2025-11-22@00:17:12 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3990

«mafarauta»:

    Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin Jihar Jigawa ta tabbatar da bada cikakken goyon bayanta ga Kwalejin Aikin Noma ta Gwamnatin Tarayya da ke Kirikasamma. Gwamna Umar Namadi ya bayar da wannan tabbaci ne lokacin da ya karɓi tawagar gudanarwar kwalejin ta farko, ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Dr. Muhammad Yusha’u Gwaram, yayin ziyarar girmamawa da suka kai...
    Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe makarantun kwana 47 da ke faɗin Najeriya. Gwamnatin ta ɗauki wannan mataki ne bayan hare-haren da ’yan bindiga suka kai makarantu a jihohin Kebbi da Neja, inda suka sace ɗalibai da ma’aikata, suka kashe mutum ɗaya. Atiku ya nemi a ayyana dokar ta-ɓaci kan satar ɗalibai a Najeriya...
    Majalisar Dokokin Jihar Kano, ta wanke Shugaban Ƙaramar Hukumar Rano da aka dakatar, Alhaji Naziru Yau, daga dukkanin zarge-zargen da aka masa. Wannan ya ba shi damar komawa bakin aikinsa da shugabancin Ƙaramar Hukumar Rano. An kama Faston da ake zargi da yi wa mambobin cocinsa 3 fyade ’Yan bindigar da suka sace masu ibada...
    Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF) sun nuna damuwarsu kan sace malamai da ɗaliban makarantar St. Mary’s da ke Ƙaramar Hukumar Agwara, a Jihar Neja. Sun ce wannan lamari babban hatsari ne ga rayuwar yara da makomar ilimi a yankin Arewa baki ɗaya. DSS ta mayar da Nnamdi Kanu gidan yarin Sakkwato Sojoji sun bar makarantar Maga...
    Gwamna Nasir Idris na Jihar Kebbi, ya nemi ƙarin bayani kan dalilin ɗauke sojojin da ke gadin makarantar GGCSS Maga, gabanin harin da ’yan bindiga suka kai tare da sace ɗalibai 25. Gwamnan, ya ce gwamnati ta riga ta sanar da hukumomin tsaro game da yiwuwar kai hari, amma sojojin suka bar makarantar da misalin ƙarfe...
    Majalisar Dokokin Jihar Kano, ta wanke Shugaban Ƙaramar Hukumar Rano da aka dakatar, Alhaji Naziru Yau, daga dukkanin zarge-zargen da aka masa. Wannan ya ba shi damar komawa bakin aikinsa da shugabancin Ƙaramar Hukumar Rano. An kama Faston da ake zargi da yi wa mambobin cocinsa 3 fyade ’Yan bindigar da suka sace masu ibada...
    Gwamnatin Jihar Neja ta tabbatar da sace ɗalibai da ma’aikatan makarantar Katolika ta Saint Mary da ke Papiri, da ke Ƙaramar Hukumar Agwara da jihar. Aminiya ta rawaito yadda ’yan bindiga suka kutsa cikin makarantar tsakanin ƙarfe 2:00 zuwa 3:00 na safiyar Juma’a. ’Yan bindiga sun sace dalibai a wata makarantar Neja ’Yan bindigar da...
    ’Yan bindiga sun kai hari makarantar Katolika ta St. Mary da ke cikin yankin Papiri a ƙaramar hukumar Agwara ta Jihar Neja, sannan suka sace ɗalibai da malaman da ba a kai ga tabbatar da adadinsu ba. Har zuwa yanzu dai babu cikakkun bayanai a kan harin, amma majiyoyi sun shaida wa wakilinmu cewa an...
    Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya umarci Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, da ya koma jihar Kebbi da aiki sakamakon sace ɗalibai ’yan mata 25 da wasu ’yan bindiga suka yi a jihar. Tinubu ya umurci Matawalle, wanda tsohon Gwamnan Jihar Zamfara ne, da ya zauna a Kebbi domin sa ido kan dukkan matakan tsaro da...
