2025-06-17@09:45:34 GMT
إجمالي نتائج البحث: 4812

«wannan cuta»:

    Hukumar gudanarwar matatar man ƙasar Isra’ila da ke yankin Haifa ta sanar cewa matatar ta dakatar da ayyukanta ɗungurungum bayan harin da Iran ta kai mata. Kamfanin Bazan Group da ke kula da matatar ya ce harin na Iran ya tilasta musu tsayar da gaba ɗaya — a yayin da sabon rikicin na yankin Gabas ta Tsakiya ke ɗaukar zafi tsakanin ƙasashen biyu da suka jima suna yi wa juna kallon hadarin kaji. Bazan Group ya bayyana harin rokokin Iran ya lalata tashar wutar lantarki da matatar ke amfani da shi. Harin na Iran ya kuma halaka ma’aikata uku a matatar ta Haifa, kamar yadda hukumomin Isra’ila suka sanar. Wannan na faruwa a ci gaba hare-haren ramuwar gayya da makamai...
    Sarkin yankin Oke Agbe a Jihar Ondo ya ci Musulmi tara, tare da barazanar koran su da kuma haramta yin addinin Musulunci a garinsa bayan da wasu dodanni suka kai hari a wani masallaci da gidan limami. Aminiya ta samu rahoto cewa, wasu dodanni sun kai hari a masallaci da gidan wani limami, suka lakaɗa wa matansa da ’ya’yansa duka a yankin Oke Agbe, da ke shiyyar Akoko a Ƙaramar Hukumar Akoko ta Arewa a Jihar Ondo Jihar Ondo. Ƙungiyar Kare Haƙƙin Musulmi (MURIC), ta bayyana cewa, “Basaraken yankin ya yi Musulmin tara da aka ci zalinsu tara, saboda sun yi ihu tare da zagin dodannin, maimakon su riƙa yin kuka suna roƙon dodannin. “Basaraken ya umarci matan limamin su...
    Sun bayyana cewa akwai hatsarin ganin wasu daga cikin waɗanda suka tuba su koma yin laifi, idan gwamnati ba ta yi hattara ba. Sun kuma jaddada cewa dole ne a tallafa wa iyalan da suka rasa ‘yan uwa da dukiyoyinsu a harin ‘yan bindiga, domin ka da su ji kamar gwamnati na goyon bayan masu laifi. Jihar Katsina na daga cikin jihohin Arewa Maso Yamma da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga, wanda ya haddasa mutuwar mutane da dama da kuma salwantar dukiya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Karancin kayan ganyayyaki na cigaba da barazana ga lafiyar ‘yan Najeriya.   Masana sun bayyana cewa akwai gibi mai girma na rashin kayan ganyayyaki da ya kamata cike. Sai dai hakan na fuskantar tasgaro sakamakon wasu dalilai. NAJERIYA A YAU: Dalilan Durƙushewar Sababbin Sana’o’i Tun Ba A Je Ko’ina Ba DAGA LARABA: Dalilan Rashin Jituwa Tsakanin Marasa Lafiya Da Jami’an Kiwon Lafiya Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan wannan matsala da zummar nemo hanyoyin magance ta. Domin sauke shirin, latsa nan
    Ministan harkokin wajen kasar Rwanda Olivier Nduhungirehe ya bayyana cewa, kwakkwaran zumunci da ake sadawa a aikace a tsakanin Rwanda da kasar Sin na yin tasiri mai kyau ga al’ummar Rwanda. A cikin wata hira da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, yayin bikin baje kolin tattalin arziki da cinikayya na Sin da Afirka karo na hudu (CAETE) da aka gudanar daga ranar 12 zuwa 15 ga watan Yuni a birnin Changsha, babban birnin lardin Hunan na tsakiyar kasar Sin, Nduhungirehe ya kara da cewa, “Muna da kyakkyawar alaka da kasar Sin.” Ya yi karin haske game da hadin gwiwa mai fadin gaske a tsakanin kasashen biyu a fannonin kiwon lafiya, ilimi, aikin gona, fasaha da makamashi. Yana mai cewar, “Muna...
    Ƴansandan jihar Kogi sun tabbatar da sace wani basarake mai suna Samuel Ajayi Bello yayin da yake aikin gona a gidan gonarsa na Ponyan da ke kan titin Ponyan-Irele, a ƙaramar hukumar Yagba ta Gabas. Mai magana da yawun ‘yansandan jihar, SP William Aya, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da ƙarfe 10 na safe a ranar Litinin. Ya kuma ce Kwamishinan ‘yansandan jihar ya tura rundunar ta musamman don taimakawa wajen gudanar da bincike da kuma ceto wanda aka sace. Ministocin Harkokin Wajen Sin Da Afirka Sun Yi Alkawarin Karfafa Alaka Ƴan Bindiga Sun Kai Farmaki Kwara, Sun Kashe Mutum 1, Sun Ƙona Gidaje Shugaban ƙungiyar ci gaban yankin Ponyan, Hon. Banjo Fabola, ya tabbatar da cewa an...
    Wani yaro mai kimanin shekaru goma a duniya ya harbe mahaifinsa wanda jami’in ɗan sanda ne mai mukamin sufeto a Jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Nijeriya. Haka kuma, wakilinmu ya ruwaito cewa yaron ya harbi wani yayansa da bindigar mahaifin nasa ta aiki kirar AK-47. Kashe jagoran addini na Iran zai kawo ƙarshen yaƙi — Netanyahu Mun bankaɗo sabuwar dabarar ’yan siyasa ta satar kuɗi — EFCC Wannan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Anambra, Tochukwu Ikenga ya raba wa manema labarai a ranar Litinin. Kakakin ya ce an gaggauta kai jamin asibiti domin a ceto rayuwarsa amma likitoci suka tabbatar da cewa rai ya riga ya yi halinsa....
    Wani yaro mai kimanin shekaru goma a duniya ya harbe mahaifinsa wanda jami’in ɗan sanda ne mai mukamin sufeto a Jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Nijeriya. Haka kuma, wakilinmu ya ruwaito cewa yaron ya harbi wani yayansa da bindigar mahaifin nasa ta aiki kirar AK-47. Kashe jagoran addini na Iran zai kawo ƙarshen yaƙi — Netanyahu Mun bankaɗo sabuwar dabarar ’yan siyasa ta satar kuɗi — EFCC Wannan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Anambra, Tochukwu Ikenga ya raba wa manema labarai a ranar Litinin. Kakakin ya ce an gaggauta kai jamin asibiti domin a ceto rayuwarsa amma likitoci suka tabbatar da cewa rai ya riga ya yi halinsa....
    Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya ta’annati ta ce ta gano wata sabuwar dabarar satar kudi da wasu ’yan siyasa ke amfani da ita a yanzu ta hanyar amfani da ’yan damfara wadanda aka fi sani da ’yan yahoo a fadin kasar. Shugaban EFCC, Ola Olukoyede na wannan furuci ne yayin ganawa da manema labarai a hedikwatar hukumar da ke Abuja a ranar Litinin. Tinubu zai je jaje bayan kisan fiye da mutum 100 a Benuwe Gwamnati ta kasa ɗaukar matakin da ya dace a kan kashe-kashen Benuwe — Atiku Olukoyede wanda ya ce wadannan matasa ’yan yahoo da suke zubar da kimar Nijeriya a idon duniya sun kuma faɗa dumu-dumu ta’adar  nan ta garkuwar...
    Ƴansandan jihar Kogi sun tabbatar da sace wani basarake mai suna Samuel Ajayi Bello yayin da yake aikin gona a gidan gonarsa na Ponyan da ke kan titin Ponyan-Irele, a ƙaramar hukumar Yagba ta Gabas. Mai magana da yawun ‘yansandan jihar, SP William Aya, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da ƙarfe 10 na safe a ranar Litinin. Ya kuma ce Kwamishinan ‘yansandan jihar ya tura rundunar ta musamman don taimakawa wajen gudanar da bincike da kuma ceto wanda aka sace. Ministocin Harkokin Wajen Sin Da Afirka Sun Yi Alkawarin Karfafa Alaka Ƴan Bindiga Sun Kai Farmaki Kwara, Sun Kashe Mutum 1, Sun Ƙona Gidaje Shugaban ƙungiyar ci gaban yankin Ponyan, Hon. Banjo Fabola, ya tabbatar da cewa an...
    Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce duk wani shiri na kashe jagoran addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei ba zai rura wutar rikicin da ake yi yanzu ba, hasali zai ma kawo ƙarshen rikicin ne. A wata hira ta tsawon minti 20 da tashar talabijin ta ABC ta Amurka ta yi da shi, Netanyahu ya kare matakin farmakin da ƙasarsa ta kai wa Iran, inda ya kwatanta jagoran addini Khamenei a matsayin wani sabon Hitler na wannan zamani. Mun bankaɗo sabuwar dabarar ’yan sisaya ta satar kuɗi — EFCC Tinubu zai je jaje bayan kisan fiye da mutum 100 a Benuwe A yayin hirar, duk wata tambaya da aka yi masa game da ko Shugaban Amurka Donald Trump ya sahale...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya ta’annati ta ce ta gano wata sabuwar dabarar satar kudi da wasu ’yan siyasa ke amfani da ita a yanzu ta hanyar amfani da ’yan damfara wadanda aka fi sani da ’yan yahoo a fadin kasar. Shugaban EFCC, Ola Olukoyede na wannan furuci ne yayin ganawa da manema labarai a hedikwatar hukumar da ke Abuja a ranar Litinin. Tinubu zai je jaje bayan kisan fiye da mutum 100 a Benuwe Gwamnati ta kasa ɗaukar matakin da ya dace a kan kashe-kashen Benuwe — Atiku Olukoyede wanda ya ce wadannan matasa ’yan yahoo da suke zubar da kimar Nijeriya a idon duniya sun kuma faɗa dumu-dumu ta’adar  nan ta garkuwar...
