2025-11-13@21:27:05 GMT
إجمالي نتائج البحث: 4719
«Ma aurata»:
Allah Ya yi wa Bebejin Katsina, Alhaji Nuhu Yashe, rasuwa a daren nan na Alhamis. Wakilimu ya ruwaito, basaraken ya amsa babban kiran ne a yayin da ake gudanar da sallar Isha’i. Kafin rasuwarsa, marigayin shi ne Hakimin Kusada, kuma suruki ne ga Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmuminu Kabir Usman. Haka kuma, shi ne...
Rahotanni sun bayyana cewa ministan harkokin wajen kasar iran ya tattaunawa da takwaransa na kasar Qatar kan dakangantar dake tsakaninsu da kuma abubuwan da ke faruwa a yankin, inda dukkan bangarorin biyu suka yi kira kan muhimmancin yin aiki tare adaidai lokacin da ake cikin wani yanayin a kudu da yammacin Asia. Wannan tattaunawar tana...
Adai dai lokacin da bikin cika shekaru 55 na kulla hulda diplomsiya tsakanin Iran da China ke kara karatowa ta , dukkan kasashen biyu suna kokarin ganin sun kara karfafa alakar dake tsakaninsu , Ambasado Ahmad Fazli ya jaddada game da muhimmancin karfafa dangantaka a mataki na kasa da kasa, bisa hangen nesa da girmama...
A yammacin wannan Alhamis ce tawagar ƙwallon ƙafar Nijeriya Super Eagles za ta fafata da ƙasar Gabon a wasan neman tikitin shiga Gasar Kofin Duniya ta 2026. Wasan da za a buga da karfe 5 na yamma a filin wasa na Prince Moulay Hassan da ke Rabat, Morocco, zai zama wasa na farko tsakanin ƙasashen...
Cibiyar Masu Binciken Adadi ta Nijeriya (NIQS) ta yi kira ga gwamnatin tarayya da Majalisar Dokoki ta Kasa da su samar da mafita wajen kayyade kudin hayar gidaje, musamman a manyan birane, kamar Abuja. Shugaban Cibiyar, QS Kene Nzekwe ne ya yi kiran a ranar Laraba a Abuja a wani taron manema labarai don tunawa...
Almayadin Ta Sami Rahoton Hukumar Makamashin Ta Duniya ( IEA) Aka Cewa Iran Tana Aiki Da Dukkanin Ka’idoji
Tashar talabijin din ‘almayadin’ ta fitar da wani rahoto da shugaban hukumar makamashin Nukiliya ta kasa da kasa Rafael Grossi ya fitar da a ciki yake tabbatar da cewa, Iran tana aiki da dukkanin nauyin da ya rataya a wuyanta. Rahoton dai ya kunshi cewa, tun bayan yarjejeniyar birnin Alkahira na kasar Masar da aka...
Janar Fadwi wanda shi ne mataimakin kwamndan dakarun kare juyin musulunci na Iran ya ce; Muna aiki akan nisan Zangon da makamanmu masu linzmai za su iya kai wa gare shi. Fadwi wanda ya gabatar da jawabi a yau Alhamis a wurin taron girmama shahidan rundunar dake kula da kare sararin samaniyar Iran, ya kara...
Gwamnatin Jihar Kwara ta jaddada kudirinta na ba da ingantaccen kulawa da kuma ƙarfafa matakan rigakafi ga waɗanda suka tsira daga cin zarafin jima’i da na jinsi (SGBV) a fadin jihar. Kwamishiniyar Harkokin Mata, Hajiya Opeyemi Afolashade, ce ta bayyana haka yayin ziyarar sa ido da tantance ayyuka a Cibiyoyin Tallafawa Wadanda Aka Yi wa...
Shugaban Karamar Hukumar Nasarawa da ke Jihar Kano, Yusuf Shuaibu Imam, ya yi kira ga mazauna yankin da su ziyarci ofisoshin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) domin yin rijistar zaɓe da kuma karɓar Katin Zaɓe na Dindindin (PVC). Imam ya yi wannan kiran ne yayin da yake kaddamar da jerin ayyukan raya...
