Nazari Kan Dabarun Taimaka Wa Masu Kiwon Kifi Domin Jurewa Sauyin Yanayi
Published: 10th, May 2025 GMT
Duba da yadda yanayin muhalli yake, zai ba da dama wajen rage fuskantar sauyin yanayi tare da inganta kiwon lafiyarsu, abincinsu da kuma ingancin ruwan shansu.
2- Fashin Baki Kan Abin Da Zai Iya Afkuwa A Wajen Kiwon Su:
Ga wanda zai fara wannan kiwo, ana so ya zabi wajen da ya dace da kuma tsarin da zai yi, don guje wa abin da zai iya afkuwa a bangaren sauyin yanayi mai tsanani.
3- Raba Kafa A Yayin Kiwon: Masu iya magana na cewa, ‘Ba a zuba kwai a cikin kwando daya’, wato ma’ana, ana so ka raba kafa ta hanyar yin wata dabara a kan kayanka, don kaucewa yin asara.
Kazalika, raba kafa na taimakawa wajen kara bunkasa kiwo da kuma kara sama wa mai kiwon kudin shiga.
4- Amfani Da Gargadin Farko: Ana so masu kiwo su rika bibiyar bayanai a kan afkuwar sauyin yanayi, wanda hakan zai ba su damar daukar mataki a kan lokaci, domin su kauce wa yin asara.
5- Amfani Da Ingannatun Kayan Aiki Don Yin Kiwo:
Kwamin kiwonsu da ake ginawa a kasa da kuma wanda ake ginawa a kan tudu, ana so a ba su kariya daga afkuwar ambaliyar ruwa. Kazalika, ana so kwamin ya kasance mai zurfi, domin bayar da kariya daga fari da kuma yanayi mai zafi.
6 Ana So Mai Wannan Kiwo Ya Rika Tuntubar Sauran Masu Kiwo:
Akasarin masu kiwo, ba zai yiwu su tafiyar da komai su kadai ba, saboda haka, ana bukatar su rika tuntubar sauran kungiyoyin da ke kiwon Kifi; don samun shawarwarin da za su taimaka musu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Fish farming
এছাড়াও পড়ুন:
Rashin wutar lantarki ta kassara kasuwanci a Kaduna, Kano da Katsina
Duk da Najeriya na cikin yanayin damina, wanda ake ganin a lokacin ta fi samar da wutar lantarki ga ’yan ƙasarta, amma jama’a a jihohin Kaduna da Kano na ci gaba da kokawa kan ƙarancin wutar.
A duk shekara jama’a na more wutar lantarki a Nijeriya a lokacin damina saboda tashoshin ruwa na samar da wutar lantarki suna aiki da cikakken ƙarfinsu.
Amma, wasu masana a ɓangaren wutar sun shaida wa wakilinmu cewa duk da matsalolin masu nasaba da lalata kayan aiki da kuma ƙin biyan kuɗin wuta da wasu masu amfani da ita ke yi, kamfanonin rarraba wutar (DisCos) suna yin iya bakin ƙoƙarinsu wajen cike giɓin.
Masu ruwa da tsaki sun bayyana cewa ana ƙoƙarin daidaita rarraba wuta tsakanin yankunan masana’antu da wuraren da aka sanya wa mita da ke biyan kuɗin wuta, da kuma sauran gidaje.
’Yan Najeriya miliyan 60 na fama da taɓin hankali — Likita Sojoji sun mutu yayin da Boko Haram ta kai hari sansanin soji a BornoA Katsina, rashin daidaito a rarraba wuta ya kawo babban cikas ga kasuwanci inda dubban masu sana’o’i suka rasa ayyukansu, gidaje kuma ke yin kwanaki ba tare da wuta ba.
Masu shayi, gidajen masu burodi, masu walda da sauran ƙananan sana’o’ da ke dogaro da wuta su ne suka fi shan wahala.
Dakta Isma’il Balarabe ya ce, “Kasuwancinmu sun durƙushe, mun yi asarar dukiya saboda rashin wuta. Wani lokaci ma, ba mu samun wutar awa ɗaya a rana.”
Shi ma Dakta Muktar Alkasim ya ce, “A gaskiya babu wutar da za ta iya tafiyar da kowace irin kasuwanci a nan Katsina. Wurin da ake samu ma, sai dai lokaci-lokaci kuma ƙarfin ba ya isa a kunna kayan aiki.”
Haka ma wata ’yar kasuwa, Misis Ngozi Anosike, ta ce sana’arta ta tsaya. “Akwai lokutan da muke yin mako guda ko fiye babu wuta. Idan ma ta zo, kusan awa ɗaya ne, kuma ba ta da ƙarfi.”
Hajiya Hannatu ta ce, “Ba zan iya sayen nama ko kifi da yawa ba saboda idan na saka a firji, zai lalace. Idan ma an samu wuta, ƙarfin bai isa ya ɗauki firji ba.”
Kano: An fifita masu biyan kuɗi da yawaA Kano kuwa, rahotanni sun nuna akwai babban bambanci a yanyanin rarraba wutar lantarki tsakanin yankunan kasuwanci da na gidaje. Wuraren kasuwanci sun fi samun wuta saboda suna biyan kuɗin wuta mai tsada, yayin da gidaje da dama ke shafe mafi yawan lokaci babu wutar.
Jama’a na ƙorafi kan cewa kamfanin KEDCO na fifita wuraren kasuwanci a yayin da al’ummomi da dama ke kwana cikin duhu.