    Wannan ya nuna ragin hauhawar farashi a faɗin ƙasar nan. Masana na ganin wannan ragi a matsayin alamar ci gaba ga tattalin arziƙi, sai dai har yanzu ‘yan Nijeriya da dama na fama da tsadar rayuwa, musamman wajen samun kayan abinci da wasu muhimman abubuwan buƙara na yau da kullum. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Yau Litinin, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin, Guo Jiakun ya gudanar da taron manema labarai na yau da kullum. Game da halin da ake ciki yanzu a yankin Gabas ta Tsakiya, Guo Jiakun ya ce, ministan wajen Sin Wang Yi ya riga ya tattauna ta waya tare da takwarorinsa na Iran da Isra’ila, inda ya yi kira ga bangarorin biyu su warware rikicin ta hanyar tattaunawa. Ya ce ya kamata bangarorin biyu su dauki matakai nan da nan don hana ruruwar wutar rikicin. Kana Sin za ta ci gaba da yin mu’ammala da bangarorin da abin ya shafa, ta yadda za ta ba da gudunmawa wajen yayyafa ruwa ga rikicin. Game da taron koli na Sin da kasashen yankin tsakiyar...
    Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya, Atiku Abubakar, ya yi Allah-wadai da kashe-kashen mutanen da ake yi a Jihar Benuwe, yana mai bayyana lamarin a matsayin mummunar masifa. Cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku ya caccakin gwamnatin Nijeriya da cewa ta kasa ɗaukar matakin da ya dace a kan lamarin. Tinubu ya bayar da umarnin binciken hare-haren Benuwe Iran ta rataye mutumin da ta kama yana yi wa Isra’ila leƙen asiri Ya nuna damuwa matuƙa kan ci gaba da zubar da jini a jihar Benue, yana mai kira ga gwamnatin tarayya da ta ɗauki matakin gaggawa domin kawo karshen matsalar tsaro da ke addabar yankin. Atiku ya ce al’ummar Benuwe na fama da hare-hare na tsawon shekaru,...
    Kazalika, cikin kwanaki hudu da aka kwashe ana gudanar da baje kolin, an sayar da nau’o’in albarkatun gona na nahiyar Afirka sama da 200 ta intanet da kuma manyan shaguna. Bugu da kari, wasu kasashen Afirka 14 sun gudanar da wasu ayyukan musamman na yayata hada-hadar tattalin arziki da cinikayya a yayin baje kolin. (Mai Fassara: Saminu Alhassan)     Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Iran ta ce ta aiwatar da hukuncin kisa ta hanyar rataya ga mutumin da aka kama yana yi wa Isra’ila leƙen asiri. Mahukunta a bangaren shari’ar sun ce an kama Esmail Fekri a shekarar 2023 yana ƙoƙarin miƙa wa Isra’ila bayanan sirri ne don samun kuɗi. KADSEMA da IOM sun fara tantance ɓarnar da ambaliya ta yi a Kaduna Sabon harin Iran ya hallaka mana mutum 8 – Isra’ila Wannan ne karo na uku a baya-baya nan da Iran ke aiwatar da hukuncin kisa saboda zargin leƙen asiri ga Isra’ila. A ranar Lahadi, Isra’ila ta ce ta kama wasu ’yan ƙasa biyu da ake zargin suna aiki da hukumar leƙen asirin Iran. Babban alƙalin Iran, Gholamhossein Mohseni Ejei, ya bayyana...
    FCCPC ta lura cewa, waɗannan sassan dokar suna kare ‘yan Nijeriya daga “rashin adalci, rashin sanin ya kamata, daga kwastomominsu.”   A wata wasika mai ɗauke da kwanan watan 13 ga watan Yuni 2025, FCCPC ta yi amfani da sashe na 32 da na 33 na FCCPA, inda ta bukaci kamfanin da ya gurfana a gaban hukumar a hedikwatar ta Abuja a ranar Litinin 23 ga watan Yuni 2025.   Hukumar ta yi gargaɗin cewa, rashin bin wannan umarni na iya haifar da tsauraran takunkumai da suka hada da tara da ɗauri kamar yadda aka bayyana a sashe na 33(3) na dokar.   Har yanzu Air Peace ba ta amsa sammacin ba har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto. ...
    Shirin dai zai kunshi abubuwa masu mahimmanci guda uku; Na farko, Taron Sevilla zai taimaka wajen zaburar da shigowar tallafi zuwa ga kasashen da suka fi bukatarsa. Na biyu, dole ne kasashe su kasance a kan kujerar tattara albarkatun cikin gida ta hanyar karfafa samar da kudaden shiga da magance rashin biyan haraji, hadin gwiwar kasa da kasa. Wannan zai samar da albarkatun da ake bukata sosai domin bayar da fifikon kashe kudade a wuraren da ke da tasiri mafi girma kamar ilimi, kiwon lafiya, ayyuka, kariya ga zamantakewa, samar da abinci, da makamashi irin na zamani. A bangare daya kuma, akwai bukatar bankunan ci gaban kasa, da na shiyya-shiyya da kuma bankunan raya kasa-da-kasa, su hada hannu domin saka...
    Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna (KADSEMA), tare da haɗin gwiwar Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Duniya (IOM), sun fara aikin tantance ɓarnar da ambaliya da iska suka yi a yankunan Kudancin Kaduna. Manufar aikin ita ce su tattara sahihan bayanai daga jama’a da shugabanninsu domin a samu taimako da kuma tsara hanyoyin kare aukuwar hakan a gaba. Sabon harin Iran ya hallaka mana mutum 8 – Isra’ila NAJERIYA A YAU: Dalilan Durƙushewar Sababbin Sana’o’i Tun Ba A Je Ko’ina Ba Yayin da suka kai ziyara Ƙaramar Hukumar Jama’a, Ko’odinetan KADSEMA na Kudancin Kaduna, Mista Ayyuka Shemang, ya ce sun fara wannan aiki ne saboda hasashen ambaliya daga Hukumar Yanayi ta Najeriya (NiMet). Ya jaddada muhimmancin...
      Dan wasan mai shekaru 27 ya zura kwallaye 20 sannan ya taimaka wajen zura bakwai daga wasanni 40 da ya buga a duk wasannin da ya buga a kakar wasan data gabata, Lookman ya ci kwallaye 17 kuma ya taimaka wajen zura 10 a kakar wasanni ta shekarar 2023/24. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Yahudawan sahayoniyya sun kashe adadi mai yawa na yaran Iran a cikin ta’addancin da suke yi  Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baqa’i ya bayyana cewa: Gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta kashe kananan yara masu yawa na Iran a cikin wannan ta’asa da take gudanarwa kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran. A cikin wani sako da Ismail Baqa’i ya rubuta a ranar Lahadin da ta gabata ya bayyana cewa: “Gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta kashe adadi mai yawa na yara Iraniyawa tare da kai hari kan asibitin yara a tsawon kwanaki uku na hare-haren soji kan Iran. Kamar yadda Ya’ir Golan, tsohon mataimakin hafsan hafsoshin sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila ya amince da cewa: Kashe...
    Jami’an tsaron kan iyakokin Iran sun harbo jiragen saman yaki marasa matuki ciki guda 44 a cikin sa’o’i 48 da suka gabata Kwamandan rundunar tsaron kan iyakokin kasar Iran Birgediya Janar Ahmad Ali Goudarzi ya bayyana cewa: An harbo jiragen sama marasa matuka ciki guda 44 da kananan jiragen saman yakin gwamnatin ‘yan sahayoniyya tare da lalata su a wasu kan iyakokin kasar. Birgediya Janar Goudarzi ya bayyana a ranar Lahadi cewa: “Bayan harin da gwamnatin ‘yan Sahayoniyya ta kaddamar kan Iran, a cikin sa’o’i 48 da suka gabata, jami’an tsaron Iran sunsamu nasarar kakkabo jiragen sama marasa matuka ciki na gwamnatin ‘yan sahayoniyya guda 44 da kananan jiragen sama na wannan muguwar gwamnati, sakamakon Sanya ido kan shige da...
    A cikin wata wasika mai kwanan wata 23 ga Mayu, 2025, mai lamba CR/3000/IGP-SEC/MU/ADM/14/ABJ/VOL 118/57, wacce aka aike wa sakataren gwamnatin jihar Kano, na cewa, IGP ya bukaci a mika Bature zuwa gaban wani jami’i, SP Mojirode B. Obisiji a ranar Alhamis 29 ga Mayu, 2025, domin amsa tambayoyi.   In ba a manta ba, IGP a watan Disamba, 2024 ya ba da irin wannan umarni tare da tura jami’an sa ido na IGP domin su kamo mai magana da yawun Gwamnan Kano tare da kai shi hedikwatar rundunar da ke Abuja. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don...