Majalisar Tarayya Za Ta Binciki Masaƙa Ta Kaduna Da Sauran Gine-ginen Gwamnati 11,000 Da Aka Yi Watsi Da Su
Ya yi nuni da rahoton 2021 da Cibiyar Binciken kasa ta Nijeriya ta fitar, wanda ya gano kimanin filaye da gine-ginen gwamnatin tarayya 11,866 da aka yi watsi da su a duk faɗin ƙasar. Daga cikin manyan kadarorin da ɗan majalisar ya lissafa akwai Cibiyar Sakatariyar Tarayya da ke Ikoyi, Legas; Ginin Otal na...
Ministocin harkokin wajen Iran da na Rasha sun tattauna ta wayar tarho gabanin taron kwamitin gwamnonin IAEA A yayin tattaunawar Araghchi da Lavrov, sun yi musayar ra’ayi kan batutuwa daban-daban, ciki har da rikicin kan iyaka tsakanin Pakistan da Afghanistan, tare da jaddada muhimmancin yin shawarwari don warware batutuwan da ba su dace ba. Babban...
A yammacin jiya ne hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar Iraki ta sanar da sakamakon farko na zaben ‘yan majalisar dokokin kasar na shekarar 2025, tare da tabbatar da cewa an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da inganci ta hanyar amfani da na’urorin lantarki. A taronta na manema labarai, Hukumar ta bayyana cewa...
Wani kamfanin hakar ma’adinai na Biritaniya ya sanar a jiya Laraba cewa, an gano tarin zinari a karkashin kasa a gundumar Kakamega da ke yammacin kasar Kenya, wanda darajarsa ta kai sama da dalar Amurka biliyan 5.28 kwatankwacin shilin kasar Kenya biliyan 683, a wani abin da jami’ai suka bayyana a matsayin wani muhimmin mataki...
A kwanakin nan ana samun raguwar kujerun maniyyata aikin Hajji daga Najeriya, abin da ya jawo fargaba ga masu shirin zuwa kasa mai tsarki da kuma masu hidimar su. A da, Najeriya na samun kujeru sama da dubu casa’in daga gwamnatin Saudiyya, amma cikin shekaru kadan da suka gabata adadin ya ragu zuwa kusan dubu...
Majalisar Dattawa ta amince da buƙatar Shugaba Bola Tinubu na karɓo rancen Naira tiriliyan 1.15 domin cike giɓin kasafin kuɗin 2025. Amincewar ta biyo bayan rahoton da Kwamitin Majalisar Dattawa kan Lamunin Cikin Gida da na Ƙasashen Waje, ƙarƙashin jagorancin Sanata Manu Haruna, ya gabatar. Matasa 12 sun mutu a turmutsutsun neman aikin soja a...
Daga Bashir Meyere Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da bukatar Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, na neman rancen Naira Tiriliyan 1.15 domin cike gibin kasafin kudin shekarar 2025. Amincewar ta biyo bayan gabatar da rahoton kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da lamuran bashi na cikin gida da na waje. Yayin da yake gabatar da rahoton,...
Rahotanni sun bayyana cewa kasar Amurka tana shirin kafa sanssanin soji don aikewa da dubban dakaru zuwa iyakar Isra’ila da yankin Gaza, adaidai lokacin da ake fargabar wata sabuwar kasada da kuma sha’awar taimakawa gwamnatin mamaya wajen karbe ikon kula da yankin a nan gaba. Masharhanta na ganin wannan shirin yana zuwa ne saboda irin...
Hukumar kula da aikin hajji ta kasar Iran ta bayyana cewa shugaban ga yarima mai jiran gado na kasar Saudiya Mohammad Bin Salman a wata ziyara da suka kai birnin Riyadh a baya bayan nan. Wannan sakon yana nuna irin kokarin da ake yi ne na ganin an daidaita da kuma kara yin aiki tare...
