Aminiya:
2025-09-24@14:03:46 GMT

Yadda matsalar wutar lantarki ke ajalin rayuka a manyan asibitoci

Published: 9th, May 2025 GMT

Matsalar wutar lantarki a asibitoci a Najeriya ta jefa marasa lafiya cikin halin ni-’yasu, lamarin da ke kara ta’azzara halin da majinyata ke ciki, har ta kai ga asarar rayuwa.

Rashin wuta ya yi sanadin mutuwar jariri a cikin wata mai juna biyu, wata ta yi awa 15 tana jiran a yi mata tiyatan haihuwa, wata kuma ta mutu sakamakon dauke wuta a yayin da ake tsada da yi wa mata tiyata, a Asibitin Jummai Babangida Aliyu, da ke jihar Neja.

’Yan uwa sun shaida wa wakilinmu cewa an shafe sama da kwana uku a jere babu wutar lantarki a asibitin gwamnatin, a yayin da rashin wuta da yanayi na tsananin zafi ya tilasta wa ’yan uwan majinyata amfani da fankoki masu amfani da caji domin samun iska a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano da ke Jihar kano.

Bincikine wakilanmu ya gano matsalar lantarkin na kawo tsaiko ga gudanar a tiyata da ayyukan karbar haihuwa da awon masu juna biyu a asibitoci.

Masan sun ƙalubalanci sojoji kan maharan ƙasashen waje NAJERIYA A YAU: Abin ya sa aka kasa kawo ƙarshen Tamowa a Arewa Maso Gabas

Majinyata a asibitocin da muka ziyarta sun bayyana cewa rashin wutar ta sa ana dage lokacin da aka shirya yi musu tiyata baya ga kawo tsaiko ga sauran nau’ikan aikin kula da lafiya.

Wannan matsala ta shafi asibitocin koyarwa, inda yawan kudin wutar da ake kamfananonin rarraba lantarki ke bin su  ya yi yi musu katutu. Shugabannin asibitocin koyarwar sun bayyana cewa sun yi kokari biyan bashin, amma duk da haka sai sun kara neman wasu kudaden domin samar wa wata hanyar samun lantarki, saboda matsalar rashin samun wutar gwamnati da ta ki ci ta ki cinyewa.

A cikin wannan hali, a watan Fabrairu Ministan Lantarki, Adebayo Adelabu, ya sanar da shirin sake kara kudin wutar, bisa hujjar cewa gwamnati ba za ta iya ci gaba da biyan tallafin lantarki ba.

‘Dauke wuta ana yi wa matata tiyata ya yi ajalinta’ 

A kwanan baya ne wani magidanci a Jihar Neja, Umar B. Shehu ya wallafa a shafinsa na Facebook, yadda dauke wutar da aka yi a yayin da ake tsaka da yi wa matsarsa tiyatar kabar ciki, ya yi sanadiyyar mutuwarta a Babban Asibitin Jummai Babangida da ke garin Minna, hedikwatar jihar.

Malam Umar ya ce, bayan minit biyar da fara yi wa matarsa, Ummi Yusuf Makusidi tiyata, “NEPA suka dauke wuta kuma babu mai a injin janareton bangaren aikin tiyatan da ke Asibitin Jummai Babangida Aliyu.
“Bayan minti biyar aka kawo mai, bayan an zuba kuma sai janareto ya ki tashi, sai da aka nemo makanike. Duk matata tana cikin dakin tiyata, wata mai aikin jinya ta ce kada in damu an ci gaba da aikin ba tare da wutar lantarki ba, suna amfani da abin haskawa — cocila — kamar yadda suka saba.

“Bayan da makaniken ya zo kuma, akwai abubuwan da dole sai ya je ya sayo a unguwar Ogbomosho da ke Minna. Duk dai matata tana cikin dakin tiyata.

“Bayan awa daya aka dawo da wuta, amma makaniken yana kan gyaran janareto. A haka a ci gaba da aikin tiyata. Aikin da bai wuci ya dauki awa daya da rabi ba, tun karfe hudu na yamma sai da ya kai karfe 7 da dare.”