    Aniaku ya bayyana cewa, an samu nasarar aikin yaki da satar danyen mai a yankin, ta hanyar amfani da bayanan sirri da NNS PATHFINDER ta samu kuma ta aiwatar cikin nasara.   Aniaku, ya kara nanata cewa, rundunar sojojin ruwan Nijeriya karkashin jagorancin babban hafsan hafsoshin ruwa, Vice Admiral Emmanuel Ogalla, za ta ci gaba da jajircewa wajen yaki da satar danyen mai, wadanda ke haifar da babbar barazana ga tattalin arzikin kasar da kuma samar da makamashi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    An samu cece-ku-ce a Jihar Sakkwato bayan da wata jita-jita ta yaɗu cewa Mataimakin Gwamnan jihar, ya karɓi shanu 400 da aka tanadar domin tallafa wa marasa galihu domin yin layya a lokacin Sallah Babba. An ce shanun wata ƙungiya ce daga ƙasar Turkiyya ta bayar da su, ta hannun Hukumar Zakka da Waƙafi ta jihar, domin tallafa wa waɗanda ba su da halin yin layya. Iran ta kai sabbin hare-hare birnin Tel Aviv da Haifa An tallafa wa mata 250 da abinci da kayan sana’a a Kaduna Sai dai an zargi Mataimakin Gwamnan da karɓe su don amfanin kansa. Wannan batu ya jawo jama’a a jihar suk dinga bayyana ra’ayoyinsu, inda wasu ke zargin an fifita jami’an gwamnati fiye...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kakakin yada labarai na rundunar sojin ‘yantar da jama’ar kasar Sin ko PLA reshen kudancin kasar, babban kanar na sojojin sama Tian Junli, ya bayyana cewa, jiya Asabar rundunar sojin ta gudanar da sintiri na hadin gwiwa a ruwan teku da kuma sama a yankin tekun kudancin Sin.   Tian ya kara da cewa, sitirin hadin gwiwa a teku da sama da Philippines ta gudanar tare da wasu kasashen duniya, ya kawo barazanar tsaro ga yankin tekun kudancin Sin, kuma ya lalata zaman lafiya da kwanciyar hankali na yankin. Don haka, rundunar za ta ci gaba da kasancewa cikin shirin ko-ta-kwana tare da kiyaye ikon mulkin kan kasar Sin, da hakki da moriyarta a tekun.(Safiyah Ma) Daga kanmu, magana...
    Iran ta kai sabbin hare-hare kan manyan biranen Isra’ila da suka haɗa da Tel Aviv da Haifa, inda ta yi amfani da makaman linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙa. A cewar gidan talabijin na Iran, gomman makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa ne suka tashi zuwa Isra’ila, kuma wasu daga cikinsu sun ƙetare garkuwar kariyar iska ta Isra’ila. An tallafa wa mata 250 da abinci da kayan sana’a a Kaduna Yadda wani ɗan sanda ya rasu a hanyar zuwa ɗaurin aurensa Sai dai har yanzu ba a ji wani bayani daga sojojin Isra’ila ba. Faɗan Iran da Isra’ila ya fara ne bayan Isra’ila ta kai hari kan wani sashen ofishin jakadancin Iran da ke birnin Damascus na Siriya, wanda...
    Wata ’yar kasuwa mai taimakon al’umma, Barista Catherine Bitrus, ta raba wa mata 250 da abinci da kayan sana’a a garin Manchok da ke Ƙaramar Hukumar Kaura, a Jihar Kaduna. Tallafin ya haɗa da injinan niƙa, buhunan shinkafa, katan-katan na taliyar yara, da man girki. Harin Benuwe: ’Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga Takarar Tinubu: Rikici ya ɓarke a APC bayan Ganduje ya ƙi goyon bayan Shettima A lokacin rabon kayan, Catherine, shugabar kamfanin Natural Beauty Secret, ta ce ta yi hakan ne domin taimaka wa matan karkara da ke fama da matsaloli a rayuwa. “Allah Ya ba ni arziƙi, shi ya sa na ga dacewa na raba da waɗanda ke bukata,” in ji ta. “Na zaɓi mata ne domin...
    A watan Janairu na shekarar 1969, Xi Jinping, wanda bai kai shekaru 16 da haihuwa ba a lokacin, ya zo kauyen Liangjiahe da ke arewacin lardin Shaanxi daga birnin Beijing. Ya ce, “Duk inda na je, zan kasance dan asalin tudun Loess.” Shekaru da yawa bayan haka, ya bayyana a cikin wata kasida cewa, “A matsayina na ma’aikacin gwamnati, yankin arewacin Shaanxi shi ne asalina, saboda wurin ne ya dasa mani imanina wanda ba zai canza ba wato yin abubuwa masu alfanu ga mutane a aikace!” (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin...
    Garkuwan sararin samnaiyar kasar Iran a lardin Zanjan ya bada labarin kakkabo jiragen yakin na HKI guda biyi wadanda ake sarrafasu daga nesa a sararin samaniyar. Kamfanin dillancin lbaran Tasnim na sojojin kasar Iran ya nakalto majiyar dakarunn juyin juya halin musulunci na kasar Iran tana fadar haka. Labarin ya kara da cewa rubuce rubucen da aka rubuta a jikin jiragen da aka tarwatsa sun bayyan cewa kirar kasar Amurka ce. Wannan yake tabbatar da irin hannun da Amurka take da shi a cikin yakin da Iran take fafatawa da HKI. A wani labarin kuma yansandar yanar gizo sun kama mutane biyu wadanda suke yada labaran karya dangane da yaki da kuma shuwagabannin kasar. Har’ila yau an kama wasu wadanda...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya bayyaana cewa kasarsa bata rufe kofar diblomasiyya dangane da shirinta na makamashin Nukliya ba, matukar HKI zata dakatar da hare-haren da take kaiwa kasar. Kamfanin dillancin  labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a yau Lahadi a taron yan jaridun da ya kira a birnin Tehran. Ya kuma kara da cewa Iran tana son ta ci gaba da shirinta na makamashin Nukliya ta zaman lafiya ta hanyar diblomasiyya idan an bata damar yin haka. Ministan ya ce ikidar JMI ne warware dukkan matsaloli da farko ta hanyar Diblomasiyya, da kuma tattaunawa amma ba zamu taba amincewa  wani ya hanamu hakkimu na mallakar makamashi nukliya ta zaman lafiya ba....
    Babban kwamandan dokarun khatamul Ambiya (s) a nan birnin Tehran ya bayyana cewa sojojinsa zasu ci gaba da fafatawa da HKI har zuwa lokacinda zata dakatar da kawowa Iran yaki, ko kuma ta sami nasara a kansu, Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Janar Ali Shudmoni, yana fadar haka a yau Lahadi bayan da suke cilla makamai masu linzami da kuma jiragen yaki wadanda ake sarrafasu da nesa kan HKI a karon farko na rana, a cikin kwanaki uku da fara yakin. Janar Shodmani ya kara da cewa zasu ci gaba da kaiwa yahudawan hare-hare har zuwa lokacinda zasu yi nadama sun daina yakin. Kwamnatin ya bayyana cewa ya zuwa yanzu sun saminar kasar lalata cibiyoyin da...
    Kakakin gwamnatin kasar Iran ta bayyana cewa, kasar Iran ta shiga yaki, kuma don haka dole sai an sami sauyi a rayuwar mutane ba. Fatima Muhajirani ta bayyana cewa daga yau ramukan layin dogo a cikin birnin Tehran wuraren mafaka da muyewa ne na mutanen da suke birnin har’ila yau za’a bude masallatai da makarantu don su zama wuraren samun mafaka. A wani bangare fatimeh Muhajirani ta bayyana cewa an rufe sararin samaniyar kasar Iran, don haka babu jirgi wanda zai tashi a ciki ko wajen kasar har zuwa abinda hali yayi ta kuma kara da cewa a halin yanzu jirgin kasa zai zama hanyarb tafiya mafi sauki a wannan haling a mutane. Tace mahajjan Iran zasu dawo ta hanya...
    An shiga zaman ɗari-ɗari a garin Makurdi na Jihar Benuwe, bayan ’yan sanda sun harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa wasu masu zanga-zanga a shataletalen Wurukum. Masu zanga-zangar sun fara taruwa da misalin ƙarfe 9:30 na safe domin nuna fushinsu kan kisan mutane sama da 100 a garin Yelewata da ke Ƙaramar Hukumar Guma, a ranar Asabar. Takarar Tinubu: Rikici ya ɓarke a APC bayan Ganduje ya ƙi goyon bayan Shettima HOTUNA: Yadda aka yi sulhu da ƙasurgumin ɗan fashin daji Ado Aliero a Katsina Tun kafin fara zanga-zangar, jami’an tsaro daga hukumomi daban-daban sun mamaye manyan hanyoyi a birnin Makurdi. Da safiyar ranar Lahadi da misalin ƙarfe 7 na safe jami’an tsaro, ciki har da motar yaƙi ta ‘yan sanda...
    Jam’iyyar APC a Yankin Sanatan Kaduna ta Arewa (Zone 1) ta bayyana goyon bayanta ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Gwamnan Jihar Kaduna Uba Sani, da Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, don sake tsayawa takara a wa’adin mulki na biyu. An yanke wannan shawara ne a wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Jami’ar Tarayya ta Ilimi da ke Zaria, inda tsoffin gwamnoni, ministoci, ‘yan majalisa, da kwamishinoni da shugabannin hukumomi na tarayya da jiha suka halarta. EFCC Ta Kama Mutane 11 Kan Zargi Aikata Damfara A Intanet A Kaduna An Karrama Dalibar Kaduna Da Ta Zo Ta Biyu A Gasar Karatun Alkur’ani Ta Duniya Masu ruwa da tsakin sun jero nasarorin da gwamnati mai ci ƙarƙashin APC...