    Ƴan ta’adda sun kai hari Makarantar St. Mary’s da ke ƙauyen Papiri, a ƙaramar hukumar Agwara da ke Jihar Neja a Najeriya, inda suka yi garkuwa da ɗalibai da ma’aikatan makaranta da ba a tantance adadinsu ba zuwa yanzu. Rahotanni daga makarantar sun ce harin ya faru ne da tsakar dare, kuma tuni aka fara...
    Daga Bello Wakili Shugaba Bola Tinubu ya umurci Ministan  Tsaro, Alhaji Bello Matawalle, da ya koma Jihar Kebbi biyo bayan sace dalibai  ’yan mata 24  a jihar. An umurci Matawalle, wanda tsohon gwamnan Jihar Zamfara ne, da ya zauna a jihar domin sa ido kan ƙoƙarin  da ake yi na kubutar da ɗaliban da aka...
    Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin jihar Jigawa ta amince da fitar da Naira Biliyan 3 a matsayin  tallafin hadin gwiwa na kowace shekara  domin inganta ilimi a matakin farko, wato UBEC 2025 Matching Grant. A wata sanarwa da Kwamishinan  Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na Jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ya fitar ya bayyana...
      Kungiyar Haɗin Kan Masu Kiwo na Gargajiya ta Afirka (CORET) tare da haɗin gwiwar ECOWAS sun hada matasan da aka horar da su da manyan abokan holda don bunkasa kiyo da bunkasa yawan madara a jihohin Kaduna da Jigawa.   A yayin zaman karawa juna sani a Kaduna, Koodinetan Aikin na CORET Dr. Umar...
    Iyalai da ‘yan uwan wadanda aka kashe a lokacin zanga-zangar da ta kawo karshen gwamnatin tsohuwar Firaminstar Bangaledash Sheikh Hasina a bara, sun yi maraba da hukuncin kisa da wata kotun birnin Dhaka ta yanke mata. An samu Sheikh Hasina da laifin cin zarafin bil adama tare da ba ‘yan sanda umurnin kashe masu zanga-zanga,...
    Daga Khadijah Aliyu  Majalisar Dokokin Jihar Kano ta karɓi wasiƙa daga Gwamna Abba Kabir Yusuf kan gabatar da kasafin kuɗi na shekarar 2026 wanda ya kai Naira tiriliyan 1, irinsa na farko a tarihin jihar. Za a gabatar da kudurin ne a ranar Laraba, 19 ga watan Nuwamban 2025. Wasiƙar, wadda Kakakin Majalisar, Alhaji Jibril...
    Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya reshen Jihar Kebbi ta tabbatar da sace dalibai ashirin da biyar daga Makarantar Sakandare ta ’Yan Mata ta Gwamnati da ke Maga a Ƙaramar Hukumar Danko/Wasagu. Lamarin ya faru ne a daren Litinin da misalin ƙarfe 4 na safe a lokacin da ƴan bindiga suka mamaye makarantar, inda suka kashe wani...
    Hukumar Zakka ta Jihar Zamfara ta sanar da shirye-shiryen aurar da marayu 200 ’yan asalin jihar a wani yunƙuri na tallafa wa marasa galihu. Sakataren hukumar, Malam Habibu Balarabe ne ya bayyana hakan, inda ya ce an kammala dukkan shirye-shirye domin gudanar da bikin auren a ranar Litinin, 23 ga Nuwamba, 2025, a harabar hukumar...
    Shugaban jam’iyyar NNPP na Jihar Kano, Hashimu Sulaiman Dungurawa, ya ce jam’iyyar APC ba ta da ƙarfin da zai kai ta ga samun nasara a 2027, sai dai idan ta jingina da tasirin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso. Yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a sakatariyar NNPP ta jihar, Dungurawa ya ce APC a...
    Mahukunta a Jahar Kwara sun sanar da rufe makarantu a garuruwan Ifelodun,Ekiti, Irepodun, Isis, da Oke Ero, saboda matsalolin tsaro da ake fuskanta Kwamishinan ilimi na Jahar ta Kwara Lawal Olohungabebe ne ya sanar da daukar wannan matakin saboda abinda ya kira bayar da kariya ga rayuwar daliban da suke fuskantar barazanar masu dauke da...
    Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta sami jagoran haramtacciyar ƙungiyar neman kafa kasar Biyafara ta IPOB, Nnamdi Kanu, da laifukan ta’addanci da aka zarge shi da aikatawa. Da yake yanke hukunci a ranar Alhamis, Mai Shari’a James Omotosho, ya amince da batutuwa uku da aka gabatar a shari’ar, inda ya yanke hukunci a kan...
    Gwamnatin Jihar Kwara ta bayar da umarnin rufe makarantu a ƙananan hukumomin jihar guda huɗu na saboda ƙaruwar hare-hare a jihar cikin sa’o’i 48 da suka gabata. Aƙalla mutane uku sun mutu a garin Bokungi da ke Ƙaramar Hukumar Edu a ranar Laraba. Wayar wutar lantarki ta kashe mutum 4 a wajen cashiya a Legas...
    a Rahotanni sun nuna cewa kungiyar gwagwarmaya Ta hamas ta yi gargadi game karuwar hadari bayan mutuwar falasdinawa guda 28 sakamakon harin da sojojin HKI suka kai a yankin Gaza, da hakan yake kara lalata yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma a tsakani. Akwai yara guda 9 daga cikin wanda harin na isra’ila...
    An sanar da dan wasan Paris St Germain, Achraf Hakimi a matsayin wanda ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Afirka na 2025, mai tsaron baya da ya lashe kyautar karon farko bayan shekara 52. Dan wasan tawagar Masar Mohamed Salah shi ne na biyu mai taka leda a Liverpool da kuma Victor Osimhen...
    Wani magidanci tare da ɗaukacin iyalinsa huɗu sun rasu sakamakon wata gobara da ta tashi a sanadin kunna maganin sauro a layin Baba Impossible da ke Unguwar Kundila, da ke Ƙaramar Hukumar Tarauni a Jihar Kano. Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ta tabbatar da tashin wutar da misalin ƙarfe 4:13 na Asubar ranar Laraba....
    Wata Kotun Tarayya da ke Abuja, ta sanya ranar 15 ga watan Janairun 2026, don fara shari’ar shugabannin ƙungiyar ’yan ta’adda ta Ansaru; Mahmud Usman da Abubakar Abba. Ana zargin su da jagorantar ƙungiyar ta’addanci ta Ansaru, kuma Hukumar DSS ce ta kama su tare da gurfanar da su a kotu. Ribadu ya jagoranci tawaga...
    Ana sa ran za a karrama shahararren ɗan damben boksin na Birtaniya, Fabio Wardley, da kambun zakarun ajin masu nauyi na WBO, bayan Oleksandr Usyk ya janye daga kare kambunsa a fafatawar da zai yi da Wardley. Janyewar ta faru ne bayan Usyk, ɗan kasar Ukraine, ya shaida wa Hukumar Damben Boksin ta Duniya (WBO)...
    Darakta Janar na Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya {IAEA} ya bayyana cewa: Suna tuntubar Tehran kuma masu binciken hukumar sun koma kasar ta Iran Darakta Janar na Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA), Rafael Grossi, ya tabbatar da komawar masu binciken Hukumarsa ta IAEA zuwa Iran da kuma ci gaba da duba wasu wurare da...
    Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta yanke wa wani shugaban ISWAP Hussaini Ismaila, hukuncin ɗaurin shekaru 20 a gidan yari bayan samun sa da aikata laifukan ta’addanci. Alƙalin kotun, Mai Shari’a Emeka Nwite, ya yanke hukuncin ne bayan Ismaila, wanda ake kira Mai Tangaran, ya amsa tuhume-tuhume guda huɗu da Hukumar DSS ta...
    Shugaban ƙungiyar masu sayar da tsofaffin ƙarafa a jihar Gombe, A.A. Laja, ya ce gobarar da ta tashi a kasuwar tsofaffin ƙarafa da ke kasuwar katakon jihar ta jawo masa asara da ta kai sama da Naira miliyan 500. Lamarin ya faru ne a daren Laraba, inda wutar ta ƙone shaguna fiye da 30 da...
