PSG Ta Yi Waje Rod Da Arsenal A Gasar Zakarun Turai
Published: 8th, May 2025 GMT
Burin Arsenal na lashe gasar UEFA a karon farko a tarihinta ba zai cika a wannan shekarar ba, sakamakon rashin nasarar da ta yi a hannun PSG a wasan zagayen na kusa da na karshe, Arsenal ta buga wasan karshe a UEFA sau daya a shekarar 2006 tsakaninta da Barcelona.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku.
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Bukaci Kasashen Turai Su Shiga Tattaunawar Nukliya Da Take Yi Da Amurka
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Baghaaei ya bukaci kasashen turai da su shiga a dama da su kan tattaunawa dangane da shirin nukliyar kasar Iran na zaman lafiya. Ya kuma jaddada cewa Iran tana turjiya ga dukkan tunanin Amurka na wargaza shirin Nukliyar kasar Iran kwata-kwata.
Baghaei ya kara da cewa duk da cewa Iran a shirye take a ci gaba da tattaunawa kan shirin makamashin nukliyar kasar, da sake farfado da yarjeniyar JCPOA ta shekara ta 2015 amma kuma ba zata taba barin hakkinta na mallakar fasahar nukliya da luma sarrafashi a hanyoyin da yarjeniyar NPT ta amince da su ba.
Kuma da alamun tattaunawar tsakanin Amurka da Iran ya daki dutse, saboda sun sami sabani a kan wasu al-amura wadanda basu shafi Nukliya ba, don haka ne aka fasa taron roma wanda yakamata a gudanar a ranar asabar da ta gabata. Batun cewa Mike Waltz mai bawa shugaban kasar Amurka shawara kan tsaro yana son cusawa gwamnatin Amurka ra’ayin Benyamin Natanyahu firai ministan HKI a tattaunawar Amurka da Iran, ya ce, wannan al-amari ne na cikin gida ga gwamnatin Amurka, amma abinda ya shafi Iran shi ne menene Amurka zata gabatar a kan teburin tattaunawa da ita.
Don haka ne Iran take bukatar kasashen Turai su shigo a dama da su a cikin wannan tattaunawar.