    “Yayin da kuka fita a yau kuma kuka samu matsayinku a wannan ma’aikata mai daraja, ku sani cewa za ku zama wani bangare na hanyoyin magance kalubalen ta’addanci da ‘yan tada kayar baya acikin al’ummarmu, don haka duk inda aka tura ku, tilas ne ku aiwatar da abinda aka horar da ku, kuma ku nuna jajircewa wajen fuskantar matsaloli.   “Tafiyar mil dubu tana farawa ne da taku daya, don haka, tafiyarku ta fara ne a ranar 13 ga watan Janairun 2025, lokacin da kuka fara amsar horo na aikin soji, an shirya muku duk wani abu da za ku iya fuskanta na kalubale, kuma ina mai tabbatar muku da cewa, za ku fuskanci kalubalen da da farko zaku ga...
    Wani jami’in ɗan sanda, SP Mustapha Garba Gumau, ya yi gamo ajalinsa a wani hatsarin mota yayin da ya rage aƙalla sa’a ɗaya a ɗaura masa aure. Aminiya ta ruwaito cewa, ajali ya katse hanzarin jami’in ne a kan hanyar Gumau zuwa Magaman-Gumau da ke Ƙaramar Hukumar Toro ta Jihar Bauchi, inda za a ɗaura masa aure. Masu ƙwacen waya sun kashe ma’aikacin Jami’ar Northwest a Kano HOTUNA: Yadda aka yi sulhu da ƙasurgumin ɗan fashin daji Ado Aliero a Katsina SP Gumau wanda hatsarin ya rutsa da shi da abokansa ya rasu ne da misalin ƙarfe 9 yayin da ake shirin ɗaura masa aure da misalin ƙarfe 10 na safiyar ranar Asabar. Wata sanarwa da mai magana da yawun...
    Wasu mazauna Jihar Katsina sun yi zaman sulhu da wasu shugabannin ’yan daban daji da suka addabe su. Wakilinmu ya ruwaito cewa an yi taron sasanci da ’yan bindigar daji ne a Ƙaramar Hukumar Danmusa, wanda rundunar sojoji ke shiryawa, inda Adamu Aliero ya jagoranci sashen ’yan bindigar. BBC ya ruwaito Kwamishinan Tsaro da Harkokin Ciki Gida na Katsina na cewa al’ummar garin Bicci da ke yankin Ƙaramar Hukumar Danmusa sun zauna tare da Ado Aliero da sauran wasu shugabannin ’yan bindigar aƙalla goma. “An zauna da Ado Aliero da Kamilu Buzaru da Dogo Nahali da Wada Jargaba da Dahiru Buzu haka ma da Nagoggo,” in ji shi. Hotuna daga Ahmed Kabiru S/Kuka
    Rahotanni sun bayyana cewa wasu masu ƙwacen waya sun kashe wani ma’aikacin Jami’ar Northwest da ke Kano, Buhari Imam, ta hanyar daba masa wuta. Bayanai sun nuna cewa barayin sun ritsa shi ne a yankin unguwar Sheka da ke karamar hukumar Kumbotso, inda suka sossoke shi da wuka a ciki kuma suka kwace wayarsa, a ranar Laraba. BBC ya ruwaito mutumin ya rasu bayan da aka garzaya da shi Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, a ranar Juma’a. Shugaban ƙungiyar ma’aikatan jami’ar (NASU), Kwamared Bashir Muhammad, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ya yi kira ga gwamnatin Jihar Kano da sauran hukumomi da su ɗauki tsattsauran mataki a kan kisan.
    “A yankin Arewa ta Tsakiya, ana sa ran za a yi tsawa da sanyin safiya a sassan jihohin Benuwe, Filato, Neja, Babban Birnin Tarayya, da Jihar Nasarawa.   “A washegari, ana hasashen tsawa da ruwan sama a wasu sassan babban birnin tarayya, Neja, Nasarawa, Benuwe, Kwara, Kogi, da Filato.   “A yankin Kudu, ana sa ran samun hadari tare da yiwuwar samun ruwan sama a sassan jihohin Enugu, Ebonyi, Cross River, Legas, Akwa Ibom, Ribas, da Bayelsa,” in ji NiMet. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
    Martanin Iran game da ta’addancin haramtacciyar kasar Isra’ila na ci gaba a rana ta biyu Ana ci gaba da mayar da martani mai girma na Iran game da harin da haramtacciyar kasar Isra’ila take kaiwa da makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuka ciki. ‘Yan mintoci da suka gabata a zaman wani bangare na biyu na “Alkawarin Gaskiya Na 3”, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta harba daruruwan makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuka kan haramtacciyar kasar Isra’ila. An harba wadannan makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuka ciki da kuma jiragen sama masu saukar ungulu daga Tehran da sauran garuruwan kasar Iran a matsayin wani mataki na murkushe laifuffukan da yahudawan sahayoniyya suka aikata a kan...
    Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana cewa: Babu wata tattaunawa da zata yi da Amurka a halin da take ciki na kare kanta A yayin da haramtacciyar kasar Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare kan yankunan kasar Iran, a hukumance Iran ta bayyana rashin yiwuwar ci gaba da zaman tattaunawa da Amurka kan batun shirinta na makamshin nukuliya, tare da dora wa Amurka alhakin abin da ke faruwa kai tsaye. Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: Akwai hadin kai tsakanin haramtacciyar kasar Isra’ila da Amurka wajen kai hare-hare kan kasar Iran domin rusa zaman tattaunawar nukiliya da haka ke bayyana kawar da duk wata magana ta hakikanin aniyar Amurka na samar da hanyar warware takaddamar Shirin Iran...
    Yarima mai jiran gadon Saudiyya ya tabbatarwa shugaban kasar Iran cewa: Saudiyya tana goyon bayan Iran Yariman mai jiran gadon Saudiyya Mohammed bin Salman ya tabbatar da hakan ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian a yammacin jiya Asabar, yana mai jaddada cewa: Masarautar Saudiyya da daukacin al’ummar musulmin duniya sun hadu a kan goyon bayan Iran. Yarima mai jiran gadon sarautar Saudiyya ya ce: Dukkanin al’ummomin kasashen musulmi a yau suna da hadin kai da jaddada goyon bayansu ga Iran, kuma yana iyaka kokarinsa a fagen diflomasiyya da matsin lamba na kasa da kasa don dakatar da wuce gona da irin da ‘yan sahayoniyya suke yi kan Iran. Bin Salman ya yi Allah...
    Iyaye su ne ke ginawa yara dabi’un farko, shi ne ma ya sa a ke so su rika kiyaye irin maganganun da za su rika yi a gaban yaransu, sannan su tsaftace mu’amalolinsu ta yadda yaran ba za su rika kwaikwayon abubuwan da ba su dace ba. hatta da yin dakuwa da nufin zagi, a wurin iyaye yara ke fara koyo. Shi ne ya sa za ka ga wani ya zama gwani a zagi, kwararren gaske. Ba a sama ya samo dabi’ar ba, abin da ya taso ya ga a na yi a gidansu kenan. Wasu kuwa gidansu mutanen kirki ne, don haka ba su iya samun daman kwaikwayon zagi a gida. Daga gida, lokacin da yaro ya fara wayo,...
    Sannan shi ne ya fi kowanne danwasa yunkurin cin kwallo a gasar, inda ya kai hari (attempt) sau 64, 23 daga cikinsu akwai munana (on target) 23. Ya yi nasarar yanka abokan hamayyarsa har sau 62, sannan ya yi bugun kwana 45.   Rapinha Zakakurin danwasan gaba na Barcelona da Brazil, Rapinha, na cikin ‘yanwasan da suka fi bai wa mabiya harkokin wasa mamaki a kakar wasa ta bana baki daya – ba a Champions League ba kawai. Tare da dan wasan kungiyar Borussia Dortmund, Serhou Guirassy, su ne kan gaba a cin mafi yawan kwallaye da 13 kowannensu. Sai dai Rapinha ya zarta shi da yawan bayar da kwallo a zira a raga, inda yake da guda 9, Guirassy...
    Ministan harkokin wajen Omani Badr Albusaidi ya sanar da cewa, ba za a gudanar da zagaye na shida na tattaunawar nukiliya tsakanin Iran da Amurka ba. Yau Lahadi ne aka shirya gudanar da zagaye na gaba na shawarwari a Muscat babban birnin kasar Oman. A cikin wani sakon da ya wallafa a kan X (tsohon Twitter), Albusaidi ya tabbatar da sokewar, yayin da ya jaddada cewa “diflomasiyya da tattaunawa sun kasance hanya daya tilo ta samun zaman lafiya mai dorewa.” “Tattaunawar Iran da Amurka, wadda aka shirya gudanar da ita a birnin Muscat ranar Lahadin nan, ba za ta gudana a yanzu ba. Tattaunawar diflomasiyyar da aka faro kan shirin nukiliyar Iran, a watan Afrilu a shiga tsakanin masarautar Oman,...