A lokacin da wakilinmu ya ziyarci asibitin da misalin karfe biyar na yamma ranar Asabar, ya lura babu wutar lantarki a daukacin asibitin. ’Yan uwan ajinyata da ke asibitin sun shaida masa cewa kwanansu uku babu wutar lantarki a asibitin, likitoci sun tura wasu, musmman mata masu juna biyu da ke nakuda zuwa asibitocin kudi.

Awa 15 muna jiran tiyata

Wani magidanci mai suna Ali Isah, wanda ya shaida mana yadda ’yarsa ta shafe awa 15 tana jiran a yi mata tiyata bayan an biya kudin aikin a asibitin.

Ya ce, “an kawo nan ne da misalin karfe 3 na dare za ta haihu. Nas ta shaida mana cewa aikin CS za a yi mata, amma ga shi yanzu karfe biyar na yamma, ba a yi aikin ba, kuma mun biya N40,000 kudin aikin.

“Dan uwana ya ba mu shawara mu je asibitin kudi, amma mun riga mun biya kudi a nan asitin na Jummal Babangida.”

Dan uwan wani mara lafiya a asibitin ya ce, “da ya mutu a cikin wata mai juna biyu ranar Juma’a bayan sun shafa awanni suna jiran a yi mata aiki, ba a yi ba. Dalilin da suka bayar shi ne rashin wutar lantarki da ruwa.

“Mijin matar da kansa ya sayo ruwa amma suka ce babu wuta. Kafin a tura matar zuwa Asibitin MI Wushishi, dan ya riga ya mutu. Yanzu kwana uku ke nan babu wuta a nan asibitin,” in ji shi.

Laifin lalacewar tiransufoma ne — Gwamnatin Neja

Mun tuntubi Gwamnatin Jihar Neja inda Kwamishinan Kula da Lafiya a Mataki mai Zurfi, Bello Tukur ya musanta cewa rashin wutar lantarki na kawo cikas wajen gudanar da ayyuka a asibitin.

Ya ce, “Ba gaskiya ba ne, tiransufoma ne ya samu matsala, kuma an kira Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na AEDC su zo su duba, bayan sun duba suka ce dole sai Kamfanin Samar da Wutar Lantarki na Kasa (TCN) ya zo ya duba layin wutar.

“Mun riga mun biya kudin da ake bukata kuma yanzu haka suna aikin. Muhimman sassan asibitin kamar bangaren haifhuwa da dakin haihuwa da bangaren masu jego suna da janareto.

“Ba za a iya kunna babban janareton da ke iya daukar asibitin gaba daya ba, saboda dole sai wutar ta bi ta babban layin, wanda shi ne ya lalace. Yanzu haka ma’aikatan AEDC da TCN na aikin gaya domin ganin ya ci gaba da aiki a asibitin.

Majinyata na zuwa da fankokinasu Asibitin Aminu Kano

Wani mara lafiya a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano da ya bayyana sunansa a matsayin Malam Umar, ya ce, “Marasa lafiya na amfani fankokinsu masu daukar caji a sibitin, saboda zafi, idan aka dauke wuta.

“Babu wutar sola, shi ya sa aka dauki lokaci idan aka dauke wuta kafina  dawo da ita ko a kunna janareto.”

Wakilimu ya lura cewa an samar da wutar lantar mai amfani da hasken rana a dakin kula da lafiya na gaggaaw da wadanda suka yi hadari.

Dalilin da muka ninka kudin aiki — Asibitin AKTH

Shugaban Kwamitin Shawarwari na Asibitin, Farfesa Muhammad Abba Suwaid, wanda ya yi magana a madadin shugaban asibitin, Farfesa Abdurrahman Abba Sheshe,  ya ce asibitin na shan man fetur na Naira miliyan 30 zuwa miliyan 100 a kowane wata, amma ba zai iya biyan abin da ya fi kashi 30% na kudin ba, shi ya sa a yanzu haka ake bin su bashi da ya kai naira miliyan 700 na kudin wuta.

“Wannan ya shafi yadda ake kula da majinyata, saboda dole ta sa asibitin kara kucin aiki da kashi 100% domin mu iya biyan kudin, amma hakan ma ya gagar.

