Ma’aunin Asusun Ajiyar Kudin Musayar Waje Na Sin Na Cikin Daidaito
Published: 8th, May 2025 GMT
Bayanai na baya-bayan nan da hukumar kula da harkokin musayar kudaden waje ta kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, ya zuwa karshen watan Afrilu, asusun ajiyar kudaden waje na kasar Sin ya kai dalar Amurka biliyan 3281.7, wanda ya karu da dalar Amurka biliyan 41 ko kashi 1.27 bisa dari daga karshen watan Mayu.
Wani jami’in hukumar musayar kudaden waje ta kasar Sin ya bayyana cewa, tattalin arzikin kasar Sin yana cikin kyakkyawan yanayi, tare da nuna juriya da karfi a ci gaban tattalin arziki, wanda hakan zai taimaka wajen tabbatar da kwanciyar hankali a ma’aunin asusun ajiyar kudaden waje. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: kasar Sin ya kudaden waje
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Kasar Iran Ya Jaddada Batun Samun Hadin Kai Tsakanin Al’ummar Kasar
Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana neman karfafa hadin kai da ‘yan uwantaka da kasashen makwabtanta
Shugaban kasar Iran Mas’oud Pezeshkian ya jaddada cewa: “Babban burinsu shi ne neman karfafa hadin kai da ‘yan uwantaka da makwabtansu, kuma ba su dauke da kiyayya a kansu.”
Shugaba Pezeshkian, a jawabin da ya gabatar a gaban taron majalisar kwararru masu zaben Jagoran juyin juya halin Musulunci a Iran a jiya litinin, ya jaddada wajabcin kiyaye hadin kai da hadin kai a cikin kasar da dukkan al’ummar musulmi. Yana mai cewa: “Tare da haɗin kan kasa, za su iya magance dukkan matsalolin cikin gida.” Sannan ya kuma yi kira da a kaucewa duk wani mataki da zai kawo cikas ga wannan hadin kai tare da daukar hanyar kawo sauyi a maimakon fada da juna.
Shugaba Pezeshkian ya ci gaba da cewa: Al’ummun da ke rayuwa a wannan ƙasar, ko da wane irin ƙabila ne, ko jinsi, ko kuma imaninsu, suna da hakkin gudanar da mu’amala a kan tubalin gaskiya da ‘yancin yin adalci da kuma samun adalci daga gwamnati.