Kasashen Iran da Pakistan sun yi kira da a yi aiki tare da ya hada da kara dankon zumunci tsakanin yan majalisar domin tunkarar babban makiyinsu, kuma sun yi tir da matakin kai hare-hare da Isra’ila ke yi da kuma ta’adanci a yankin A wani bayani da suka fitar a wata ganawa da suka yi...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya tattauna ta wayar tarho da twakaransa na kasar Rasha Sergei lavrov inda suka mayar da hankalin kan batutuwan da suka shafi yankin dama na kasa da kasa Ma’aikatar harkokin wajen kasar iran ta bayyana cewa Iraqchi ya jaddada game da muhimmancin zaman lafiya a yammcin Asiya lokacin...
Babban abin lura a nan shi ne irin alfanun da Nijeriya za ta samu tare da sauran kasashen Afrika daga wannan bikin baje koli. Na farko dai Nijeriya da sauran kasashen Afirka za su kara kaimi wajen noman irin waɗannan amfanin gona domin fitar da su zuwa Sin, hakan kuwa zai kara samar da aikin...
Mataimakin wakilin dindindin na Sin a MDD Sun Lei, ya gabatar da jawabi yayin taron kwamitin sulhu game da batun Sudan ta Kudu da aka gudanar jiya Talata, inda ya yi kira da a inganta mika mulki cikin kwanciyar hankali a Sudan ta Kudu. Sun Lei ya ce, Sin ta bukaci dukkan bangarorin kasa da kasa da...
Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin jihar Jigawa ta jaddada kudurin ta na ci gaba da samar da ingantaccen kiwon lafiya ga al`ummar jihar. Babban sakataren ma’aikatar lafiya na jihar, Dr. Kabiru Ibrahim ya bada wannan tabbacin a dakin taro na ma’aikatar lafiya ta jihar a Dutse. Yace ayyukan da za’a gudanar a asibitocin sun hada...
Daga Usman Muhammad Zaria Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da Naira Biliyan daya da miliyan dari uku domin gyara da inganta tsofaffin ayyukan wutar lantarki a fadin jihar. Kwamishinan yada labarai, matasa, wasanni da al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ne ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse....
Hukumar tsaro ta DSS ta gurfanar wani matashi mai suna Innocent Chukwuemeka Onukwume, mai shekaru 27, bisa zargin kiran sojoji da su yi juyin mulki a Najeriya. Hukumar dai ta shigar da ƙarar matashin ne cikin tuhuma shida a gaban Kotun Tarayya da ke Abuja. Ɗan Majalisar Wakilai daga Kano Sagir Ƙoƙi ya fice daga...
Daga Khadijah Aliyu Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da Kwamitin Jagorancin Shirin Ilimi da Ƙarfafa Matasa a Arewa maso Yammacin Najeriya (EYEPINN) wanda kungiyar Tarayyar Turai ke daukar nauyinsa domin fadada damar samun ingantaccen ilimi da kuma karfafa gwiwar matasa a yankin. An gudanar da bikin kaddamarwar ne a Kano, karkashin jagorancin Kwamishinan Ilimi na...
A jiya Talata ne dai MDD ta yi kira da a gudanar da bincke akan kashe-kashen da aka yi sanadiyyar zaben da aka yi a watan karshe. Wannan kiran na MDD ta zo ne a daidai lokacin da mahukuntan kasar ta Tanzania su ka tuhumi wasu daruruwan mutane da cin amanar kasa saboda Zanga-zangar kin...
A yau Laraba ne aka sanar da zaman Iran memba a cikin wannan kungiyar ta ( ISKO) wacce aka bude reshenta a cikin kasa tun a 2011. Farfesa Rahmatullah Fattahi ne ya bude reshen kungiyar ta ” Ilimomin Tattara Bayanai Da Kere-Kere” wacce kuma ta ci gaba da gudanar da ayyukanta har zuwa 2019. An...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Majalisar Wakilai Ta Yi Tir Da Harin Da Aka Kai Wa Tawagar Ɗan Majalisar Neja November 7, 2025 Siyasa Dalilin Da Ya Sa Sanatoci Ba Su Goyi Bayana Ba Lokacin Da Aka Dakatar Da Ni – Natasha November 4, 2025 Labarai “Ƴan Adawa Sun Wuce Gona da Iri...