    Amina Hassan, matar Yakubu Makuku, mai gadin makarantar ’yan mata ta GCGSS Maga da ke Ƙaramar Hukumar Danko Wasagu a Jihar Kebbi, wadda aka kai wa hari da safiyar Litinin, ta bayyana yadda aka kashe mijinta. Da take magana da ’yan jarida a wurin da lamarin ya faru, ta ce bayan da maharan suka kutsa...
    Wata mummunar gobara ta tashi cikin daren Laraba ta ƙone shaguna a kasuwar Katako da ke Gombe, lamarin da ya yi sanadin salwantar dukiya ta miliyoyin naira. Shaidu sun ce gobarar ta fara ne wajen misalin ƙarfe 1:00 na dare sakamakon zargin matsalar wutar lantarki, inda ake kyautata zato cewa an bar wasu na’urorin lantarki...
    Kasar Saudiyya ta sanar cewa za ta kara hannun jarinta a Amurka zuwa dala tiriliyan daya, daga dala biliyan 600 da kasar ta zuba a baya. Yariman Saudiyyar ne Mohammed Ben Salman ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai tare da Shugaban Amurka Donald Trump a ziyarar da ya kai fadar...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Batun kubutar da ɗalibai mata da masu garkuwa da mutane suka sace na makarantar GGCSS Maga dake karamar hukumar Danko Wasagu a jihar Kebbi na daya daga cikin abubuwan da alumma suka maida hankali a kai.   Iyayen wadannan yara, da sauran masu ruwa da tsaki na ganin...
    Gwamnan Taraba, Agbu Kefas ya sanar da dakatar da sauya sheƙa daga jam’iyyarsa ta PDP zuwa APC a dalilin sace ɗalibai mata ’yan sakandire da aka yi a Jihar Kebbi. Gwamnan ya ce zai ci gaba da tattaunawa da kuma nazari kan lokacin da ya fi dacewa ya sauya sheƙar tare da magoya bayansa. Mutane...
    Masu gangamin da adadinsu ya kai 100 sun tsaya a gaban babbar kofar shiga wurin taron kare muhalli na MDD da aka bude a garin Belem dake yankin Amazon na Brazil. Sojojin kasar Brazil sun bai wa masu gangamin kariya, tare da kaucewa yin taho mu gama saboda su sami damar isar da sakonsu akan...
    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barau FC ta doke Enugu Rangers da ci 2-0 a wasan mako na 13 na Firimiyar Najeriya da suka buga a filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar Mata a Jihar Kano. Umar Bala Mohammed ne ya fara zura ƙwallo ta farko a minti na 25, kafin Joseph Kemin ya...
    Ministan harkokin wajen Najeriya ya ce kasar ta soma tattaunawa da Amurka, bayan barazanar da Shugaba Trump ya yi na kai wa Najeriya harin soji kan kisan kiristoci da ya ce ana yi a kasar. A wata hira da kamfanin dillancin labarai na AFP, yayi da Yusuf Maitama Tuggar ya ce abin da suke tattaunawa...
    “Lokacin da Wike, Makinde, Ugwuanyi, Ikpeazu da Ortom suka kafa G5, bana are da su. Amma duk da haka, Wike abokina ne sosai. Lokacin da PDP ta samu matsala Wike ne ya yi ƙoƙarin tallafa mata,” in ji Anyanwu. Ya ƙara da cewa Wike bai fice daga PDP ba. Anyanwu ya kira taron gangamin PDP...
    “Cikin hukuncin Allah, sojojin Daularmu sun kama ‘Kwamandan Runduna’… bayan ya gudu daga harin kwantan-ɓauna… Bayan mun yi masa tambayoyi, Mujahidai suka kashe shi.” An kuma wallafa wani hoto a kafafen sada zumunta da ya nuna Janar Uba a ɗaure. Har yanzu rundunar sojin Nijeriya ba ta fitar da wata sanarwa game da wannan lamari...
    Masu gabatar da kara a kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) a ranar Litinin din nan sun bukaci kotun da ta zartar da hukuncin daurin rai da rai kan Ali Muhammad Ali Abd-Al-Rahman, wanda aka fi sani da Ali Kushayb, kwamandan rundunar Rapid Support Forces (RSF), saboda rawar da ya taka a...