    Shugaban aksar Iran, Massoud Pezeshkian, ya bayyana cewa martanin sojojin kasarsa ga Isra’ila zai zama mafi muni idan hare-haren Isra’ilar suka ci gaba. A wata tattaunawa ta wayar tarho da firaministan Pakistan Shehbaz Sharif, shugaban kasar Iran Massoud Pezeshkian ya tabbatar da cewa dakarun gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran za su dauki kwararan matakan mayar da martani mai tsauri idan har gwamnatin Isra’ila ta ci gaba da kai farmaki kan Iran. “Masu da’awar kare hakkin bil’adama ba wai kawai suna goyon bayan zaluncin gwamnatin sahyoniyawa ba ne, har ma suna karfafa mata gwiwar aikata wadannan munanan ayyuka ta hanyar ba ta makamai da kayan aiki,” in ji shi. Mr. Pezeshkian ya kara da cewa gwamnatin Isra’ila da ke samun goyon...
    Wasu Hare-haren da gwamnatin Isra’ila ta kai ya haddasa gobara a wasu matatun mai a lardin Bushehr da ke kudancin kasar Iran. Gobarar ta tashi ne a wurin a ranar Asabar bayan da wasu kananan jiragen yakin Isra’ila guda biyu suka kai hare-hare a kan kayayyakin sarrafa iskar gas da ke yankin kudancin Pars. Hare-haren sun yi haddassa fashe fashe a matatar iskar gas ta Fajr-e Jam, daya daga cikin mafi girma a Iran, da kuma wata karamar matatar mai a mataki na 14 na tashar iskar gas ta Kudu Pars. Har yanzu ba a fitar da kiyasin barnar a hukumance ba. Bayan gobarar, ma’aikatar mai ta Iran ta fitar da wata sanarwa inda ta tabbatar da harin. Sanarwar ta...
    Shugaban Amurka Donald Trump ya umarci jami’an hukumar kula da shige-da-ficen-kasar da su dakatar da aikin samamen kama baƙin-haure ’yan ci-rani, a gonaki da otal-otal da ma gidajen sayar da abinci na fadin kasar. Jaridar New York Times ta Amurka ta rawaito ma’aikatar tsaron cikin gida na tabbatar da samun umarnin, wanda aka mika shi ga hukumar kula da shige-da-fice da kuma ta yaki da fasa-kwauri, to sai dai kamfanin dillancin labarai na Reuters bai kai ga tabbatar da sahihancin umarnin ba. ’Yan bindiga sun kashe mutum 100 a Benuwe Wutar lantarki ta kashe mutum 5, ta jikkata 13 a Gombe Tun a lokacin yakin neman zaben shugabancin Amurka zango na biyu ,Mista Trump ya alkawarta korar bakin-hauren da suka...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    An fargabar cewa ’yan bindiga sun kashe akalla mutum 100 a wani hari da suka kai a garin Yelewata da ke yankin Karamar Hukumar Guma a Jihar Benuwe. Aminiya ta ruwaito cewa maharan sun far ma al’ummar garin na Yelewata ne a cikin daren ranar Juma’a wayewar garin Asabar. Wutar lantarki ta kashe mutum 5, ta jikkata 13 a Gombe Damina: NiMet ta gargaɗi jihohi 13 kan barazanar ambaliyar ruwa Wadanda suka shaida harin na Yelewata sun ce maharan sun mamayi garin ne kafin karfe 12 na dare, inda suka kwashe sama da sa’a biyu suna ta’annati ba tare da wani dauki daga jami’an tsaro ba. Da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labarai na AFP, wani mai magana da yawun...
    Rundunar ’Yan Sandan jihar Gombe, ta tabbatar da mutuwar mutum biyar da kuma jikkatar wasu 13, sakamakon tashin wutar lantarki a unguwar Tudun-Wada, Pantami a jihar. Wutar ta tashi ne da safiyar ranar Asabar sakamakon matsala da ta taso daga wata tiransifoma a yankin, kamar yadda kakakin ’yan sandan jihar, DSP Buhari Abdullahi, ya bayyana. Sojoji sun kama ɗan China da wasu 4 kan zargin safarar makamai a Borno da Yobe Damina: NiMet ta gargaɗi jihohi 13 kan barazanar ambaliyar ruwa Cikin waɗanda suka rasa rayukansu har da Babban Sakatare na Ma’aikatar Ayyuka ta Musamman ta jihar, Alhaji Muhammad Yusuf Kulani, tare da ’ya’yansa da wasu mazauna unguwar. Marigayin shi ne shugaban ƙungiyar ƙwararrun akantoci ta Jihar Gombe (ANAN). ’Yan...
    Gwamnatin Tarayya ta roƙi ƙasashen Isra’ila da Iran da su daina rikici, su zauna lafiya su sasanta tsakaninsu.  A wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Waje ta fitar, ta bayyana damuwa kan yadda rikicin ke ƙara ta’azzara, inda ta nemi ɓangarorin biyu da su kai zuciya nesa don samar da zaman lafiya a duniya baki ɗaya. Mahara sun kashe mutum 26 a sabon hari a Binuwai Mulkin Tinubu ya fi kowane muni tun bayan dawowar mulkin farar hula — Dalung Sanarwar ta ce faɗa da ramuwar gayya na jefa rayukan fararen hula cikin hatsari, kuma yana iya haddasa rikici mai muni a yankin Gabas ta Tsakiya, wanda hakan zai iya barazana ga tsaron duniya da kuma ci gaban tattalin arziƙi dunuya....
    Dakarun Operation Haɗin Kai sun kama mut biyar da ake zargin suna taimaka wa ’yan ta’adda da kayan aiki. Daga cikinsu har da wani ɗan ƙasar China da ya ce shi mai harkar ma’adinai ne. Damina: NiMet ta gargaɗi jihohi 13 kan barazanar ambaliyar ruwa Ya kamata Isra’ila da Iran su kawo ƙarshen rikicin da ke tsakaninsu — Gwamnatin Tarayya An kama su ne a lokacin kai wani samame da aka gudanar daga 5 zuwa 7 ga watan Yuni a ƙananan hukumomin Kukawa da Ngala na Jihar Borno, da kuma Geidam a Jihar Yobe. A lokacin wannan aiki, dakarun sun ƙwato wasu kayayyaki da suka haɗa da mota, babur, wayoyin salula, fasfo na ƙasar China, da kuma kuɗi Naira 10,000....
    Semenyo ma ya taka rawar gani saboda kwallo biyun da ya ci a wasan karshe sun sa ya ci wa kungiyarsa Bournemouth kwallo 11 kenan a karonfarko. Danwasan Najeriya Aled Iwobi ya fi abokan wasansa kokari a Fulham da kwallayensa tara da ya ci da kuma taimakawa wajen cin shida, sannan ya dan dara Amad Diallo na Manchester United (wanda ya ci takwas kuma ya bayar aka ci shida). Amma Iwobi ya fi shi buga wasanni saboda Diallo ya yi jinyar wajan watanni uku a kakar da ta gabata. Iwobi ne dai kan gaba wajen kirkirar damarmaki (59) da kuma bayar da cikakken fasin (508) a cikin bangaren abokan hamayya, inda shi kuma. Thomas Partey na Ghana ya fi yawan...
    Kungiyar cinikayya ta duniya wato WTO, ta gudanar da taron shekara-shekara na biyu, na hukumar zartaswar cinikayyar hidimomi a birnin Geneva dake kasar Switzerland a jiya Juma’a, inda bangaren Sin ya yi nuni da cewa, matakin Amurka game da harajin kwastam na tattare da rashin fahimta da rashin gaskiya a wasu fannoni, don haka ya bukaci bangaren Amurka da ta bi ka’idojin kungiyar WTO, da daidaita matsaloli ta hanyar yin hadin gwiwa a tsakanin bangarori daban daban, da dakatar da daukar matakai daga bangare daya, don tabbatar da tsarin ciniki na duniya tare da bangarori daban daban. (Zainab Zhang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye...
    Yayin da taro na biyu na tattauna hadin gwiwar Sin da kasashen yankin tsakiyar Asiya ke kara matsowa, sakamakon kuri’un jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta kasar Sin ta gudanar, sun nuna gamsuwa da hadin gwiwa bisa matsayin koli dake tsakanin Sin da kasashen nan biyar na yankin tsakiyar Asiya, a matsayin wata hadaka ta al’umma mai kyakkyawar makomar bil’Adama, wadda ke kara shigar da sabon kuzari, na daidaito cikin yanayin duniya dake kara shiga yanayin tangal-tangal. Tun dai taro na farko na tattauna hadin gwiwar Sin da kasashen yankin tsakiyar Asiya, hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen biyar ya shiga wani sabon zango na ci gaba. Har ma kuri’un na jin ra’ayin jama’a suka nuna yadda kaso 90.4...
    A wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta fitar, ta yi tir da harin na Isra’ila akan Iran tare da bayyana cewa, ya haifar da rikici a tsakanin bangarorin biyu da kuma musayar harba makamai masu linzami. Gwamnatin ta Najeriya ta nuna bakin cikinta akan abinda ya faru, tare da kuma da yin kiran a tsagaita wutar yaki da gaggawa, da kai zuciya nesa. Har ila yau, sanarwar ma’aikatar harkokin wajen ta Nigeria wacce kakakinta Kimiebi Imomotimi Ebienfa ya rattabawa hannu a yau Asabar,14 ga watan Yuni 2025, ta jaddada cewa; yaki ba zai maye gurbin tattaunawa ba, kuma hanyar diplomasiyya ce za ta kai ga samar da zaman lafiya mai dorewa, girmama juna da aiki da dokokin kasa...