Hukumar Tsarawa da Raya Birane ta Jihar Kano (KNUPDA) ta gudanar da horon cikin gida na farko ga ma’aikatanta, wanda ya mayar da hankali kan aiwatar da dokokin aikin gwamnati, kyawawan ɗabi’un aiki da kuma ingancin ayyuka. Wannan horo, wanda ya zama muhimmin mataki a shirin ƙarfafa ƙwarewar ma’aikata na hukumar, an shirya shi ne...
Pars Today – Jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Pakistan, yana Allah wadai da fashewar da ta faru a babban birnin Pakistan, ya ce ta’addanci barazana ce ga dukkan yankin kuma fuskantar wannan mummunan lamari yana buƙatar haɗin gwiwa, ƙuduri, da haɗin kai daga dukkan ƙasashe. Reza Amiri-Moqaddam, Jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Pakistan,...
Ministan Harkokin Wajen Iran Sayyed Abbas Araghchi, ya ce masana’antar nukiliya yanzu ta zama babban fanni kuma tana kara samun ci gaba cikin sauri a fannoni daban-daban. Sabanin yadda ake ganin cewa wannan masana’antar ta takaita ne ga tace uranium, ya kara da cewa ana gudanar da ayyuka da dama da suka shafi fannoni daban-daban...
Babban Sakataren Hezbollah Sheikh Naim Qassem ya bayyana cewa “Amurka, ta hanyar wakilanta na Isra’ila, tana neman kawar da karfin gwagwarmayar Lebanon da kuma ba sojojin kasar makamai don fuskantar Hezbollah,” yana mai jaddada cewa manufar wannan matakin shine “kawar da karfin soja da duk wani karfi fadin Lebanon domin Isra’ila ta ci gaba da...
UNICEF ta yi gargadin cewa Isra’ila na hana shigar da muhimman kayan aikin da ake buƙata don allurar rigakafi a Gaza, wanda hakan ke kawo cikas ga ƙoƙarin isa ga yara a yankin da yaƙi ya daidaita. Hukumar ta ce kayayyakin, ciki har da sirinji da ake amfani da su don allurar rigakafi na yau...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A Najeriya, an saba ganin jami’an ‘yan sanda suna gadin manyan mutane ‘yan siyasa, ‘yan kasuwa, ko shugabanni maimakon su kasance a cikin al’umma suna tabbatar da tsaro ga kowa. Wannan tsarin ya haifar da tambayoyi masu zurfi game da adalci da yadda ake rarraba jami’an tsaro a...
Ban da wannan kuma, game da batun cewa kasashen kungiyar EU suna shirin cire na’urorin kamfanonin sadarwa na kasar Sin, Lin Jian ya bayyana cewa, kamfanonin kasar Sin suna aiwatar da ayyukansu bisa doka a nahiyar Turai na dogon lokaci, wadanda suka samar da kayayyaki da hidimomi masu inganci ga jama’ar Turai, tare da...
Bugu da kari, abu mafi muhimmanci shi ne, kasar Sin ta ba da jagoranci ga kasashen duniya ta fuskar kara bude kofa ga waje. Ta hanyar shigowa da kayayyaki da fitar da kayayyaki, kasar Sin ta ba da gudummawar bunkasa tattalin arzikin duniya, da kara yawan kayayyakin da kasashen duniya suke fitarwa, tare da...
Gwamnan Jihar Legas, Babajide Olusola Sanwo-Olu, ya ce a wannan zamanin na mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, babu wani gwamna ko shugaban ƙaramar hukuma da zai yi ƙorafi kan ƙarancin kuɗi. Sanwo-Olu ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin wani taron ƙarawa juna sani na yini ɗaya da ƙungiyar Arewa Think Tank (ATT) ta...
Shugaban tsaron kasar ta Iran ya yi watsi da rahotannin da ake yayatawa cewa iran ta bude wasu hanyoyin tuntuba da Washington, yana mai jaddada cewa ba a isar da wani sabon sako ga Amurka ba. Ali Larijani ya jaddada cewa fifikon Iran a koyaushe shi ne dage takunkumin da aka kakaba mata, wanda ya...
