Yaran Bello Turji sun ƙwace garin su tsohon Gwamnan Sakkwato, Bafarawa
Published: 12th, May 2025 GMT
’Yan bindiga da ake zargin yaran fitaccen jagoran ’yan bindiga Bello Turji ne, sun ƙwace yankin Bafarawa, garin su tsohon gwamna Attahiru Dalhatu Bafarawa.
’Yan bindigar sun kai harin tare da ƙwace wasu ƙauyuka huɗu ne a ranar Asabar a Ƙaramar Hukumar Isa ta Jihar Sakkwato.
Harin, wanda ake zargin wani kwamandan Turji mai suna Danbakolo ne ya jagoranta, ya kuma shafi ƙauyukan Gebe, Kamarawa, Garin Fadama da Haruwai.
Ana zargin harin da aka kai da kusan ƙarfe 11 na safe ran Asabar, martani ne ga ayyukan sojoji na baya-bayan nan da suka yi niyyar fatattakar ’yan bindiga a yankin.
NAJERIYA A YAU: Gaskiyar Tasirin Amfani Da Irin Noma Na GMO NDLEA ta kama matar da ta ɓoye hodar iblis a al’aurartaMajiyoyi a yankin sun ce an kashe mutane uku—ciki har da wata mata da ɗanta—a lokacin harin, wanda wasu mazauna ke zargin na hannun Turji ne ya jagoranta.
Maharan sun yi wa Bafarawa ƙofar rago, inda suka zargi mazauna da bai wa sojoji bayanan sirri.
Wani mazaunin yankin ya shaida wa wakilinmu cewa maharan, “Sun tafi kai tsaye fadar Sarkin Gabas na Bafarawa, Alhaji Muhammad Dalhatu, wanda shi ne babban ɗan uwan tsohon gwamnan.
“Sun yi ta neman sa, sun tafi da kuɗinsa da wayoyinsa, kuma sun yi wa al’umma gargadi game da haɗa kai da jami’an tsaro.”
Mazauna ƙauyukan da abin ya shafa sun gudu zuwa garin Shinkafi da ke kusa domin tsira.
Sai dai rahotanni sun ce sojoji sun ƙarfafa musu gwiwa da su koma gida a ranar Lahadi, tare da ba su tabbacin ingantaccen tsaro.
Lokacin da aka tuntube shi domin jin ta bakinsa, kakakin ’yan sanda na Jihar Sakkwato, DSP Ahmad Rufa’i, ya musanta faruwar lamarin.
Ya ce, “Ba na tunanin akwai wani abu kamar haka saboda akwai jami’an tsaro da yawa a waɗannan yankunan.”
Duk da musantawar, majiyoyi da yawa sun tabbatar da cewa hare-haren sun faru kuma sun bar mazauna cikin tsoro.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Bafarawa Sakkwato
এছাড়াও পড়ুন:
An kama mutum 78 da makamai da kwayoyi a Kano
An kama mutane 78 tare da kwace tulin miyagun kwayoyi da makamai da kayan sata a wani samame da ’yan sanda suka kai kwanan nan domin ayyukan laifi a Jihar Kano.
A yayin samamen, an kama gawurtaccen dillalin miyagun kwayoyi, Sulaiman Danwawu, da wasu haramtattun kwayoyi bayan an taba kama shi a shekarar 2022.
Daga cikin sauran wadanda aka kama har da wani da ake zargin dan fashi da makami ne da bindigogi biyu da harsasai.
Kwamishinan ’yan sanda, Ibrahim Adamu Bakori, ya sanar a taron ’yan jarida da ya gudana a hedikwatar rudunar da ke Bompai a ranar Juma’a cewa aikin kamen ya yi daidai da umarnin Shugaban ’Yan Sanda na Kasa kan a aiwatar da ingantattun matakai domin dakile ayyukan laifi.
Nijeriya ta soke ba da tallafin karatu a ƙetare Yadda yara 5 suka mutu a cikin motar da aka yi watsi da ita Yadda rashin wutar lantarki ke ajalin rayuka a manyan asibitociYa bayyana cewa hnyoyin da rundunarsa ta yi amfani da su sun hada da sintiri na sa’o’i 24, kai samame bisa bayanan sirri, da kuma hadin gwiwa da al’umma.
Tsakanin 23 ga Afrilu zuwa 9 ga Mayu, ’yan sanda sun kama mutane biyar bisa zargin fashi da makami, bakwai bisa zargin sayar da miyagun kwayoyi, da wasu bisa zargin satar shanu, damfara, sata, da kuma ‘yan daba.
Kayayyakin da aka kwato sun hada da bindigogi, miyagun kwayoyi, motoci, babura mai kafa uku, babura, muggan makamai, kudin jabu, dabbobi, da kayan lantarki.
Kwamishina Bakori ya jaddada alakar da ke tsakanin safarar miyagun kwayoyi da aikata laifuka masu hadari, yana mai cewa kama mutanen da kwace kayayyakin sun nuna irin nasarar da ake samu wajen rage irin wadannan laifuka.
Ya bukaci al’umma da su ba da goyon baya ta hanyar bayar da sahihan bayanai domin tabbatar da zaman lafiya a Kano.