    A yau Asabar aka gudanar da bikin ranar ” Idin Gadir” a nan birnin Tehran, wanda ya tashi daga dandalin “Inqilab” zuwa dandalin ” Azadi” mai nisan kilo mita 10. Bisa la’akari da halin yake da ake ciki, an bai wa bikin na bana taken: Iran ce, takobin Zulfikar Na Imam Ali.” Miliyoyin mutane ne dai su ka cika filin bikin na birnin Tehran da mutane su ka fara taruwa tun da tsakar rana, har zuwa bayan faduwar rana. A bisa kirdado kusan  mutane miliyan 3 ne su ka taru a nan Tehran. A cikin sauran birane da garuruwan Iran an yi wannan irin gangamin na raya ranar Idin Gadir wanda yake tattare da girmama shahidan da su ka kwanta...
    Mai magana da yawun hukumar da take kula da filin saukar jiragen sama ta Ben Gorion ta sanar a yau Asabar cewa an rufe filin saukar jiragen saman har zuwa wani lokaci a nan gaba, bayan da aka dauke dukkanin jiragen sama zuwa kasashen Cyprus, Greece da kuma Amurka. Mai Magana da yawun hukumar filin saukar jiragen saman na Ben Gorion  Lisa Daiper ta bayyana ce; Babu wani lokaci takamaimai da aka tsayar domin sake bude filin saukar jiragen saman na Ben Gorion.”  A gefe daya jaridar “Maariv’ ta bayyana cewa; An dauke dukkanin jiragen sama zuwa filayen  jiragen saman a kasashen turai. Haka nan kuma ta kara da cewa; An dauki 14 daga cikin jiragen saman na HKI zuwa...
    Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Arakci wanda ya tattauna ta wayar tarho da jami’ar harkokin waje ta tarayyar turai ya bayyana cewa, ci gaba da tattaunawa a tsakanin Iran da Amurka ba shi da wata ma’ana, kamata ya yi jami’an tarayyar turai din su yi Allawadai da wuce gona da irin HKI akan Iran. Da safiyar yau Asabar ne dai jami’ar diplomasiyyar ta turai Kaja Kallas ta kira yi minsitan harkokin wajen jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Arakci inda su ka tattauna halin da ake ciki a yammacin Asiya da ya hada da harin da HKI ta kawo wa Iran. Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana harin na HKI da cewa, wuce gona da iri ne da...
    Hukumar Kula da Yanayi (NiMet), ta sake fitar da gargaɗi game da yiwuwar ambaliyar ruwa a wasu jihohin a daminar bana. A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, hukumar ta bayyana cewa Jihar Akwa Ibom ce ke fuskantar barazana mafi tsanani a halin yanzu. Gwamnan Kaduna ya bai wa sabon Sarkin Moro’a sandar mulki Farashin fetur ya tashi a kasuwar duniya bayan harin Isra’ila a Iran Sauran jihohin da abin ka iya shafa sun haɗa da Sakkwato, Zamfara, Filato, Yobe, Bauchi, Bayelsa, Nasarawa, Binuwai, Ogun, Ekiti, Delta da kuma Ribas. NiMet ta shawarci al’umma, musamman waɗanda ke zaune a cikin waɗannan jihohin, da su tabbatar sun yashe magudanan ruwa domin bai wa ruwa hanyar wucewa. Haka kuma...
      Yadda ake hadawa: Da farko za ki gyara shinkafarki ki wanke ta ki tsane ta sai ki bar ta ta dan bushe, sannan a barzo miki ita a inji sai ki ajiye a gefe. Sai ki wanke namanki ki dora a wuta ki sa maggi, da gishiri da tafarnuwa da citta da albasa. Sannan sai ki zo ki tankade wannan shinkafar da kika barzo ta saboda da tsakin ake amfani. Sai ki sa ruwa ki wanke tsakin ki tsane shi, sai ki zuba shi a madambaci ki dora a wuta. Sai kuma ki gyara zogalenki, ki wanke, ki hada da tsakin sai ki rufe. Ki tsame namanki, ki yanka kayan miyanki ko ki jajjaga duk daya ne ki ajiye...
    Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya bai wa sabon Sarkin Moro’a, Mai Martaba Isiaku Tagwai Sambo sandar mulki, a wani biki da aka gudanar a garin Manchok da ke Ƙaramar Hukumar Kaura. Gwamna Sani, ya bayyana cewa sarakunan gargajiya na taka muhimmiyar rawa wajen zaman lafiya, haɗin kai da kuma ci gaban al’umma. Ya kamata Isra’ila da Iran su kawo ƙarshen rikicin da ke tsakaninsu — Gwamnatin Tarayya Mahara sun kashe mutum 26 a sabon hari a Binuwai Ya ce gwamnatinsa na bai wa sarakunan gargajiya cikakken goyon baya saboda irin rawar da suke takawa a harkar mulki da ci gaban jama’a. “Mun jajirce wajen haɗa kan al’umma a faɗin Jihar Kaduna, ba tare da nuna bambanci ba. “Yanzu Jihar...
    An rufe taron ministocin Sin da Afirka mai tabbatar da ci gaban hadin gwiwar da aka samu a dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afirka wato FOCAC, wanda aka gudanar daga ranekun 10 zuwa 12 a birnin Changsha na lardin Hunan, matakin da ya bayar da sabbin damammaki ga kasashen Afirka, bisa shirin “manyan ayyuka 10 na abota tsakanin Sin da Afirka”. Sa’an nan, bayan an kammala taron, nan take, an kaddamar da bikin baje kolin kayayyaki hajojin Sin da Afirka karo na 4, duk a birnin Changsha, matakin da ya zamo daya daga cikin jerin ayyukan da ake gudanar da su don aiwatar da shirin “manyan ayyuka 10”, inda aka baje kolin ci gaban da aka samu, da tattara...
    Gwamnatin Tarayya ta roƙi ƙasashen Isra’ila da Iran da su daina rikici, su zauna lafiya su sasanta tsakaninsu.  A wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Waje ta fitar, ta bayyana damuwa kan yadda rikicin ke ƙara ta’azzara, inda ta nemi ɓangarorin biyu da su kai zuciya nesa don samar da zaman lafiya a duniya baki ɗaya. Mahara sun kashe mutum 26 a sabon hari a Binuwai Mulkin Tinubu ya fi kowane muni tun bayan dawowar mulkin farar hula — Dalung Sanarwar ta ce faɗa da ramuwar gayya na jefa rayukan fararen hula cikin hatsari, kuma yana iya haddasa rikici mai muni a yankin Gabas ta Tsakiya, wanda hakan zai iya barazana ga tsaron duniya da kuma ci gaban tattalin arziƙi dunuya....
    Gwamnatin Tarayya ta roƙi ƙasashen Isra’ila da Iran da su daina rikici, su zauna lafiya su sasanta tsakaninsu. A wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Waje ta fitar, ta bayyana damuwa kan yadda rikicin ke ƙara ta’azzara, inda ta nemi ɓangarorin biyu da su kai zuciya nesa don samar da zaman lafiya a duniya baki ɗaya. Mahara sun kashe mutum 26 a sabon hari a Binuwai Mulkin Tinubu ya fi kowane muni tun bayan dawowar mulkin farar hula — Dalung Sanarwar ta ce faɗa da ramuwar gayya na jefa rayukan fararen hula cikin hatsari, kuma yana iya haddasa rikici mai muni a yankin Gabas ta Tsakiya, wanda hakan zai iya barazana ga tsaron duniya da kuma ci gaban tattalin arziƙi dunuya....
    Ba tare da saninmu ba, yawancin al’ummar Afirka musamman ma naYammacin Afirka suna fama da abinda ake kira da suna irin hali ko yanayin da aka shiga sanadiyar lamarin cinikin Bayi.Bayan shekara 100 da aka yi daga shekarar 1801 zuwa 1901, an yi wani kokarin da ake yi ma kallon tamkar wani takune na yadda za’a kubuta daga irin cin fuskar da ake yi kowace rana. Kafin dai a tsunduma sosai cikin lamarin cinikin Bayi, yana da matukar kyau a fara yin bayani kan yadda abin ya fara:Lamarin cinikin Bayi ba manufa bace ta Yammacin Turai.Duk lamarin ya zarce wani hasashen da za’a iya yi ko wani rubutun,da aka yi aka aje.Idan kuma aka duba ta bangaren nahiyar Afirka ita...
    Haka zalika koda ba ki fuskanci matsalar zubar jini ba, ki daure ki shayar da jaririnki hakan zai ci gaba da sa mahaifarki harbawa ta taso daga mararki ta koma kasan cikinki cikin sati 2 da haihuwa, hakan zai rage miki tsananin ciwon mara duk da shayarwa akwai zafi wani lokacin. Za Mu Ci Gaba Mako Mai Zuwa Insha Allahu   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Aƙalla mutum 26 ne suka rasu sakamakon wasu sabbin hare-haren da aka kai wasu ƙauyuka a Jihar Binuwai. Hare-haren sun faru ne a yankunan Ƙaramar Hukumar Makurdi da Katsina-Ala tsakanin ƙarfe 12 na dare zuwa 2 na daren ranar Alhamis. Farashin fetur ya tashi a kasuwar duniya bayan harin Isra’ila a Iran An kashe masu garkuwa da mutane da kuɓutar da wasu A Ƙaramar Hukumar Makurdi, wasu ’yan bindiga sun kai hari ƙauyukan Mtswenem da Akondotyough Bawa, inda suka kashe mutum 25. Haka kuma, an kashe mutum ɗaya a wani hari daban da aka kai ƙauyukan Kenvanger da Agbami a Ƙaramar Hukumar Katsina-Ala. Wasu mazauna yankin sun ce ’yan bindigar sun shiga gidajen mutane suna harbin su yayin da suke...
