HausaTv:
2025-11-08@21:08:59 GMT

 An Zabi Robert Francis  Dan Asalin Amurka A Matsayin Paparoma

Published: 9th, May 2025 GMT

A jiya Alhamis ne dai majami’ar Roman Katolika ta sanar da zabar Robert  Farncis wanda ya zabi sunan Leo 14,a matsayin shugabanta.

Zabar Robert Francis a matsayin Paparoma na 267 ya zo ne bayan kwanabi 2  da manyan malaman addinin majami’ar Roman katolika su ka dauka suna yin zaben.

 A bisa al’adar majalisar, farin hayaki yana fitowa daga saman majami’ar da yake nuni da cewa an zabi sabon Paparoman, da hakan ya sa a ka rika kada karaurawa a cikin maja’mi’un birnin Roma.

Sabon Paparoman  dan shekaru 69 ya zabarwa kansa sunan  Leo 14 domin sake dawo da aiki da kyawawan halaye a cikin harkokin tafiyar da majami’ar kamar yadda Leo na farko ya yi a 1878 zuwa 1903.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Barau ya nemi Trump ya janye kalamansa, ya nemi afuwar Najeriya

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Jibrin Barau, ya nemi Shugaban Amurka, Donald Trump, ya janye barazanar da ya yi wa Najeriya kan zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi.

Trump, ya yi barazanar ɗaukar matakin soji a kan Najeriya saboda zargin ana zaluntar Kiristoci.

Barazanar Trump: Ya kamata shugabannin Najeriya su farka daga bacci — Bishop Kukah Tinubu ya gana da Sarkin Musulmi a Aso Rock

Barau ya ce maganar da Trump ya yi ba ta dace ba, kuma ta saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa.

A cikin wani bidiyo da aka fitar a ranar Juma’a, Mataimakin Shugaban Majalisar, ya ce Najeriya, a matsayinta na ƙasa mai cin gashin kanta, ba za ta yadda a ci zarafinta ko a tsangwame ta ba.

“Shugaban Amurka ya fito ya ce, ‘Najeriya wulaƙantaciyyar ƙasa ce, za mu kai muku hari,’ wannan bai dace ba.

“Ya kamata ya janye wannan maganar ya kuma nemi afuwar Najeriya,” in ji Barau.

Ya ƙara da cewa maganganun Trump sun karya dokokin diflomasiyya da na ƙasa da ƙasa.

“Idan kuna da ƙorafi a kan ƙasarmu, ku bi hanyoyin shari’a. Ku je Majalisar Ɗinkin Duniya, ku nemi izini, sannan ku aiwatar da shi yadda ya dace. Tsallake wannan hanya ba abin da ya dace ba ne,” in ji shi.

Barau, ya jaddada cewa kalaman Trump ba za su firgita Najeriya ba, kuma ya kamata shugaban Amurka ya girmama ƙasa mai cin gashin kanta.

“Ba za mu ji tsoron faɗin gaskiya ba. Da Trump yana nan, da na faɗa masa kai-tsaye cewa abin da yake yi ya saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa kuma ba daidai ba ne,” in ji shi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga
  • Barau ya nemi Trump ya janye kalamansa, ya nemi afuwar Najeriya
  • Ɗan shekara 2 ya rasu bayan faɗawa rijiya a Kano
  • An gano gawar wata mai shekara 96 a cikin masai
  • Barazanar Amurka Na Kawo Wa Nijeriya Hari 
  • An Rantsar Da Paul Biya A Matsayin Shugaban Kamaru Karo Na Takwas
  • Mun fara tattaunawa da Amurka kan barazanar Trump – Gwamnatin Tarayya
  • Amurka Ta Yi Barazanar Ƙwace Kadarorin Ƙungiyoyin Makiyaya A Nijeriya 
  • Najeriya ta yi watsi da sanya sunanta cikin jerin kasashen da ake tauye ’yancin addini
  • Gwamnatin Tarayya ta fara shirin sayar da matatun manta ga ’yan kasuwa