Aminiya:
2025-05-06@22:24:58 GMT

Majalisar Dattawa ta kafa kwamitin lura da gwamnan riƙo na Jihar Ribas

Published: 6th, May 2025 GMT

Majalisar Dattawa ta kafa kwamiti mai mambobi 18 domin sanya idanu kan yadda gwamnan riƙo na Jihar Ribas Vice Admiral Ibok Ete Ibas mai ritaya ke tafi da aikinsa.

Majalisar ta ce ta ɗauki matakin ne a wani yuƙuri na ƙarfafa shugabanci na gari ba tare da rufa-rufa ba a jihar da ke kudu maso kudancin Najeriya.

Alƙaluman sakamakon jarabawar bana — JAMB Friedrich Merz ya zama sabon shugaban gwamnatin Jamus

Shugaban Majalisar Dattawan, Godswill Akpabio ya sanar yayin zaman majalisar na yau Talata cewa kafa kwamitin na da matuƙar mahimmancin wajen sa ido kan abubuwan da ke faruwa a jihar.

Shugaban masu rinjaye Opeyemi Bamidele ne shugaban kwamatin, yayin da mambobin kuma sun haɗa da Adamu Aliero, da Osita Izunaso, da Osita Ngwu, da Kaka Shehu, da Aminu Abass, da Tokunbo Abiru, Adeniyi Adebire.

A wannan Talatar ce shi ma Kakakin Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen ya sanar da cewa za su kafa kwamitin da zai jiɓanci tabbatar da sulhu kan rikicin siyasa da ya yi wa Jihar Ribas dabaibayi.

Abbas wanda ya ce kwamitin wanda za su yi tarayya da Majalisar Dattawa wajen kafa shi zai ƙunshi wasu manyan ƙasar nan da ake mutuntawa domin tabbatar da wanzuwar dimokuraɗiyya a jihar.

Ana iya tuna cewa a watan Maris ne Shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a Ribas sakamakon abin da ya kira “karyewar doka da oda” wanda ya auku sanadiyyar rikicin siyasa tsakanin Gwamna Similanayi Fubara na PDP mai adawa da tsohon Gwamna Wike mai ƙawance da APC mai mulki.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Jihar Ribas Majalisar Dattawa

এছাড়াও পড়ুন:

Xi Da Shugaban Majalisar Turai Da Shugabar Kwamitin EU Sun Tayawa Juna Murnar Cika Shekaru 50 Da Kulla Hulda

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Jigawa Ta Kaddamar Da Kwamitin Likitocin Da Su Duba Lafiyar Mahajjatan Bana A Saudiyya
  • Gwamnan Bauchi Ya Yi Allah-wadai Da Kisan ‘Yan Banga A Alkaleri
  • Xi Da Shugaban Majalisar Turai Da Shugabar Kwamitin EU Sun Tayawa Juna Murnar Cika Shekaru 50 Da Kulla Hulda
  • Matashi ya kashe mahaifinsa da adda a Jigawa
  • Gwamna Fintiri Ba Zai Bar PDP Ba – Humwashi
  • Abin da ya hana ni cika alƙawarin da na yi wa ma’aikata — Gwamnan Sakkwato
  • Gwamnan California: California Za Ta Ci Gaba Da Bude Kofa Ga Sin Domin Gudanar Da Kasuwanci
  • Ghana Za Ta Hada Gwiwa Da Gwamnatin Jihar Kebbi Kan Noma
  • An Share Filin Noma Kadada 100 Don Karfafa Matasa Su Yi Noma A Babura Jihar Jigawa