Sudan ta katse hulda da Hadaddiyar Daular Larabawa bisa goyon bayan dakarun RSF
Published: 7th, May 2025 GMT
Gwamnatin Sudan ta katse dangantakar diflomasiyya da (UAE), bisa zarginta da goyan bayan dakarun RSF.
A cikin jawabin da aka watsa a talabijin, Ministan Tsaron Sudan, Yassin Ibrahim ya bayyana cewa Sudan ta “katse dangantakar diflomasiyya da UAE,” tare da janye jakadanta da rufe ofishin jakadanci da konsulat dinta a kasar .
Da yake magana a gidan talabijin na gwamnatin kasa, ministan tsaron Sudan, Yassin Ibrahim Yassin, ya zargi Abu Dhabi da keta hurumin ‘yancin Sudan ta hanyar mara baya ta fuskar soji ga RSF, ciki har da samar da makamai, da jiragen yaki marasa matuka, da makamai masu linzami wadanda aka kai hari da su a baya-bayan nan a tashar jiragen ruwa, da filin jiragen sama, da kuma tashoshin wutar lantarki na Sudan.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An Kaddamar Da Shirin Dashen Itatuwan Dabino Miliyan 50 A Jigawa
Hukumar Yaki da Hamada da Sauyin Yanayi ta Kasa ta kammala shirye-shiryen dasa itatuwan dabino miliyan hamsin (50,000,000) a jihohi goma sha ɗaya 11 da ke fama da fari a Najeriya.
Daraktan Hukumar, Alhaji Salihu Abubakar ne ya bayyana hakan a lokacin ƙaddamar da shirin dasa itatuwan dabinon da aka gudanar a Dutse, babban birnin jihar Jigawa.
Ya ce za a dasa itatuwan dabino guda dubu dari biyar (500,000), tare da wasu nau’o’in itatuwa na gida a faɗin jihar Jigawa.
Alhaji Salihu Abubakar ya yi kira ga jama’a da su rungumi al’adar dasawa da kula da itatuwa domin magance matsalolin hamada, zaizauar ƙasa da sauyin yanayi.
A cewarsa, Hukumar tana aiki tukuru a jihohin da ke fama da fari a Najeriya don yaƙi da hamada, farfaɗo da wuraren da suka lalace a sanadiyar girgizar kasa,, da kuma inganta rayuwar al’ummar karkara.
Ya ce bisa shirin dasa itatuwa, da kuma amfani da albarkatun ƙasa ta hanyar haɗin gwiwar al’umma, Hukumar ta dasa miliyoyin itatuwa tare da farfaɗo da wuraren da ke tallafa wa rayuwa a yankunan da fari ke addaba.
Daga ƙarshe, ya nuna jin daɗinsa bisa jajircewar da gwamnatin jihar Jigawa ta nuna wajen karɓar bakuncin wannan biki na shekara-shekara da aka gudanar a Dutse.
Usman Muhammad Zaria