikata laifukan da suka shafi yanki.” Kana, ya yi gargadin cewa, “aikin kwashe mazauna Gaza” wani...
Ministan Harkokin Wajen Iran ya shawarci shugaban Amurka da ya mayar da yahudawan sahayoniyya zuwa Greenland Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya yi tsokaci kan kalaman shugaban Amurka Donald Trump da ya yi kan ba da shawarar korar Falasdinawa daga Zirin Gaza, maimakon haka Araqchi ya ba da shawarar kwashe ‘yan sahayoniyya Greenland. Ministan harkokin wajen Iran ya yi ishara da haka ne a wata hira da kafar yada labarai ta Sky News, yana mai bayyana cewa: A mahangar ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, a bayan da Trump ya shiga fadar White House a farkon wa’adinsa ya gabatar da shawarar korar Falasdinawa daga Zirin Gaza, amma kokarinsa ba ta yi nasara ba. hakan yana nufin rashin yiwuwar korar Falasdinawa...
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta kasar Iran ya bayyana cewa: Atisayen sojin mai take “‘Manzon Allah Mai Girma na 19” ya bayyana ƙarfin sojojin Iran Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran, Muhammad Baqir Qalibaf ya bayyana cewa: Atisayen “Manzon Allah Mai Girma na 19” a cikin ruwan Tekun Fasha ya bayyana Alamar da ƙarfin sojojin Iran suke da shi. Mohammad Baqir Qalibaf ya bayyana haka ne a yayin zaman majalisar shawarar Musulunci a yau Lahadi: Atisayen “Manzon Allah Mai Girma na 19″ na sojojin ruwa da ke karkashin dakarun kare juyin juya halin Musulunci suka yi a cikin ruwan tekun Fasha, da kuma makaman tsaro da aka mika wa sojojin kasa na sojojin Iran, wanda a lokacin aka yaye shamakin...