Iran Ta Yi Tsokaci Kan Jita-Jitar Da Ake Yadawa Cewa: Shugaban Kasar Iran Zai Gana Da Shugaban Amurka
Published: 8th, May 2025 GMT
Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta yi tsokaci kan jita-jitar cewa: Shugaban kasar Iran zai gana da shugaban kasar Amurka
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya yi watsi da jita-jitar da ake yadawa game da batun cewa shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian zai yi wata ganawa da shugaban Amurka Donald Trump a mako mai zuwa, da rashin gamsuwar bangaren Amurka da Iran da shiga tsakanin masarautar Oman, da kuma cewa Iran ta gabatar da shawarar gudanar da shawarwari kai tsaye da Amurka, da sauran da’awar karya a matsayin batutuwa na jita-jita maras asali da tushe.
Dangane da wata tambaya game da jerin jita-jita da ake yadawa a kafafen yada labarai game da matsayin tattaunawar da ake yi tsakanin Iran da Amurka, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa duk wadanda batutuwa da suke fitowa daga majiyoyi marassa tushe da asali kuma mafi yawansu labarai ne na karya na bogi da ba su da wata madogara mai tushe. Baqa’i ya jaddada cewa: Ma’aikatar harkokin wajen kasar ita ce ke da alhakin ba da bayanai dangane da ayyukan jami’an diflomasiyya, ciki har da batun tattaunawar da ba na kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka, cikin gaskiya, kwarewa, da kuma lokacin da ya dace.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: aikatar harkokin wajen
এছাড়াও পড়ুন:
Xi Na Kan Hanyar Kai Ziyarar Aiki A Rasha
A yau Laraba ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tashi daga birnin Beijing domin kai ziyarar aiki a kasar Rasha da kuma halartar bikin cika shekaru 80 da samun nasarar yakin ceton kasa na tarayyar Soviet a birnin Moscow, bisa gayyatar da shugaban kasar Vladimir Putin na Rasha ya yi masa. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp