2025-05-12@15:00:38 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1602

«hukumar Shira»:

    Shugaba Bola Tinubu ya rantsar da sabbin Kwamishinonin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) kafin fara taron Majalisar Zartaswa ta Tarayya a fadar gwamnati da ke Abuja.   Sabbin Kwamishinonin INEC din da aka rantsar su ne Mallam Tukur Yusuf, mai wakiltar yankin Arewa maso Yamma, da Farfesa Sunday Aja, mai wakiltar Jihar Ebonyi.   Haka kuma, an rantsar da mambobi biyu na Hukumar Da’a ta Kasa (CCB).   Mambobin su ne Ikpeme Ndem, daga Jihar Cross River, da Mai Shari’a Buba Nyaure mai ritaya, daga Jihar Taraba.   Daga Bello Wakili.        
    Wannan rangwamen farashin duk da cewa ba a hukumance yake ba, amma ya bai wa kwastomomin Dangote damar siyar da mai akan farashi mai rahusa a tsakanin Naira 830 zuwa N835 kan kowacce lita.   Wannan nasarar ta zo ne makonni kadan bayan da matatar ta yi ragin farashi sau biyu a jere a cikin mako guda a cikin watan Afrilu, inda ta rage farashin man ta daga N880 zuwa N835 kan kowace lita.   Ana kyautata zaton cewa, ragin na da nasaba da sabunta tsarin sayen danyen mai da takardar Naira, biyo bayan dakatarwar da aka yi na wucin gadi.   Kokarin samun wata sanarwa a hukumance daga Kakakin Rukunin Dangote, Anthony Chiejina, kan batun rangwamen ya ci tura...
    ‘Hudu daga cikin ‘yan majalisar shawarar musulunci ta Iran sun isa birnin Jakarta na kasar Indonesia domin halartar taron majalisun kungiyar kasashen musulmi. A yau Litinin ne dai aka bude taron majalisun kasashen kungiyar kasashen musulmi a birnin Jakarta na kasar Indonesia wanda shi ne karo na 19. Taken da aka bai wa taron karo na 19 shi ne: “Kafa Gwamnatoci masu hikima a kuma cibiyoyi masu karfi a matsayin ginshikin jajurcewa.”  Tawagar ta Iran dai wacce Ruhullah Mutafakkir Azad yake jagoranta, ta kuma kunshi Sara Fallahi, Sayyid Yahya Sulaimani, da Muhammad Mahdi Shahriyari. Taron zai ci gaba har zuwa ranar 15 ga watan nan na Mayu da ake ciki, kuma tawagar ta Iran za ta gabatar da jawabi a...
    Saraki, shi ne zai jagoranci kwamitin sai kuma ƴan kwamitin da suka haɗa da gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare; gwamnan jihar Filato, Caleb Muftiwang da kuma gwmanan jihar Enugu, Peter Mba.   Sauran ƴan kwamitin sun haɗa da Sanata Seriake Dickson da Sanata Ibrahim Dankwambo da tsohon gwamnan jihar Abia, Chif Okezie Ikpeazu.   Waɗanda suka halarci taron sun haɗa da gwamnonin Enugu da Zamfara da Adamawa da Taraba da Osun da Oyo.   Ministan babban birnin tarayya Abuja kuma tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyeson Wike shima ya je taron sai kuma tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ahmed Maƙarfi.   Suma ƴan jam’iyyar irin su Sanata Aminu Waziri Tambuwal da Sule Lamido da Samuel Ortom da Gabriel Suswan da Seriake...
    Shugaba da mataimakinsa an tsige su ne kan zargin almundahana, rashin ɗa’a, rashin mayar da hankali kan aiki da kuma cin zarafin ofisoshinsu.   Kafin masa wannan naɗin riƙon kwarya, Wali ya kasance Kansila da ke wakiltar gundumar Tumfafi kuma shi ne ya kasance shugaban Kansiloli na ƙaramar hukumar.   Gwamnatin jihar Bauchi ce ta sanar da rasuwar nasa a ranar Lahadi ta cikin sanarwar manema labarai da kakakin gwamnan jihar, Mukhtar Gidado, ya fitar.   Da ya ke miƙa ta’aziyyasa ga iyalan mamacin, gwamna Bala Muhammad ya misalta marigayin a matsayin jajirtaccen mutumin da ya hidimta wa jama’a tare da bayar da gudunmawarsa wajen kawo cigaba a ƙaramar hukumar Shira da ma jihar Bauchi.   Gwamnan ya yi addu’ar...
    Ɗan Majalisar Wakilai, Honorabul Yusuf Gadgi, ya yi iƙirarin cewa mayaƙan Boko Haram sun ƙwace makaman sojoji da kuɗaɗensu ya kai tiriliyoyin naira a hare-haren da kungiyar ta kai kan sansanonin soji a yankin Arewa maso Gabas. Gadgi ya bayyana haka ne a yayin da yake tsokaci kan ƙudirin da Honorabul Ahmed Satomi daga Jihar Borno ya gabatar a zauren Majalisar, kan gobarar da ta tashi a ma’ajiyar makamai ta rundunar soji da ke Barikin Sojoji na Giwa da ke Maiduguri da kuma ƙaruwar hare-haren Boko Haram a jihohin Borno da Yobe a baya-bayan nan. Ɗan malisar ya ce yawan yadda ’yan ta’adda ke lalata kayan yaƙin sojoji a yanzu, ba a taɓa ganin irinsa ba a baya. Ya ƙara...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa tattaunawa ba kai tsaye ba tsakanin JMI da Amurka zagaye na hudu, yana tafiya kamar yadda ya dace. Kuma kasashen buyu sun kara fahintar ra’yin juna. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran da nakalto Aragchi yana fadar haka a wani hira da da ya gabatar bayan kammala zagaye na 4 na tattaunawar a jiya. Ministan y ace bangarorin biyu sun tattauna babututuwan da suke da zurfi a cikin matsalolin da kasashen biyu suke son su warware, na farko gamsar da Amurka kan cewa shirin makamashin Nukliya na kasar Iran ban a tsaro bane. Da kuma maganar daukewa Iran takunkuman tattalin arzikin da aka dora mata. Yace tattaunawar jiya   yafi...
    Sojojin HKI sun ci gaba da kai hare hare kan birane da garuruwan yankin yamma da kogin Jordan. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, hare-haren jiya sum sun fi maida hankali ne a garin Tulkaram da kuma sansanin yan gudun hijirar yankin A wannan karomma sojojin HKI sun bada umurni ga ma zauna garin Tullaram mata da maza da yara da tsoffi duk su fice daga gidajensu. Kwanaki 105 da suka gabata ne gwamnatin HKI ta fara wannan shirin na korar falasdinwa da kuma rusa gidajensu da nufin korarsu kwatakwata daga yankin. MDD ta bayyana a baya ya zuwa yanzu sun kori falasdinawa kimani 40,000 daga gidajensu, inda suka rusa su suka kuma . A wani...
    Kungiyar Magajunan Gari Na Kasashen Asiya Ta Zabi Birnin Esfahan na tsakiyar kasar Iran a matsayin cibiyar yawan bude ido na wannan shekara ta 2025. Manufar zaben birnin Esfahan a wannan karon shi ne gabatar da shi ga kasashen Asiya saboda sa mutanen Nahiyar Asiya su su ziyarci kasar da kuma birnin don sanin dumbin wuraren tarihin da suke cikin birnin da kuma kewayensa. Labarin ya bayyana cewa birnin Esfahan ayana daga cikin birane mafi tsufa a kasar , sannan yana dauke da wuraren kallo da kuma bude ido a cikin birnin Har’ila yau labarin ya kammala da cewa ana da kayakin tarihi kimani 200,000 a cikin birnin, sannan wasu 1940 na kayakin tarihin kasar, hukumar UNESCO ta zama wurare...
    Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bukaci shugaban kasar Ukraine ya amince da tayin shugaban Putin na Rasah na sun hadu a birnin Istambul na kasar Turkiya don tattauna yiyuwar  tsagaita budewa juna wuta. Kamfanin dillancin labaran Sputnik na kasar Rasha ya nakalto shugaban Trump yana fadar haka a jiya Asabar ya kuma bayyana cewa wannan wata dama ce kawo karshen zubar da jinni tsakanin kasashen biyu na fiye da shekaru uku da suka gabata. Trump ya bayyana haka ne a shafinsa na yanar gizo, ya kuma kara da cewa, haduwar shuwagabannin biyu zai fayyace matsayin yakin, da kuma yiyuwar dakatar da shi nan kusa. Banda haka haduwarsu zai bawa kasar Amurka damar gane matakin da zata dauka nan gaba,...
    Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya ba da shawarar yin  tattaunawa “kai tsaye” ba tare da sharadi ba” tsakanin kasarsa da Ukraine a ranar 15 ga Mayu a Istanbul. A martanin da ya mayar, shugaban na Ukraine ya ce a shirye ya ke don tattaunawa kai tsaye, amma ya zama dole a tsagaita bude wuta a gabanin haka, yana mai nuni da shawarar da kawayensa na yammacin duniya suka bayar na tsagaita bude wuta na kwanaki 30 ba tare da sharadi ba daga ranar Litinin. Ba tare da yin tsokaci a kai tsaye kan shawarar kasahen ba, shugaban na Rasha ya caccaki turawan da ya ce sun yi wa Rasha “rashin ladabi da kakkausan lafazi” ya kuma ce ya kamata...
    Sabon shugaban darikar ‘yan katolika na duniya Fafaroma Leo na 14 ya ce yana matukar bakin ciki da abin da ke faruwa a zirin Gaza, inda ya bukaci a tsagaita wuta nan da nan, a ba da agajin jin kai ga fararen hula da suka gaji, kuma a sako duk wadanda aka yi garkuwa da su.” Fafaroman ya kuma yi kira ga “manyan kasashen duniya” da su dakatar da yaki, ya kuma yi kira da a samar da zaman lafiya “adalci” mai “dorewa” a Ukraine a wani jawabi da ya gabatar yau Lahadi a sallarsa ta farko bayan zama fafaroma. Shugaban ‘yan katolika na duniya ya kuma yi maraba da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma tsakanin Indiya da...
    Iran ta bayyana aniyarta ta karfafa hadin guiwar ‘yan sanda da Nijar. Wanna bayanin ya fito ne a wani bangare na ziyarar da, Birgediya Janar Ahmad-Reza Radan, babban kwamandan rundunar tsaron Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya kai ziyara a kasar Nijar a ran gadinsa a Afrika. A ziyarar tasa ya gana da firaministan Nijar Ali Lamine Zeine, da ministan harkokin wajen kasar Bakary Yaou Sangaré, da ministan harkokin cikin gida Janar Mohammed Tomba, da shugaban ‘yan sandan Nijar Janar Omar Chiyani. A yayin ganawar, M. Zein ya jaddada karfafa hadin gwiwar ‘yan sanda a tsakanin kasashen biyu inda ya ce: “A shirye muke mu yi amfani da gogewar da ‘yan sandan Jamhuriyar Musulunci ta Iran suke da ita a dukkan...
    Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya bayyana fatan ganin kasashen India da Pakistan sun kai zuciya nesa, tare da warware sabani ta hanyar shawarwari da tattaunawa, kana su gujewa sake rura wutar tashin hankali. Wang ya bayyana hakan ne a jiya Asabar, yayin tattaunawa ta wayar tarho da mashawarcin gwamnatin India ta fuskar tsaro Ajit Doval, inda ya ce Sin na goyon baya, da fatan sassan biyu za su kai ga cimma cikakken yanayi mai dorewa na dakatar da bude wuta ta hanyar tattaunawa, wanda hakan muhimmiyar moriya ce ta kasashen biyu, kuma zai cika burin sassan kasa da kasa. Ya ce Sin ta yi tir da harin ta’addanci da ya auku a yankin Pahalgam, tana kuma adawa...
    Wata muhawara ta kunno kai a Jihar Kano da ma wajenta bayan gwamnatin jihar ta ba da umarni a cire naira miliyan 670 daga asusun ƙananan hukumomin jihar domin saye da kuma gyaran motocin Mai Martaba Sarkin Kano, Muhanmmadu Sanusi II. Gwamnatin jihar ta bayyana cewa za a kashe naira miliyan 50 daga cikin kudin wajen gyaran wasu motoci biyu na sarkin, ragowar kuma za a sayo wasu sababbin motoci huɗu. Shekara 10: Me ya sa Kofin Zakarun Turai ya gagari Barcelona? Za a kwaso ’yan Nijeriya 15,000 da ke gudun hijira a ƙetare Ɓullar takardar da ke ɗauke da umarnin ta haifar da ce-ceku-ce, amma gwamnatin jihar ta hannun Kwamishinan Watsa Labarai, Ibrahim Waiya, ta kare matakin da cewa...
    A Talatar makon jiya ce Inter Milan ta ƙara lalata wa Barcelona mafarkinta na ɗaukar Kofin Zakarun Turai a shekaran nan, bayan an yi kare-jini-biri-jini tsakanin kungiyoyin guda biyu a wasan kusa da na karshe. An tashi wasan ne da ci 4-3 a San Siro gidan Inter Milan bayan sun yi 3-3 a gidan Barcelona. Lautaro Martinez da Hakan Calhanoglu ne suka fara zura wa Inter ƙwallo a ragar Barcelona. Za a kwaso ’yan Nijeriya 15,000 da ke gudun hijira a ƙetare Matakan da gwamnonin Arewa suke so a ɗauka kan matsalar tsaron yankin Davide Frattesi ne ya ci ƙwallon da ta bai wa Inter nasara a cikin ƙarin lokaci, bayan ƙwallon ne kuma aka kaure da ruwan sama. Barça,...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta iran, Dr. Isma’ila Baka’i ya bayyana cewa; Tsagaita wutar yakin da aka yi a tsakanin Indiya da Pakistan abin yin maraba da shi ne, sannan kuma ya kara da cewa; Ya zama wajibi kasashen biyu su yi amfani da wannan dama domin rage tashin hankali a yankin da kuma tabbatar da zaman lafiya. Baka’i ya yaba da hikimar shugabannin kasashen biyu da su ka dakatar da yaki, yana kuma nuna fatansa na ganin kasashen biyu sun mayar da alakarsu kamar yadda take a baya a cikin gaggawa. A jiya Asabar ne dai ministocin harkokin wajen kasashen biyu su ka sanar da tsagaita wutar yaki,bayan kwanaki da su ka dauka suna musayar wuta a...
    Gwamnatin Nijeriya ta ce tattaunawa ta yi nisa domin kwaso ’yan ƙasar guda 15,000 da suke gudun hijira a ƙasashen Kamaru da Nijar da Chadi da wasu ƙasashen cikin mutunci. Kwamishinan hukumar kula da ’yan gudun hijira ta Nijeriya, Alhaji Tijjani Ahmed ne ya bayyana haka a zantawarsa da manema labarai a Abuja. Matakan da gwamnonin Arewa suke so a ɗauka kan matsalar tsaron yankin An kama matashi da kawunan mutanen a Legas Ya ce akwai aƙalla ’yan Nijeriya miliyan shida da ke zaman gudun hijira a cikin ƙasar, sannan akwai wasu dubbai da suke zaune a wasu ƙasashen na duniya. “Akwai ’yan Nijeriya 15,000 da suke so su dawo da kansu; haka kuma muna da ’yan ƙasashen waje aƙalla...
      Sai dai a cikin takardar murabus din, Edema ya bayyana rashin tsarin jam’iyyar a matsayin dalilin da ya sa ya fice daga jam’iyyar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana fuska biyu na kasashen yamma, dangane da shirin magakamashin nukliya na kasarsa, da kuma yadda basa magana kan makaman nukliya wanda HKI take da su. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a jiya Asabar, a birnin Doha na kasar Qatar a inda yake halattan taron JMI da kasashen larabawa a jiya Asabar. Ministan ya kara da cewa, wannan rashin adalci ne a fili sannan nuna fuska biyu, Iran wacce babu tabbas kan shirinta na makamashin nukliya na soje ne, an cika duniya da cewa tana son ta mallaki makaman nukliya amma ga HKI wacce aka tabbatar da cewa tana da makaman na nukliya, babu...
    Jakadan JMI a MDD ya musanta zargin kamfanin dillancin labaran reuters dangane da rotohonsa na cewa JMI tana aika makamai masu linzami zuwa kasar Rasah don taimakawa kasar Rasha yakin da take fafatwa da kasar Ukraine fiye da shekaru 3 da suka gabata. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Ofishin jakadancin JMI dake birnin NewYork ya kara da cewa, abin mamaki da kamfanin dilancin laraban reuters, shi ne ba wannan ne karo na farko yake yada labaran karya a duniya wanda wai yake samu daga wasu wadanda basa son a bayyana sunansu. Kafin haka dai JMI ta sha nanata cewa bata bayan wani bangare daga cikin bangarori biyu da suke fafatawa a kasar Ukraine. Don haka bata...
    Manistan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya gana da tokwaransa na kasar Saudiya Faisal Bin Farhan a birnin Jeddah inda bangarorin biyu suka tattauna kan al-amuran da suka shafi yankin, musamman batun Falasdinawa da kuma halin da suke ciki musamman a yankin gaza. Inda HKI take kashesu da yuwan,  sannan tana ci gaba da rusa gidajensu a yankin yamma da kogin Jordan. Har’ila yau, kasashen biyu a matsayin manya-manyan kasashen a yankin yammacin Asiya sun yi kokarin kyautata dangantaka a tsakaninsu. Kuma Aragchi ya je kasar ta saudiya ne don kyautata dangantaka tsakanin kasashen biyu da kuma zurgaga al-adu da al-amura da suka hada kasashen biyu daga ciki har da kasancewarsu kasashe musulmi. A wani bangare Aragchi ya fadawa...
    A jawabinsa a wajen tarbar Jirgin Ruwan na na yankin Asia Jim Stewart, ya bayyana jin dadinsa ga Hukumar ta NPA, bisa goyon bayan da ta bayar wajen samar da kyakyawan yanayi a babban wajen da Jiragen Runwan na Tashar Onne suke tsayawa. “Muna da kyakaywar dangantakar gudanar da ayyuka da Manajan Tashar ta Onne Mista Abdulrahmon Hussain da kuma sauran ‘yan tawagar Hukumar ta NPA, “Inji Stewart. Ya ci gaba da cewa, a karkashin shugabancin shugaban Hukumar ta NPA Dakta Abubakar Dantsoho, wanda kuma kashin bayan duk wata nasara da muka zamu. “Sake farfado da babban wajen tsayawar Jiragen Ruwan a Tashar Onne, hakan ya kara mana kwarin Guiwa”. A cewar Stewart. Kazalika, Stewart ya yi kira ga Gwamnatin...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Dole ne duniya ta dauki matakin kalubalantar laifukan ‘yan sahayoniyya da magoya bayansu kan zaluncin Gaza Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, yayin da yake karbar bakwancin dimbin ma’aikata a yau Asabar, a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan “Makon ayyuyka da Ma’aikata” ya bayyana cewa: A yau duniya ta shaida yadda ake daukar manufofin son zuciya kan wasu kasashe. Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ci gaba da cewa daga cikin wadannan manufofi na son zuciya da ake aiwatarwa a yau akwai kokarin mantar da al’umma batun da suka shafi Falasdinawa, yana mai cewa: Kada al’ummar musulmi su kuskura wannan kyale hakan ya faru, domin ko dan...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Amfanin da fira ministan gwamnatin mamaya ya yi da ƙungiyar ta’addanci babbar alama ce ta cikakkiyar yanke ƙauna Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Matakin da fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya dauka na yi amfani da wata karkatacciyar kungiyar ta’addanci ta “MKO” wato kungiyar Munafukai wajen yada labaran karya game da shirin makamashin nukiliyar Iran, don tsoratar da al’ummar duniya kan Iran, wata babbar alama ce ta yanke kauna. A sakon da ya wallafa shafinsa na X ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa: Yayin da ake ci gaba da zaman tattaunawa ba na kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka, ana...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran yayi Allah wadai da harin da aka kai kan ginin ofishin jakadancin kasarsa da ke Stockholm na kasar sweden Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya yi Allah wadai da harin da aka kai ofishin jakadancin Iran da ke Stockholm tare da yin kira ga gwamnatin Sweden da ta dauki mataki mai tsanani kan wadanda suka kai harin. A yayin wata tattaunawa ta wayar tarho tsakanin ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi da ministar harkokin wajen Sweden Maria Malmer Stenergård, bangarorin biyu sun tattauna batutuwan da suka shafi kasashen biyu da kuma na ofishin jakadancin. A yayin tattaunawar, ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya yi Allah wadai da harin da aka kai ofishin...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei  ya fada a yau Asabar cewa: Ma’aikata ne jari mafi muhimmanci na samun zaman lafiya a cikin al’umma da kuma cimma manufar sunan da aka bai wa wannan shekarar na : “Zuba Hannun Jari Domin Yin Kere-Kere.” Ayatullah Sayyid Ali Khamnei wanda ya gana da ma’aikata da su ka fito daga sassan Iran, ya yi ishara da sake bude kamfanoni da dama a zamanin shugabancin Shahid Ra’isi, alhali gabaninsa an rufe su,tare da bayyana hakan da cewa daya ne daga cikin ayyukan da Shahidin ya aiwatar. Jagoran juyin musuluncin na Iran ya kuma bayyana ma’aikatar da cewa, su nekashin bayan kowace al’umma, yana kuma mai yin addu’ar Allah ya ba su...
    Shugaban kungiyar ya yi magana Ibrahim Yusuf Babayo,Shugaban kungiyar  Miyetti Allah masu kiwon dabbobi na kasa ya bayyanawa jaridar karshen mako cewar dukkan hare- haren da ake kaiwa dabbobin da kuma kashesu an sanar da jami’an tsaro daban- daban,da suka hada da Kwamanda na rundunar soja ta,3 kuma kwamandan Operation Safe Haben (OPSH), Manjo- Janar Foluaho Oyinlola,Kwamishinan‘yansanda na Jihar, Emmanuel Adesina,da kuma darekta na bangaren jami’an farin kaya DSS. Ya ce jami’an tsaro da suke a bangaren Karamar Hukuma an kai su can wuraren da aka kai hare- haren domin su ganewa idanunsu yadda lamarin yake. Sa Wa Shanu 110 guba Kamar yadda jagorancin kungiyar MACBAN a Jihar yace,an kashe Shanu a kalla 110 ta hanyar guba a hare- haren...
    BBC ta rawaito cewa, babban abin da ke damun kamfanin na Meta shi ne, yadda al’amarin ya shafi Hukumar Kare Bayanan Sirri ta Nijeriya (NDPC), wanda kamfanin ke zargin karya dokokin kare bayanan sirrin kasar. Baya ga tarar Hukumar FCCPC, hukumar ta NDPC ta ci tarar kamfanin Meta dala miliyan 37.8, bisa zargin satar bayanan sirri, yayin da hukumar kula da tallace-tallace (ARCON) ta fitar da wani hukuncin daban na dala miliyan 37.5, kan abin da ta kira da cewa, tallan da ba a ba da damar aiwatar da shi ba.    Daga cikin ka’idojin da ake da su, akwai bukatar kamfanin na Meta ya samu izini kafin tura bayanan ‘yan Nijeriya zuwa kasashen waje, yanayin da kamfanin ke ganin “ba...
    Kamfanin man fetur da gas na kasar Iran zai fara aikin nema da hakar man fetur a tekun Caspian da ke arewacin kasar, wanda mataki ne na ci gaba ga kamfanin musamman a halin da ake ciki. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto jami’an kamfanin na cewa tuni sun kai kayakin aiki zuwa wuraren da suke zata akwai danyen man fetur a cikin tekun, sannan a shirye suke su fara aiki don hakar man daga yanzun. Ba wannan ne karon farko wanda gwamnatin kasar Iran take hakar danyen man fetur a cikin tekun Caspian ba, saboda a shekara ta 1997 ne ta dakatar da hakar mai daga gabar tekun, sannan ta dakatar da hakar man a tsakiyar...
    Janar Hussain Salami babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran ya kaddamar da sabon sansanin jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa na karkashin kasa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Janar Salami yana cewa, wadannan jiragen yakin da ake sarrafasu daga nesa, suna iya daukar hotunan jiragen yakin Amurka wadanda suka kasance sansanin jiragen saman yaki na kasar wadanda suke cikin tekuna, don amfani da hotunan saboda kai wa sansanin hare hare. Salami yace gabatar da wannan sansanin gargadi ne ga mjakiya, sannan duk wata kasa a yankin wacce ta bar Amurka ta yi amfani da dandanin sojojinta da ke kasar don kaiwa kasar Iran hare0hare kasar ma ta zama filin daga....
    Dakarun Yeman sun sanar da sake kai hari kan filin jirgin saman Isra’ila na Ben Gurion da ke kusa da birnin Tel Aviv da makami mai linzami mai linzami. Bayanai sun ce ko wannan karo tsarin garkuwa daga hare haren sama na Amurka samfarin THAAD ya gaza kakkabo harin. Sanarwar da rundunar ta fitar ta hannun mai magana da yawunta Birgediya Janar Yahya Saree ta bayyana cewa, an kai harin ne yau Juma’a. Kakakin rundunar ‘yan Houthi Yahya Saree ya ce, sun yi amfani da makami mai linzami mai gudun tsiya,” Isra’ila dai ta sha alwashin mayar da martani mai karfi kan harin. Kasar Yemen dai na mai kai hari kan kaddarorin Isra’ila domin nuna goyan baya ga al’ummar Gaza...
    A wani lokaci a gobe Asabar ne ake sa ran ministan harkokin wajen Iran zai fara wata ziyara a kasashen Saudiyya da kuma Qatar. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa, ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi zai ziyarci Saudiyya da Qatar a, bayan rahotannin da ke cewa akwai yiwuwar yin wata sabuwar tattaunawa tsakanin Tehran da Washington. M. Baghai ya bayyana cewa ziyarce ziyarce da Araghchi zai yi na daga cikin manufofin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na ci gaba da karfafa alakarta da makwabtanta. “Ministan harkokin wajen kasar ta Iran, zai fara tafiya birnin Riyadh don ganawa da manyan jami’an Saudiyya, sannan kuma zai tafi Doha don halartar taron tattaunawa tsakanin Iran da kasashen Larabawa.” Bayanin hakan ya...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa, Hamas, ta yi kakkausar suka kan rufe makarantu guda 6 na MDD da Isra’ila ta yi a yammacin gabar kogin Jordan, tare da bayyana hakan a matsayin keta dokokin kasa da kasa  ranar Alhamis 8 ga watan Mayu, Hamas ta bayyana cewa harin da aka kai kan makarantun hukumar agaji ta MDD UNRWA da ke birnin Quds da aka mamaye, da kuma rufe su da aka yi bayan korar dalibai da malamai da aka yi, ya zama harin kai tsaye ga daukacin tsarin MDD da cibiyoyinta. Sanarwar da kungiyar Hamas ta fitar ta ce, irin wadannan matakai na aikata laifuka wani bangare ne na yakin da gwamnatin Isra’ila ke yi da wanzuwar Falasdinu da kuma asalinsu. Don...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce za a gudanar da zagaye na hudu na tattaunawa tsakanin Iran da Amurka ranar Lahadi. Araghchi ya bayyana a yau Juma’a cewa Oman ce, zata kasance mai shiga tsakani, kuma ita ce ke tantance lokaci da wurin da za a yi tattaunawar. Ya kara da cewa bisa ga dukkan alamu kasar Oman ta tattauna da bangaren waccen bangaren. Babban mai shiga tsakani na Iran ya jaddada cewa tattaunawar Tehran da Washington tana ci gaba. Iran da AMurka dai sun yi jerin tattaunawa har guda uku a Oman, sannan a Italiya sai kuma a Oman. Dukkan bangarorin dai sun bayyana tattaunar da mai kyakyawan fata.
    Kasashen NIjar da Iran sun cimma yarjejeniyar fahimtar juna a tsakaninsu a bangarori da dama. Bangarorin sun sanya hannu a yarjejeniyar ne a yayin ganawar data wakana tsakanin ministan harkokin cikin gida da tsaron jama’a da wata tawagar Iran karkashin jagorancin babban kwamandan rundunar tsaron kasa Birgediya Janar Ahmad Rezaei RADAN. A yayin wannan zama Nijar da Iran sun amince da kafa kwamitin kwararru domin yin musayar ra’ayi lokaci-lokaci da karfafa hadin gwiwa. Nijar da Iran, sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da nufin karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu, musamman a fagen yaki da ta’addanci, da manyan laifuffukan kasa da kasa, tsaron iyakoki, da kuma shige da fice ba bisa ka’ida ba.
    Matsalar wutar lantarki a asibitoci a Najeriya ta jefa marasa lafiya cikin halin ni-’yasu, lamarin da ke kara ta’azzara halin da majinyata ke ciki, har ta kai ga asarar rayuwa. Rashin wuta ya yi sanadin mutuwar jariri a cikin wata mai juna biyu, wata ta yi awa 15 tana jiran a yi mata tiyatan haihuwa, wata kuma ta mutu sakamakon dauke wuta a yayin da ake tsada da yi wa mata tiyata, a Asibitin Jummai Babangida Aliyu, da ke jihar Neja. ’Yan uwa sun shaida wa wakilinmu cewa an shafe sama da kwana uku a jere babu wutar lantarki a asibitin gwamnatin, a yayin da rashin wuta da yanayi na tsananin zafi ya tilasta wa ’yan uwan majinyata amfani da...
    A jiya Alhamis ne dai majami’ar Roman Katolika ta sanar da zabar Robert  Farncis wanda ya zabi sunan Leo 14,a matsayin shugabanta. Zabar Robert Francis a matsayin Paparoma na 267 ya zo ne bayan kwanabi 2  da manyan malaman addinin majami’ar Roman katolika su ka dauka suna yin zaben.  A bisa al’adar majalisar, farin hayaki yana fitowa daga saman majami’ar da yake nuni da cewa an zabi sabon Paparoman, da hakan ya sa a ka rika kada karaurawa a cikin maja’mi’un birnin Roma. Sabon Paparoman  dan shekaru 69 ya zabarwa kansa sunan  Leo 14 domin sake dawo da aiki da kyawawan halaye a cikin harkokin tafiyar da majami’ar kamar yadda Leo na farko ya yi a 1878 zuwa 1903.
    Kwamandan dakarun kare juyin musulunci na Iran Janar Husaini Salami ya bayyana cewa; Dangane da Shirin Nukiliyar Iran, muna bai wa diplomasiyya fifiko, amma kuma a lokaci daya muna cikin Shirin fuskantar kowane irin yaki duk yadda ya zo. Janar Salami wanda ya gabatar da jawabi a wurin karrama shahidan yi wa kasa hidima, a hubbaren Imam Ridha ( a.s) ya kuma kara da cewa;  Ya kamata Amurkawa su kwana da sanin cewa, idan su ka yi mana barazana, to a shirye muke domin fuskantar kowane irin yaki, a duk yadda ya zo. Kwamandan dakarun kare juyin juya halin musuluncin na Iran ya kuma zargi Amrukawa da cewa su, ba masu cika alkawali ba ne, saboda yadda su ka yi...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa akwai bukatar kasashen Indiya da Pakisatan su daure su daina musayar wuta a tsakaninsu saboda tabbatar da zaman lafiya a yankin Asiya. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a safiyar yau Alhamis bayan isarsa birnin News Delhi. A jiya larabace sojojin kasar Indiya suka cilla makamai masu linzami kan kasar Pakisatan da kuma yankin Kashamir da ke karkashinn ikon Pakisatn. Inda mutane 31n sauka rasa rayukansu a yayinda wasu 46 suka suka ji Rauni. Shehbaz Sharif firai ministan kasarPakisatan ya bayyana cewa kasar Pakisatan zata rama, kuma ya sha alwashin maida martani kan duk wani jinin mutanen Pakisatan da sojojin Indiya suka zubar....
    Wasu yan jaridu masu bincike a kasar Amurka sun gano sunan sojan HKI wanda ya bindige yar rahoton tashar Aljazeera ta kasar Qatar a shekara ta 2022 a lokacinda take Shirin bada rahoton hare-harenn da sojojin yahudawan suke kaiwa kan wata unguwa ta Falasdinawa a birnin Jenin na yankin yamma da Kogin Jordan. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto wadanda suka shirya film na tattara bayanai yadda aka kashe Shirin Abu Akela wato ‘ Zeteo’ dake da cibiya a birnin Washington na kasar Amurka na cewa sunan sojan HKI ta ya kashe Shirin shi ne Alon Skajio, wanda shima daga baya an kashe shi a birnin na Jenin daga bayan a wani farmakin da sojojin yahudawan suka...
    A yau ne aka bude kasuwar baje koli na kayakin da suka shafi man fetur da gasa wadanda aka kera a JMI karo na 29  a yau a nan birnin Tehran. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa kasuwar zata ci ne daga yau 8-11 ga wannan watan na mayu da muke ciki. Labarinn ya kara da cewa kamfanoni fiye da 2000 daga ciki da kuma wasu kasashen duniya  14 ne suka halarta ta. Baje kolin yana nuna matsayin JMI a fagen makamashi a duniya.
    Gwamna Soludo zai shirya babban taron girmamawa domin tarbi shugaban ƙasa kafin ya dawo Abuja daga bisani. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Tawagar jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal ta haɗa da sakataren gwamnatin jihar, da masu ba da shawara na musamman guda biyu, da babban sakataren ZITDA, tare da Siobhan Wilson, shugaban Oracle na Ingila da kuma babban mataimakin shugaban EMEA.   Sanarwar ta ƙara da cewa: “Gwamnatin jihar Zamfara ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya mai muhimmanci tare da Oracle don bunƙasa fasahar dijital a faɗin jihar, wanda aka samu ta hanyar Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta Zamfara (ZITDA), haɗin gwiwar za ta yi amfani da ƙwarewa da ayyukan koyo na makarantar Oracle da jami’ar Oracle a ƙoƙarinsu na kawo sauyi. “Haɗin gwiwar yana nuna sadaukar da kai ga ilimi da saka hannun jari a makomar matasan Zamfara,...
    Houthis sun kai hari kan babban filin jirgin sama na Isra’ila kusa da Tel Aviv a ranar Lahadi, a wani ɓangare na yaƙi da ‘yan tawayen ke yi kan Isra’ila, a matsayin tallafin ga Falasdinawa a Gaza. Iran ta musanta cewa ta goyi bayan Houthis a harin. Duk da haka, Isra’ila ta mayar da martani kan Houthis tare da kai hare-hare kan filin jirgin sama na babban birnin Sana’a da ke hannun ‘yan tawayen da kuma tashoshin wutar lantarki a kewayen birnin. Amurka da Houthis sun cimma yarjejeniyar sasantawa, kamar yadda Oman ta sanar a ranar Talata, inda ta ce yarjejeniyar za ta tabbatar da ” ‘yancin kewayawa” a cikin bahar maliya, inda ‘yan tawayen suke kai hare-hare kan jiragen...
    Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta yi tsokaci kan jita-jitar cewa: Shugaban kasar Iran zai gana da shugaban kasar Amurka Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya yi watsi da jita-jitar da ake yadawa game da batun cewa shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian zai yi wata ganawa da shugaban Amurka Donald Trump a mako mai zuwa, da rashin gamsuwar bangaren Amurka da Iran da shiga tsakanin masarautar Oman, da kuma cewa Iran ta gabatar da shawarar gudanar da shawarwari kai tsaye da Amurka, da sauran da’awar karya a matsayin batutuwa na jita-jita maras asali da tushe. Dangane da wata tambaya game da jerin jita-jita da ake yadawa a kafafen yada labarai game da matsayin tattaunawar da ake yi tsakanin Iran...
    Kakakin gwamnatin kasar Iran ta bayyana cewa: Duk wanda ya canza sunan Tekun Fasha, tabbas ya jahilci tarihin dubban shekaru na Iran Mai magana da yawun gwamnatin Iran Fatimah Mohajerani ta yi tsokaci kan rahotannin da suke cewa: Shugaban Amurka Donald Trump na yunkurin sauya sunan yankin tekun Fasha. Ta jaddada cewa “wadanda ke neman canza sunan Tekun Fasha ba su fahimci tarihin dubban shekaru na Iran ba.” Malama Mohajerani ta rubuta a dandalin na X cewa: Tekun Fasha bai takaita da kasancewa sunan yanki kadai ba, a’a ya zama wani muhimmin bangare na tarihin al’ummar Iran. Ta kara da cewa: “Wadanda ke neman canza sunan ‘Tekun Fasha’ ba su fahimci tarihin Iran na dubban shekaru ba. Wannan yunkuri na...
    Kasar Yemen ta jaddada cewa: Ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen kai munanan hare-hare kan Amurka idan ta dawo da kai hari a kan kasarta Sojojin Yemen sun sanar da aiwatar da hare-haren soji guda uku kan tashar jiragen sama na Ramon, wani muhimmin wuri ne na makiya yahudawan sahayoniyya, da a wurin akwai jirgin ruwan Amurka Truman mai dauke da dauke da jiragen saman yakin Amurka da kuma wasu kayayyakin yakinta. Majiyar sojojin Yemen ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa, sojojin samanta sun gudanar da ayyukan soji guda biyu, na farko a kan filin jirgin saman “Ramon” na haramtacciyar kasar Isra’ila da ke yankin Umm al-Rashrash a kudancin kasar Falasdinu da aka...
