Dubban daruruwan mutane a kasar Yemen sun fito kan tituna suna bayyana jin dadinsu da samun nasara a kan kasar Amurka a yakin da suka dau makokinni suka fafatawa.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa an daw makonni jiragen yakin Amurka suna kai hare-hare kan wurare daban daban a kasar Yemen da sunan tilastawa kasar dakatar da kaiwa jiragen ruwan Amurka da kuma na HKI wucewa da tekun Red sea don tallafawa mutanen Gaza, wadanda HKI take masu kissan kare dangi da kuma hana shigar abinda zuwa cikin gaza don kashesu da yunwa.

A ranar Laraban da ta gabata ce shugaban kasar Amurka Donal Trump ya fito ya fadawa duniya kan cewa, ya cimma yarjeniya da kasar Yemenkan cewa ba zasu sake kaiwa jiragen ruwan Amurka hare-hare a tekun Maliya ba. Don haka ita ma Amurka zata janye daga tekun red sea tare da kawo karshen yaki da mutanen kasar Yemen.

Majiyar gwamnatin ceto ta kasar Yemen ta ce ta yarda da matakin da Amurka ta dauka, amma kuma hare-hare a kan HKI zasu ci gaba har zuwa lokacinda zata dakatar da hare-hare a kan Falasdinawa a Gaza da kuma bude hanya don shigar abinda da kuma bukatun Falasdinawa a gaza.

Sai dai majiyar da gwamnatin kasar Yemen tace idan Amurka ta sake kaiwa mutanen kasar Yemen suma zasu dawo da kai mata hare-hare.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: a kasar Yemen

এছাড়াও পড়ুন:

Sudan ta katse  hulda da Hadaddiyar Daular Larabawa bisa goyon bayan dakarun RSF

Gwamnatin Sudan ta katse dangantakar diflomasiyya da (UAE), bisa zarginta da goyan bayan dakarun RSF.

A cikin jawabin da aka watsa a talabijin, Ministan Tsaron Sudan, Yassin Ibrahim ya bayyana cewa Sudan ta “katse dangantakar diflomasiyya da UAE,” tare da janye jakadanta da rufe ofishin jakadanci da konsulat dinta a kasar .

Da yake magana a gidan talabijin na gwamnatin kasa, ministan tsaron Sudan, Yassin Ibrahim Yassin, ya zargi Abu Dhabi da keta hurumin ‘yancin Sudan ta hanyar mara baya ta fuskar soji ga RSF, ciki har da samar da makamai, da jiragen yaki marasa matuka, da makamai masu linzami wadanda aka kai hari da su a baya-bayan nan a tashar jiragen ruwa, da filin jiragen sama, da kuma tashoshin wutar lantarki na Sudan.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Iran Zata Fara Aikin Nema Da  Kuma Hakar Danyen Man Fetur A Cikin Ruwan Tekun Caspian
  • Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Halarci Bukukuwan A Moscow
  •  Al-Husy: Yakin Gaza Shi Ne Kisan Kiyashi Mafi Muni A Cikin Karni Daya
  • Shugaban Kungiyar Hizbullah Ta Kasar Lebanon Ya Ce Gwagwarmaya Zata Ci Gaba Har Zuwa Nasara
  • Yemen Ta Jaddada Cewa: Idan Amurka Ta Kai Mata Hari, Tabbas Yarjejeniyar Kawo Karshen Bude Wuta Tsakaninsu Zata Ruguje  
  • Gwamnatin Siriya Tana Neman Tattaunawa Da Gwamnatin Mamayar Haramtacciyar Kasar Isra’ila
  • “Amnesty International”: Korar Falasdinawa Daga Gaza Laifin Yaki Ne
  • Sudan ta katse  hulda da Hadaddiyar Daular Larabawa bisa goyon bayan dakarun RSF
  • Ansarullah: Yarjejeniya da Amurka ba za ta dakatar da hare-haren da Yemen ke kaiwa Isra’ila ba