“Hukumar gudanarwar asibitin na shirni sanya wuta mai amfani da hasken rana a wurare masu muhimmanci da suka hada da dakunan tiyata da wurin jinya mai tsanani da wasu dakunan majinyata.”

Jinkirin gwaji ya yi ajalin kawuna — Ladi

Wata wadda aka garzaya da kawunta wani asibitin gwamnati ranga-ranga a bara, Ladi Adukwu, ta ce likitoci sun tura su a yi masa hoto ranar Asabar, amma ma’aikatan sashen suka ce a jira sai ranar Litinin da safe za a yi.

Ladi ta ce, washegari, ranar Lahadi da safe kawun nata ya rasu. “Da an yi masa a ranar, wata kila da an gano abin da damun an yi masa magani kafin hakan ta kasance.”

Daga Ojoma Akor (Abuja) Ahmad Datti (Kano) Adebyo Gbenga (Legas), Abubakar Akote (Minna).

Fassara: Sagir Kano Saleh

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: lafiya Tiyata wutar lantarki a rashin wuta

এছাড়াও পড়ুন:

Yadda Ƴan Agbero’ Ke Cin Karensu Ba Babbaka A Abuja

Abdulahi, wanda ke jigilar kaya daga Agbara a Jihar Ogun zuwa Ibadan, ya ce yana kashe har Naira 25,000 a kowace tafiya da yake yi, inda mafi yawan kuɗin ke shiga hannun ƴ an Agbero a Legas, waɗanda ke gudanar da ayyukansu sa’o’i 24 a rana, kwana 7 a mako.

Ya ce daga Berger, gefen Legas, zuwa Agbara, manyan motoci kan gamu da aƙalla tashoshi 15 na ta’annati, inda ake karɓar kuɗi tsakanin Naira 1,000 zuwa Naira 3,000 a kowane wuri.

Manajan Daraktan wani kamfani da ke aiki a cibiyar masana’antu ta Agbara a Jihar Ogun, wanda ya nemi a sakaya sunansa ba, ya shaida wa wannan jarida cewa jigilar kwantena na kayayyakin masarufi daga tashar jiragen ruwa ta Apapa a Legas zuwa Agbara na iya kaiwa har Naira 700,000, sakamakon ayyukan waɗannan ƴ an Agbero da ba su da izinin doka.

Babu shakka, waɗannan kuɗaɗen ana sauke su ne kan masu sayen kayayyakin da kamfanonin masana’antu ke samarwa.

Haka nan, fasinjoji na jayayya cewa nauyin kuɗin da aka ɗora wa direbobi a ƙarshe ana sauke shi ne a kan su ta hanyar ƙarin kuɗin haya.

“Kuɗin haya na tashi kullum, kuma wani ɓangare na matsalar waɗannan kuɗaɗen haramtattu ne,” in ji Chidinma Okafor, wata fasinja da ke zama a Legas.Ga wasu direbobi ma, cin zarafin ya wuce batun kuɗi. “Idan ka ƙi biyan kuɗi, za su fasa gilashin motarka ko kuma su cire madubin gefe,” in ji Sani Mohammed, direban Abuja. “Ya zama kamar muna yi musu aiki ne, ba wai don kanmu ba.”

A Fatakwal kuwa, fasinjoji na cewa rashin tsaro na zama babban ƙalubale. “Tashoshin motoci cunkushe suke kuma waɗannan ƴ an Agbero na tsoratar da fasinjoji ma,” in ji wata ɗaliba, Amara Nwankwo.

Ta ƙara da cewa: “Ba ka da tabbacin ko adadin kuɗin da kake biya shikena, ko kuma ana tilasta maka ka biya ƙarin kuɗi.”

A Legas kuwa, matsalar ta fi tsananta. Wani shugaban ƙungiya a Legas, da ya nemi a sakaya sunansa, ya ƙiyasta cewa ƴ an Agbero suna tara sama da Naira biliyan 100 a duk shekara daga harajin da ba na doka ba da suke ƙaƙaba wa direbobi a Legas.

Masu ruwa da tsaki na cewa waɗannan kuɗaɗe ba sa komawa wajen inganta ababen more rayuwa ko samar da ayyuka.

Masana suna gargaɗi cewa ƙara yawaitar wannan rashin gaskiya na da illa ga tattalin arziki da kuma zamantakewa.