    Falasdinawa da dama ne suka yi shahada tare da jikkata sakamakon hare-haren bama-bamai da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan wani gidan abinci da wata shahararriyar kasuwa a Gaza Akalla Falasdinawa 20 ne aka kashe tare da raunata wasu da dama a jiya Laraba a wani sabon kisan kiyashi da jiragen saman yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai a wani gidan cin abinci na kasar Thailand da wata shahararriyar kasuwa a yammacin birnin Gaza. Sannan suka ci gaba da kai wasu hare-haren wuce gona da iri kan yankunan zirin Gaza a rana ta 213 a jere. Majiyoyi watsa labarai a Gaza sun rawaito cewa: Jiragen saman yakin mamayar Isra’ila sun kai wani hari kai tsaye kan gidan cin abinci...
    Fira ministan kasar Siriya ya bayyana cewa: Kasar Siriya zata gudanar da tattaunawa ba na kai tsaye ba da haramtacciyar kasar Isra’ila! Shugaban gwamnatin rikon kwarya na kasar Siriya Abu Mohammed al-Julani ya sanar a jiya Laraba cewa: Kasar Siriya zata gudanar da zaman tattaunawa ba na kai tsaye ba da gwamnatin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila ta hanyar masu shiga tsakani domin kwantar da hankulan al’amura da kuma hana bullar rashin kwanciyar hankali a yankin. Al-Julani ya yi nuni da cewa: “Shisshigin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi ba bisa ka’ida ba ne, kuma sun bayyana cewa: Siriya ta amince da yarjejeniyar kawo karshen rikici ta shekara ta 1974,” yana mai cewa “Tsarin mulkin kasar Siriya zai tantance ‘yancin...
    Burin Arsenal na lashe gasar UEFA a karon farko a tarihinta ba zai cika a wannan shekarar ba, sakamakon rashin nasarar da ta yi a hannun PSG a wasan zagayen na kusa da na karshe, Arsenal ta buga wasan karshe a UEFA sau daya a shekarar 2006 tsakaninta da Barcelona. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Sumaila, tsohon mataimaki na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harkokin majalisar dokokin kasar, ya bayyana jam’iyyar NNPP a matsayin “jam’iyyar da ke da rabe-rabe da tabarbarewar al’amura, inda ya ce, rikicin da ya dabaibaye Jam’iyyar a fili yake babu mai musantawa, wadanda suka hada da shari’o’i a kotuna da dama da kuma gwagwarmayar shugabancin jam’iyyar.”   A karshe, Sumaila ya kafa uzuri a karkashin doka ta 42, inda ya bayyana godiyarsa ga takwarorinsa da jama’ar mazabarsa, inda ya yi alkawarin kara zage damtse wajen gudanar da ayyukansa na ‘yan majalisu domin yi wa kasa hidima. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku....
    Ayatullah Sayyid Ali Khamnei wanda ya aike da sako zuwa wurin taron tunawa da cikar  shekara 100 daga kafuwar cibiyar koyar da addinin musulunci ta “Hauza” wanda aka yi a yau a birnin Kum, anan Iran, ya bayyana cewa: Aiki mafi muhimmanci na makarantar addini shi ne isar da sakon addinin musulunci domin gina sabon ci gaba na addinin musulunci. Jagoran juyin musuluncin na Iran ya kuma bayyana cewa da akwai ayyuka masu yawa da suke na cibiyar koyar da addinin musulunci ta Hauza ne da sun kunshi bayar da jawabi akan sabbin batutuwa na zamani da suke bijirowa,  ruhin ci gaba, tsarkake zukata, da kuma siffa ta juyin juya hali.” Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya kuma bayyana cewa daga...
      Rundunar sojan Ruwan Amurka ta sanar da cewa; Jirgin sama samfurin F-18 wanda kudinsa ya kai dalar Amurka miliyan 67 ya fadi akan jirgin dakon jiragen ruwa na ” USS Harry Truman” a tekun “Red Sea”. Jaridar ” Washington Post” ta buga labarin dake cewa; Jirgin ta fado ne a lokacin da yake kokarin sauka akan doron jirgin ruwan dakon jiragen saman na ” USS Harry Trauman”. Sanarwar ta kuma kara da cewa; Matuka jirgin sun fice daga cikinsa ta hanar lema, kuma an tserato da su daga cikin ruwa ta hanyar jirgi mai saukar angulu. Matukan, kamar yadda sanarwar ta sojojin na Amurka, sun ji rauni. Wani jami’in soja wanda ya bukaci a sakaya sunansa  ya fada wata kafar...
    Assalamu alaikum masu sauraro sharhin bayana labarummu na yau zai yi magana dangane da ‘Mahangar Jumhuriyar Musulunci na Iran ta yadda za’a kai ga fahintar juna a tattaunawanta da kasar Amurka da suke yi wanda ni tahir amin zan karanta. Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi a wata tattaunawa ta wayar tarho da tokwaransa na kungiyar tarayyar turai wato Kaja Kallas, ya bayyana mata yadda bangarorin Amurka da Iran za su kai ga cimma yarjeniya dangane da shirin makamashin nukliya na kasarsa. Ministan ya kara da cewa tun kimani shekaru 20 da suka gabata ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran bangaren tattaunawa dangane da shirin nukliyar kasar ta zaman lafiya. Kuma batun shirin nukliyar kasar Iran tana daga cikin ayyuka...
    Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya yi zargin cewa sojoji da sauran jami’an tsaro na bayar da gudunmawar aikata miyagun laifuka da cin zarafin jama’a a Nijeriya. Zulum ya faɗi hakan ne yayin da yake haramta sayar da barasa a birnin Maiduguri da kewaye. Ka-ce-na-cen da ya biyo bayan ziyarar Tinubu a Katsina DAGA LARABA: Ɓoyayyun Dalilan Da ke Sa Faɗuwa Jarabawa A Najeriya Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Talata a wajen ƙaddamar da wani kwamitin da aka kafa don “ƙwace haramtattun otal-otal da gidajen karuwai da gidajen kwana da maɓoyar miyagun laifuka da kuma daƙile illolin munanan ɗabi’u. Gwamnan ya ce tsofaffin jami’an tsaron Nijeriya da na yanzu da suke aiki sun taka rawa wajen jawo...
    Kasashen duniya na ci gaba da nuna matukar damuwa game da rikicin da ya barke tsakanin Pakistan da Indiya. Iran na daga cikn jerin kasashen da a baya bayan nan suka nuna damuwa. Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Iran ta fitar ta ce “Jamhuriyar Musulunci ta bayyana matukar damuwarta kan yadda takun saka tsakanin Indiya da Pakistan ke ci gaba da ruruwa. Iran ta ce a matsayinta na kasa mai iyaka da Pakistan wacce kuma ke da kyakkyawar alaka da Indiya, ta yi tayin shiga tsakani a rikicin tun cikin watan Maris. Kasar Turkiyya ma ta yi gargadin game da rikicin. Inda a wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta fitar ta yi Allah wadai da hare-haren da ake...
    Gwamnatin Sudan ta katse dangantakar diflomasiyya da (UAE), bisa zarginta da goyan bayan dakarun RSF. A cikin jawabin da aka watsa a talabijin, Ministan Tsaron Sudan, Yassin Ibrahim ya bayyana cewa Sudan ta “katse dangantakar diflomasiyya da UAE,” tare da janye jakadanta da rufe ofishin jakadanci da konsulat dinta a kasar . Da yake magana a gidan talabijin na gwamnatin kasa, ministan tsaron Sudan, Yassin Ibrahim Yassin, ya zargi Abu Dhabi da keta hurumin ‘yancin Sudan ta hanyar mara baya ta fuskar soji ga RSF, ciki har da samar da makamai, da jiragen yaki marasa matuka, da makamai masu linzami wadanda aka kai hari da su a baya-bayan nan a tashar jiragen ruwa, da filin jiragen sama, da kuma tashoshin...
    Kungiyar gwagwarmaya ta Ansarullah ta bayyana cewa yarjejeniyar tsagaiat wutar da ta cimma da Amurka, ba ta sauya matsayin kasar ba na kai wa Isra’ila hari. Kakakin kungiyar Ansarullah Mohammed Abdul-Salam ya jaddada cewa Dakarun Yeman za su ci gaba da kai hare-hare kan Isra’ila domin goyan bayan Falasdinawa a zirin Gaza. Yarjejeniyar da Amurka ba ta da alaka da matsayinmu na goyan bayan Gaza, inji Abdul-Salam. A jiya ne masarautar Oman ta sanar cewa Amurka da kungiyar Ansarullah da aka fi sani da ta ‘yan Houtshis a Yeman suka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta. Ma’aikatar harkokin wajen kasar Oman ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa: Bayan tattaunawa da tuntubar juna da aka yi a baya-bayan...