    Gwamna Ahmed Idris na Jihar Kebbi ya ba da tabbacin cewa jami’an tsaro za su ƙwato ’yan matan da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Kwalejin ’Yan Mata ta GGCSS Maga da ke Ƙaramar Hukumar Danko Wasu ta jihar cikin ƙoshin lafiya. Gwamnan ya bayar da tabbacin ne a yayin ganawarsa da iyayen...
    Ma’aikatar ma’adinai a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ta sanar da tsawaita dokar hana fataucin ma’adinai na tsawon watanni shida daga wuraren hakar ma’adinai da dama a lardunan  Kivu ta arewa da ta kudu da ke fama da rikici. Sabunta haramcin zai kara kawo tsaiko da cikas wajen samar da wasu ma’adanai a duniya, musamman ma’adaanai irin...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Adadin Motocin Da Sin Ke Fitarwa Waje Ya Karu Da Kashi 15.7 Cikin Watanni 10 Na Farkon Bana November 17, 2025 Daga Birnin Sin An Bude Taron Tattaunawa Kan Wayewar Kai Tsakanin Sin Da Kasashen Larabawa Karo Na 11 A Beijing November 17, 2025 Daga Birnin...
    Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International ta yi kakkausar suka kan sabon harin da ’yan bindiga suka kai makarantar sakandare ta ’yan mata da ke garin Maga a Jihar Kebbi, wanda ya kai ga sace ɗalibai mata sama da 25 tare da halaka mai gadi da mataimakin shugaban makarantar. A wata sanarwa da ta...
    A Damaturu, farashin mudun shinkafa ya ragu daga N5,000 zuwa N2,500, yayin da wake, masara da gero suma suka sauka fiye da rabin tsohon farashinsu. Masana tattalin arziki sun ce yawaitar shigo da hatsi kamar shinkafa da alkama ya taimaka wajen rage tsadar abinci da ake fama da ita a watannin baya. ShareTweetSendShare MASU ALAKA...
    A yau ne aka bude taron tattaunawa game da wayewar kai takanin Sin da kasashen Larabawa karo na 11, wanda sashen cudanya da kasashen waje na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta Sin da sakatariyar kawancen kasashen Larabawa suka dauki nauyin shiryawa a Beijing. A gun taron, shugabanni na jam’iyyu da kungiyoyin siyasa, ‘yan majalisa, jami’an...
    Gobara ta laƙume rayukan wasu yara biyu ’yan gida ɗaya a unguwar Rumuola da ke ƙaramar hukumar Obio/Akpor a Jihar Ribas. Bayanai sun ce ibtila’in ya auku ne da misalin ƙarfe 10 na dare a ranar Lahadi, lokacin da gobarar ta tashi a ɗaya daga cikin wasu ɗakunan haya da mahaifiyar yaran ta kulle ’ya’yanta...
      An samu wannan raguwar ne sakamakon sauye-sauyen da aka samu a shekarar da muke ciki. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai ‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaron Iyakokin Kano Bayan Hare-haren ‘Yan Bindiga  November 17, 2025 Labarai Rashin Tsaro: Atiku Ya Yi Allah-wadai Da Harin Makarantar ‘Yan Mata Ta Kebbi November 17, 2025 Labarai MACBAN Ta...
      Ya bayyana cewa, zaman bitar ya yi daidai da umarnin Sufeto Janar na ‘Yansanda, IGP Kayode Egbetokun, musamman kan karfafawa jami’an rundunar. Don haka, CP Bakori ya umurci Kwamandojin da su zurfafa wayar da kan jama’a a yankunan karkara da birane domin sanar da su irin rawar da suke takawa wajen wanzar da zaman...
    Rushewar ramukan hako ma’adinai ta kashe ma’aikata 32 a kudancin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo Akalla ma’aikatan hakar ma’adinai 32 ne suka mutu a ranar Asabar sakamakon zaftarewar ƙasa a wani ma’adinan cobalt a kudancin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, yayin da ake ci gaba da neman waɗanda har yanzu ba a same su ba a yankin. Zaftarewar ƙasa...