“Ayyukan ƴ an Agbero da ba a sarrafa su ba suna hana zuba jari na doka a fannin sufuri, suna ƙara taɓarɓarewar tsaro a tashoshin motoci, sannan suna ƙara tsadar rayuwa ga talakawan ƴ an Nijeriya,” in ji tsohon ƙaramin ministan harkokin sufuri a wani taron masu ruwa da tsaki, Prince Ademola Adegoroye.

“Gwamnati dole ta matsa zuwa ga tsari na doka da kuma inganta tafiyar da harkokin tashoshin mota idan ana son wannan ɓangare ya bayar da gagarumar gudummawa ga tattalin arzikin ƙasa,” in ji Dr. Feliɗ Echekoba, masanin tattalin arziki daga Jami’ar Nnamdi Azikiwe.

Ƙungiyoyin farar hula ma sun yi kira da a yi gyara. Bisa ga Centre for Justice and Peace, wata ƙungiya mai zaman kanta (NGO), tsarin karɓar haraji ta hanyar da ba ta doka ba na rage amincewar jama’a da hana gaskiya ta bayyana a fili.

“Idan hukumomin gwamnati suka ɗauki nauyin karɓar kuɗaɗen kai tsaye, hakan zai rage satar kuɗaɗe, ya inganta gaskiya da riƙon amana, tare da kare direbobi daga cin zarafi da tsangwama a kullum,” in ji ƙungiyar a cikin wata sanarwa.

Kuma jami’an tsaro sun amince cewa tsarin yana jawo ruɗani. “A lokuta da dama muna kama direbobi saboda laifukan hanya, amma idan ka duba sosai, da yawa daga cikinsu waɗanda ne aka zalunta da haraji na ƙarya ne daga hannun ƴ an Agbero,” wani babban jami’in ƴ ansanda a Legas ya shaida wa wakilinmu cikin sirri.

Ya ce wannan shi ne dalilin da ya sa ake yawan ganin tashin hankali a kan tituna.

Ƙungiyoyin direbobi, duk da sun amince da ƙalubalen, sun dage cewa yin doka da tsari kan harkokin ne ya dace fiye da kawar da ayyukansu baki ɗaya.

“Ina buƙatar kulawa ta musamman daga gwamnati domin a tabbatar da cewa an daidaita haraji kuma ana bayar da rasit. Ta haka ne direbobi za su san ainihin abin da suke biya, kuma fasinjoji ba za su ɗauki nauyin biyan kuɗaɗen da ba su dace ba,” in ji Sunday Ogunleye, wakilin ƙungiya a Ota, Jihar Ogun.

Haka kuma, talakawa ma suna bada ra’ayinsu. “Ya kamata gwamnati ta ƙirƙiro tsarin tikitin zamani irin na e-payment a tashoshin motoci, kamar yadda ake da shi a BRT na Legas. Idan aka yi haka, direbobi da fasinjoji za su samu cikakken bayani, kuma babu wanda zai iya karkatar da kuɗi ba bisa ƙa’ida ba,” in ji Maryam Dennis, ma’aikaciyar gwamnati a Fatakwal.

Yayin da al’amarin ke ƙara ta’azzara, ƴ an Nijeriya da dama suna kira ga gwamnati ta tarayya da ta jihohi su ɗauki mataki ta hanyar samar da manufofi bayyanannu, tsarin tikitin zamani, da kuma tsauraran matakai kan karɓar kuɗaɗen haram.

A halin yanzu, direbobi da fasinjoji suna cewa wannan harajin na tilas ya zama abin da suke fuskanta kullum, wanda ke ci gaba da raunana rayuwarsu tare da tsananta matsalar tsadar rayuwa a faɗin ƙasar.

Abuja

Ko’ina ka juya, musamman a tashoshin motoci da aka fi sani a tsakiyar birni da unguwannin FCT, sawa’un direba ne kai ko fasinja, ɗaya daga cikin abubuwan da ake yawan gani shi ne ƴ an Daba, da aka fi sani da ‘Agbero’. Suna tsangwamar masu motoci da suke amfani da hanyoyi, suna karɓar kuɗaɗe Agberon-Agberon ba tare da wani tsari daga hukumomin gwamnati ba.