Ofishin yada labarai na gwamnatin zirin Gaza ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar cewa ‘yan mamayar Isra’ila sun karya yarjejeniyar tsagaita wuta ta Gaza sau 282 tun bayan aiwatar da ita. Sanarwar ta nuna cewa tun lokacin da aka fara yarjejeniyar tsagaita wuta, an kashe fararen hula 242 tare da raunata wasu...
‘Yan Iraki sun kada kuri’a don zaben sabbin ‘yan majalisar dokoki wadda za ta fayyace alkiblar siyasar kasar na tsawon shekaru hudu masu zuwa. Kimanin ‘yan kasar miliyan 21 ne aka tantance domin kada kuri’a ga ‘yan majalisar dokoki 329, Wadannan za su zabi shugaban kasa kuma su amince da sabuwar gwamnatin, wadda sabon firaminista...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi Allah wadai da amincewar da majalisar dokokin Isra’ila ta yi a karatu na farko da wani kudiri da aka gabatar mata na yin hukunci kisa kan wadanda aka kama da laifin ta’addanci a kasar. Dan majalisar kasar mai tsattsauran ra’ayi, Itama Ben Gvir ne ya gabatar da kudirin,...
Gidauniyar Tallafawa Al’umma ta Abba Aliyu Gandu da ke jihar Kano ta bada horo sana’o’in hannu tare da raba tallafin Solar ga al’umma 500. Wannan shi ne karo ba adadi da wannan gidauniyar ta Kogunan Kasar Hausa kuma shugaban hukumar Samarda Lantarki a yankunan Karkara Alhaji Abba Aliyu ta gudanar. An raba kayan Solar guda...
Rundunar sojin Operation Hadin Kai (OPHK) da ke yaƙi da ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas ta sake samun nasara bayan ta ceto mutane 86 da kuma kama wasu mutum 29 da ake zargi da samar wa ’yan ta’adda kayayyaki a Jihar Borno. A cewar sanarwar da Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Laftanar Kanar...
Rundunar sojin Operation Hadin Kai (OPHK) da ke yaƙi da ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas ta sake samun nasara bayan ta ceto mutane 86 da kuma kama wasu mutum 29 da ake zargi da samar wa ’yan ta’adda kayayyaki a Jihar Borno. A cewar sanarwar da Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Laftanar Kanar...
Shugaban Hukumar Sararin Samaniya ta Iran ya sanar da cewa za a harba tauraron dan adam guda uku zuwa sararin samaniya cikin watanni biyu masu zuwa. Hassan Salarieh, shugaban Hukumar Sararin Samaniya ta Iran, a yayin jawabi a wani taron fasahar sararin samaniya a Tehran, ya nuna muhimmancin ayyukan da suka shafi bayanai na tauraron...
Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya jaddada kudirin gwamnatin sa na ci gaba da bunkasa hanyoyin sufuri a fadin jihar. Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya kaddamar da wani muhimmin aikin gina hanyoyi a karamar hukumar Mallam Madori. Yayin taron kaddamarwar, Gwamna Namadi ya bayyana cewa aikin...
Tawagar lauyoyin Trump ta ce an ɓata masa suna da mutunci, inda ta bayyana cewa BBC ta yi hakan ne don siyasa. Trump ya taɓa shigar da ƙorafe-ƙorafe makamantan wannan a kan wasu manyan kafafen yaɗa labarai na Amurka, ciki har da ABC, CBS, da The New York Times, bisa zargin yaɗa labaran ƙarya a...
Shugaban kasar Amurka ya yi wa ma’aikatan filayen jiragen sama masu sa idanu akan sauka da tashin jirage, barazana. Ma’aikatan da suke sanya idanu a cikin hasumiyoyin dake filayen jiragen sama da dama ne a Najeriya su ka dakatar da ayyukansu saboda rufe ayyukan gwamnati da aka yi a kasar, domin ba za su sami...
Wani mutum da ba a gano sunansa ba ya mutu bayan da ya shiga wani gidan karuwai domin ganawa da ’yan mata masu zaman kansu a birnin Fatakwal. Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, inda rahotanni suka ce mamacin ya shiga gidan karuwai ne domin yin hulɗa da ’yan mata, sai dai ba a...