    Gwamnatin Tarayya ta bayyana aniyar ɗaukar matakai masu tsauri kan duk wanda aka samu da hannu a harkar fasa bututun mai da satar ɗanyen mai a yankin Niger Delta. Daraktan Tsaron Makamashi a Ofishin Mai baiwa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaro (ONSA), Hon. Ojukaye Flag-Amachree, ne ya bayyana haka yayin wani taron masu ruwa da tsaki da kamfanin Pipeline Infrastructure Nigeria Limited (PINL) ya shirya a birnin Fatakwal. A cewarsa, tuni sama da mutum 100 da ake zargi da hannu a wannan haramtacciyar harka an gurfanar da su a gaban kotu. Ya ce duk wanda aka kama, komai muƙaminsa, za a hukunta shi bisa doka. Ya kuma roki shugabannin al’umma da su ja kunnen matasa da yara kada su shiga...
    Ciwon Olsa Ga mai fama da ciwon Olsa, sai ya nemi garin ‘ya’yan Gwanda cokalin shayi daya; ya zuba a kunu sau daya a rana, har tsawon kwana bakwai, za a rabu da ita da yardar Allah.   Ruwan Maniyyi Ga masu fama da karancin ruwan maniyyi, sai ya nemi garin ‘ya’yan Gwanda da Madara ya hada ya rika sha, wannan hadi na matukar kara ruwan maniyyi. Ciwon Siga: Shan garin ‘ya’yan danyar Gwanda cokali daya a ruwan dumi, na sauke Siga cikin kankanin lokaci a jikin mutum da izinin Allah.   Hana Daukar Ciki Ga masu son yin tsarin iyali, shan garin ‘ya’yan Gwanda cokalin shayi daya a ruwan dumi bayan yin jima’i, na hana ciki ya shiga.  ...
    Ma’aikatar Gona da tsaron abinci ta ƙasa ta dakatar da shirinta na gudanar da addu’a da azumi na kwanaki uku, bayan martani mai zafi daga jama’a. Tun da farko, an tsara addu’ar ne domin neman taimakon Ubangiji wajen tabbatar da tsaron (wadataccen) abinci a Nijeriya. Wata takarda da ta bayyana ga jama’a, wadda Daraktar Gudanarwa ta Ma’aikatar, Mrs. Adedayo Modupe O., ta sanya wa hannu, ta gayyaci daraktoci da sauran manyan ma’aikata domin halartar wannan taron addu’a a shalƙwatar ma’aikatar a Abuja, a ranakun 16, 23 da 30 ga Yuni, 2025. Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Addu’ar Kwana 3 Don Samun Isasshen Abinci Wani Gidan Gona A Jihar Ogun Zai Fitar Da Tarwada Ta Kimanin Naira Biliyan Shida A 2025...
    A tsayin wadannan shekarun, Nijeriya ta fuskanci kalubale da dama da suka hada da fafutukar tabbatar da mulkin dimokuradiyya, siyasar yanki, rikita- rikitar addini da kabilanci da kuma gagarumar matsalar tsaro daga Kudu zuwa Arewa. Mafi yawan al’ummar Nijeriya na bayyana shekaru 26 na mulkin dimokuradiyya a matsayin shekarun gurbataccen mulki, shekarun mulkin danniya da zalunci, cin hanci da rashawa, tabarbarewar tsaro, rugujewar tattalin arziki kana shekaru 26 na satar danyen mai, rashin wutar lantarki, koma baya a sha’anin ilimi, aikin gona da rashin ayyukan yi tare da hauhawar farashin mai da tsadar rayuwa. Akasin murnar wannan ranar, kungiyoyi a Arewa da Kudu, jam’iyyun siyasa, kungiyoyin farar hula da na matasa da dalibai sun bayyana ‘yan siyasa a matsayin matsalar...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci ya aike da sako ga al’ummar Iran bayan harin da yahudawan sahayoniyya suka kai kan kasar A yammacin jiya ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gabatar da sakon ta gidan talabijin ga al’ummar Iran bayan harin ta’addanci na baya-bayan nan da yahudawan sahayoniyya suka kaddamar kan kasar Iran. Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana a cikin wani sakon da ya aike ta gidan talabijin ga al’ummar Iran cewa: Sojojin Iran za su yi aiki da dukkanin karfinsu, kuma za su mayar da martani kan wannan mugunyar aniya ta ‘yan sahayoniyya kaskantattu marasa tunani da basira. Jagoran ya jaddada cewa: Yahudawan sahayoniyya ba za su fita cikin wannan aika-aika ba,...
    Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta zama kasa ta farko a duniya da ta harbo jiragen saman yaki kirar F-35 Iran ta zama kasa ta farko a duniya da ta yi nasarar harbo jiragen yaki kirar F-35, bayan da ta yi nasarar auna wasu jiragen saman yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila kirar F-35 guda biyu, kuma ta barar da su kasa. Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi amfani da wadannan jirage masu tsananin ci gaban zamani wajen kai hare-haren wuce gona gona da iri kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran da safiyar ranar Juma’a, wanda hare-haren suka yi sanadiyyar shahadar wasu manyan jami’an sojan Iran da masana kimiyyar nukiliya da fararen hula da suka hada da mata da kananan yara. Ma’aikatar hulda...
    Ma’aikatar Gona da tsaron abinci ta tarayya ta sanar da gudanar da addu’a da azumi na kwanaki uku domin neman taimakon Allah wajen kare ƙasar nan da kuma tabbatar da wadatar abinci. Wannan na ƙunshe ne a wata takarda da aka fitar a ranar 11 ga Yuni, 2025, wadda Daraktar Gudanarwa, Mrs. Adedayo Modupe O., ta sanya wa hannu. A cewar sanarwar, dukkanin daraktoci, da mataimakan daraktoci, da shugabannin sassan sarrafa kayayyakin amfanin gona da sauran ma’aikatan ma’aikatar za su halarta. An sanya wa wannan shiri suna “Neman Taimakon Ubangiji Don Kariya da Cigaban Kasa.” Kudaden Da Ake Karba A Kogin Hadejia Jama’are Daga Hannun Manoma, Ba Haraji Ba Ne – HJRBDA Gwamnatin Gombe Ta Yi Albishir Ɗin Gina Babban...
    Jami’in kungiyar Hamas ya bayyana cewa: Kakkausan martanin da Iran ta mayar ya tabbatar da cewa babu mai girman kai da ba zai fuskanci mayar da martani ba Izzat al-Rishq mamba na ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ya jaddada cewa: Kakkausan martanin da Iraniyawa suka mayar ya tabbatar da cewa; babu mai girman kai da ba zai fuskanci mayar da martani kan zaluncinsa ba, kuma babu wuce gona da iri ba tare da hukunci ba. Izzat al-Rishq ya yi nuni da cewa: Tabbas makamai masu linzami da jiragen saman yaki marasa matuka ciki na Iran sun yi nasarar kai wa cikin tsakiyar haramtacciyar kasar Isra’ila, duk kuwa da kace-nacen da ake yi na girke na’urorin kakkabo makamai...
    Ya kuma bukaci da a ci gaba da hada hannu da masu ruwa da tsaki a fannin, musamman domin dakile kalubalen da ake fuskanta na rashin amfana da albarkatun da ke madatsar ruwan, musamman domin kara bunkasa fannin aikin noma da kuma kara samar da wadataccen abinci. A nasu martanin daban-daban, wasu daga cikin manoman sun yi kira ga hukumar ta HJRBDA, da ta samar musu da Taraktocin noma a daminar bana da kuma lokacin noman rani. Tawagar ta hukumar HJRBDA, ta ziyarci wuraren adana ruwa; ciki har da na Challawa, Dam din Gorge, wanda ke adana ruwa mai karfin tsawon zurfin mita miliyan 962 da Dam din Tiga, wanda ke iya adana ruwan da zurfinsa ya kai kimanin mita...
    Bugu da kari, akwai kuma masu kiwon Tarwada a gonar da sama da su 600, wadanda aka rage yawan adadinsu daga 1,327 zuwa 600, bayan bullar cutar annobar Korona, saboda kalubalen ci gaba da gudanar da sauran ayyukan gonar. A shekarar 2024, masu kiwon Tarwadar a gonar; sun samar da Tarwadar da yawanta ya kai kimanin tan 1,700, wadda kuma aka kiyasata cewa; kudinta ya kai na Naira biliyan 4.5. Wannan ba karamin ci gaba ba ne, musamman duba da cewa; gonar ta kasance abin koyi ga sauran kungiyoyin da ke kiwon Tarwada a daukacin fadin wannan kasa. Bisa wannan nasarori da gonar ta samar, hakan ya nuna yadda take ci gaba da samun yabo daga kasashen duniya, cikin masu...
    A wata hira tare da gidan talabijin na Arise, Obi ya ce duk da cewa cire tallafin mai yana da muhimmanci, amma ya kamata a aiwatar da wannan tsari cikin tsari. Ya ce ya amince cewa tallafin mai yana cike da ta’asa da cin hanci wanda akwai bukatar a kawo karshensa, amma ya yi suka ga hanyoyin da gwamnatin Tinubu take bi, yana bayyana su a matsayin wadanda aka yi ba bisa kwarewa ba. Obi ya tambayi jagororin kula da kudin da aka ajiye daga cire tallafin, yana cewa, “Tun da aka ce manatallafin man fetur, ana cewa an cire ne saboda ba a so mu dunga ciyo bashi kuma kudaden za su ba da dama wajen zuba jari a...