Ko a Gadar Mabushi, Gadar Baneɗ, shatale-talen Berger, Jabi, Gadar Area 1, Area 3 Junction ko Gwarinpa, yanayin iri ɗaya ne, yayin da ƴ an Agbero ke ci gaba cin karensu ba babbaka. A ƙasar da ke fama da laifuka da matsalolin tsaro irin su sace-sace, ƴ an bindiga, da ta’addanci, yawancin mazauna FCT suna ƙara fuskantar tashin hankali game da tsaron jama’a.

Alal misali, wani mai motar da ke ƙoƙarin ɗaukar abokin aikinsa ko ɗan uwansa a kan hanyarsa ta zuwa aiki ko dawowa daga aiki, yana cikin tsoro na tsangwamar ƴ an ‘Agbero’, waɗanda ke neman “bayanan motoci” ko wasu kuɗaɗen haram kafin a ba shi damar ɗaukar wanda yake so.

Duk abubuwan da suke yi ya saɓa doka, kuma hakan na iya haifar da barazanar da za ta bayu izuwa fashewar tayoyi ko kama mutum ba bisa ƙa’ida ba zuwa “ofishinsu.” Har ma ƴ an Agbero suna da gadarar bincikar direbobi su basu wasu takardu mallakinsu, tikitin biyan kuɗin haraji ko katin shaida kafin su yi tuƙi a kan titunan FCT.

Hatta masu motocin da ba na haya ba na ƙashin kansu ko ma’aikatan gwamnati da ke ƙoƙarin samun na cefane idan za su ɗauki fasinjoji don taimakawa kansu sayen mai ba a barsu a baya ba, saboda ƴ an Agbero na takura musu, suna neman a biya su wasu kuɗaɗe; in ba haka ba, direbobi da motocinsu ba za su bar su su wuce lafiya ba.

Abin lura a nan shi ne, yawancin mazauna na zargin wasu jami’an ƴ ansanda masu karɓar cin hanci da haɗa kai da ƴ an Agbero wajen tsangwamar direbobi yayin da suke aiki ba tare da la’akari da wanda abin ya shafa ba. Ba a cika kama su ba, yayin da duk wani Agbero da aka kama a cikin lokaci kaɗan ƴ ansanda ke sakin sa, wanda hakan ke ƙara ƙarfin gwiwar ayyukansu na miyagun laifuka.

Mummunan Al’amarin da ya afku a Mabushi

Kimanin ƙarfe 1:30 na ranar wata Laraba, 3 ga Satumba, wani mummunan lamari da ya shafi wani iyali ya faru ƙarƙashin gadar Mabushi a Abuja. Wani mutum, mai suna Emeka Ehekweme, tare da matarsa, yana tuƙa wata Toyota Highlander mai launin toka, mai lambar rajista ABJ 206 EC, lokacin da ƴ an Agbero uku da ba a tantance ba suka firgita su da wasu mutane.

Ana zargin cewa ƴ an Agberoran sun tilasta lallai sai sun shiga gaban motarsa, inda ɗaya daga cikinsu ya yi ƙoƙarin kama sitiyarin motar. Sakamakon haka, kan motar ya ƙwace motar ta tafi ta buge wata Mazda da aka ajiye a gefen hanya, ta sake dukan ginin gada sannan ta faɗa rami, hakan ya faru a kan babbar titin Nnamdi Azikiwe.

A cewar mai magana da yawun ƴ ansanda ta FCT, Josephine Adeh, lamarin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama yayin da direban Highlander, matarsa da wasu biyu daga cikin masu kai farmaki suka rasu a Asibitin ƙasa, yayin da wani wanda ake zargi na uku ke karɓar magani a halin yanzu. Direban Mazda ɗin Suleiman Mohammed, bai ji rauni mai haɗari ga rayuwa ba.

Sakamakon haka, mazauna wurin da suka fusata sun bi ƴ an Agberoran uku, suka kashe su nan take tsaye sannan suka ƙone su. Ana zargin cewa ƴ an Agberoran na daga cikin Abuja Municipal Area Council (AMAC) ne.