    Gwamnatin Sudan da ke da goyon bayan sojoji ta katse dangantakar diflomasiyya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE), tana bayyana ƙasar a matsayin mai katsalandan, a cewar Ministan Tsaron Sudan, Yassin Ibrahim. A cikin jawabin da aka watsa a talabijin ranar Talata, Ibrahim ya bayyana cewa Sudan ta “katse dangantakar diflomasiyya da UAE,” tare da janye jakadanta da rufe ofishin jakadanci da konsulat ɗinta a ƙasar Gulf ɗin. Dalilin faɗuwar ɗalibai a jarabawar JAMB bana — Ministan Ilimi Inter Milan ta kori Barcelona daga Gasar Zakarun Turai Ya zargi UAE da take hurumin Sudan ta hanyar “ƙawarta”, wato Rundunar RSF, wacce ke yaƙi da sojojin Sudan tun watan Afrilu 2023. “Dukkan duniya ta shaida, fiye da shekaru biyu, laifin kai hari...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa; Ana nazarin lokacin gudanar da zagaye na huɗu na shawarwari tsakanin Iran da Amurka Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya sanar da cewa: Ana nazari kan lokacin gudanar da zagaye na gaba na tattaunawar Iran da Amurka wand aba na kai tsaye ba, kuma mai shiga tsakani na Oman zai sanar da karin bayani da zarar an tantance lokaci da wurin da za a yi. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya shaidawa kamfanin dillancin labaran kasar Iran cewa: Ana duban lokacin da za’a gudanar da zagaye na gaba na tattaunawa tsakanin Iran da Amurka. Baqa’i ya kara da cewa: Mai shiga tsakani na Oman zai sanar da bayanai...
    Inter Milan ta samu nasarar tankaɗo Barcelona daga Gasar Zakarun Turai, lamarin da ya ba ta damar kaiwa zagayen ƙarshe na gasar ta bana. A daren wannan Talatar ce aka buga wasa falle na biyu a zagayen kusa da na ƙarshe a Gasar Zakarun Turai ta bana tsakanin ƙungiyoyin biyu. ‘Raini ne ya sa ake ƙalubalantar yunƙurin kafa ƙungiyar Hausawa zalla’ Majalisar Dattawa ta kafa kwamitin lura da gwamnan riƙo na Jihar Ribas Inter Milan ce ta yi nasarar doke Barcelona da ci 4-3 a filin wasanta na San Siro da ke Italiya, bayan a makon jiya sun yi kunnen doki 3-3 a Nou Camp da ke ƙasar Sifaniya. A wasan na yau da aka barje gumi har tsawon mintuna...
    Inter Milan ta samu nasarar tankaɗo Barcelona daga Gasar Zakarun Turai, lamarin da ya ba ta damar kaiwa zagayen ƙarshe na gasar ta bana. A daren wannan Talatar ce aka buga wasa falle na biyu a zagayen kusa da na ƙarshe a Gasar Zakarun Turai ta bana tsakanin ƙungiyoyin biyu. ‘Raini ne ya sa ake ƙalubalantar yunƙurin kafa ƙungiyar Hausawa zalla’ Majalisar Dattawa ta kafa kwamitin lura da gwamnan riƙo na Jihar Ribas Inter Milan ce ta yi nasarar doke Barcelona da ci 4-3 a filin wasanta na San Siro da ke Italiya, bayan a makon jiya sun yi kunnen doki 3-3 a Nou Camp da ke ƙasar Sifaniya. A wasan na yau da aka barje gumi har tsawon mintuna...
    Majalisar Dattawa ta kafa kwamiti mai mambobi 18 domin sanya idanu kan yadda gwamnan riƙo na Jihar Ribas Vice Admiral Ibok Ete Ibas mai ritaya ke tafi da aikinsa. Majalisar ta ce ta ɗauki matakin ne a wani yuƙuri na ƙarfafa shugabanci na gari ba tare da rufa-rufa ba a jihar da ke kudu maso kudancin Najeriya. Alƙaluman sakamakon jarabawar bana — JAMB Friedrich Merz ya zama sabon shugaban gwamnatin Jamus Shugaban Majalisar Dattawan, Godswill Akpabio ya sanar yayin zaman majalisar na yau Talata cewa kafa kwamitin na da matuƙar mahimmancin wajen sa ido kan abubuwan da ke faruwa a jihar. Shugaban masu rinjaye Opeyemi Bamidele ne shugaban kwamatin, yayin da mambobin kuma sun haɗa da Adamu Aliero, da Osita...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa hanyar deblomasiyya ce kadai zata warware matsakar shirin nukliyar kasar iran da kasashen yamma. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a zantawa ta wayar tarho da jami’a mai kula da al-amuran harkokin waje na kungiyar tarayyar Turai Kaja Kallas. Labarin ya kara da cewa ministan yana ganin matsalolin shirin Nucliya da kuma tsaron kasar ba za’a iya warwaresu ba sai ta wannan hanyar. JMI ta dauki wannan hanya ce don ita ce kadai wacce zata kai da gamsuwar ko wani bangare a cikin al-amuran da suke sabani a cikinsu. Aragchi ya fadawa Kallas kan cewa da wannan dalilin ne JMI ta dauki hanyar...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Baghaaei ya bukaci kasashen turai da su shiga a dama da su kan tattaunawa dangane da shirin nukliyar kasar Iran na zaman lafiya. Ya kuma jaddada cewa Iran tana turjiya ga dukkan tunanin Amurka na wargaza shirin Nukliyar kasar Iran kwata-kwata. Baghaei ya kara da cewa duk da cewa Iran a shirye take a ci gaba da tattaunawa kan shirin makamashin nukliyar kasar, da sake farfado da yarjeniyar JCPOA ta shekara ta 2015 amma kuma ba zata taba barin hakkinta na mallakar fasahar nukliya da luma sarrafashi a hanyoyin da yarjeniyar NPT ta amince da su ba. Kuma da alamun tattaunawar tsakanin Amurka da Iran ya daki dutse, saboda sun sami sabani a...
    Mamba a majalisar gudanarwa ta kungiyar Ansarulla ta kasar yemen Muhammad Bukhaiti ya bayyana cewa hare-haren da HKI da Amurka suka kai fararen hula a kasar yemen wuce jan layi, ko ketare haddi ne na kungiyar don haka su jira maida martani mai tsanani. Kamfanin dillancin labaran Iran ya nakalti yana fadawa tsahar talabijin ta Al-mayadeen ta kasar Lenamon a yau Talata.  Ya kuma kara da cewa hare-haren da Amurka suke kaiwa ma’aikatu da wuraren fararen hula a kasar Yemen na baya-bayan nan duk sun nuna cewa an sami nasara a kansu. Albukhaiti ya kara da cewa sadaukarwa da mutanen kasar Yemen suke yi saboda Gaza, ba zai tsaya ba, sannan muna son fadawa kasashen Amurka da ingila da kuma...
    A safiyar yau ne jiragen yakin HKI suka kai hare-hare kan tashar Jiragen sama na birnin San’a na kasar Yemen inda ake ganin hakan kara ruruta wutan yaki a yankin ne. Klamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a dai-dai lokacinda jiragen yakin Amurka suka dauki kimani watannin biyu suka kai hare hare kan kasar Yemen a yau jiragen yakin HKI sun kai wasu sabbin harehare a kan birnin san’a baban birnin kasar. A cikin makon nan ne kungiyar Ansarulla.. ta kai hare hare da makamai masu linzami a kan tashar jiragen sama na bengerio tashar jiragen sama mafi girma, a kasar wanda ta dakatar da tashin jiragen sama na kwanaki sannan wasu dan kadan suka fara...
    Karamar Hukumar Birnin Kdu tace tana nazarin samar da cibiyar horas da maniyyata aikin hajji ta dindindin a yankin domin karawa mahajjata kaimi wajen gudanar da aikin karbabbe.   Shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Muhammad Uba Builder ya bada wannan tabbacin a lokacin rufe bitar da aka shiryawa maniyyatan yankin na Birnin kuudu.   Yana mai cewar, idan aka samar da cibiyar zata kunshi dukkanin muhimman wuraren da ake ziyarta a lokacin gudanar da aikin hajji.   Alhaji Muhammad Uba, yace za a kuma samar da ajujuwan horas da maniyyata da ofisoshin malaman bita da sauran dukkan abubuwan daya dace a cibiyar.   Kazalika, Shugaban Karamar Hukumar, ya biya malaman bitar alawus dinsu na wannan shekarar da ma kwanton na shekarar...
    Friedrich Merz na jam’iyyar CDU ya zama sabon shugaban gwamnatin Jamus. Majalisar Dokokin Jamus ta Bundestag ta zabi Merz a matsayin sabon shugaban gwamnati lokacin zaɓen zagaye na biyu, bayan ya gaza samun ƙuri’un da yake buƙata a zagayen farko na zaɓen. A zaɓen farko Merz ya samu ƙuri’u 325 na jam’iyyun ƙawance daga majalisar mai mambobi 630. Kafin zama shugaban gwamnati ana buƙatar kuri’u 316 kuma jam’iyyar CDU/CSU da kuma jam’iyyar SPD suna da kujerun majalisar 328, fiye da adadin da ake buƙata. Merz zai maye gurbin Olaf Scholz wanda ya faɗi zaɓen ƙasar da aka gudanar a watan Fabrairu Upon announcing the second vote, the head of the Union bloc in parliament, Jens Spahn, said, “The whole of...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    “Mun rufe dukkan sansanonin ‘yan gudun hijira da ke cikin Maiduguri. Yanzu haka saura biyu da ba na hukuma ba. Mun riga mun dawo da kashi 75 na ‘yan sansanin Muna gida, saura kashi 25 za su koma cikin kwanaki masu zuwa.” Kowane iyali sun samu tallafin abinci, kayan gini da kulawar lafiya. Haka kuma, kowane magidanci mace ko namiji za a ba shi Naira 100,000, yayin da matan gidan za su ƙara samun Naira 50,000 don taimaka musu da buƙatunsu na yau da kullum. Za a Ƙara Inganta Cibiyar Koyo Sana’o’i a Gidan Gyaran Hali Tun da safiyar ranar Litinin, Gwamna Zulum ya kai ziyara gidan gyaran hali na manyan laifuka da ke Maiduguri. Ya ce za a inganta...