    Biyo bayan sauya sheka da aka yi kwanan nan, a zauren majalisar dattawa, APC na da kujeru 68; PDP na da 30; LP na da 5; SDP na da 2; NNPP na da 1; APGA na da 1 da kuma kujeru guda biyu da babu kowa, guda daya daga Jihar Edo da daya daga Jihar Anambra. Masana harkokin siyasa na ganin cewa bisa yadda lamura suke a halin yanzu, adadin na iya haurawa lokacin da majalisar tarayya ta dawo daga hutu, bayan sauya shekar Gwamna Umo Eno na Jihar Akwa Ibom daga PDP zuwa APC. Ana sa ran wasu daga cikin ‘yan majalisar tarayya na jihar za su iya bin sahunsa. A halin yanzu, Jihar Akwa Ibom tana da sanatan...
    Iran ta kaddamar da wasu jerin hare-haren makamai masu linzami kan Isra’ila a matsayin maida martani kan haren haren da Isra’ila ta kai wa kasar a cikin daren ranar Juma’a. Bayanai sun ce hare-haren na Iran sun lalata gine-gine da dama da jikkata mutane yayin da wasu rahotannin ke cewa an samu hasarar rayuka na akalla mutum biyu. A cewar rahotannin kafofin yada labaran Isra’ila daban-daban, makamai masu linzami na iran sun fada a yankunan Tel Aviv, Haifa, Beersheba da wasu wurare. An bayar da rahoton barna mafi muni a birnin Tel Aviv, inda akalla makami mai linzami guda ya afkawa wani bene mai hawa 50, lamarin da ya janyo fashewar wani abu mai karfi wanda ya sa hayaki ya...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce matakin da gwamnatin Isra’ila ta dauka a kan kasar tamkar shelanta yaki ne. Araghchi ya bayyana hakan ne a cikin wata wasika da ya aikewa babban sakatare na MDD da kuma shugaban kwamitin sulhu bayan da Isra’ila ta kai munanan hare-hare kan wuraren soji da cibiyoyin nukiliya da kuma wuraren zama wanda ya yi sanadiyar mutuwar wasu manyan kwamandojin dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC), masana kimiyyar nukiliya da fararen hula na iran. “Wadannan ayyuka na zalunci ba wai kawai sun zama babban cin zarafi ne ga ‘yancin kan kasar Iran a matsayinta na mamba mai cin gashin kanta a Majalisar Dinkin Duniya ba, amma kamar yadda dokokin kasa da kasa...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce sojojin kasar Iran ba za su sararawa gwamnatin Isra’ila ba. Jagoran ya bayyana hakan ne a wani sakon bidiyo ga al’ummar Iran ranar Juma’a biyo bayan hare-haren wuce gona da iri da Isra’ila ta yi kan kasar wanda ya kashe fararen hula, masana kimiyya da kwamandojin soji. Ayatullah Khamenei ya kara da cewa gwamnatin Isra’ila ba za ta kubuta daga wannan aika-aika ba, yana mai tabbatar wa al’ummar Iran cewa ba za a yi sakaci kan hakan ba. Jagoran ya jaddada cewa muguwar gwamnatin sahyoniya ta tafka babban kuskure, sannan kuma shelanta yaki ne kan Iran. Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: dukkanin jami’an kasar Iran...
    Wani babban jami’in sojan Iran ya ce an kai hare-hare a kalla wurare 150 a farmakin ramuwar gayya kan gwamnatin Isra’ila, ciki har da wasu sansanonin soji masu matukar muhimmanci. Da yake zantawa da gidan talabijin na kasar da sanyin safiyar Asabar, Birgediya Janar Ahmad Vahidi, babban mai ba da shawara ga babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran ya ce, rundunar ta IRGC ta yi nasarar aiwatar da shirinta na Operation True Promise III. A cewar kwamandan na IRGC, an kuma kai hari kan ma’aikatar harkokin soji da cibiyoyin soji da masana’antu a lokacin da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ke daukar fansa. Daga cikin wadanda harin ya rutsa da su sun hada da Manjo Janar Mohammad...
    Da yake magana kan muhimmancin bikin Ranar Dimokiraɗiyya ta bana, Idris ya ce wannan ba lokacin murna kaɗai ba ne, har ma lokaci ne na nazari kan cigaban ƙasar wajen ƙarfafa dimokiraɗiyya da farfaɗowar tattalin arziki.   Ya bayyana cewa ana amfani da kuɗaɗen da aka tara daga cire tallafin man fetur wajen gina muhimman ababen more rayuwa, ciki har da manyan tituna guda biyu da za su haura kilomita 1,700, waɗanda za su taimaka wajen bunƙasa harkokin kasuwanci da haɗa yankuna daban-daban.   Ya ce: “Manufar ba wai haɗa yankuna ba ce kawai, amma samar da damarmakin tattalin arziki.   “Nijeriya na ƙoƙarin komawa kan sahihiyar hanyar ta. Tana sake zama ƙasa mai daraja a idon duniya.   “Martabar...
    Bayan hakan, Pogba ya kunce kwantiraginsa da Juventus a watan Nuwamban 2024, kuma tun watan Maris da ya gabata ya samu damar komawa fili domin shirya dawowarsa. Yanzu haka yana ci gaba da atisaye tare da fatan ƙulla sabuwar yarjejeniya da Monaco domin ci gaba da taka leda a ƙasarsa ta haihuwa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ya yabawa hukumar bisa yadda ta aiwatar da dokar da ta ba da damar, ‘Dokar Ci Gaban Man Fetur da Gas ta Nijeriya (NOGICD) ta 2010. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kafofin yada labarai na kasa da kasa na matukar zura ido kan taron farko na tsarin tattaunawa game da tattalin arziki da cinikayyar Sin da Amurka da aka gudanar tsakanin ranekun 9 zuwa 10 ga watan nan da muke ciki a London na kasar Burtaniya. An yi muhimmin shawarwarin ne kan matsaya daya bisa manyan tsare-tsaren da shugabannin kasashen biyu suka cimma a ran 5 ga watan nan. A wadannan raneku 2, wakilan Sin da Amurka sun yi mu’ammala mai zurfi cikin sahihanci, kuma sun amince da tabbatar da matsaya daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma ta wayar tarho da ba da tabbaci kan ci gaban da aka samu a yayin tattaunawar ciniki da tattalin arziki da aka gudanar...
    Hukumomin ’yan sandan Najeriya tare da haɗin gwiwar wasu hukumomin tsaro sun samu gagarumar nasara a ƙoƙarin da suke na daƙile munanan laifuka a ƙasar. Na baya-bayan nan dai shi ne ceto mutanen da aka sace, da kashe wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne da kuma ƙwato manyan bindigogi da alburusai a jihohin Delta da Katsina. Mulkin Tinubu ya fi kowane muni tun bayan dawowar mulkin farar hula — Dalung An kama ’yar Najeriya da laifin safarar ɗalibai 15 a Australia A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan, Olumuyiwa Adejobi ya fitar, ya ce a jihar Katsina an samu gagarumar nasara a ranar 8 ga watan Yunin 2025, inda haɗin gwiwar JTF...
    Jagoran juyin musulunci na Iran wanda shi ne babban kwamandan rundunonin sojan kasar Iran, ya nada sabbin kwamandoji da maye gurbinsu da wadanda su ka yi shahada. Bayan shahadar kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci Shahid Hussain Salami, da kuma  babban hshahid Muhammad Hussain Bakiri, sai Shahid Gulam Ali Rashid wanda shi ne kwamandan Bakirin soja na “Khatamul-Anbiya, jagoran juyin ya sanar da sunayen wadanda su ka maye gurbinsu. Birgediya Muhammad Pakphur shi ne wanda jagoran ya sanar a matsayin sabon kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci, sai kuma  Manjo Janar Musawi a mastayin sabon kwamandan rundunar sojan kasar, yayin da aka nada janar Ali Shadmani a matsayin kwamandan Barikin soja na Khatamul-Anbiya.
    Kwamandan  sararin samaniya na dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran Janar Amir Ali Haji Zadeh yana cikin wadanda su ka yi shahada sanadiyyar harin da sojojin HKI su ka kawo wa  da asubahin yau Juma’a. Kamfanin dillancin labarun “Mehr” ya nakalto majiyar juyin juya halin musulunci ta Iran tana tabbatar da shahadar Janar  Amir Ali Haji Zadeh.
    Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta Lebanon Sheikh Na’im Kassim ya yi Allawadai da harin da HKI ta kai wa Iran, wanda ya bayyana shi da cewa; Yana da hatsarin gaske, kuma ‘yan sahayoniyar sun yi hakan ne bisa cikakken goyon bayan Amurka. Sheikh Na’im Kassim ya kuma bayyana cewa; Harin na ‘yan sahayoniya ba shi da wani dalili da ya wuce a rufe bakin gaskiya wanda yake taimakawa al’ummar Falasdinu a Gaza da ake yi wa kisan kiyashi, haka nan kuma taimakawa da goyon bayan gwgawarmayar Lebanon da dukkanin wannan yankin. Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya kuma kara da cewa; Wannan harin da wuce gona da irin za iyi tasiri mai girma a cikin wannan yankin, sannan ya kara...