Lamarin ya jawo damuwa a bainar jama’a kan ayyukan ƴ an Agbero a Abuja, inda yawancin mazauna ke kiran gwamnati da ta ɗauki mataki na gaggawa don dakile tsangwama a tituna da kuma tsaurara dokokin hanya.

Koke

A yayin da take magana da wakilinmu, wata ma’aikaciyar gwamnati, Ruth Ayodele, ta ce ƴ an Agbero sun mamaye FCT kuma hukumomi ne ya kamata su ɗauki mataki a kansu. Ta yi ƙorafi cewa jami’ai ba sa aikinsu kamar yadda ya kamat.

Ta ce: “Idan aka duba abin da ya faru kwanan nan a Mabushi, inda wasu ma’aurata da wasu Agbero biyu suka rasa rayukansu, abin mamaki ne cewa har yanzu ba a bayar da sanarwar hukuma ta haramta ayyukansu a FCT ba.

“A ƙasa mai aiki haka, irin wannan lamari zai sa a ɗauki mataki cikin gaggawa. Alal misali, Jihar Anambra ta riga ta haramta ayyukan Agbero saboda yadda suke gudanar da ayyukan da suka saɓa wa al’umma.

Gwamnati ta basu damar samun ayyukan yi, matuƙar sun yi rajista da hukumomin ƙananan garuruwa. A bi hanya madaidaciya domin magance matsalar a maimakon a zuba musu ido. Wannan lamari abin takaici ne sosai.”

“Ƴan Agbero suna ko’ina, suna addabar masu motoci. Yanayin na ƙara fitowa daga iko kuma yana buƙatar kulawar gaggawa daga hukumomi domin kauce wa ƙarin asarar rayuka da dukiya, kamar abin da ya faru a Mabushi,” in ji wata ma’aikaciyar gwamnati.

Haka kuma, wani likita, Jacob Nnaemeka, ya ce sau da dama ƴ an Agbero suna tsangwamarsa yayin da yake ɗaukar ko sauke da abokan aikinsa, inda ya buƙaci hukumomin da abin ya shafa su dubi lamarin.

Ya ce: “Kowa ya san cewa ƴ an Agbero na tsangwamar fasinjoji a FCT. Ni ma na ta zama wanda abin ya shafa a lokuta da dama. A wata rana ta musamman, ina son ɗaukar abokin aikina a Area 1. Kafin na yi wata-wata, ƴ an Agbero sun shiga motata sun fara ƙoƙarin cire min makulli. Na tambaye su menene matsalar, sai suka ce ina ɗauka da ajiye da fasinjoji; kuma dole sai na biya su.”

“Bayan na nuna musu katin shaidar PCRC na, sai suka bar ni in tafi tare da neman afuwa. Amma duk haka sai da basu Naira 1,000. Tun daga wannan lokaci, na yi matuƙar taka tsantsan kuma sau da yawa ba na ɗauka ko ajiye abokan aiki, maƙwabta ko ƴ an uwa.

“A kwanakin nan, idan na yanke zan ɗauku abokin aikina sai na yi nisan daga tashar su sannan na tsaya, saboda ko’ina suna nan. Suna da ɗaurin gindi, don haka ne suke nuna halayyar rashin tarbiya.”

Nnaemeka ya ci gaba da cewa: “Ko da ka yi tunanin taimaka wa wani don ka ɗauke shi kyuata ba za ka iya ba saboda tsoron ƴ an Agbero. Yanayin ya wuce gona da iri. Haƙiƙa gaskiya ne cewa wasu jami’an ƴ ansanda na aiki tare da su; in ba haka ba, ba za su yi ƙarfin hali su  riƙa takura wa mutane ko’ina a FCT ba.”

“Abin da ya faru a Mabushi bai hana su aiki ba, domin har yanzu suna gudanar da ayyukansu a sassa Agberon-Agberon na birni. Lallai abin takaici ne a FCT; hukumomi dole ne su duba wannan lamari.”

“Suna da iyayen gida”

A yayin da yake magana da Blueprint Weekend, Shugaban Police Reform Secretariat, Farfesa Olu Ogunsakin, ya ce shi ma sau da yawa ƴ an Agbero sun farmake shi a FCT. A cewarsa, suna da masu goya musu baya kuma jami’an ƴ ansanda sun san wannan matsala.

