Sojoji sun kama mutum 4 kan zargin ta’addanci a Taraba
Published: 8th, May 2025 GMT
Dakarun Birget na 6 na Sojin Najeriya da ke Jalingo Jihar Taraba sun cafke wasu mutane huɗu da ake zargin cewa ’yan ta’adda ne.
Kama waɗanda ake zargin ya biyo bayan wani samame da sojojin suka gudanar a ranar 7 ga Mayu, 2025 a Ƙaramar Hukumar Arɗo-Kola da ke jihar.
Kakakin Rundunar, Kyaftin Oni Olubodunde, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a garin Jalingo.
Ya bayyana cewa rundunar ta sami kiran gaggawa dangane da shigowar wasu mutane ɗauke da makamai a yankin.
’Yan sanda sun kama harsasai 500 a Filato Jami’an tsaro na ba da gudunmawar aikata miyagun laifuka a Nijeriya — ZulumKyaftin Oni ya ƙara da cewa dakarun sun yi gaggawar kai ɗauki wurin, inda hakan ya kai ga kama mutanen huɗu, uku daga cikinsu na rike da makamai.
Ya ce makaman da aka ƙwato daga hannunsu sun haɗa da bindigogi uku, adduna guda 3, alburusai guda 42, wayoyin hannu guda 4 da katin shaidar ƙasa guda 1.
Binciken farko ya nuna cewa ana zargin wani mai mutum da kiran wadannan mutanen zuwa yankin, kuma ana ci gaba da bincike kan rawar da ya taka a lamarin.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan fashi sun kashe magidanci a Kano
Ana fargabar cewa wasu da ake zargin ’yan fashi ne sun kashe wani magidanci a unguwar Ɗanbare da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso a Jihar Kano.
Bayanai sun ce waɗanda ake zargin sun kashe magidancin ne da adda, bayan sun shiga gidansa da yake zaune domin sata da asuba.
To sai dai mazauna unguwar sun bayyana wa Aminiya cewa sun samu nasarar kama wanda suke zargin shugaban ’yan fashin ne, sun kuma miƙa shi ofishin ’yan sanda na Ɗorayi.