    Hukumar Kula da Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna za ta fara jigilar maniyyata zuwa kasar Saudiyya a ranar 14 ga watan Mayu, 2025. Shugaban hukumar, Malam Salihu S. Abubakar, ne ya bayyana hakan a wani shirin rediyo kai tsaye da aka watsa daga Kaduna, inda ya bayyana shirye-shiryen da jihar ta kammala domin aikin Hajjin bana. Ya bayyana cewa maniyyata 4,060 daga jihar Kaduna za su sauke farali a bana, kuma kamfanin jirgin sama na UMZA ne zai yi jigilarsu. Shugaban hukumar ya bayyana cewa domin kammala matakan da ake bi kafin tafiya, za a yi duk maniyya cikakken gwajin lafiya a sansanin alhazai da ke Mando. Wata mata ta auri maza biyu a lokaci guda a Kano NAJERIYA...
    EFCC ta ce za ta gurfanar da shi a gaban kotu da zarar ta kammala bincike. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana neman karfafa hadin kai da ‘yan uwantaka da kasashen makwabtanta Shugaban kasar Iran Mas’oud Pezeshkian ya jaddada cewa: “Babban burinsu shi ne neman karfafa hadin kai da ‘yan uwantaka da  makwabtansu, kuma ba su dauke da kiyayya a kansu.” Shugaba Pezeshkian, a jawabin da ya gabatar a gaban taron majalisar kwararru masu zaben Jagoran juyin juya halin Musulunci a Iran a jiya litinin, ya jaddada wajabcin kiyaye hadin kai da hadin kai a cikin kasar da dukkan al’ummar musulmi. Yana mai cewa: “Tare da haɗin kan kasa, za su iya magance dukkan matsalolin cikin gida.” Sannan ya kuma yi kira da a kaucewa duk wani mataki da zai kawo...
    Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da zaluncin ‘yan sahayoniyya a kan kasar Yemen Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi kakkausar suka kan harin wuce gona da iri da sojojin yahudawan sahayoniyya suka kai tashar jiragen ruwa na Hodeidah da sauran ababen more rayuwa na kasar Yemen, yana mai bayyana hakan a matsayin babban laifi da kuma keta ka’idoji da dokokin kasa da kasa. A cikin bayaninsa da sanyin safiyar yau Talata, Baqa’i ya yi nuni da cewa: Hare-haren da ‘yan sahayoniyya suka kai kan tashar jiragen ruwa, da masana’antu, da kuma wuraren zama a kasar Yemen, ana aiwatar da su ne tare da goyon baya da kuma taimakon Amurka. Ya bayyana wadannan hare-haren...
    Jamhuriayar Musulunci ta Iran ta sha alwashin mayar da martani cikin gaggawa ga duk wani kasadan ‘yan Sahayoniyya da Amurka kan kasarta Jakada kuma zaunannen wakilin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’ed Irawani ya jaddada cewa: Duk wani kasadan harin soji da Amurka ko wakilliyarta gwamnatin ‘yan  sahayoniyya suke yi, ko da kuwa wani mataki ne da ya sabawa ‘yancin kai, ko cikakken amincin Iran ko kuma muhimman muradun kasa na Jamhuriyar Musulunci ta Iran, za a mayar da martani cikin gaggawa, da ya dace kuma halastacce. Wannan dai ya zo ne a cikin wata wasika da Amir Sa’ed Irawani, jakada kuma wakilin din-din-din na Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya, ya aikewa babban...
    Tawagar jiragen saman yaki da dama ne suka kai munanan hare-hare kan sassa daban-daban na kasar Yemen a jiya Litinin Kafofin yada labaran kasar Yemen sun rawaito a jiya litinin cewa: Wata tawagar jiragen saman yakin Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai hare-hare kan yankuna daban-daban na kasar Yemen da suka hada da gundumar Bajil da wasu wurare a gundumar Al Hudaydah da ke yammacin kasar ta Yemen, da kuma gundumar Sinjan da ke birnin San’a. Ma’aikatar lafiya ta kasar Yemen ta sanar da cewa: Mutane 21 ne suka jikkata sakamakon hare-haren bama-bamai da aka kai kan masana’antar siminti na Bajel da ke gundumar Al Hudaydah. A nata bangaren, tashar talabijin ta 12 ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta nakalto...
    Falasdinawa fiye da 50 ne suka yi shahada yayin da wani adadi da dama suka jikkata a hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila suka kai Gaza a jiya Litinin Rahotonni sun bayyana cewa: Fiye da Falasdinawa 50 ne aka suka yi shahada wasu adadi da dama kuma suka jikkata sakamakon hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila ke ci gaba da kai kan yankin Zirin Gaza na Falasdinu. Daga cikin hare-haren har da hare-haren da jiragen mamayar Isra’ila suka kai kan wani gini mai yawan jama’a a unguwar Al-Karama da ke arewacin Gaza, wanda ya yi sanadin kisan kiyashi kan mutane ciki har da mata da kananan yara 20 da kuma fararen hula na daban. A wani labarin kuma, Falasdinawa a yankin Al-Karama...
    Ya ce an kama matashin tare da addar da ake zargin ya yi amfani da ita, kuma yanzu ana ci gaba da bincike domin gano dalilin da ya sa ya aikata hakan. “Matashin yana hannunmu, kuma muna ci gaba da gudanar da bincike,” in ji shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban Ghana a wannan Litinin ɗin ya bayyana ɗaukar mataki kan ministoci da sauran masu riƙe da muƙaman siyasa fiye da 40 da suka gaza bayyana kadarorin da suka mallaka. Wannan na zuwa ne a yayin da Shugaba John Mahama ke ci gaba da zage dantse wajen yaƙi da cin hanci da rashawa a ƙasar da ke yammacin Afirka. ’Yan bindiga sun kashe matar aure bayan karɓar N10m kuɗin fansa ’Yan fashi sun kashe matashi a Kano A yayin karɓar rantsuwar kama aiki a watan Janairun bana ne Shugaban Ghana ya sha alwashin yaƙi da rashawa domin fitar da ƙasar daga ƙangin matsalar tattalin arziki A watan Afrilun da ya gabata ne mahukunta suka gurfanar da wani babban jami’in tsaro...
    Assalamu alaikum masu sauraro sharhin bayan labarammu zai yi magana dangane da “Bankasar tattalin arzikin Iran duk tare da takunkuman tattalin arziki masu tsanani wadanda kasashen yamma musamman Amurka suka doramata, wanda ni tahir amin zan karanta. ////…A dai-dai lokacinda gwamnatin kasar Amurka take barazanar zata hana sayan danyen man fetur daga kasar Iran kwatakwata, sannan take barazanar zata farwa kasar da yaki saboda shirin na makamashin nukliya, sabbin rahotanni sun bayyana cewa iran tana gaba a fitar da kayaki kasuwanci zuwa kasar China sannan ita ce ta 9 a duniya wajen samar da kwan kaji da sauran tsuntsaye. Kamfanin dillancin labaran Parstoday na kasar Iran ya bayyana cewa, yawan danyen man fetur wanda kasar Iran take sayarwa kasar China...
    Bisa kididdigar da kamfanin layin dogo na kasar Sin ya fitar, daga fara zirga-zirgar hutun ranar ma’aikata a ranar 29 ga Afrilu zuwa ranar 4 ga Mayu, jiragen kasa na kasar Sin sun yi jigilar fasinjoji miliyan 112, adadin da ya karu da kashi 10.5 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bara, tare da tabbatar da zirga-zirga cikin aminci, kwanciyar hankali da kuma tsari. A yau, yawan fasinjojin da ke kan hanyarsu ta dawowa daga hutun ta jiragen kasa na ci gaba da karuwa, inda a yau ake sa ran za a yi jigilar fasinjoji miliyan 21.1 ta hanyar jirgin kasa na kasar, yayin da ake shirin kara jiragen kasan fasinja 1896 a kan adadin jiragen da...
    ’Yan bindiga sun kashe wata mata da suka sace tare da mijinta Yakubu Dada watanni bakwai da suka gabata a yankin Kontagora da ke Jihar Neja. Aminiya ta ruwaito cewa ’yan ta’addan sun halaka matar mai suna Lami bayan karɓar Naira miliyan 10 kuɗin fansa. ’Yan fashi sun kashe matashi a Kano Kwankwaso: Abba ya mayar wa Baffa Bichi martani Kazalika, ’yan bindigar sun kuma nemi ƙarin Naira miliyan 20 da baburan Bajaj huɗu, tare da yin barazanar kashe mijinta muddin aka gaza kai musu abubuwan da suka buƙata. Aminiya ta ruwaito cewa, tun a ranar 31 ga watan Oktoba na 2024 ne Yakubu Dada da mai ɗakinsa suka faɗa tarkon masu garkuwa yayin da suke kan hanyar zuwa Kontagora....
    Tashar talabijin din HKI ta channel: 12 ta nakalato sojoji suna sanar da kai wa Yemen hare-hare. Sanarwar ta kuma ce; jiragen yakin HKI sun kai hare-hare ne a wurare 9 a lokaci daya da su ka hada da tashar jiragen ruwa ta Hudaidah. Sojojin na HKI sun ce jirage 30 ne su ka kai harin. Haka nan kuma sun ce an kai hare-haren ne sau takwas ba a lokaci daya ba. Daga cikin wuraren da aka kai wa harin har da gidan Bulo.
    Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta yi watsi da zarge-zargen da aka yi ma ta dangane da kasar Yemen.  A wani bayani da ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran din ta fitar ta bayyana cewa: Abinda mutanen Yemen suke yi domin taimakawa al’ummar Falasdinu, mataki ne na kashin kansu da su ka dauka cikin ‘yanci saboda lamirinsu na ‘yan adamtaka da kuma taimako na musulunci ga ‘yan’uwansu Falasdinawa.” Bayanin ya kuma ci gaba da cewa; Jinginawa jamhuriyar musulunci ta Iran abinda mutanen na Yemen suke yi, ba shi da tushe, kuma manufar hakan ita ce, rufe laifukan da ‘yan sahayoniya suke yi a Falasdinu.” Bayanin ya kuma ce; Jamhuriyar musulunci tana sake jaddada matsayarta akan wajabcin kiyaye da karrama kasashe...
    ’Yan fashi sun harbe mafarauta da fararen hula kimanin 19 har lahira a Karamar Hukumar Alƙaleri ta Jihar Bauchi. A yayin ziyarar da ya kai wurin, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Bauchi, Sani-Omolori Aliyu, ya ba da umarnin yin cikakken bincike da kuma tura karin jami’an tsaro yankin. Mazauna kauyen Mansur sun ce an kashe ’yan farauta guda tara da kuma fararen hula guda goma, kuma an yi jana’izar ’yan bangar a kauyen Mansur kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. Amma ’yan sanad da jami’an Ƙaramar Hukumar Alƙaleri ba su ce komai ba kan adadin mamatan ba. Kakakin ’yan sanda na jihar, CSP Ahmed Mohammed Wakil, ya ce kwamishinan ya tattauna da masu ruwa da tsaki a yankin, inda ya buƙaci...
    ’Yan fashi sun harbe mafarauta da fararen hula kimanin 19 har lahira a Karamar Hukumar Alƙaleri ta Jihar Bauchi. A yayin ziyarar da ya kai wurin, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Bauchi, Sani-Omolori Aliyu, ya ba da umarnin yin cikakken bincike da kuma tura karin jami’an tsaro yankin. Mazauna kauyen Mansur sun ce an kashe ’yan farauta guda tara da kuma fararen hula guda goma, kuma an yi jana’izar ’yan bangar a kauyen Mansur kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. Amma ’yan sanad da jami’an Ƙaramar Hukumar Alƙaleri ba su ce komai ba kan adadin mamatan ba. Kakakin ’yan sanda na jihar, CSP Ahmed Mohammed Wakil, ya ce kwamishinan ya tattauna da masu ruwa da tsaki a yankin, inda ya buƙaci...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kotu ta yanke wa wani matashi hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan kan laifin kashe wata karuwa bayan ya yi lalata da ita. Babban Kotun Jihar Ekiti ce ta yanke masa hukuncin bayan an gurfanar da shi kan zargin haɗa baki da kuma garkuwa da matar da kuma amfani da maganin kashe ciyawa wajen halaka ta a ranar 18 ga Afrilun 2024. Tun da farko mai gabatar da ƙara, Ibironke Odetola, ya bayyana wa kotun a ranar 6 ga watan Fabrairu, cewa wanda ake zargin ya haɗa baki d da wani abokinsa wajen sace matar da ke sana’ar kasuwanci. Wanda ake zargin, David Isaiah, mai shekara 26, ya shaida wa kotun cewa bayan ya yi lalata da matar ne ya...
    A yau 5 ga watan Mayu 2025 tsohon Shugaban Kasa Marigayi Umaru Musa ’Yar’adua ya cika shekaru 10 da rasuwa. ’Yar’Adua wanda ya rasu a bayan dogaruwar jinya yana daga cikin daidaikun zaɓaɓɓun shugabannin Najeriya da talakawa ke kewar su, saboda kyakkyawan kamun ludayin mulkinsa. Sai dai kuma an lura cewa shugabannin da suka fi samun irin wannan yabo daga talakawan Najeriya, ba su fiye yin tsawon kwana ba, a kan mulki suka rasu. Zuwa yanzu, shugabannin Najeriya huɗu ne suka mutu a kan mulki, kuma dukkansu daga yankin Arewa. Lakurawa: Yadda mafarauta 13 suka gamu da ajalinsu a Sakkwato NAJERIYA A YAU: Abin da ke kai matasan Najeriya ci-rani wasu ƙasashen Afirka Ya kamata a zuba jari a harkar...
    Iran ta yi kakkausar suka da kakkausar murya kan zargin Amurka da da na Isra’ila suka cewa ta na da hannu a hare-haren ramuwar gayya na kasar Yemen. Iran ta ce zarge zagren basu da tushe balle makama. Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya fada a yammacin jiya Lahadi cewa, matakin da kasar Yemen ta dauka na goyon bayan al’ummar Falasdinu, wani mataki ne mai cin gashin kansa, wanda aka dauka a matsayin goyan bayan Palasdinawa. Babban jami’in diflomasiyyar na Iran ya jaddada cewa, sojojin Amurka ne suka shiga yakin domin tallafawa kisan kiyashin da gwamnatin sahyoniyawa ke ci gaba da yi a zirin Gaza. Don haka Araghchi ya soki Amurka da aikata laifukan yaki ta hanyar kai...
    Kasashen Iran da kuma Saudiyya sun jaddada kiran su na ganin an kare hurumin kasar Siriya tare kuma da yin tir da hare-haren da Isra’ila ke kai wa kasar. Jami’an Iran da Saudiyya sun tabbatar da aniyarsu ta tabbatar da ‘yancin kai da kuma ‘yancin yankin Siriya, tare da yin Allah wadai da harin da sojojin Isra’ila suka kai kan al’ummar kasar Larabawar. An bayyana hakan ne a wata ganawa da aka yi a ranar Lahadi a birnin Riyadh tsakanin Mohammad-Reza Raouf Sheibani, wakilin Iran na musamman kan Syria, da Saud al-Sati, mataimakin ministan harkokin wajen Saudiyya kan harkokin siyasa, a yayin da suke magana kan yadda ake samun sauyin yanayi a kasar Siriya, da kuma mafi girman tasirin hare-haren...
    Iran ta mayar da martani kan zargin da ake mata game da alakar ta da Yemen tana cewa; Taimakon da Yemen ke yi wa Falasdinu hukunci ne mai cin gashin kansa Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fitar da wata sanarwa dangane da zargin da ake yi wa Iran dangane da alakar da ke tsakaninta da kasar Yemen, inda ta yi la’akari da wadannan tuhume-tuhumen a matsayin maimaita zargin karya da nufin karkatar da hankali daga laifukan yahudawan sahayoniyya ‘yan mamaya. A sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta fitar ta ce: Wadannan tuhume-tuhume ne da maimaita zarge-zargen karya da ke alakanta matakan gwagwarmaya da al’ummar Yemen suka dauka na kare kansu da kuma goyon bayan al’ummar Falastinu ga Iran....
    Ministan Tsaron kasar Iran ya jaddada cewa: Za su mayar da martani mai tsanani da karfi kan duk wani ta’addanci da kasarsu za ta fuskanta Ministan tsaron kasar Iran Birgediya Janar Aziz Nasirzadeh, yayin da yake mayar da martani ga barazanar Amurka, ya tabbatar da cewa Iran za ta mayar da martani mai karfi tare da kai hare-hare kan dukkanin wasu muradun Amurka da sansanoninta da suke wannan yankin. Birgediya Janar Nasirzadeh ya kara da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana da tarin makamai masu linzami, kuma idan aka kakaba mata yaki, to za ta yi amfani da su ba tare da bata lokaci ba, ko kuma a duk kan muradun makiya. Ministan ya jaddada cewa: “Ba su da wata...
    Sojojin Yemen sun sanar da killace sararin samaniyar Falasdinawa da yahudawan sahayoniyya suka mamaye Sojojin Yemen sun sanar a yammacin jiya Lahadi cewa: Za su kakaba wa haramtacciyar kasar Isra’ila cikakken takunkumi ta sama, yayin da kamfanonin jiragen sama na kasa da kasa suka yi gargadin hadarin da ke tattare da zirga-zirga daga filayen jiragen saman yankunan Falasdinawa da aka mamaye. Wannan dai na zuwa ne a matsayin martani ga karuwar hare-haren da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke kai wa a zirin Gaza. Kakakin rundunar sojin Yemen, Birgediya Janar Yahya Sari’e, ya ce za su kakaba takunkumin ne ta hanyar kai hare-hare akai-akai kan filayen jiragen saman haramtacciyar kasar Isra’ila, musamman filin jirgin sama na Ben Gurion. Sanarwar ta yi...
    Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa: Gaza na gaf da afkawa cikin babbar masifa saboda zaluncin ‘yan mamayar Isra’ila A yayin da gwamnatin mamayar Isra’ila ke ci gaba da killace Zirin Gaza sama da watanni biyu, abubuwan da ke faruwa a kowace rana, abubuwa ne da suke yadda bala’i ke shafar kowane gida, kowane titi, da kowane yaro, tare da cewa a kowace rana, ana kara gargadin cewa; Lokaci ya fara kurewa don ceton abin da za a iya cetowa. Ofishin yada labarai na gwamnati a Gaza ya sabunta gargadi game da bala’in da ke tafe saboda ci gaba da rufe mashigar yankin da kuma tsaurara matakan hana shigowa da madarar jarirai, da abinci mai gina jiki, da kuma...