Ya ce: “Zan iya ba ku dalilai da dama kan wannan, amma abu ɗaya da ya kamata ku fahimta shi ne na yi aiki a fannin ƴ ansanda na tsawon shekaru da dama. Ni ba jami’in ƴ ansanda bane, don haka ba zan yi magana kan ayyukansu na gudanarwa ba.

Amma a matsayina na mai gudanarwa, wannan wani abu ne da zan iya gaya muku wanda ba sirri ba ne a gare su.

“Suna sane da wannan, kuma ba zan faɗa muku ko suna aiki a kai ko a’a ba, amma ina tabbatar muku cewa su ne ke da alhakin tsaron FCT kamar yadda suke da alhakin tsaro a ko’ina.”

Ya ƙara da cewa: “Idan kuka tambaye ni ra’ayi na na kaina a matsayin ɗan ƙasa, zan ce dole ne mu duba tsarin da ke cikin FCT. Wannan saboda lokaci-lokaci, ina tuƙa Hiluɗ ko I-Luɗury kamar yadda suke kiransa, kuma ina fuskantar farmaki daga mutane da dama. Suna tambayar bayanai, haƙiƙa, akwai yawan hukumomi Agberon-Agberon, da kayan aiki Agberon-Agberon, waɗanda wataƙila suna da masu goyon baya a wani wuri.”

“Al’amari game da tsaron jama’a abu ne mai matuƙar rikitarwa, musamman ganin abin da na fuskanta. Ba abu ɗaya ne zai iya bayyana ba. Akwai dubban dalilai da za su iya amsa wannan tambaya. Amma a kaina, ina da tabbacin suna aiki a kai.

“Amma ɓangaren gyaran tsari game da haƙƙin mutane, lallai a wannan fannin akwai wasu ƴ an ƙasa na musamman. Ra’ayina shi ne cewa ƴ ansanda dole ne su kasance suna ɗaukar mataki. Muna da kwamishinan FCT, muna da DCP mai kula da ayyuka, kuma muna da sashen gudanarwa, doka za ta iya ɗaukar mataki kan kowa. Idan ka yi magana da ƴ ansanda yanzu cewa za su yi akwai wani aiki na musamman da ake yi wanda ba za su iya tattauna shi ba.”

Hukumar Ƴansanda ta FCT na Kaucewa ba da Bayanai

Duk ƙoƙarin da aka yi don samun martanin Hukumar Ƴansanda ta FCT kan matsalar ƴ an Agbero a FCT ya ci tura, yayin da PRO, Josephine Adeh, ta ƙi amsa tambayoyin da ke neman ra’ayin ƴ ansanda a kai.

Bayan karanta saƙonni da dama da wakilinmu ya aika mata a ranar Talata da safe ta WhatsApp ɗinta da aka sani game da batun, ba ta amsa ba, ko da lokacin da wakilin ya kira ta lokaci-lokaci, ta ƙi amsa kiran, kuma har lokacin rubuta wannan rahoto ba ta ce komai ba.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kasashen Afirka Uku Sun Sanar Da Ficewa DagaKotun Hukunta Manyan Laifuka Ta Duniya
  • DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Cin Kifi Yadda Ya Kamata
  • Gavi Zai Yi Jinyar Watanni 5 Bayan Yi Masa Tiyata
  • UNGA: Shettima Ya Tallata Damar Zuba Jari Na Dala Biliyan 200 A Fannin Makamashi A Nijeriya
  • Hindi: Amurka Da Kasashen Yamma Ba Sa Son A Dakatar Da Bude Wuta A Gaza.
  • Ballon d’Or: Wa zai lashe kyautar 2025?
  • Ballon d’Or: ’Yan wasa 5 da ke iya lashe kyautar 2025 
  • Lokaci Yayi Da Shugabannin Arewa Za Su Kawo Ƙarshen Matsalar Tsaro A Yankin –  ACI
  • Hatsarin mota ya yi ajalin mutum 4, 16 sun jikkata a Yobe
  • Yadda Ƴan Agbero’ Ke Cin Karensu Ba Babbaka A Abuja