Wani mazaunin unguwar Na’ibawa, Ahmad Aminu, ya ce, “A da idan damina ta yi, mukan samu wuta sosai saboda tashoshin ruwa suna aiki da cikakken ƙarfi. Amma bana abin ya canza. Sai sa misalin ƙarfe 11 na dare ake kawo wuta, a ɗauke ƙarfe 5 na asuba.”
Yusuf Idris daga unguwar Kuntau ya ce, “A baya muna biyan kusan N5,000 a wata. Amma watanni biyu da suka gabata an ƙara zuwa fiye da N17,000. Amma duk da haka ba mu samun wutar sosai.”
Ya ƙara da cewa mutane da dama sun daina amfani da wutar gwamnati, sun koma mai amfani hasken rana.
Amma duk da haka, kwastomomi da ke biyan kuɗaɗe masu yawa, musamman masana’antu, suna amfana da ƙarin wuta bisa sabon tsarin.
Sama’ila Sulaiman, mai sana’ar ƙanƙara a yankin Farm Centre, ya ce, “Yanzu muna samun wuta har ta awa 22 a rana saboda mu muna biyan kuɗaɗe masu yawa.”
Martanin KEDCOKakakin Kamfanin KEDCO, Sani Bala Sani, ya ce a zahiri akwai tsayayyiyar wuta a yankunan Kano da Katsina da Jigawa, sai dai iska da ruwan sama kan karya turakun wuta a wasu wurare.
Ya ce, “A wasu lokuta ana samun ɗan tsaiko saboda gyaran da Kamfanin Tura Wutar Lantarki ta Ƙasa (TCN) ke yi, haka nan yajin aikin ma’aikatan PENGASSAN ya shafi rarraba wutar.”
Ya bayyana cewa kamfanin yana zuba jari a sabbin kayan aiki da kuma samar da wuta daga hasken rana. “Mun fara amfani da Hasken Solar a Kano domin ƙara ƙarfinmu. Muna fatan kafin ƙarshen shekara mai zuwa mu samar da aƙalla megawatt 150 daga hasken rana.”
Kaduna: Al’umma na cikin duhuMazauna yankin Tudun Wada da ke Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Kudu ta Jihar sun koka cewa tun watan Satumba aka rage ba su wuta.
Hadiza Adam, wadda ke sana’at sayar da ruwan leda ta ce, “Yawanci dai ciki dare ake kawo mana wuta, lokacin da kowa ke barci. Don haka ribar da nake samu kullum tana raguwa.”
Muhammad Ahmed ya ce, “Yanzu wutar sai da ƙarfe 1 na dare ake kawo ta su kuma ɗauke da safe. Mu ba masu gadi ba ne da za mu rika zama don jiran wuta. Amma duk wata sai sun kawo mana bill cewa suna bin mu dubban nairori.”
Unguwanni da dama a Kaduna—kamar Rigasa da Hayin Ɗan Mani da Zango da Sabon Gari da sauransu—sun kai watanni suna yin kwanaki babu wuta. Wasu sun koma yin rajista kai wayoyinsu wajen masu cajin ko amfani da injin janareta.
Badamasi Isa da ke yankin Hayin Ɗan Mani ya ce,
“Tun watan Fabrairu ba mu samun wuta da dare. Hakan ya rusa kasuwancin masu kayan sanyi da masu walda.”
Mustapha Baban Sultan daga yankin Millennium City ya ce, “Yanzu tsarin ya zama ‘iya kuɗinka iya shagalinka’. Masu arziki suna Band A, suna samun wuta sosai amma suna biyan kuɗaɗe masu yawa. Talakawa kuwa babu wuta amma ana cajin su.”
Wasu mazauna sun bayyana cewa saboda rashin wuta sai sun koma amfani da hasken rana wajen samun ruwan sha da gudanar da rayuwa.
Duk da haka, Kamfanin Wutar Lantarki na Kaduna ya alaƙanta matsalar da lalata layin wuta da iska mai ƙarfi ta yi a wannan daminar.
Rahoton Hukumar Rarraba Wuta ya nuna cewa daga cikin megawat 4,025 da ake samarwa a Nijeriya, yankin Arewa na samum kusan kashi ɗaya bisa huɗu ne kawai.
Masu ruwa da tsaki sun danganta hakan da matsalar rashin saka hannun jari a ɓangaren rarraba wutar da matsalar satar kayayyakin wuta da kuma rashin biyan kuɗin wuta daga jama’a.
Shugaban Ƙungiyar Kare Haƙƙodin Kwastomomi ta Nijeriya, Kunle Olubiyo, ya ce rushewar masana’antu a Arewa ta rage buƙatar wuta, sannan satar wuta da rashin kayan aiki na zamani su ma suna kawo cikas.
Ya ce, “A da masana’antu a Kano, Kaduna da Maiduguri suna jan wuta sosai. Amma yanzu sun lalace, sai Kano kawai ta rage. A Kanon ma akwai matsalar sata da kuma rashin isassun kayan aiki a layin rarrabawa.”
Ya ƙara da cewa, “Kamfanonin rarraba wuta kan fifita wuraren da za su iya dawo da kuɗaɗensu. Idan aka kai wuta wuraren ba a biyan kuɗi, sukan ki karɗar nauyin rabon. Wannan shi ne abin da ya fi dagula lamarin a Arewa, inda wasu wurare ke samun ƙarin wuta, wasu kuma ba su samu wutar ba,” in ji shi.